← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 97

Sashe 22

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A wuce dashi gida......zan shigo cikin gidan yanzunnan.......zamu tako da qafa". Ya qarashe maganar yana sauke idanunsa akan taarik dake shigowa,da alama shima akwai baqin daya sallama.

Jijina kai salawi yayi yana juyawa yana barin gurin,tare da jinjina irin jarumtar uban gidan nasa,da cikakkiyar lafiyar da Allah ya hore masa. Wuni guda yau a tsaye suka yita,saboda tarbar baqin da bai zauna ba.....dashi aka dinga karbar baqin me martaba da sukazo taron har sai daya tabbatar anyi komai yadda zai dace da muradin mooti din......amma duk da haka yakejin zai qarasa gida a qafa ta hanyar kebantacciyar hanyar da zata sadaka da cikin gidan tun daga masallacin,wadda keda tsahon kilometers da kuma jami'an tsaron dake aiki a cikinta duk da ba kasafai ahalin gidan ke amfani da hanyar ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 16

Cike da mutuntawa ya qarasa cikin baqin da yawansu suka kasance abokansa ne.... Abokai kuma irin wanda suka hadu da juna ta hanyar Neman ilimi. Kallo daya zaka yiwa kowa a cikinsu ka karanci yadda ilimi yayi musu ado da wata irin nutsuwa ta musamman. Duk da kowa a cikinsu matashine da jini ke guda na a jikinsa yadda ya kamata......da yawansu matasa ne da suka fito daga gidajen sarauta da gidajen mulki......irin mulki da sarautar da suka mallakawa kowa jin dadi dukiya me yawa da wani irin kwarjini na musamman.......saidai wannan nutsuwar......wannan kamalar da wannan haibar da ilimin addini da qur'ani ke saukarwa kowanne ruhi dake da abota dashi ta mamaye kowannensu. Hatta da yadda lafuzansu na magana da yadda suke tsokana da raha a junansu ta tsaftatacciyar hanya kadai abun burgewa na. Kusan matasa irinsu da suka hada baiwa irin tasu,kyau.....mulki......sarauta,ilimin addini dana zamani......mafi yawa daga cikinsu lokacine nacin duniyarsu da tsinke ta hanyoyi daban daban,sharholiya da sauran abubuwan da suka saba da addini da al'adunsu.

Kusan hirar tasu ta tuna baya ce.......don a cikinsu akwai wadanda aka jima ba'a hadu da juna ba,yau irreechaa day ta hadasu. Zolayar juna,tuna wasu abubuwa masu muhimmanci,abubuwa masu dadi da rashin dadin suketa yi wanda ya faru cikin makarantun da sukayi tare. Wahala da irin qalubalen da suka fata wajen haddar qur'anin da sukayi a shekarun qananun shekarunsu.

"Har yanzu ina mamakin yadda muke kwamciya da dare baka kammala haddarka.......amma da safen saika tashi ka haddace karatun gaba daya harda qari akan qa'idar daya kamata a tsaya?". Siririn murmushi ya saki yana lumshe kyawawan idanunsa dake da wani irin shape da yafi almond shafe tsaho kadan.

"Wannan baya baccin dare me yawa tun asalinsa.......amma nima ina da ayar tambaya a kansa wallahi.......inajin anya mooti bai bashi wasu sirrika ba irin na masarauta?". Dariyar dake cike da hankali suka saki,ya bisu da murmushi yana aza hannunsa gadon bayan wanda yayi maganar. Cikin sautin nan nasa da yasha banbam dana maza da yawa yace

"Indai ina da sirrika na sarauta.......lallai ba shakka kai din bappi ya baka sirrikan mulki.......shi yasa kujerar ka da gadonka har muka kammala ba wanda ke kwanciya akai" Dariyar suka sakeyi,yana tuna musu da rigima irin ta mutallab. Yafi kowa rigima a cikinsu,sannan yafi kowa bata musu daki a wancan lokacin,to amma duk randa ya taqarqare yayi gyaran dakin tofa kowa ma ya shiga uku a wajensa,basu da sukuni basu da sakat.

