← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 97

Sashe 69

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Captain sheikh" Ya fadi yana takowa a nutse. Baice komai ba sai daya shiga ya zauna,ya daga idonsa yana duban Omari. Gira kawai ya dagewa Omari din,a karon farki kuma Omari ya fahimci yau 'yan miskilancinne a kusa.

Maganan da zasuyin me muhimmanci ce,banda hakan zai qyaleshi ne ya tafi,yasan idan 'yan mode din nasa suka sauka zaya nemeshi da kansa.

Screen din system dinsa dake hannunsa ya juya ya nuna masa,sai baice masa komai ba bayan ya kalla ya masa nuni da hannu yana matsawa ciki omari din ya samu gurbin shiga.

Ba wanda yace da kowa komai,omari na qoqarin qarasa saita bayanan da zaiwa haisam din,yayin da haisam din ya maida hankalinsa ga qari'ar dake fita can qasa cikin motar. Sanda Omari ya yunqura zaiyi magana sai ya dauki remote din dake gefansa ya kashe karatun.

"Captain sheikh.......mr Ilaalcha gadi buusuun" Ya fadi yana murmushi ba tare daya kalli haisam din ba.

"No more oromo dialogue here mr man......ka kiyaye" Ya fadi yana maida mode dinsa na senior oga kaman yadda yakeyi wani lokacin.

Murmushi me kama da dariya sosai Omari ya saki,yayi saluting nasa yana cewa.

"Yes sir......but am sorry,Allah saina fadi,mr lowering gaze.......amma komai naka ya zama me daukan hankali.......ta yaya su matan zasu iya kame idanunsa daga kanka?......ka kalli kanka yau kuwa?,kasan Allah?......am very serious,duk yarinyar da tayi falling a kanka saina tayata yaqin samunka?". Ido kawai haisam ya zubawa omari,ganin yadda yake maganar da dukka gaskiyarsa. Sai ya janye idanun ganin Omari shima ya dauke dubansa ya mayar ga system dinsa yana qananun mitoci qasa qasa.

"Haka kawai,rashin adalci ne ka dinga tunanin 'yammata ba zasu soka ba,......suma da laifinsu.......mu su somu su gani mana".

Bai shirya yin dariya ba sam,duk da dama ba al'adarsa bace,amma duk da haka sai da omari yayi sanadin fitar murmushi a fuskarsa,ya kuma kaiwa Omari dind duka,sai shima ya saki dariya yana wani mazewa.

"Allah,da gaske......inajin akwai wani laqanin da kake karantawa a kansu"

"Inda akwai Omari saika riga kowa sani......inda kuma akwai da tuni na dade da baka omari,kaje kayi kaji yadda nakeji......banaso omari,sau da dama yawaitar mata a rayuwa mutum irin haka idan baiyi takatsantsan ba,idan kuma baiyi da gaske ba sharri suke zame masa......amma kaima kaji tsoron Allah,ka manta ma'eesha?.....ka manta khansaa?,ka manta batul......"

"Qyaleni haka" Omari ya fada da sauri yana boye dariyarsa,sai kawai haisam din ya dauke kai yana qyale Omari din kamar yadda ya buqata.

Ba wai shi kadai ba,ba kuma Omari kadai ba,kusan dukkaninsu su bakwai dinnan wani baiwa garesu na musamman. Sun hada wani irin qualities ne da ba kowa Allah yake baiwa shi ba,wannan dalilin ya sanya suka zama masu nuna godiyarsu ga Allah ta hanyar kame kansu da kuma kare mutuncinsu da mutuncin iyayensu dama na addininsu gaba daya.

"Duba nan" Omari ya fada yana jiye system din a tsakiyarsu.

A hankali haisam ke duban bayanan daya fitar masa din yana saurarensa.

