← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 97

Sashe 91

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai maganar akhnan ta yiwa mammina dadi,kamar ta shiga rai da zuciyarta taga kalar tambayar dake kai kawo a ranta,amma kuma tana takatsantsan da fitar tambayar daga ranta. Irin kallon da sultane ya ajewa akhnan ya tabbatarwa mammina inda ta yarda tambayar ta fita daga gareta ne data gama tozarta,gefe guda kuma zuciyarta ta cika fal da fargaba,kada sanadin wannan maganar tata ya kawo cikas gurin samun sauqin cikar muradinsu. Cikin wannan salon nata data saba amfani dashi tayi kiran sunan akhnan.

"Biftu......kul dinki da jayayya ko qalubalantar hukuncin sultane,akwai wani abu da sultane zai yanke hukunci akai ace bai tabbata ba?". Wani murmushin ne daga qasan zuciyarsa da ba alamarsa saman fuska ko labbansa ya subuce masa,akwai wani boyyen sauti cikin lafuzzan matar,akwai boyayyen yanayi da ke bayyana wani abu da aketa qoqarin turashi nesa da zuciya nesa da mafitar magana saboda wani babban dalili na cimma quduri.

"Wacece wannan?" Muryar omari ta ratsa kunnensa ta Bluetooth din kunnensa,cikin hikima ya dora yatsansa kan Bluetooth din daya saje da shape din kunnensa bata yadda zaka gani yadan latsashi,wanda daga wancan bangaren ya bawa omari sign na ya dakata kawai,sai ya gyada kansa a hankali yana sake matso da na'urar gabansa.

"Da zaki qyaleta zaituna.....wataqila ta kawo wani abun da yafi nawa dacewa da muhimmanci..." Ya furta muryarsa na nuna alamun bacin rai,da kuma fara tunzura da yake dab dayi.

Ta karanci wannan,bataso kuma komai ya kwabe,batason wannan raunin nasa da take qoqarin tayarwa ya koma ya kwanta,don haka ta miqa hannu ta matsa hannun akhnan data motsa da zummar yin magana,abinda ya faru cikin idanun haisam daya dan budesu cikin kallon qasan idanu da idan yana yinsa zaka tsammaci bacci yake.

"Me yasa ta hanata ci gaba da magana?" Ya ajewa ranshi tambayar yana qoqarin janye idanunsa kan hannuwan nasu gudun wucewa iyakar kallon shari'a,saidai kuma kamar an fusgi kallon nasa sai ganinsa ya sauka kan tsintsiyar hannun mammina din.

"Kayi mana afuwa.....kayi mana aikin gafara.....kada wannan abun ya zama silar kasa yi mata alfarma cikin alfarmar nan taka,cikin tausayin nan naka da jin qanka,don Allah.........muna fata ayi mana gafara" Ta fadi tana sadda kanta tare da sake matsa hannun akhnan a karo na biyu,kalaman da suka sauka kunnuwan haisam tare da dogon nazarin banguls din dake zagaye da tsintsiyar hannun mammina.

Idanunsa ya janye a hankali cikin yanayin da ba zaka fahimta ba,daidai sanda ake sallama daga daga bakin qofar falon kuma aka daga labulen farko ana neman izini.

Sautin muryar ya sake jan hankalinsa saboda jin wani sabon accent din kamar a yankin Ethiopia yake ba agadez ba. Kakkaurar muryar data masa kama sak da muryar mutumin da yaji a dazu.

"Kana iya qarasowa" Maimartaba ya furta yana saisaita muryarsa.

Cikin second daya ya bayyana cikin parlor,da shigar kayan sarki na yankin agadez......amma ba abinda haisam yake gani saman fuskarsa sai qasar Ethiopia a kalamansa,wanda sun bace bat daga kamanninsa babu ko qwara daya.

A hankali ya aza hankalinsa a yanayin tafiyarsa,yana takawa ne da qwarin gwiwar da zata gaya maka wani ne a wajen sultane......da yanayin da zai gaya maka yana da girman matsayi da isa a gurinsa,sannna ya qaraso gabansa ya zube da yanayin da ya tunawa haisam ZAMAN GABAN SARAKUNAN QASAR ETHIOPIA.

