← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 97

Sashe 39

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali tutocin qasar niger suka fara dagawa a gurin,suka soma yiwa gurin rumfa saboda dukka wanda yake kallon wasan ya gama yiwa wasan alqalanci. Bata yadda za'ayi abokin buga wasan ya farke wannan wasan,sun gama miqa wuyan bai iya komai a wasan ba.......akhnan din ita ke da nasara......da gaske ita din kallabi ce tsakanin rawuna.

Wuceshi da tayi da waiwayowa da tayi ta masa wani sign da hannuwanta ya fusgi hankalinsa. Abubuwa guda biyu ne suka tabashi. Na farko sign din data masa alamun raini ne ga duk wanda ke buga wasan horse race........abu na biyu kuma har cikin jikinsa yaji hasashen da yakeyi tun dazun......yanayin da jikinsa yake bashi yaji yana sake tabbata. Tun dazu jikinsa yake bashi wannan din da suke wasan macace,ba namiji bace,yanayin sarrafa dokinta da yanayin sarrafawar mace yayi masa kama.

"Me yasa omari?" Yaji ranshi yana baci da abinda omari yayi masa. A hankali idanunsa suka sauka akan team dinsa.....maleek,mutallab,omari,amjad,khaleed,khadeem. Tutar Ethiopia suka ware me fadi sosai.....kowannensu kuma yana riqe da wani bangare nata,sun kuma dan bada tazara a tsakanin su,abinda ya bawa tutar damar bayyana sosai.

Idanunsa ya zare a hankali,qasaitaccen murmushin nan nasa yana kubce masa,take yadda ya dauki wasan a ransa ya canza cikin qasa da second biyar. Ko basu ce komai ba yasan me suke nufi.....yasan saqon da sukeson aika masa.

A wajensa ba wani wasa bane me muhimmanci ba,wasa ne na samun damar shiga agadez da niger gaba daya ba tare da kowa ya gane ba.......amma a yanzun a ranshi shima yana jin koda hakanne,bai kamata ya bari qasarsa tasha kayi ba,bai kamata qasarsa taji kunya ba. A yanzun su suke wakiltar Ethiopia gaba daya,duk da duka dukansu a filin irgen yatsun hannu ne......amma ya kamata su barwa al'ummar niger suna da tambarin ETHIOPIA.

Ta saki jiki sosai,ta kuma bada amanna tana sarrafa dokinta hankali kwance......saijin iskar wucewarsa tayi,kafin tayi kowanne yunquri kuma ya soma mata nisan daya sanya hankalinta tashi,ta kuma qarawa thunder qaimi.

Murmushi ya sake ajewa ta cikin helmet dinsa,yana iya jiyo sautin takun dokinta,koda bai waiwaya ba kuma yana iya qididdige adadin tazarar data rage da zata iya bata damar taddoshi,don haka sai yayi mata qofar rago kawai.

Tana daf da iskoshi ya sake bata badda mata tunani,ya cilla da wani irin salo daya dauki hankalin kowa,ya sanya filin yin shuru ba tare da kowa ya shirya ba,ya kuma sauya akalar magana da tunanin me sharhin dake can sama yana ganin yadda abubuwa suke so su canza a mintunan qarshe na wasan.

Wani irin wasa da hankali ya soma yi da ita,wani walagigi ya fara yi da nutsuwarta da dukkan qwarewarta. Cikin mintuna qalilan gaba days ya ruda tunanin ya kuma rudata. Tsalle kawai zuciyarta keyi cikin qirjinta,wani irin tsoro taji yana saukar mata. Tunda take bata taba ganin salo irin wannan ba,ya toshe duk wani tunanin ta inda zata cimmashi ma bare ta gotashi......ya toshe duk wata kafa da zata tsammaci nasararta a kusa.

Fargabarta ta sake qaruwa da ganin adadin qananun mintunan da suka rage wasan ya tashi gaba daya..... Tashin hankali ne taji yana lullubeta a hankali,RASHIN NASARA yana daya daga cikin tarin abubuwan data tsana.......ta tsani FADUWA ta kuma tsani A FITA. Ta rayu ne a saman nasara......ta rayu a tudun fifiko,ta bude idanunta ne ta tsinci rayuwarta saman ta wasu......ta tsinci rayuwarta a qulle data wasu.....ba zata taba lamunta ba ace wani can yazo ya kunyatata a tsakiyar 'yan qasarta ba......a gaban talakawansu ba........wannan ya bata qaimin data miqe saman dokin ta kuma bashi wani irin qaimi da ya gigita hankalin dokin ya fita daga tsari da kuma horon da aka bashi.

Yadda dokin yake misbehaving ya mugun tsoratata ya kuma daga mata hankali,ta sake riqeshi da dukka hannuwanta tana jin wani gumi yana tsarto mata,domin ta tabbatar a irin wannan yanayin ta sake ta fadi ba shakka sunanta gawa.

Wani irin abu me nauyi ne taji ya saunar mata sanda dokinsa ya tsallakar iyakar dake tabbatar da kasantuwar nasara a hannunsa. Sautinsu amjad a amsa kuwwar da baisan inda aka samota ba da taken qasarsu ya sake ruda tunaninta da wani irin kalar zallar tashin hankali.

Tayi zaton dokin zai dakata daga inda ya cimma wannan layin shima......amma aah sai ya zarce yaci gaba da shillawa da ita da wani irin gudun walqiya.....daidai da sunan data bashi.

Wannan karon zuciyarta tsinkewa tayi gaba daya da wani irin tsoro,take ta fara gwada dukkan wasu dabaru ja tsaida doki a irin wannan yanayin.

Dabararta ko daya batayi ba,firgici ya sake shigarta,tasan irin wannan yanayin idan doki ya shiga iya controlling dinsa sai Allah. Zuwa sannan hankulan mutane sun fara yowa kanta,musamman hadimanta da masu tsaronta wadanda suke da alhakin kula da lafiyarta.

Sosai hankula sukayo kanta,al'ummarmu da son daukan abubuwa idan suka faru,da son ace sune suka fara dauka ko suka fara haskawa tuni suka fara nadar yadda abun yake kasancewa.

Da wasu dawakan aka soma bin nata dokin da zummar shan gabansa,saidai hakan ya sake zama kamar wani qaimi suka bashi,don tunaninsa yana sake bashi anci gaba da wasanne......ana kuma son cimmasu,yanason cika umarnin uwar dakinsa ne kawai na tserewa duk wata halitta da zata wucesu,bama halittar doki dan uwansa kawai ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 33
____________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*👘🥻

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana goma KACAL!✌🏽*

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*🙌🏽
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________

Cak yayi a gurin yana kallon yadda suke bata kashi a tsakaninsu. Idanunsa ya dauke daga gurin,bacin ransa yana sake ninkuwa.

Tseren doki da mace?,macen ma irin wannan da ba gama sanin yadda tsarin halittar dawakai da yadda ake hora doki da bashi umarni tayi ba?.

"Kaje kace musu su tsaida dukkanin mutanen da suke binta" Haisam ya motsa labbansa yana furtawa omari dake tsaye kusa da dokinsa cikin bacin rai.

Karon farko tun bayan wani lokaci da omari yaga shimfidadden bacin rai akan fuskar haisam din,sai ya juya a hankali cikin sanyin jiki yana nufar gurin masu bada sanarwa a wajen.

"Kowa ya dakata!.....a dakata.....mahayan dawakai duka su fita a filin" Sanarwa data isa kunnuwansu kenan. Da yawansu abun bai musu dadi ba.....suna cike kuma da kokwanton yadda zasu bari dokin yaci gaba da galabaitar da ita. Wasu a cikinsu kuwa tuni sun fara hasashen irin tarin kadara da dukiyar da zasu mallaka sanadin tsaida wannan dokin.

Tabbas sunsan cewa muddin ka zama silar tsiranta.......Allah ne kadai yasan daukakar da zaka samu a wajen sultane of agadez,don haka ba tare da abun ya musu dadi ba kowa ya janye abun hawansa daga filin,filin ya zamana ba kowa,daga dokin nata dake sake rikicewa,sai haisam da yayi tsaye saman nasa dokin yana dubanta.

Idanuwa hankula da wayoyin dake tsakiyar filin suna nadar abinda ke faruwa Allah yayi yawa dasu. Da yawansu kuma sai suka maida daukar LIVE kai tsaye kenan daga hippodrome Niamey,wannan saqon ya bada notification a wayar tarin miliyoyi kuma dubbannin al'umma,kai tsaye kuma ya fada wayar falaak dake kwance cikin sofa tana qoqarin duba tafsirin wata aya a YouTube dinta,notification daga channel din SAUTI HIKIMA ya bayyana daga saman wayartata,sai kawai ta samu kanta da dannawa ta shiga ganin live video ne.

Da fari bata fahimci komai ba,illa dai gudun da dokin yakeyi da matashiyar a samanta itama sai da taji ya tsinka mata Zuciya. Tana shirin sauka sunan yaja hankalinta. Princess khadeeja muhammad hammud(akhnan),sai kuma idanunta suka sauka akan comment da mutanen dake kan live din.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Falaak ta fadi tana fidda dukka idanunta cikin tsananin tsoro,sannan ta sauka daga saman sofa din da wani irin gaggawa tana qwalawa momma kira a gaggauce.

Kusan kowa ya sare a wajen......yana ganin shima bazai iya tsaidashi ba,ganin yana tsaye kyam akan nashi dokin,ko saukowa baiyi ba.

Wucewar farko ya bawa dokin wani sauti da ita kadai ta jishi,sautin da yafi kama da fito saidai ba fito bane.......ya sake wucewa a karo na biyu.......daya hangi yana shirin zagayawa karo na uku,sai ya saki linzamin nasa dokin ya diro daga samansa ya tsaya saman qafafunsa,ya riqe linzamin yana takawa dashi a hankali zuwa wannan iyakar yayi tsaye yana kallon yadda dokin yake tayar da qura yana nufoshi da gudun da ya rage da maganar daya masa dazu daga kaso dari cikin dari zuwa kaso saba'in cikin dari.

Baya kadan yaja,sannan ya zube a qasa ya kafu akan gwiwoyinsa yana daga hannuwansa sama da wani irin yare da yasan ana tsaida dokunan hadaddiyar daular larabawa wato dubai.

Duk da itace a saman dokin......duk da irin birkicewar data gama yi amma hakan bai hanata hasashen yadda nan da 'yan mintuna ko sakanni dokin nata zai murqesheshi yabi ta kansa ba. Tuna iya adadin yadda zai murjeshi ya canza masa kamanni kawai ya sanya tsigar jikinta zubawa. Wanne irin rawar kai ko tsautsayi koma dai tace qarar kwana ce zata sakashi tsaiwa haka gaban thunder a irin wannan yanayin?.
Chapter 39 · 0% Book details