Sashe 36
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Karki roqeni akan kada nace ki sake kiranta falaak......saidai ki canza wata buqatar.......a wadda zaki canza ma din kada ki sako batun nesanta da ita,.....kada kuma ki sako batun yanke mu'amala da ita". Momma ta fada fuskarta na komawa yanayi na gaske. Shuru falaak tayi tana duban momma din,kafin ta zare idanunta ta maida gefe tana qoqarin hadiye sosuwar da ranta yakeyi,tanason cinye zafin da taji wai ko hakan zai bata damar fuskantar abinda momma ke sln gaya mata. Duk da tasani har yau,ko sau daya bata taba fuskantar momma a irin wannan yanayi da zance irin haka zai wanzu tsakaninsu ba.......bata sani ba,momma dince bata fahimceta ba,ko kuma itace bata da fadin qirjin fahimtar momma din?.
Tattausan hannun momma daya kamo nata hannun shi ya janyo hankalin falaak gareta. Idanunta suka sauka cikin na momma,take wani abu ya taso ya daki zuciyarta ya kuma karyata.
Wannan raunin da ta saba gani a idanun momma......wannan raunin da bata taba ganinsa akan komai ba sai akan akhanan......akhnan din dai?,wanne irin qauna ce haka take mata?,wacce irin soyayya ce wannan?.
"Falaak......ki taimakamin wajen raya wannan zumuncin.........koda bayan raina falaak ban amince ki yarda akhnan ba,koda bana raye ban yarda ki zubda zumuncinku da akhnan ba,dukkaninku abu guda ne....jini daya ne yake zagayawa a jikinku......iyayenku daya maza da mata.....kaman yadda iyayen iyayenku ma daya ne......ki taimaki wannan igiyar karta tsinke da mafi munin tsinkewa" Da sauri falaak ta kama hannuwan momma gaba daya ta riqe da kyau. Idan har da gaske tayi gani me kyau hawaye ne suke neman taruwa qasan idanun momma din nata......me yayi zafi har haka?.
"Kar kice zaki zubda mana qwalla.......zata zame mana masifa momma........nayi alqawari daga yau......kome yaaya zatayi......kome zata yimin ba zaki sake ganin koda bacin raina ba......zanyi saboda ke......zanyi saboda sultane......zanyi saboda zumuncin". Wani murmushi dake cakude da wani irin pain morsa safiyya ta saki,ta jawo falaak jikin ta ta rungumeta tana fadin.
"Allah yayi muku albarka,ya shiryamin ku......ya baku nagartattun mazajen da zasu riqe mana ku bisa amana,su kama hannuwanku su doraku akan tafarki madaidaici". Har can tsakiyar zuciyarta addu'ar momman ke ratsawa,tana jin wani qarin nutsuwa da kuma relief sosai a zuciyarta.
★Cikin tarin nutsuwar nan tata take takowa gaban nanay din. Hannunta dauke da madaidaicin kwanon da yafi kama da akushin da aka zamanantar dashi da ado da kuma tambarin dake nuna sarautar JIMMA.
Kanta a qasa ta qaraso gabanta,ta tsugunna a hankali ta ajiye kwanon gabanta.
"galatoomaa(na gode)" Nanay ta fada cikin murmushi tana duban samee data zame a hankali kanta a qasa ta zauna a gabanta.
Bude kwanon tayi wanda ke dauke da dafaffen maganinta da wasu irin ganyayyaki dake qarawa masu shekaru irin nata kuzari da kyan jiki. Yankin jimma manoma ne na gaske.....manoman da bawai iya abinci kadai suke komawa ba.....aah,hatta da coffee tarin magungunan da qasashen turawake rububin zuwa siyan ganyayyakin su kuma maidasu maganin bature......irin wannan abun ya sanyawa haisam tunanin bude makeken kamfanin sarrafa magunguna......wannan tunanin ya sanyashi saka Aadel da hussam karantar pharmacy.
Bismillah tayi,ta dauki maganin tasha sau uku sannan ta ajiye,samee ta matso ta dauki murfin ta rufe sannan ta maidashi gefe,har a sannan idanun nanay suna kanta.
"Samee" Nanay ta kirata,har cikin jikinta taji kiran,tayi kaman zata dubeta amma ta kasa,saita amsa kiran tana maida kanta qasa.
