Sashe 25
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*H U G U M A*
PAGE 19
Sanye yake da Moroccon jallabiyya ta maza,wadda ta sa haskashi sosai tayi masa wani irin kyau tana kuma sake haska fatarshi dake da wani irin launi,shi baiyi haske me yawan da zai kashe maka idanu ba,hakanan baiyi duhun fata ba,don kusan launin fatarsa yadan saba kadan data ainihin 'yan qabilae oromo.
Lallausar baqar sumarsa me santsi irin ta 'yan qabilar oromo din sai wani sheqi takeyi da walainiya,sumar da ta take kwance saman kansa zuwa gefe da gefen fuskarsa da kuma habarsa. Kansa wata qaramar hula ce irin ta larabawan morocco,wanda hakan bai hana bayyanuwar baqar sumar tasa ba data yiwa fuskarsa wani irin ado.
Shi daya ne cikin dakin,wanda kai tsaye ya amsa sunan library me wani irin tsari me daukan hankali da gasken gaske. Wani irin ma'ajiyar litattafai ne kewaye da ita,dauke da tarin litattafan da suka wuce ka iya qididdige yawansu,domin kuwa kowanne bango sune......bangon kuma tun daga samanshi har qasanshi. Akwai litattafan dake rubuce da yare kala kala......tun daga kan English......french.....oromo.......yayin da litattafan addini na larabci suka mamaye kaso mafi girma na library din.
Komai na library din ya bada wani irin yanayi da nature me kwantar da hankali da daukan hankali,gurine da yafi kowanne guri sama masa nutsuwa a duniya.........baya ji a jikinsa akwai wani abu daya mallaka da yakai wannan library din muhimmanci a wajensa.
Yana iya rayuwarsa shi kadai a wajen.......zai iya qarar maka da awanninsa na rana duka a wajen ya kebance kansa. Karatun addini ruhinsa ne......fatarsa ne.....kuma rayuwarsa ne,ya kuma sameshi,don babu wani abu da yake sanyashi nishadi kamar lokaci irin wannan. Lokacin da zai kebanta cikin yanayi na shuru da wata irin kyakkyawar nutsuwa cikin dakin karatun,yana yin bincike da zaqulo mas'aloli masu yawa daga mazhabobi da malamai iri daban daban.
Ya tsara wajen daidai da yadda zai dace da tsarinsa da kuma yanayinsa da abinda yafiso. Wasu irin kujeru da lausasan carpet aka yiwa gurin ado dasu,sai wani sashe na daban na library din da aka sake zuba wasu rukunin kujerun da kuma teburansa,yadda zai dace da zaman me bincike.
Daga gaban kadan dan qwarya qwaryan table ne me dauke da wasu qananun cabinet,wanda ba komai a ciki sai nau'in coffee kala kala.....coffee makers har biyu da wasu irin mugs da trays masu daukan hankali.
Yankin jimma dama qabilar oromo gaba daya coffee yana daya daga cikin manyan al'adunsu.......sukan ware babban fili me girman Hector me yawa suyi noman coffee zallah. Su kullum ranar shan coffee ce a wajensu bayan rana ta musamman da suka ware mata,ba abinda yake da muhimmanci a gurinsu irin coffee. Wannan jinin da wannan al'adar ta gudana a jikinsa sosai,don ko cikin masu son shan coffee din shi na daban ne.
Sake miqe dogayen qafafunsa yayi saman ottoman sofa dake gabansa yana fidda wani sassanyan numfashi. Sosai yake jin dadin zaman nasa a nan safiyar lahadin,duk da rabin hankalinsa yana kan wata 'yar qaramar danja dake gefansa.
