← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 97

Sashe 23

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na farko shi wanda yake akai a sannan ya fishi shekaru nasa ba kusa ba......sannan babban aboki ne ga mahaifinsa me martaba abba jifar.......ya riga ya sani,komai iliminka......komai wayewarka da saninka......akwai wasu dabaru da wasu hange hange da sai wanda ya baka shekaru zai iya hangensu........yana kunyar abba muhammad dawuud ya sauka a matsayi shi yahau kai.....duk da lokacin retired dinsa yayi.....amma ya nema alfarmar a barshi cikin office din yaci gaba da zama......shi zai zama a madadin mabiyinsa.

Dalili na biyu......yakan ware wasu watanni a shekarar da qasar Ethiopia ke dashi da suka saba da namu watannin goma sha biyu......su din suna da watanni sha uku ne.....a ciki yana daukan wata daya yayi hutu,hutun da ba inda yake qarar dashi sai yin visa ya sayi ticket na wata qasar dake nesa da yankinsu da al'ummarsu.....masu babancin halaye dabi'u al'adu dama halitta irin tasu...... Wani lokacine da yake na musamman a rayuwarsa.......wani lokaci da yake jinsa na musamman shi kansa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 17

Yana samun wani 'yanci......yana jinsa cikin tarin sukuni da sakewa.......babu wadannan hadiman a tare dashi........ba wadannan masu kula dashi din,hadiman da mooti ko sau daya baya yarda haisam ya motsa ba tare da ko mutum daya ba......illa idan zai shiga NISS,kasancewar wani sirrintaccen abune da ba kowa yasa ma'aikacin hukumar bane......daga shi sai karan kansa a irin wannan yanayin da yakeyin nesa da qasarsa da mutanensa. Yakan yi tilawar qur'ani sosai fiye da yadda ya saba saboda samun sakewa da sukunin zuciya. To muddin ya karbi wannan matsayin zai rasa wannan damar,dole ya zauna ya dinga bada umarni.......shi kuwa yana ganin kamar hakan koma bayansa ne kuma koma baya ga baiwar fikira da basirar da Allah ya bashi ce.

Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai idanunsu sun hange musu ita. Cikin hanyar data kadaita ga kowa. Sanye cikin wani wadataccen hijabi daya sauka ya lullube har saman qafafunta. Matashiya ce da shekarunta gaba daya ba zasu haura sha tara ba........lullube da wannan kebantacce kuma sirrintaccen kyan na 'yan asalin Ethiopia kuma 'yan qabilar Oromo.......wannan kyan da aka bar musu kayansu,hannunta dauke da wani madaidaicin kwali,idanunta kuma manne akan fuskar haisam din.

"Saami" Omari ya fada qasa qasa,abinda ya sanya idanun haisam qiftawa yana saukesu daga kansa. Daga randa suka zauna sukayi sharhi da fashin baqi akan ayar da Allah yake magana akan LOWERING GAZE cikin qur'ani da suka yiwa take da yaren oromo da *Ilaalcha gadi buusuun* cikin qur'ani Allah yana cewa

"Ka gayawa muminai su kame ganinsu kuma su kula da farjinansu......wannan shine yafi tsarkaka a garesu" Sai ya sake zama me tsantseni da kulawa sosai akan wannan din. Komai Allah yayi jan kunne gargadi umarni ko hani akai ba shakka akwai babban lamari da kuna batu akai......daga ranar da bincikensa yakai kai kuwa baya sake kusantar wannan abun.

Ko kafin sannan mutum ne shi me tsantseni ta wannan bangaren......tun daha sanda ya mallaki hankalin kansa ya kuma fahimci irin halittarsa sai ya zamana ya dauki matakin kame ganinsa.......sake nesanta kansa daga dukkan wani jinsi da ba nasa jinsin ba......bai sha wahala ba,don dama dabi'arsa daban take.......tun asali kuma shi din mutum ne me kiyaye hakan,sai komai yazo masa da sauqi,har wani lokacin suna tsokanarsa da MR LOWERING GAZE. Wani lokaci su fada da turancin da dukkan su sun iyashi......wani lokaci kuma da yaren oromo din *Mr ilaalcha gadi buusuun*

Qasa tayi da kanta,hakan kuma bai hanata takowa zuwa inda suke din ba,saidai ta rage saurinta sosai.