Wani irin team garesu a sannan me abun mamaki,ba wani a cikinsu da ubansa ba wani bane cikin qasar ta Ethiopia da maqwabtanta.......'ya'yan gata ne iya gata.......saidai gatan da yasha banbam da sauran gara gata,saboda wata irin tarbiyya da ilimin addini daya ratsa ruhin kowannensu,ya maidashi mutum me wata irin nagarta ta daban.

"Banda dare yayi lokaci ya soma ja.......da mun taba musaffa koda ta izu daya ce......don bana tunanin nan kusa akwai wani lokaci da zai sake hadamu kamar haka......duk kowa a cikinku yaqi fidda mata yayi aure bare mu saka ran haduwa a kusa kaman haka" Daya daga cikinsu da suke kira da naseeb wanda dan asalin Egypt ne ya fada yana duba agogon hannunsa sannan ya sauke dubansa akan haisam.

Shi din mutum ne me asalin fahimta da daukan haske akan magana ko motsin mutum.........hakan yake tun asalin halittarsa.......wannan ya bada gudunmawa sosai kan aikinsa na yanzu da yakeyi personally ba tare da kowa yasan wayeshi din ba. Yanayin yadda naseeb yayi maganar yasan me yake nufi,ina ya dosa. A cikinsu shidan naseeb yayi aure bada jimawa ba.......mutallab......khadeem.....maleek......amjaad......dukka suna da tsayayya.......shine har yanzu da babu koda wannan tsarin a gabansa,sau tari koda conference call sukeyi a tsakaninsu mutallab din kan tsokaneshi da cewa.

"Don Allah ku nema masa tsayayya wannan.......wannan an rasa me tsaya masa". Omari ne kanyu murmushi......saboda shi daya ne yafi kowa a cikinsu sanin wayeshi.......yafisu saninsu rufaffen sirri me girma dake cikin rayuwarsa.

Cikin qasa da mintuna talatin tawagarsu ta soma fita daga masallacin zuwa inda kowannensu abun hawansa da guards dinsa ke jiransa. Cikin wannan hirar da barkwancin gami da qaunar junansu,kamar ba zasu rabu ba haisam din daya kasance me masaukin baqi ya takawa kowa zuwa bakin motarsa cikin musabahar bankwana suka rabu.

Ya rage dagashi sai omari da suke takawa a nutse zuwa sirrantacciyar hanyar da yakejin kamar nan ne kawai yafi dacewa suyi magana da omari,bayan masu tsaron qofar sun bude masa cikin rusunawa bayan ya wuce suka maidata suka rufe.

"Omari......" Ya kira sunansa da tsinkakkiyar muryar nan tasa dake da wani irin amo......amon da hatta maza 'yan uwansa tana musu dadi ballantana diya mace.

"Wani lokacin sai na dinga jin kamar wannan matsayin......wannan girman da ake bamu kaman yana neman wuce gona da iri.......kamar akwai sabawa mahalicci a cikinsa" Ya fada calmly kyawawan idanunsan nan dake da wani irin haske suna motsawa wajen rufe kansu da budesu a lokaci guda yana duban tsahon hanyar da suke takawa cikin nutsuwa.

Murmushi omari ya saki......shi dinma daga gidan sarauta ya fito,da akwai banbancin yare tsakaninsa da haisam.....shi din yaren amheric ne......amma yanayin aikinsu ya sanya shida haisam din sukejin yaruka masu tarin yawa,harda yaren da ba na qasarsu bama,ciki kuwa harda yaren turanci bayan na larabci daya zame musu kamar yarensu na haihuwa. Sun iya hausa kasancewarta cikin yare mafiya girma da fadada cikin yarukan yankin africa,hakanan sun iya French......yarukan da suke cikin qasarsu kuwa kusan kowannensu saida suka iya shi,a qalla idan aka lissafa yare kusan goma suke ji,saidai ba kowa ne yasan da wannan ba.