"Wadannan guraren,suna daya daga cikin guraren da na samu information gurine na haduwar jama'a masu yawa kuma mabanbanta a qasar nan da garin nan,sannan a nan ne kadai a bincike na za'a iya samun wani da yasan yaren oromo,ko yake yarawa ko kuma ya taba jinsa. Koda taba jinsa yayi zai samar mana haske gurin kusantar samun inda TURAAD ya boye a qasar nan". Shuru haisam yayi yana ci gaba da duban bayanan,kafin a hankali ya janye idanunsa.

"Ka hada dukka bayanan ka turamin ta e-mail,sannna ka turawa abba muhammad dawud.......amma ban gamsu da hakan ba". Ido omari yadan zuba masa. Ya iya magana a dunququne da qananun jimloli,mai hankali yana iya faffasata yayi dogon sharhi a cikinta. Duk abinda ya fadi yana da hujja,kuma akwai dalilin da yasa ya fadi haka.

"Me yasa kace baka gamsu ba?".

" A nan unguwa ko nan garin da muke tabbas akwai yaren oromo" Ya fadi cikin harshen turanci. Idanu Omari ya fidda sanda motar ke gangarawa don tsaiwa a gurin da haisam din yace duka satinnan a nan zasu dinga tsaiwa su jirashi,idan akwai yuwuwar sauya guri cikin satin zai fadi musu.

"Ka bari na dawo......ka jira abeer.......ka gaya masa yau su sauya unguwa,su matso maqotan unguwannin da suke kusa da nan,a yau dinnan basai gobe ba......idan na dawo zamu qarasa magana" Ya qarasa fada yana bude murfin motar gami da sanyo qafafunsa waje bayan ya tabbatar ba gilmawar kowa.

Da kallo Omari da yayi zaune cikin motar yake binsa dashi. Qaramin murmushi ya subuce masa a hankali.
(08187255862 lu'u lu'u)

Komai nasa yana nuna sarautar dake zagayawa a jininsa,tsananin nutsuwarsa da kamun kansa,takunsa kadai yasha banban dana maza da yawa,gashi kuma cikin gidan sarautar wasu. Muddin akwai mutane irinsa cikin gidan,muddin akwai mutane masu kaifin hange da dogon nazari irinsa,to babu abinda zai hana su kasa gasgata zukatansu akan cewa shi din malami ne kawai......malamin da zai koyar da yara kawai a biyashi.

A nutse yake karantar kowanne sauyawar motsi da yanayi na gidan. Yana wuce kowacce qofa....kowanne shinge yana fahimtar kamanceceniyar yanayin jiya dana yau.

"Shalelen sultane.......akhnan yau zata sake baqon da zai zama final choice dinta dana mahaifinta". Maher ya furta qasa qasa wanda yake biye da haisam a nutse. A qofar shiga gidan suka hade da Maher din.

Sarai yaji abinda Maher din yake fada amma kuma baiko waiwayo ba bare ya alamta ya jishin.

Abinda ya faru jiya sai yaji ya dawo masa fes cikin kanshi. Baya ko shakka yarinyar jiya ce,baya kokwanto ita din ce wani mara sanin ciwo da darajar kan zai sake taka qafarshi muhallinta. Tsaki yakeso yaja,amma yana ganin ba wani dalili na yin hakan,matsalar wasu ce.....matsalar cikin gidan.....matsalar mutanen dake zuwa gurinta.

A iya saninshi,babban abu guda daya dake janye hankalin nutsatsen namiji zuwa ga mace shine nutsuwa da kuma tarbiyyarta. Bai ganta a ido ba ballantana yasan nutsuwarta,amma kuma duk inda nutsuwa take tana damfare da tarbiyya.......tarbiyya da bayajin akwai sauran b'urbushinta a gurin.

Har qasan ransa yakejin idan ya fadi hakan baiyi laifi ba,don ba tarbiyya a muhallin da d'iya mace zata iya daga hannunta ta mari d'a namiji.....baligi. Ya jima baiga wani abu da bai shafeshi ba wanda yazo yayi masa tsaye a rai irin wannan ba. Besan dalilin da yasa wannan din ya zame masa karan tsaye ba,ya tsaye masa a rai,ya kasa cireshi.