Green light da yayi blinking shi ya sakashi daga kansa a hankali,lumsassun idanun nan nasa suna sake rusunawa da wata irin nutsuwa yana duban light din don tabbatar da motsawar da yayi. Ya sake bada green color kuwa......don haka ya sauke qafafunsa a hankali yana rufe littafin bayan ya sanya alama,ya miqe da cikakkiyar nutsuwarsa yana zare hular kansa ya ajiyeta saman ottoman din,sannan ya dauki wani irin nau'in Bluetooth ya latsashi ya sakashi a kunnensa yana nufar wata bookshelf data banbamta da nau'in da yanayin kowacce daya dake wajen,labbansa masu sulbi dake da wani irin color suka motsa a hankali suna bada sautin husky voice dinsa da ta rage boldness yana fadin.
"Assalamu alaikum warahmatullah" Daidai sanda ya latsa wani abu jikin bookshelf din take ya juya kansa ya canza siffa daga bookshelf zuwa qofa,sai ya murza handle din ya shiga sannan ya maidata yadda take bookshelf a dazu.
"Wa'alaikumussalam.........mun tashi lafiya haisam?". Babban mutumin da muryarsa kadai ta bayyana nutsuwarsa da dattijankarsa ta bayyana sosai ya fada.
"Alhamdulillah babbo". Ya amsa yana kunna switch na dakin,take haske ya mamaye ko ina.
Wani lafiyayyen daki ne da tun daga gininsa zaka tabbatar ya samu ingantaccen tsari da wannan irin sirri na musamman,don hatta da windows din dakin suna da wani irin yanayi ne,ba normal winduna na yau da kullum bane. Cike yake da tarkacen kayan wuta iri daban daban......wayoyi tsayayyu alluna na zane.......da sauran wasu abubuwan da ko sunansu ba lallai ka sani ba. Saidai duk da wannan kayan komai yana ajjiye a muhallinsa a kuma tsare,don a kallon farko ma abinda zai fara zuwa kanka shine wani office ne na musamman dake koyar da harkar na'ura me qwaqwalwa.
"Nayita qoqarin samunka a jiya......sai omari na barwa saqo.......ka duba email naka yanzu yanzu".
"Okay bobbo". Ya amsa masa a girmame yana danne makunnin Bluetooth din nasa sannan ya isa a hankali gaban wata qaramar system yaja kujerar dake gabanta ya zauna.
Waving hannunsa kawai yayi a fuskarta ta kunna kanta da kanta,ya matsa gaba sosai ya fara sarrafata. Wasu irin tarin password ya saka mata kafin ya budeta,password din da zakayi mamakin yadda akayi suka zauna daram cikin kwanyarsa.
Wata irin nutsuwa ya bawa na'urar yana bin kowanne saqo daya bayan daya da idanu da kuma hankalinsa,nutsuwar da zata gaya maka muhimmancin aikinsa a wajensa da yadda komai na aikinsa yayi masa ya dace da tsarinsa da muradinsa. Hasken screen din ya sake haska fararen idanunsa da suke juyawa a hankali cikin screen din,har zuwa sanda ya kammala duba saqon. Bayansa ya jinginar jikin kujerar yana yin relaxing sosai,still bai dauke fararen idanunsa daha kan allon computer din ba. Yatuntsa guda uku cikin sumar dake kwance saman habarsa yana dan yamutsasu a hankali.
Paragraph din qarshe na saqon da bobbo ya rubauta masa da kalmar turanci ya motsa labbansa a hankali ya karanta *_operation into AGADEZ_*
Ya kafe kalmomin da idanu yana maido tunaninsa baya. Duk tsahon wadannan lokutan?,duka tsahon shekarun?,me yasa tunaninsu da bincikensu baikai can ba sai yanzu?.
Idan zai iya tunawa shine ya fara kawo wannan idea na baza komarsu zuwa ga qasashen dake cikin fadin africa gaba daya. Bai manta osama yana daya daga cikin mutanen da sukayi Challenging nasa a lokacin......saboda dalilai na ganin cewa duka duka yaushe ya shigo hukumar tsaro ta sirri?......bai wuce watanni da fara aiki dasu ba amma ya samu nasarar shigowa babban team irin nasu na goggaggun ma'aikatan sirri.......ya tsinci kuma case din kisan gillar Abban ajani Ahmed......duk da akwai abota me qarfi da girma tsakaninsa da mahaifinsa me martaba abba jifar,amma osama yana ganin wannan daban da wannan. Ya raina tunaninsa a wancan lokacin,yana kallonsa a wanda baisan komai ba akan aikin........taka haye ne shi. Ran osama yayi fari qal a sanda aka soma fadada binciken zuwa wasu qasashen Africa din.......kuma basu samo komai a kai ba.......sai matsala ma da yaso jawowa ta alaqar diplomacy tsakanin Ethiopia din da maqwabtanta.