Ta sanshi,sannan ta karanci abubuwa da yawa daga halayensa......wannan ya sanya dab da zasu isa ga junansu ta buda bakinta cikin nutsuwa.

"Assalamu alaikum" Ta fada da cikakkiyar sallama.

"Wa'alaikumussalam" Omari ya amsa yana niyyar wucewa,saidai tuni haisam ya riqe yatsunsa ya kuma dawo dashi baya.

"Barka da warhaka" Saami din ta fada tana dan duban sashen da omari yake. Fuska yadan sake mata,a iya shigowarsa gidan yasan saami.......da fari bai dauki wani abu game da samee din ba da yadda take girmama haisam da damuwa da lamuransa ba.......sannu a hankali ya fahimci akwai wani babban al'amari a game da haisam din a zuciyar yarinyar.

Tana da wata irin nutsuwa da kuma kamun kai..... Irin wadda ya jima bai ganta game da wata yarinya matashiyar budurwa me irin shekarunta ba.....wannan ya sanya shi kansa yake girmamata da kalar girmamawar da yaga haisam din yanayi mata.

"Barka da dare" Ta fada tana dan rusunawa haisam din ba tare data iya kallon fuskarsa ba.

"Barka.......ina zaki haka da daren nan a hanyar da ba jama'a?". Har tsakiyar zuciyarta taji tambayar da yayi matan.......yanayin yadda yayi tambayar da mamaki cikin muryarsa dake nuna da gaske baisan me ha fiddota zuwa ga hanyar ba a irin wannan lokacin.......bai fahimci ta fito bane kawai don ta samu ta ganshi ko yaya.......ta fito ne don ta kebanta dashi koda na daqiqa ashirinne.

Bata iya ce masa komai ba,saita miqa masa kwalin hannunta,duk kuwa da yadda kunya ke dawainiya da ita. Kwalin yabi da kallo a nutse kafin ya maida dubanshi ga fuskarsa. Yanaso yayi tambaya ne game da kwalin amma sai omari yayi masa riga malam masallaci ta hanyar sanya hannu ya dauke kwalin daga tafukan hannayenta.......hakan ya bata damar juyawa ta basu baya sannan tace.

"Saqo ne daga wata baiwar Allah" Daga haka ta soma takawa da hanzari tana bacewa ganinsu ta tsakanin wasu qananun bishiyoyi.

"Wani lokacin sai naga kamar ta bangaren aikinka da karatunka kawai kanka yake kawo wuta..... Kamar ta fanninsu kawai kake gane komai". Fararen manyan idanunsa dake tsakiyar rawaninsa ya zubawa omari.........kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa.

"Tana buqatar ke kebe ne da ita fa.......kai kuma kayi kaman baka fahimta ba?......."

"Na fahimta mana omari.....na fahimta" Ya amsa masa yana soma takawa yana yin gaba ba tare daya damu da sanin meye a kwalin ba.

"Ba inda musulunci ya bamu daman kebewa nida ita irin hakan......ka manta ne omari?" Kai ya jinjina yana takowa don cin masa,duk da cewa hankalinsa yana kan kwalin daya dan budashi kadan yana leqa cikinsa.

"Amma ya kamata ka fahimta.......ya kamata ka gane me yarinyar nan ke nufi......ko baka fahimta ba har yanzu sai anyi maka fashin baqi?". Kansa ya girgiza yana kafe hanya da ido kamar meson gano wani abu.

" Na fahimta omari.......sameera sona takeyi.......so takemin irin na aure.....amma ni kuma........"

"Karka soma cemin samee batayi ba......zanyi abinda ban taba yi maka ba wato qaryataka......kamar yadda nasan kaima kayi abinda baka taba yi ba wato qarya" Miskilin murmushin nan nasa ya saki,yana ci gaba da takawa ba tare daya dubi omari ba. Sai da yaja fasali sosai sannan ya maida masa amsa.