Wani irin zama ne da aka gaji yanayinsa daga manyan da tsofaffin qasar,yanayin zaman dake nuna zallar sadaukarwa......zallar bada kai.....zallar amanna da kuma biyayya.

Idan har idanunsa sun nuna masa daidai,sai daya saci kallon akhnan kafin yakai hankalinsa ga sultane dake fadin.

"Tamim sarkin aiki.......tamim gandun hidima" Wani kirari da yake bala'in farantawa tamim din rai,yana kuma sake bashi tabbacin cewa da gaske yakai wani qololuwar matsayi wajen sultane din.

"Allah ya baka kyakkyawan qarshe,ya kula da dukka sha'aninka.....an kammala komai" Ya fada da tsantsar ladabin da ko idanunsa baya iya dagawa ya kalli sultane.

"Amma tamim.......baka fahimtar muhimman lokuta da bai kamata ka dinga tsoma kanka a ciki ba?" Mammina ta furta da wata irin izza da qasaitar data hau kanta yanzu yanzu tana qure tamim din da wani irin kallo,gabanta kuma yana tsananta faduwa,wani irin bahaguwar bugun zuciya daga sanda tamim din ya bayyana,wanda batasan meye dalilinsa ba,amma tunda har hakan ta kasance take jin yaqini a zuciyarta AKWAI WANI ABU DA BA DAIDAI BA.

"Tamim yana da matuqar qoqari zaituna,yana kuma da amanar da idan aka bashi aiki saiya tabbatar da gamsuwar wanda ya bashi aikin......ba laifi bane don yayi hakan......kaje tamim....zamu ganka in sha Allah"

"Godiya nake Allah ya baka yawan rai.....ubangiji ya firgita maqiyanka". Ya fadi yana yunqurawa da zummar miqewa,daidai lokacin idanunsa ya sauka kan haisam,wanda har yanzu ga duk me idanun kallo idan ya dubeshi zaiga hankalinsa kacokam yana a kan wayarsa ne.

Wani irin abu me qarfi yaji ya fusgeshi,zubawa haisam din idanu na wasu sakanni kafin ya janye dubansa a hankali yana takawa gami da ficewa daga shiyyar.

"Inajin wannan maganar tazo qarshe......ni muhammad hammud na bayar da akhnan ga hakeem,watanni biyu kacal na bawa kowane bangare su gama shirinsu". Wani abu taji ya dunqule mata saman qirjinta,kamar yana shirin hanata shaqa da kuma fidda numfashi.

*_BAYAN WASU SA'O'I_*

Cikin qasaitaccen takunsa ya isa ga sassansa,wanda yana dab da dora hannunsa saman handle aka bude masa qofan.

Abdii ne tsaye,yana dubansa da murmushi kan fuskarsa.

"Welcomw captain obbo" Ya fadi da yanayin daya gayawa haisam a tsaye yaron hake tun dazu yana jiran dawowarsa.

Da idanu kawai ya amsa masa,ya saka kai yana wucewa ciki abdii din ya take masa baya. Akwai maganganu da yawa a bakinsa da tambayoyi,amma yanayin obbo din ya nuna masa kaman akwai wata lafiyayyar gajiya a jikinsa. Mamaki kadan ya kamashi,mutumin da ya amsa gayyatan cin abinci,meye ya hadashi da gajiya kuma?.

"Sai da safe zamuyi magana......i'm not cool now......karka sakani magana da yawa.....,ka kira salawi ka gaya masa yazo ya daukeni,qarfe sha daya na safe,kada ya wuce hakan." Ya qarasa fadin maganan yana tattakawa yan wucewa zuwa stairs din ba tare daya tsaya ba.

