← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 97

Sashe 31

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace ta waiwaya,saidai hankalinta a kwance yake. Hijabin data sanya daga kowanne idanu da zai iya ganin wanzuwarta a wajen ita da tamim......kamar yadda tafisun bata isa ta qara koda taku guda daga inda take tsayen ba. Uwa uba tafisun amintacciyarta ce.....kalar amintacciyar da ba irinta kaf cikin hadimanta,saidai kuma kowanne mutum tana tsaidashi a matsayinsa......a gurbinsa......a kuma matakinsa.

Sai data numfasa na tsahon wasu mintuna sannan ta daidaita muryarta da kanta.

"Ya akayi?".

" Maude ne yazo da wani saqo,yakeso ya gabatar miki dashi" Yalwa ta fada girmame.

Maude din yana daga cikin mutanenta na amana......kamar yadda ta tabbatar tunda tafisu ta tsallako har nan nemanta ba shakka abune me muhimmanci ya taso. Bata amsawa tafisu ba,tadai juya ta yiwa tamim kallon da yake gaya masa ta jirata,ta juya da takun mulkinta tana nufar qofar fita.

Idanu ta zubewa maude bayan ta zauna,baice komai ba ya matso yana miqa mata wayarsa. Tafisu ce ta matso tana karbar wayar daga hannunsa sannan ta qarasa da ita fuskar mammina.

Kallon mintina goma ta yiwa wayar......tana dab da cewa tafisu ta janye wayar sunan akhnan ya bayyana a jikin dokinta sanda take zabga gudu kamar bata tsoro ko hasashen abinda zai iya faruwa da ita idan ta fadi

"Me nake gani wannan?" Mammina din ta furta tana janye dubanta daga fuskar wayar,tana kuma hade girarta sosai tana son dora yanayin saman fuskarta yadda zai dace da fuskartata. Can qasan ranta kuma wani abu yana motsawa,wasu tarin abubuwa suka fara motsawa sannu a hankali.

Qasa maude yayi da kansa cikin tsananin ladabi.

"Ki gafarceni.....kiyimin afuwa........gimbiya akhnan ce,cikin gasar tseren dokuna ta yankin Niamey"

"Gasar tseren dokuna?" Ta fada cikin mamaki tana duban maude. Sake qasa yayi da kansa.

"Tabbas.....kiymin afuwa Allah ya baki yawan rai........na durfafeki da maganar ne saboda na tabbatar abune dake ba zakiso ba.......banason kuma ace me martaba yaji wannan maganar......na tabbatar zaki tsawatar zaki kuma yiwa tufkar hanci don lamari ne da bai dace da al'adunmu ba" Shuru kawai tayi tana juya maganar cikin ranta. Ma'aunai guda biyu ta aza maganar maude......ma'aunai masu nauyi da kuma zurfi tanason gane a wanne ma'auni ya kamata ta dora maganar.

Shuru ne yaci gaba da wanzuwa cikin parlor din. Tsahon wasu daqiqu,a hankali ta sauke wani boyayyen numfashi daya fito da wani sirrintaccen murmushi daga fuskarta. Duk da ba'a yanyin murmushin take ba......hasalima ba lokaci bane daya dace da fitar hakan saman fuskarta ba.....amma gilmawa da haskawar wani tunani cikin kanta ya sanya dole murmushin ya qwace mata. Yatsunta ta murza guda biyu wanda suka bawa maude hasken abinda take nufi,don haka ya sake rusunaw yana fadin.

"Na barki lafiya". Har yakai bakin qofa ta kira sunansa cikin izza.

"Maude"

"Allah shi baki yawan rai".

"Bana buqatar komai.....bana buqatar kowanne motsi......idan da wani buqata zan magantu".

"Yadda kikeso haka za'aci gaba dayi.......ba'a gidan bama.....a qasar agadez gaba daya" Ya furta da wani salo daya sake sanyata jin qarfin nata girman yana sake ninkuwa.

"Kiramin biftu ki bani ita" Ta sake cewa da yalwa ba tare data kalli yalwar ba. A ladabce ta miqe ta taka da hanzari ta fita. Ba jimawa ta dawo da wayar ta budeta ta kuma kira layin akhnan din kai tsaye.

Su uku ne kacal cikin motar banda motoci biyu a gaba da bayanta suke musu rakiya daga filin wasan zuwa gida. Wani irin nishadi takeji a zuciyarta,kalar nishadin data jima bata samu irinsa ba. Sosai takejin walwala,tana jin wani alfahari da kanta yana saukar mata.

Babban abinda yake qara ninka farincikinta........maza guda goma sha daya data yiwa zarra ta kuma zubdasu a filin........ta zame musu kallabi tsakanin rawuna. A cikin qwayar idanunsu taga zafin hakan,a cikin motsinsu ta hangi daci da bacin ran da sukaji game da hakan......hakan takeso........shine buri da muradinta.

Ta bata ran kowanne namiji da yakejin yakai.......tabar masa tabo da ciwo me taba zuciya a matsayinta na diya mace.

Dukkansu qwararrun 'yan wasa ne da akeji dasu cikin Niamey,tasha kallon wasansu,kusan kowanne a cikinsu tana da record dinsa....mayun wasa ne da ake matuqar ji dasua Niamey din da kewayenta.......sai gashi a yau bugun farko dukka ta zubdasu.

Daga nan inda take tana iya jiyo yadda ake kiran sunanta ta amsa kuwa. Lambobin yabo da na girmamawa......shaidar lashe gasar dukkaninsu ta watsar bata tsaya saurara ba bare ta karba ta taho abinta.