"Tako ina samee tayi.......kamilar mace ma'abociyar addini.......mahaddaciya sittin da tafsir......wadda ta haddace litattafan addini masu tarin yawa,ba inda ta sani,daga gidansu sai makaranta.......sai nan gidan.......idanma akwai wani abu da samee bata cikashi ba......saidai cikar nan da ake cewa duk dan adam tara yake bai cika goma ba.......matsalar kawai ni dinne". Ya fada calmly har hakan na bayyana cikin maganarsa.

Dakatawa omari yayi cikin mamakinsa. Ya dauka dukka daya jero wadannan maganganun zai gaya masa cewa ya jima shima da fara son samee ko accepting nata.

"Kai din me?".

" Ban shirya soyayya ba......ban kuma taba jin son samee a zuciyata ba so irin na soyayya......donme zan bata mata lokacinta?" Ya qarashe maganar da sigar tambaya yana kuma waiwayowa gaba dayansa hannayensa zube a aljihunsa yana zubewa omari su.

Kallon kallo suka fara yi a tsakaninsu. Mamaki yana kashe omari.......yayin da haisam ke jiran ko zaiji wani qwaqwaran dalili da zai sanyashi bawa samee lokacinsa ko hankalinsa.

Gaba daya ya gama gogewa omari hadda,sai yaja jikinsa kadan ya zauna saman kujerun concrete dake kusa dashi.

"Sai yaushe kenan zaka shirya yin soyayyar......ka shirya kuma accepting wata?". Wannan boyayyen murmushin nasa dake cikin rawaninsa ya saki,ya kuma yi qas da kansa yana zubawa qananun fararen duwatsun da aka qawata wajen dasu idanu kamar yanason qididdige lokacin da zai jarrabawa wata macen ko ya bata dama a rayuwarsa.

"Not now omari......ba yanzu ba,ina da sauren abubuwa masu muhimmanci daya kamata na gama dasu omari".

"Haisam....." Omari ya kirashi a sanyaye yana aza dukka hannayensa saman kwalin..

"Ina jiye maka haqqin 'dubban 'yammatan da wannan shu'umin murmushin naka kadai ya jefa zuciyarsu kogin soyayya......ka kasa kuma taimaka musu da komai". Dole wannan karon murmushinsa ya fito da wani irin sauti.

" Laifina ne omari?......" Kasa bashi amsa omari yayi......dondai da gaske kai tsaye bazaice laifin haisam bane.......hasalima dukka cikinsu yafi kowa takatsantsan da lamarin mata,banda jaruma kuma tsayayyar zuciyar da sukasan yana da ita tabbas ba abinda zai hanashi soma kiransa da ME TSORON MATA.

Wani irin magnet ne cikin halittarsa dake fusgar hankalin 'yammata a kanshi........kusan dukkansu suna da irin wannan baiwar,amma nasa kaman yafi nasu zafi da yawa.

"Karkayi kwantai ko kayi zaben tumun dare fa?......" Omari ya fada yana fidda idanunsa waje. Kai kawai haisam keta girgizawa kaman dariya nason qwace masa,fararen jerarrun haqoransa da haskensu ya fita harta qyallen bakinsa suka bayyana.......a wannan karon sai da yakai hannun nasa ya zame qyallen zuwa wuyansa don ya bawa dariyarsa damar fitowa sosai.......wannan ya sanya qarashen cikamakin kaykkyawar fuskarsa damar bayyana gaba dayanta.

Wani lafiyayyen ajiyayyar baqa sidik din suma ce ta bayyana data gewaye habarsa da kumatunsa da wani iri qawataccen shape da zai gaya maka zallar qwarewa da sanin haqqin qasumba name askinsa. Kyawawan jajayen lips dinsa dake qyalli kamar an shafa musu man labba suka bayyana suna kuma sake zama ado ga jerarrun fararen haqoransa.

"Ba damuwa.......sai na jira sanda d'iyarka ta farko zata isa aure saika bani ita". Wani harara omari ya watsa masa.
Chapter 23 · 0% Book details