A yadda omari yake kallon komai,duk wani motsi na gidan sarautar abba jifar yana cike ne da zallar ilimin addini dake magana. Hatta da shigar bayi hadimai da dogaran gidan yasha banbam dana masarautu da dama. Tsarin aurar da hadimai da bayi......gidajensu prison dinsu da makarantunsu.......komai nasu yasha banbam dana sarakunan qasar da dama. Omari bai samu damar cewa dashi komai ba.......babban saqon da yake qunshewa a cikinsa tun dazun ya fado masa

"Shugaba yayi kira.........yace kuma lallai gobe mu sauka addis ababa". A nutse haisam ya waiwaya yana duban omari,saidai mamaki ya bayyana sosai saman fuskarsa.

"Da gaggawa haka?". Kai omari ya gyada yana dubansa shima.

" Yace bai sameka ta kowanne platform ba.....shi yasa ya ajemin saqon......ajemin saqon da ganin da nayi kuma dole ya sakani cikin operation din.......dama wannan shine burina,addu'ata ce ta karbu" Omari ya qarasa maganar murmushi yana subuce masa. Dauke dubansa haisam yayi daga kan omari fuskarsa na nuna alamun qaramin murmushi ta yankin rawanin da har yanzu bai saukeshi qasan fuskarsa ba.

"Inaji a jikina kamar lokaci yayi......kamar wani abu ya bayyana game da abba *AJANI AHMED*" Yayi maganar da dukka yaqininsa.

"Ka duba mana tickets da suke available daga jimma zuwa addis ababa......idan baka samu available ba ka sanarmin mu tafi a mota....."

"Dama kafison hakan ai" Omari ya fada yana dan tsuke girarsa. Haisam bai waiwayo ya kalleshi ba......saboda yasan hade rai omari din yayi,sai wani lafiyayyan murmushi abinsa daya sake cikin rawaninsa.

"Kuyi duba izuwa tasirin rahamar Allah yadda yake rayar da qasa bayan mutuwarta............haqiqa cikin halittar sama da qasa da sassabawar dare da rana akwai ayoyi ga ma'abota hankali......omari ka manta da wadannan ayoyin?". Kai ya jinjina omari din yana sakin murmushi alamun aah.

"Akwai abubuwan lura da tunani da yawa akai kan ayoyin ubangiji......baka taba sanin hakan sai kayi yawo a duniya......ka keta dazuzzuga da tsaunuka......ka hadu da hadura masu yawa......abubuwan firgitarwa masu tsananin girma......ka tuna cewa duka mallakar madaukakin sarki ne......iya wannan kadai ya isheka ka qara imani da yarda da ubangiji" Kai sosai omari ya jinjina......shi kansa akwai surori cikin qur'ani da idan yana karantasu yakan tafi ne zuwa wata duniya ta daban ta zurafafa cikin lamarin ubangiji.

08187255862

A cikin jini da dabi'ar haisam suke........yana da bala'in son binciken boyayyun abubuwa irin wannan da suka shafi hikima da qudira ta ubangiji.......yana son nature sosai.......yana da son zuwa baqin gurabe muhalli da qasashen da baisan komai a kansu......qasashen da zai zama baqo da gasken gaske akan komai nasu.......baya da tsoro ko digo dis a ransa........baya tsoron shiga risk da hatsari kowanne iri ne......wannan shine ya zame masa sanadin shiga aikin masu bincike na farin kaya cikin sauqi wato Dss. Cikin qanqanin lokaci da fara aikinsa sai ya zamana kamar da experience dinsa ya shigo aikin gaba daya......wanda halitta ce a jininsa data zame masa dalilin samun qarin matsayi nan da nan......cikin shekaru kadan ya zama babba cikin NATIONAL INTELLIGENCE AND SECURITY SERVICE(NISS). Yakai matakin da zai zama shine na daya a wajen.......amma zuzzurfan tunani da kaifin hankali irin nasa ya sanya hangensa yakai kan abubuwa guda biyu.
Chapter 22 · 0% Book details