Baki abdii ya saki kawai,shi yasa shifa yazo obbo ya barshi ya masa rakiya can cikin gidan,don ga ganewa kansa komai da komai. Saboda yasan halin 'yan miskilancin obbo din nasa, taba zama ya bashi labarin komai yadda yakeso ba,gashinan ma ko zama ya masa kyakkyawan kallo baiyi ba ya wuce sama abinsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Har ya juya,sai kuma ya laluba wayarsa dake aljihunsa da sauri. Sai yanzu ya tuna saqon da Menelik ta bashi ya isar dashi ga obbo din,sam ya manta,kuma a girmansa da mutuncinsa da take gani bai kamata ace bai isar da saqon a daren ba kamar yadda ya mata alqawari,don haka ya soma haurawa saman shima cike da tantama da d'ari d'arin kada haisam din yayi rejecting dinsa.

Bawai gangar jikinsa bace ta gaji,a'ah,kwanyarsa dake cakude da tunani da hasashe iri daban daban ce ta saukar da gajiya ga kowacce gabarsa. Akwai abubuwa da yawa daya gani,wasu yayi hasashensu,wasu kuma jikinsa ya bashi. Cikin kowanne jini dake harbawa zuciyarsa yana sake samun tabbaci da yaqinin samuwar nasara.......yana ganin wani haske me girma kaman ya wulga cikin aikinsa,sai yakejin tamkar wata tafiya ce sukayi kuma sukazo bakin gaba.

Bai shirya yin bacci da wuri ba,yana buqatar raba dare ya kammala dukka wani hasashe na kuma next plan dinsa as document kamar yadda ya saba cikin kowanne aiki,cikin kuma kowanne motsi. Yasa hannu ya zame amama din kanshi,take lallausan gashinsa me sulbi ya warware saman kanshi. Hannu yasa yana balle button din rigarsa,so yake ya zareta ya watsa ruwa me dumi da zai wartsakeshi daga duk yanayin da yakeji,sannan ya hada da zazzafan coffee dinnan daya zama jinin jikin duk wani d'a na asalin qasar Ethiopia.

Yana balle button din hannunsa yaji an knocking qofar,da gajiyayyun idanunsa ya watsawa qofar kallo,bai kuma tsaya tambaya ba kawai ya taka ya murza lock ya budeta sannan ya jawota baya yana duban bakin qofar.

Suna hada idanu da abdii din ya aza hannunsa saman tashi sumar yana shafata gami da fara sunne kai.

"Dhiifama obbo". Da idanun nan nasa kadai ya tambayeshi dalilin knocking din,sai kawai ya fidda hannunsa a aljihunsa ya miqa masa wata fara qal din envelope.

Duban takaddan yayi kafin ya maida duban nasa ga abdii,still da idanu ya sake tambaya ba tare da yayi magana ba.

Har qashinsa yakejin girman kallo haisam irin wannan,da wannan body language din nasa me dafa mutum gwara ya buda husky voice dinsa ya maka magana.

"Menelik ce obbo......don Allah karkayimin fada,alfarma tace nayi mata" Yayi maganan idanunsa suna nuna da gaske bayason ya masa fadan. Shuru yayi kaman bazaice komai ba,sai ya miqa masa hannunsa. Amamakance abdii yabi tattausan tafin hannun nasa da kallo sai kuma yayi saurin aza masa takardar ya juya yana boye dariyar farincikinsa.

Da qafa ya maida qofar ya rufe,ya juya takardar sau biyu a hannunsa,sai ya qarasa ya jawo drawer ya zurata ya maida ya rufe. Sai da yayi hakanne ma ya tuna wancan saqon nata ma ko budashi baiyi ba. Idanunsa yadan lumshe yana budesu gami da kama jubah din nasa ya zare,lallausar vest dinsa fara qal ta bayyana,wadda ta tsumu da wannan qasaitaccen unique scents din nasa.

Inda menelik zata fahimta......ba ita kadai bama,da sun samawa kansu sassauci. Bayason kowacce mace ta tsinci kanta a wahala ta sanadinsa. Baisan me zaiyi musu da zasu fahimci yana da sauran abubuwa da yawa a rayuwarsa.......ayyukansa masu muhimmanci da yinsu da kuma kammalasu yake jinsa ya zame masa tamkar Ibada,eh dole ne......don kubutar da rayuwar MOTII daga hatsari da barazanar da yake ciki tsahon shekaru ashirin da suka shude.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*
Chapter 91 · 0% Book details