← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 97

Sashe 62

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da kasancewar yanayin na shigowar dare da kuma fara nisansa,don a qalla sha daya ne harda rabi na dare,amma hakan bazai hanaka ganin qawatacciyar rigar dake sanye a jikinta ba.

Doguwar riga ce irin ta asalim larabawan saudiyya data kasance free size me fadi sosai,wadda keda wani irin adon duwatsu masu kyau da daukan hankali da kuma adon zare mabanbanta.

Daga saman rigar wani yalwayaccen mayafi ta sanya da yake kama da hijab kalar data dace da rigar jikin nata. A yanayin duban da zaka mata na farko zaka fahimci shigar bata dace da irin shigar da takanyi cikin gida ba,bata kuma dace da shigar da takeyi a lokaci irin wannan ba.

Yadda gidan ya dauki shuru sai sassanta ya zaman shurunsa yafi na ko ina,don ta jima da bada umarnin tafiyar dukka wani hadimi zuwa makwancinsa,idan ka dauke hadiman dake tsaron qofa bayan qofa da zaka yita wucewa har ka iso babbar qofar da zata sadaka da sassanta. Su biyu ne rak a dukka manyan falukan nata,ita da kuma amintacciyar hadimarta yalwa,wadda ke zaune kanta a qasa tsakanin kujerun falon.

Tayi kai kawo tsakanin falukanta har batasan adadi ba,har bata duban yalwa dake zaune ba tare da wani qwaqqqwaran motsi ba,da alama tana cikin irin yanayin da uwar dakin nata take ciki ne.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

A takowar da mamminan ta sakeyi ne yalwa taja numfashi gami da daga kanta.

"Allah ya baki yawan rai,sai nake ganin kamar daren ya tsawaita.........kamar dadewar tayi yawa,tafiya daga cikin saharar camaroo zuwa nan baikai ace ta dauki lokaci me tsaho irin wannan ba......" Yalwa ta furta cikin alamun nuna damuwa sosai.

Hannayenta ta goye a qirjinta,a hankali ta qara taku biyu sannan ta zauna hannun kujerar dake kusa da ita.

"Akwai qarin jami'an tsaro da 'yan sanya ido a tsakanin dukkanin saharorin dake kewaye damu,saboda dalili na tsaro da ake fama dashi,saidai kuma bana tunanin zaya bari su biyo ta irin wadannan hanyoyin.......don shi din masanin dazuzzuka ne da barayin hanyoyin cikin sahaara" Ta fadi damuwa fal muryarta. Sake duban agogon dake gefanta yalwa tayi,sannan ta sake daga kanta tana kallon mammina.

"Allah shi baki yawan rai,yanzu mene abun yi?" Ta qarasa maganar tana sake rusunawa,duk da cewa daga zaune take.

Sakin hannayenta tayi,ta miqe tana furzar da iska daga bakinta gami da yin taku uku.

"Ko meye zai faru yalwa.......a daren nan nakeso almaz ya kasance cikin qasar agadez......babu wata rana da tafi dacewa da dukka shirina irin wannan ranar......irin wannan lokacin......irin wannan daren kuma,don ina ganin wani haske da dacewa,wanda banaso wannan sa'in ya kubce daga cikinta..... Ki lissafamin bugawar mintuna sittin cif......awa guda kenan,idan ba wani motsi zan bibiyi komai,koda kuwa da kaina ne" Ta qarashe maganar tana miqewa tsaye,gami da hada hannayenta guri guda.

Daidai da bugawar mintuna sittin din cif cif,wanda ya dace da qarfe sha biyu da mintuna ashirin da bakwai na dare wayar da bata ringing saidai qara ta cilla haske. Da sauri yalwa ta daga kai tana kallonta.

"Tamim ne"

"Daga" Ta bata umarni a taqaice tana tattara hankalinta.

Sauraron abinda ya fadi kawai tayi ta gimtse kiran,fuskarta a washe da fara'a ta dubi mammina.

"Anyi nasara uwar dakina" Idanu mammina ta lumshe tana sakin wata ajiyar zuciya me nauyi.

"Suna ina?"

"Unguwar daura......"

"Ina buqatar haduwa dasu" Ta furta tana duban yalwa.

Idanu yalwa ta fiddo waje tana dubanta.

"Ranki ya dade.......kinsan dokar fitarku daga cikin masarauta ai,ballantana fitar ma irin wannan lokacin?,irin wannan lokacin ma a aiki irin wannan dake buqatar dukkanin sirri da takatsantsan?". Kai mammina ta girgiza.

" Bazan fahimci kowanne bayani naki ba yalwa.......bakisan waye almaz a guri na ba......."

"Allah ya baki yawan rai,da kinyi haquri zuwa safiya,sai muyi tunanin ta yadda zamu shigo dashi cikin gidan ba tare da kowa ya sani ba.......amma bana tunanin akwai wata hanya guda daya da zaki iya fita wadda babu masu tsaronta a ciki,ba tare kuma da koda su sun ankara ba"

"Me yasa wani lokaci kwanyarki kamar tana rage kaifi?......me yasa wani lokaci kamar tana rage gudu me makon ta qara?" Tayi maganar tana soma zare mayafin kanta Idanunta akan yalwa.

Qasa tayi da kanta,tana kasa cewa mammina komai,don ta kasa gane hikimarta kwata kwata.

"Tashi ki kiramin ayaana.......kice ta taho da tufafinta guda daya da kowa yafi saninta dashi" Mammina ta fada tana komawa saman kujerar ta zauna hankalinta kwance

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 54

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

A hankali ya saki handle din daya kama dazu,tunaninsa yana dawowa baya kadan.

Hoton kayan ya sake gilma masa,take Muhammad hammud palace ya dawo masa. A hankali yake jinjina kai.......tabbas kayan na masarautar ne.......amma kuma ba wani abu da zai bashi daman zurfafa tunaninsa,duk da cewa cikin jikinsa yakejin kamar akwai wani abun na daban.

★★★★

Cikin takun dake nuna zallar qasaita da kuma nutsuwarta take takawa cikin filin da yake da fadi da wasu lafiyayyun grass carpet,wanda aka tsarashi aka kuma tanadeshi ne kawai saboda ita din,saboda jin dadinta,da kuma yadda ta kasance ma'abociyar son wasannin motsa jiki kala kala.

Tayi kyau cikin wata irin kyakkyawar over sized sweet shirt fara qal me ratsin adon royal blue,wadda ke hade da wani skirt da duka duka tsahonsa qaurinta,don baikai idon sahu ba. Tsaf ta daure gashinta a tsakiyar kai da wani farin ponytail holder da aka qerashi da wasu irin fararen duwatsu masu daraja,jelar gashin ta tsaya a tsakiyar kanta tana lilo daga hagu zuwa dama saboda yanayin yadda take takawa kamar wani qasaitaccen dawisu.

Leggings ne a jikinta wanda yabi jikin nata sosai ya kuma fidda qirar shape din da Allah ya bata da wadatattun cinyoyin da ba zakace nata bane,wadanda suka sake fidda shape dinta sosai.

wani siririn scarfs ne kawai data dan lullube saman kanta dashi wanda ba komai ya rufe mata na gashinta ba.

Hannunta tana dauke da wasu irin hockey sticks guda biyu farare masu kyau. Ma'abociyar son abubuwa ne farare,don kusan komai nata zai wahala ka cire farin kala a ciki.

Birra,buhaina bushira da bara'atu ne a bayanta,birran na dauke da wani babban back pack da tarkacen kayan hockey dinta ke ciki,bara'atu kuwa water bottle ne a hannunta da wani silver vacuum flask me wani irin Royal colour,sai bushira da ita kuma ke riqe da dan qaramin kyakkyawar jakar towel dinta.