Daga qarshe bobbo yace a haqura a ajjiye binciken......aci gaba da taba case din lokaci bayan lokaci. Yana da wani abu guda daya a rayuwarsa daya zame masa silar nasararsa.........JAJIRCEWA DA TSAIWA akan dukkan abinda yasa a gaba,ya kuma samu gamsuwa cewa eh zaiyi. Baya tunkarar komai da ka,sai ya gabatar da ISTIKHARA irin wadda ma'aiki ya koyar da sahabbansa......sannan ya dora da addu'o'i. Wasu lokutan harda azumi,muddin ya gama wadannan ya samu nutsuwa da gamsuwa akan komai.....to ko meye wannan abun,komai girman hatsarinsa baya jin fargaba ko digo akai,domin yasan Allah ya bawa zabi......kuma ya gama zabar masa koma meye..........so bashi da wani sauran haufi tsoro shayi ko shakka.
Tun daga wancan shekarun bai qara bari zuciyarsa da jikinsa sun huta ba akan case din ajani Ahmed.......musamman daya zama aboki sosai ga mooti abba jifar........wannan sai yake sake motsa zuciyarsa a duk sanda hira ta hadashi da me martaba zancan ajani Ahmed ya fado ciki.
Komai yayi farko yana da qarshe.......kamar yadda akace komai nisan jifa qasa zai fado......komai girman gona kuma akwai kunyar qarshe.........cikin watan daya wuce yana tsaka da bincikensa game da wanda dukkan hukumarsu ke qarfafa zato a kansa.
Ya samu wani irin haske daya sanyashi jimawa yana duba bayanan gami da hadesu da wasu bayanai dake ajiye a kwanyarsa. Ya ajiye bayanan yana musu kyakkyawar ajiya......sannan ya miqe ya daura alwala yayi sallah,a sujjadar qarshe kuma ya jima yana ganawa da ubangijinsa ta hanyar karanta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin. A wunin ranar duka ya lazumci istigfari da ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis.
Aiki ne me hadarin gaske daya tabbatar samuwar nasararsa wata samuwar nasara ce me zaman kanta ga gwamnatin Ethiopia. Mutuwar abba ajani Ahmed ta kusan zamewa gwamnatin Ethiopia gaba daya barazana......kasancewar abba ajani Ahmed mahaifinsa dan asalin qasar America ne......kuma shi kansa acan aka haifeshi,don haka halalin qasar ne.......kasuwanci ya dawo da mahaifansa qasar Ethiopia shekaru masu yawan gaske a baya,har suka rasu suka barshi da tarin nashi iyalin har zuwa sanda ajalinsa ya riskeshi shima. Bashi da kokwanto akan bobbo game da case din......amma addu'ar da yayin ta sake saka masa nutsuwar bobbo ya sani.
Ya jima shuru yana duban haisam bayan gabatar masa da dukkan bayanan. Ya rasa me zaya fada a kanshi?. Tabbas yana ji a ransa irin haisam din duk bayan qarni guda ake haifar mutum daya irinsa. Jajirtacce dan kishin qasarsa al'ummarsa dama iyayensa. Kafadarsa ya dafa yana jin zuciyarsa tana narkewa.
"Ina sake taya mooti murnar samun d'a kamarka haisam.......kaidin wata kadara ce me tsadar gaske.......ko yau ko kuma a iya nan ka ajjiye aikinka tabbas qasarmu zatayi alfahari dakai".
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 20
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX