← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 97

Sashe 67

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Morsa......hakeem zinder?......hakeem din abba liman?" Kai morsa ta jinjina tana duban falaak cikin tsakiyar idanunta. Sai falaak din ta zare idonta tayi gefe dashi tana jinjina kai.

"Bai dace da ita ba?.....ko bai cancanta ba?" Morsa tayiwa falaak tambayar da ajiyayyar manufarta. Tanason gwada mizanin hankalin falaak din,tanason kuma gano zurfin nata burin akan kalar nata mijin auren.......cikin fargaba da fatan kada zaqin sarauta ya sanya tabi sahun burika da zabukan 'yar uwarta.

Da sauri ta maido dubanta ga morsa tana girgiza kai.

"Ko kadan morsa......hakeem fa?,ba shine yake zuwa ma niger na daya a gasar karatun qur'ani ba shekara biyar a jere?.......ba shine wanda ya wakilci niger ba a gasar izu sittin da tafseer na duniya ba?......ko ba shine dalibin da yafi kowa hazaqa ba a shekarar daya bar jami'atu ummulquraa?" Kai morsa ke jinjinawa tana jin tashin hankalinta kan kokwanton bin sahun akhnan daga falaak yana raguwa.

"Shine falaak" Sai data saki murmushi sannan tace.

"Ya cancanta morsa.....wallahi yakai......Allah yasa yaa akhnan ta fahimci hakan. Akwai wata nutsuwa ta daban tattare da maza irinsa......" Sai kuma ta dakata da maganan ganin yadda morsa ta zuba mata ido.

"Meye naki burin game da mijin aurenki?" Morsa safiyya ta samu kanta da tambayar falaak kai tsaye.

Wani irin nauyi da kunyar morsa irin wadda bata taba ji ba ta saukowa falaak. Sai ta miqe kawai da dan saurinta tana qunshe dariya tana barin gurin da sauri sauri.

Samun kanta tayi da kifewa saman gadonta,tambayar morsa na mata amsa kuwwa a kunne,sai ta tsinci kanta da tambayar kanta ta hanyar maimaita tambayar da morsa tayi mata yanzu yanzu.

"Meye zabinki?....ko kuma burinki dangane da kalar mijin aure?" Ta maimaitawa kanta da kanta wannan tambayar,wadda ta taho ne gilmawar kamannin hakeem kafin cikin qiftawar ado ya kauce,hoton sheikh haisam ya maye gurbinsa.

Wani matsanaciyar faduwa gabanta yayi,har tana jin sautin bugun zuciyarta cikin kunnenta,ta runtse idanunta da sauri tana jin kamar kowacce kafar jikinta na tsatstsafo mata da gumi. Da hanzari ta miqe ta zauna,ta laluba makunnin qwayayen dakin nata tana qara musu haske,don wani irin qara tsananta bugu zuciyarta keyi da duk gilmawar second da wanzuwar wannan tunanin cikin kwanya da idanunta.

★Cikin babbar saharar data kasance wani guri na debe kewa,wani guri na gudanar da bukukuwa ko kwanan al'ada daya zama wani abu da aka saba dashi cikin yarensu da qabilarsu ta buzaye.

Filinne me cike da sahara.......saidai kuma wannan saharar wani irin farin rairayin yashine mai taushi,amma kuma duk da tsananin taushin nasa tana jin yadda take iya zabga gudu saman raqumin da yake tafiya da wani irin kuzari kamar yana raka tsandaurin qasa bawai yashi ba.

Nishadi takeji sosai,raquminta.......yashin dama suturar jikinta dukkaninsu farare ne,sai wata irin iska me dadi dake kadata hankali kwance.

Tsaiwa tayi saman raqumin maimakon zama saman bayansa saboda dadin gudun da yakeyi da ita,ta ware dukka hannayenta kamar me shirin kama iskar dake wuceta da wani irin gudu,saidai ba zato ba tsammani ta hangeshi yasha gabanta yana nashi gudun ba tare daya ko juyo ya kalleta ba.

Jikinta a sanyaye ta zauna saman raqumin tana sake bashi qaimi don isa gareshi,ta kuma wuceshi.kamar yadda shima ya wuceta,tana gudun tana duban bayansa.

Shiga yayi irin ta cikakken buzu,rawaninsa da wandon yadin jikinsa,saidai kuma maimakon yasa rigar kayan,fara qal din t.shirt ce a jikinsa.

Tana gudun tana qara kusa dashi,amma still bai waiwayo ba bare ya duba ta kusa cimmasa,wannan farincikin ya sakata miqewa kaman dazu tana ware hannayenta,saidai a wannan karon sai taji an cafki hannun nata,abinda ya sanyata juyawa bangaren hagunta inda aka riqe mata hannun don ganin waye.

Saman wani raqumi yake shima,fuskarsa nannade da baqin rawanin da bazaiyiwu ta fahimci waye ba,kwanyarta bata gama daidaituwa ba mutumin dake riqe da hannun nata ya wani finciketa,abinda ya sakata sakin wani razanannen ihu tana duban nisan dake tsakanin raqumin nata da qasa a razane,qarar kuma data sakashi cin wani irin birki ya juyo da raquminsa da akalarsa gaba daya yana tunkaro nata raqumin da kuma mutumin da har yanzu yake niyyar kaita qasa.

Dab da zata isa ga qasa taji ya cafkota,shige yadda ya cafketa a wancan karon da thunder yake shirin kaita qasa. Duk da a razane take amma hakan bai hana haduwar idanunsu ba,wata irin iska ta taso zata yaye nadin dake tsakanin bakinsa da hancinsa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 58

A hankali taja ana janye lullubin jikinta,wanda yayi kusan yi mata daidai da lullubin mayafin da tayi cikin filin sukuwar dawakan,abinda ya sanyata riqe mayafin da kyau,tayi wani juyi daya tilastata bude idanunta da sauri ba tare data shirya ba.

Saman fuskar aisa suka sauka,aisar dake tsaye a kanta tana duban fuskarta cike da mamakin kalar wannan abun da takeyi cikin baccinta,wanda ta tabbatar da cewa ba komai bane mafarki ne.

Maida idanunta tayi yana lumshesu,gabanta yana wani irin dokawa,zuciyarta na wani irin gudu tamkar yadda taji a sadda komai ya faru a zahiri.

Wani matsanancin bacin rai ne taji yana saukar mata,haushin aisa da haushin kanta da kanta yana cikata. Don me yasa aisa zata tasheta a sanda take dab da ganin fuskarsa?,me yasa ita din bata kai hannunta ta yaye lullubin da hanzari ba kafin aisa takai ga tashinta?.......me yasa aisa zata mata haka?,fuskar data jima tanaso ta gani ko hakan zai taimaka mata wajen gane wayeshi?.

"Ki tashi hakanan da wannan mafarkin naki........ko ba'a fadi ba wannan mafarkin ne daya zame miki jiki.......awa guda kacal ta rage baqonki ya qaraso inji mammina......ki tashi birra na jiranki". Blue eyes dinta ta bude a nutse,tana kuma watsasu saman fuskar aisa din.

Muhimmancin mafarkin.......da kuma muhimmancin da ganin fuskarsa yake a wajenta yafi muhimmancin baqon da aisa din ke magana akai,inda aisa tasan muhimmancin abun a gurinta da bata soma tadata ba akan wani mutum can da tuni ta gama yi masa nasa kalar matsayin. A yanzu duk duniya bata jin tana da buri na biyun sanin wayeshi?......waye wannan daya bata dukkan wani record na rayuwarta,ya bata mata kyakkyawan tarihin da take dashi na tabbatuwar NASARA cikin kowanne taku motsi da gasa. Alwashi taci......sai kuma ta cikashi,ko waye shi sai ta bincikashi,sai ta yaye duvet din a hankali tana jan jikinta zuwa bakin gadon ta sauke qafafunta.

"Kada ki dinga wani abu kamar kin damu dani......kamar kuma kin damu da halin da nake ciki" Akhnan ta fadi cikin nuna halin ko in kula,tana kuma qin duban koda sashen da aisa take ne.

Idanu kadan aisa ta zuba mata,ta fahimci a birkice take,a kuma wannan yanayin da take ciki bata buqatar suyi rigima ko kadan. Ta karanci wani abu,duk sanda zai ziyarci mafarkinta,da dukkan zuciya da kuma feelings dinta takejin komai da zai faru a mafarkin kaman a gaske ne.

Bata fiya daukan FADUWA ba.......amma kuma zuciyarta bata da riqo irin wannan. Kafiya da taurin kai tabbas wannan cikin halayenta ne,amma riqo kam idan ta sakashi a cikin dabi'unta tasan da gaske ta mata qazafi.

"Biftu" Aisa ta kira sunanta,sai tayi kamar bata jita ba,ta qarasa gaban masaqalin da lausasan towel dinta ke a jere ta dauki dan madaidaicin ciki tana wucewa toilet.

*HAISAM*

Cikin nutsuwa ya zube dukka idanunsa saman system din gabansa,wadda a qalla kusan awa biyu ya kwashe a zaune din.

Sun gama tattaunawa dasu beena,wanda kowannensu yake wani sashe na daban cikin niger din don baza komarsu yadda ya dace. A yanzu da hussam yake waya,wanda kusan duka tattaunawar akan kamfanin turarensa ne da a yanzun suka samu labarin fitar wani qamshi dake shige da nasu a kasuwa.

Numfashi yaja yana lumshe kyawawan idanunsa masu yawan eye lashes,ya sakeyin relaxing yana ci gaba da duban hussam.

Ya fara gajiya da wannan tarin complain din da tun dazun yaketa abu daya,baisan me yakeso ba kuma.

"Hussam" Ya kirashi da wannan coolness din nasa.

"Obbo.....Allah obbo ka..."

"Ya isa.....,magananka yayi tsaho da yawa haka,da nazari nakeyi zuwa yanzu na karanta fuula(pages) masu yawa......maimakon hakan ka bata duka wannan lokacin mana wajen binciken sabon scent mana?" Ya qarasa maganar da sigar tambaya wanda kai tsaye hussam yasan umarni ne.

Kai hussam din ya jinjina,yana nufin cewa wani abu sallamarta da muryarta ya sauka a kunnensa.

Ci gaba da kallon screen din haisam yayi ba tare daya ware yatsunsa dake cikin na juna ba. A hankali taci gaba da takowa tana jin yadda sautin bugun zuciyarta yake qaruwa.

Tunda ta iso dab da gurin taji sassanyar muryarsa na fita ta system din radau kaman yana a wajen. Wannan sautin da take kwana ta kuma tashi da kewarsa. Ba'a maganar kyakkyawar fuskarsa data mata wani irin nisan da ba wanda yasan me takeji?,ya kuma takeji?,daga ita sai Allahnta kawai.

"Ani dagadheera saamee(na manta samee)" Hussam ya fadi yana waiwaya kadan ya dubeta,abinda ya bawa haisam daman hangota kenan.

Kamar kullum cikin jilbab dinta da yake yawaita dacewa da fatarta da kuma doguwar fuskarta,ma'abociyar siririn hanci,sak kamannin kyawawan 'yammatan qabilar oromo. Kanta a qasa,saidai hakan ya qaryatata. Ga duk me zuzzurfa da dogon nazari irin haisam din,kai tsaye zai fuskanci hankalinta yana fusguwa ga son kallon screen din system din hussam din,saidai tana qoqarin hana kanta faruwar hakan.

"Daqiiqaa tokko naaf kenni(bani minti daya),zamuyi sallama da captain obbo" Ya fadi tare da waiwayowa gaba daya yana duban haisam din.

"Obbo......ina ganin zan siya ticket kawai,zan wuce addis ababa gobe da safen.....zamu tura wasu sample na hadin sabon scent zuwa china.......akwai yuwuwar na tafi china din da kaina,akwai yiwuwar mu tura". Kansa yake gyada masa a nutse,kafin yace.

"Ka sallameta tukunna". Yayi maganar yana masa nuni da idanunsa
Chapter 67 · 0% Book details