Maganganu ne sosai a ran nanay da takeso tayi da samee.....amma kafin tace wani abu kira ya shigo wayarta dake aje a gefe,kiran daya dauki hankulansu su duka ita da samee din.
Tana karance da ita,daga yadda taga reaction na samee din ya gaya mata me kiran tun kafin takai ga qarasa miqo mata wayar,ta miqa matan da wani irin sanyin jiki sannan ta soma takawa zata fice don basu guri.
"Koma ki zauna" Nanay ta fada a nutse tana daga kiran sannan ta kara a kunnenta.
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Ya maidawa nanay martanin sallamartata da muryar nan tasa dake cike da wani irin sauti me fusgar hankali da kunnuwa,walau karatun qur'ani yakeyi ko magana yakeyi dakai.
"Akkam jirta nanay?(kina lafiya nanay?)"
"am fine hojjechaa jira alhamdulillah(ina lafiya alhamdulillah)".
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana sauke qafafunsa daga saman lallausan gadon nasa. A duk sanda zai matsa daga inda suke koda na kwana d'aya ne......sai ya dinga jin kamar wani abu zai samesu. Ya sani wannan din tasirin shaidanne......don yayi imani yayi kuma yaqinin ba abinda ya isa ya samu wani bawa saida nufin ubangiji.
"Komai lafiya lau nanay?" Ya sake tambayarta yana dubansa kansa cikin madubin daya koma gabansa ya zauna.
Armless shirt ce a jikinsa sakakkiya,sai wandon daya sanya da duka duka iyakacinsa qaurinsa,ya zarta gwiwa amma baikai idon sahu ba. Dukkan kayan baqaqe ne sidik,cotton masu dauke da tambarin kamfanin LV wato.
"Muna cikin amincin Allah Muhammad".
" Ma sha Allah" Ya amsa mata yana aza hannunsa saman gashin dake habarsa da kuma kuncinsa. Yana wassafa ta yadda zaiyi magana ne da nanay......ta yadda zata kuma fahimceshi da kyau.
"Magana kakeso kayi muhammadu......gayamin me yake faruwa". Lumsassun idanunshi ya lumshe,wani qwataccen murmushi yana subuce masa. Nanay ta daban ce......wata irin uwa da tasha banban da dukka uwayen daya sani,nanay kyauta ce daga Allah,tana iya fahimtar maganar da d'anta yake mata da kowanne yare. Idan yace yare bawai yana magana akan yare na harshe ba,yare na yanayi.....yare na gabbai da kuma yare na motsi.
Qafafunsa ya aza saman stool din dake gabansa,yayi relaxing sosai cikin kujerar sannan ya fara mata bayani.
Batace komai dashi ba harya kammala. Shurun nata har yayi yawan da sai daya kira sunanta.
"Nanay?"
"Tunani nake muhammadu".
" Karkiyi tunanin komai Nanay.....Allah shine me rayuwa.....shi yake tsarewa".
"Muna fata kuma yaci gaba da tsarewar.......wacce qasa ce muhammadu?" Ta tambayeshi a karye.
"Niger agadez". Wani siririyar faduwar gaba ta saukar mata. Kiran sunan qasar hade da garin ya zame mata tamkar wani tuni akayi mata.....tuni a KANTA.....fuskar da har yanzu taqi bacewa cikin idanunta.....kaman yadda sautin muryarta taqi bacewa daga kunnuwanta.
"Agadez muhammadu?"
"Eh nanay......da wani abu ne?" Kai ta girgiza a hankali,saita zarce da jan hankalinsa kamar yadda ta saba,da rufewa da tarin addu'o'i.
"Kada kace zaka rufemin komai bayan tafiyarka......ina da buqatar sanin kowanne hali kake ciki......inaso a wannan karan na zama qawarka kuma abokiyar shawararka fiye da ko yaushe.....Allah ya albarkaci rayuwarku gaba daya".
" Ameen nanay " Ya amsa yana lumshe idanunsa. Haka kawai yaji zuciyarsa kamar tayi rauni kadan,ya sani a yanzun idan aka zubewa nanay zabin ya tafi ko ya zauna.....tabbas da gudu zata zabi ya zauna din,saidai wannan tafiyar nada tarin muhimmanci a rayuwarsu gaba daya.....amma yana sanya ran tafiyar ta zama ta qarshe da zata kasa samar da gamsuwa cikin zuciyar nanay kamar yanzun.