(08187255862 for lu'u lu'u payment)

Tasan akwai tarin daruruwan mutanen da suke son daukar hoto tare da ita. A wajenta wannan din duka shirmene,bata shirya bawa kowa dama yazo kusa da ita ba,uwa uba ita ba wani lambar yabo tazo karba kona girmamawa ba. Girma dashi dama suka ganta,yabo kuwa iya na bakin mammina da sultane sun isheta. Ta shiga gasar ne kawai don rad'in kanta,ta shiga ne kawai don farincikinta,ta kuma shiga ne don haka takeso haka kuma take sha'awa.

Cikin Lamborghini din da tazo musamman saboda daukarta suke ta barsu da kururuwar kiran sunanta. Ita da aisa sai shehnaz. A nutse take cire helmet din kanta ta miqawa birran. Karba tayi sannan ta matso tana zare mata boot din qafarta. Barratu ta miqa mata tataccen ruwan cranberry juice me matsaikaicin sanyin da bazai cutar da haqora ba.

"Biftu wannan wasan bai cika ba......Vouse avez fait un mauvais choix(kinyi yanke hukunci mara kyau),IIs te réclament toujours au micro(har yanzu kiranki sukeyi ta mic)".

Ajjiye cup din tayi a saman tafi hannun birra dake duqe gabanta tana jira ta gama,ta karba cup din ta matsa can wajen wani madanni daban dake jikin motar ta latsashi tana maida komai saman dan tray din daya fito.

Lallausan handkerchief dinta ta sanya yana goge dogayen yatsunta farare sol da babu digon komai koda saman farcenta,daidai sannan aisa itama ta tanka.

"Ki gaya mata dai.......wannan wasan bai kamata ya tafi a banza ba........Tu as joué un bon match(kin buga wasa me kyau.....ni kaina nayi mamaki". Shigowar kira wayarta da number mammina yaja hankalinta fiye da qorafinsu,sai kawai ta yiwa birra alamu,da hanzari ta ciro mata Bluetooth dinta ta miqa mata ta maqala a kunnenta tana relaxing sosai cikin kujerar

"Ba abinda ya kaini kenan ba......ba yabo nake buqata ba bare na karbi nombre(number).....me so a cikin ku tana iya komawa ta karba daga baya" Ta qarasa maganar tana daidaita Bluetooth din a kunnenta cike da dokin son yin magana da mammina din da take jin kewarta har zuciyarta.

Aisa ce ta watsa mata harara tana dora qafarta daya saman daya.

"Eh ga gantalallu ba". Bata ma ji abinda take cewa ba saboda hankalinta ya tafi ga wayar.

"Bonjour mammina" Ta fada a shagwabe kaman yadda ta saba yin waya da ita. A duk sanda take gaban mammina......ko take waya da ita,tana jin kanta kamar qaramar yarinya. Wani girma da izza takeji sosai a duk sanda take tare da mammina din. Itace mutum ta farko data dasa sarauta da kuma izza sosai a tattare da ita......ta sanar da ita wacece ita a aikace......ta sanadin mammina tasan irin daukakar da Allah ya bata. Nisan tazara da banbancin dake tsakaninta da sauran yaran masarautar dama qasar agadez gaba daya.

"Me kikayi haka AKHNAN?". taji saukar tambayar daga bakin mammina ba tare da tabi takan welcoming nata da tayi ba.

Gabanta ya fadi......saboda taqi jinin dukka wani abu da zata yiwa mammina din har ya kawo motsuwar ranta ko rashin jin dadi a tattaare da ita,harma kuma hakan ya nuna ga fuskarta.

"Kinason ki manta ke wacece akhnan?.......kinaso ki manta tsada da darajarki?.......me kaiki shiga tseren doki?.......har kina yin kamar zaki fadi bayan kinsan tsada da darajarki?......bakisan kin wuce ajin irin wadannan abubuwan ba?......me kike nema?". Boyayyar ajiyar zuciya ta saki kafin ta narke murya,har cikin ranta tana jin ba dadi da yadda tasa ran mammina din ya baci har taji ba dadi har irin haka a kanta.

"S'il vouse plaît mammina.......nayi hakanne kawai don nishadi na fa?" Ta fadi kaman zata saka kuka. Ta fadi da wannan narkakkiyar shagwabar da mammina din da kuma sultane kadai takejin kanta a hakan a gabansu.......batasan ko akwai wata halitta a doron qasa data cancanci wannan zubin yanayin da kuma tsarin ba.

"Amma idan sultane ya gani yace me?,kina zaton ranshi zaiyi dadi?".

"Excusez-moi(sorry)mammina........Je suis vraiment désolé(am really sorry),don Allah karki fadawa sultane mana mammina". Shuru mammina din tayi,kaman ba zata sake cewa komai ba kafin tace.

"Shikenan,kada hakan ya qara faruwa"

"Je ferai preuve de diligence(zanyi qoqarin hakan sosai)" Ta amsawa mammina tana sauke boyayyar ajiyar zuciya na samun sukuni.

"Kika ce?"

"Mammina zanyi qoqari sosai akan hakannnn" Ta sake fada kama zata saki kuka,saita dora da

"Salut......À plus tard(sai anjima)" Tana dan boye sirrintaccen murmushin nan nata.

A nutse ta yiwa yalwa alamun ta gimtse kiran. Cikin cika umarni yalwa din ta janye kiran ta kashe kiran ta dora wayar daga saman wani tattausan tuntum.

"Murmushi.......kulawa......nuna qauna.......damuwa da dukkan lamurannan.......bansan daga ina kike iya zaqulosu daya bayan daya ba" Muryar yalwa ta maye gurbin shirun da parlor din ya dauka,kafin a hankali yalwan ta waiwayo tana zube idanunta cikin na mammina,kamar ba itace a dazun kanta yake qasa da inuwar mammina din ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*
Chapter 31 · 0% Book details