Ta jima bata buga wasan ba,don su kansu sun manta lokaci na qarshe da tayi wasan. Itama tasan hakan,abubuwa sun mata yawa akai da yasa ta dade rabonta dashi,amma a yau din nishadi take nema........tana neman abinda zai dauke mata hankalinta ne daga dukkan wata damuwa da kuma tsimayin jiran isowar baqon da QADDARA tasa ya zabi ganawa da ita a yau.

A irin wannan yanayin cikin tsaro take kasancewa shi yasa take duk kalar shigar da take so bisa yaqinin koda a mata sai wanda ta amince zai iso shiyyar da take ballantana maza. Ba wani namiji da ya isa ya rabo koda hanyar sassanta ma ballantana ya shigo mata.

Cikin sanin aikinsu suka dire mata komai,ta zauna a hankali tana gyara madaurin snickers din qafarta,sannan ta zari hockey stick dinta guda daya gami da miqewa,birra dake dauke da ragowar balls din ta biyota a baya gami da tsaiwa agurin data saba tsaiwa din a duk lokaci irin wannan.

A nutse da kuma wata irin qwarewa ta fara buga wasan. A hankali zuciyarta dama jikinta ya fara sakewa,ta fara samun nishadin da take muradin samun,saidai bata jima sosai ba muryar shehnaz ta sauka a kunnenta.

A nutse ta waiwayo ta kalli shehnaz kadan kafin ta maida hankalinta ga wasanta. Dukkaninsu haushinsu takeji ita da aisa din,amma tayi targeting lokacin da zata maida musu magana.

A nutse shehnaz ta rage jayan jikinta,sannan ta dauki sandan hockey dayan daya rage tayi joining akhnan.

Jeki mutu akhnan din batace da ita ba,bata ma sake koda kallonta ba amma ta ware da buga wasan da daga qarshe ta bawa shehnaz kashi sosai. Yarda sandan tayi ta koma baya a hankali bayan wasan ya kammala,ta zauna tana karbar towel daga hannun barratu tana goge qura da dan gumin da jikinta ya fara yi.

Hakan ko kadan bai damu shehnaz ba,tayi joining nata ne kawai don tayi making nata farinciki ko yaya ne. Ba jiya ko yau ba,dukkaninsu a dukka wani wasa da za'a buga,tun zamanin quruciya har yau ba wanda yake buge akhnan din,sun saba da wannan,idan kaga an cinyeta to d'ai d'aikun wasan da bata iyasu ba,a nan ma sakar musu take,bata fiya yarda a buga wasan da ita ba ballantana a cinyeta.

Ta saba koda yaushe nasara tana bangarenta,ba kowanne lokaci bane take daukan rashin nasara tayi haquri dashi ba.

"Nanniee tace tunda tazo bata ganki ba......tanata kuma aiken kizo,ko saqo bai sameki ba?" Shehnaz ta fadi idanunta akan akhnan tana zama kujerar dake facing dinta.

Sai data sha kusan rabin ruwan kafin ta miqawa barratu,tasa hannu da sauri ta karba tana rufe bottle din.

Blue eyes dinta ta zubewa shehnaz kafin ta janyesu tana rage musu girma.

"Zuwa kukayi daukan gawata kenan?,an gaya muku sultane yayi layya da nama na ne?" Ta fadi da wani irin taushi saidai a tsakiyar muryarta da zancanta zaka fahimci da yanayi na jin haushi take maganar.

A nutse shehnaz ta dauke dubanta daga kan akhnan din. Bata shirya gaya mata komai ba a yanzun,don zai zamana kamar qarin rikita mata lissafi ne kawai. Duk da akwai buqatar su zauna da ita,akwai buqatar sanin da saninta komai yake tafiya a sahel couture ko kuwa?.
Chapter 62 · 0% Book details