Yana shirin ajiye wayar tasa ya fahimci da shigowar sabon saqon email. Budeta yayi ya kuma wuce kai tsaye zuwa gmail dinsa.
Da sauri ya aje qafafunsa qasa yana bude lumsassun idanunshi da dukka girmansu.
"Welcome to NIAMEY horse race........you're successful registered to the special horse race batch 2 and final.....muhammad ja'afar". Sau uku yana maimaita karanta email din da baisan daga inda ya fado ba......saidai a iliminsa na karatun na'ura me qwaqwalwa,bata yadda za'ayi saqon haka kawai ya fado email address dinsa saida wani dalili.
Omari na ya fado a ransa,sai ya sauka da dukkan nutsuwarsa ya sanya lallausan bedroom slippers dinsa ya fara takawa a hankali ya nufi balcony din da ya baro Omari din dazu a zaune yana qoqarin tattara bayanai.
Sama sama yake jiyo muryar omarin,da alama waya yakeyi,kuma wayar ta masa dadi da gaske,don kuwa yana iya jin fitar sautin dariyarsa.
Yana dab da shiga balcony din ya fahimci conference call yakeyi shi dasu mutallab naseeb khadeem da Amjad,muryar maleek ne kawai bai samu jiyowa ba.
(08187255862 lu'u lu'u novel paying)
"Yauwa......gashinan ma" Omari ya fada yana karkato da fuskar system din saitinsa sanda yake qoqarin zama saman bean bag din dake gefan omari. Zama yayi Normal zama a wajensa......amma a idanun me kallonshi zama ne dake nuna zallar qasaita da sarauta dake yawo a jininsa.
Murmushi Amjad ya saki daga allon system din yana duban haisam.
"Ya zame maka jiki.....yabi jikinka da kyau......yanzun idan nace wani qasaitaccen zama kayi fa ba zaka yarda ba" Dukkaninsu dariya suka sanya,abinda ya sanya haisam fidda wani siririn miskilin murmushi yana kuma gyara zaman nasa daga yadda yake a dazun.
"A'aha......an kuma dai" Mutallab ya fada yana duban haisam din. A wannan karon dole suka sanya ainihin murmushi subuce masa,wanda har sai da jerarrun fararen haqoransa suka bayyana.
"Ba zaku canza hali bane?" Haisam din ya fadi da wani irin nutsuwa wadda tun asali tasa ta bambanta da tasu.
"Indai akan fadin gaskiya ne ba zamu canza ba......ina aka kwana ne?......ba wani labari?" Mutallab ya tambaya yana karbar cup daga hannun matarsa wanda iya hannunsa ne kawai daya miqa ya karba cup din ya bayyana.
Hannu haisam ya aza saman sumarshi yana shafata a nutse,yasan me haisam ke nufi,indai yace ba wani labari?.....to da gaske yake,yana son yaji labarin yayi budurwa......ko ya samu matar aure.
"Akwai labarai" Omari ya fada da sauri sannan ya dawo da fuskar system din saitinsa. Idanu haisam ya zube ma omari,wanda sosai yaji a jikinsa haisam din ya kafeshi ne da wadannan mayatattun idanuwan nasa,shi kuma a yanzun bayajin akwai abinda zai dakatar dashi daga bawa su Amjad wannan labarin,musamman da signal ya harba ya nuna amsa maleek ma ya iso online.
Hannu kawai haisam ya miqe ya bame fuskar system din ya hadeta da juna yana tsare omari da ido bayan ya danne mic din.
"Me kakeson gaya musu?,labarin qanzon kurege?" Yayi maganar yana dage masa dukka girarsa biyun ba yare daya dauke hannunsa daga system din ba. Shima girar ya dage masa masa dariya tana kubce masa.
"Idan kai baka sonsu su suna sonka ai......ya kamata a nema musu tallafin masu yi musu campaign ko zaa dace daya a cikin su suyi wuf dakai.....ko duka biyun ma"
"Biyu.....waye da waye."
"Saami da Menelik". Sosai ya tsaya yana duban omari.