"Ya isa" Ya tsawatarwa da zuciyarsa cikin don zare abinda bai shafeshi ba daga ransa. Ya dinga takawa a nutse cikin kebantaccen masallacin da zummar bada faralin sallar la'asar kamar kullum,kafin yakai ga qarasawa cikin makarantar.

Ya lura da yadda shiga ainihin cikin masallacin yau ya zama wani kebantaccen abu ga wasu kebantattun mutane,amma hakan bai hanashi takawa a nutse ba yana wucewa ciki abinsa,ba tare da jiran izini ko dama daga bakin kowa ba.

Su kansu basusan dalilin da ya sanya suketa dage masa kowanne shinge yana shigewa ba. A cikin jikinsu ba wani me zarrar dakatar dashi ko masa bayanin yau dinma sultane zaiyi sallah ne cikin masallacin tare da surukinsa.

Akwai ragowar mintuna da suka rage,wannna ya sanya ya zauna cikin sahu a nutse,ya sanya hannunsa yana fidda wani dan qaramin littafin daya soma dubawa daren jiya bai kammala ba,ya bude ya fara dubawa a nutse,wannna ya sanya kusan duka abinda ke faruwa cikin masallacin bai sani ba.

Rufe littafin yayi a hankali sanda yaji alamun fara daidaita sahun sallah,ya miqe a nutse yana gyara cloak robe dinsa.

Satar kallonshu Maher yayi,har qasan zuciyarsa burgeshi haisam yake sakeyi. Yayi imanin inda wani ne Allah ya bashi mulki kudi da qarfin iko irin haka,bazai taba aiki da hukumar national intelligence ba,saidai su suyi masa aiki. Inda wani ne....bazai taba yarda a jashi ko a jagoranceshi sallah ba......saidai shi yaja. Yana da tarin ilimin da iya zamansu na kwanakin nan Maher ya fahimta. Baya daukan kansa da nisa,shi yasa da yawa wadanda ke tare dashi basusan irin ilimin da Allah ya hore masa ba.

Ranar daya fahimci yarukan da yakeji ya jima yana juya abun. Tabbas rayuwa kowa da irin nashi nasibin. Ya iya French ya iya English,ga amheric ga oromo ga larabci,sai hausa da bata kama bakinsa sosai ba,don bashi da sabga me yawa da ita. Bai bari ya gane yasan ya iya duka yarukan ba,don ya fahimci kamar yana sirranta hakanne.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 60

"Salamu alaikum" Yaji sautin sallama daga gefan damansa. Idanunsa da suka rusuna kadan ya daga yana dubansa na wasu sakanni sanda yake sakar masa murmushi,shima sanye cikin cloak robe da zaunennan rawanin da kana dubanshi kasan qwararru ne suka zauna suka masa wani nadin burgewa saman kansa.

"HAKEEM" Sunan yazo kansa lokaci guda,sai yayi qoqarin daidaita fuskarsa yana rage mata daurewar da take dashi tun a dazun,daidai sanda hakeem din ke qoqarin masa bayanin yana tunanin bai ganeshi bane,don ya fahimci kadan daga halayensa na rashin son shiga sabgogin da basu shafeshi ba,saidai shikam ya jima yana burgeshi,tun daga wancan ranar a Riyad har yau ya kasa mancewa da fuskar sheikh din.

Musabaha sukayi da juna,haisam ya zame hannunsa,don babu dogon magana kasancewar an fara tayar da iqama.

Cikin mintuna bakwai suka kammala sallar. Hakeem na gefansa bai tashi ba yana nashi azkar din na bayan sallah.

Ya gane hakeem,a wata musabaqa da suka gabatar a Riyad akan wasu kebantattun litattafan addini daga dukkan qasashen duniya. Kwanaki uku sukayi a wani kebantaccen hotel,wanda kusan duka haisam dinne ya dauki nauyin komai,amma kasancewarsa mutum wanda baison asan yayi wani aiki na alkhairi gudun shigar riya ayyukansa,sai bai bada dama ga kowa yasan shi ya dauki nauyin komai ba.
Chapter 69 · 0% Book details