Sashe 18
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannu tasa ta dafe kanta jin ana ci gaba da knocking din kamar ba'a san dakinta ake qwanqwasawa ba. Ta miqe a fusace tana wantsalowa daga saman gadon,cikin ranta takejin ko waye wannan yau yake mata wannan gangancin ya kade a wajen ta.
Mutum biyun data gani a tsaye a gabanta sun kaure da magana a tsakaninsu,wanda maganar da sukeyi ma ta sanya basuga ta bude qofar ba. Bataji hayaniyarsu ta ciki ba don qofar irin qofofinnan ne da ba zakaji hayaniya daga waje ba,hakanan daga cikin ma kaima ba za'a jika ba.
Aisa da Shehinaz........sashenta.......'yan uwanta kuma aminanta. Idanunta da suka qara girma saboda bacci ta zuba musu,ganin bilhaqqi hira suke kaman wadanda suka shekara basuga juna ba tare da sun kula da fitowarta ba.
Ta shiga uku.....ciwon kanta guda dayar ta dawo,wadda wani lokaci har tafi aisa daga mata hankali. Baqar buzuwar da kalar fatarta tasha bamban da tasu fatar ita da aisa,saidai akwai wani sirrantaccen kyau itama da take dashi qasan chocolate colour skin dinta.
Shehinaz dince ta fara lura da an bude qofar
"Elle a ouvert la Porte(ta bude qofar)" Ta fada tana fincikar hannun aisa. Matsawa gefe tayi tana basu hanya sanda suke wucewa ciki abinsu suna mita
"Tu pionces comme un mort(kina bacci kamar gawa)" Still Shehinaz ta sake fadi tana yin ciki abinda. Goshinta ta dafe kawai tana ci gaba da jin hargaginsu sanda suka isa dakin. Wannan me shegen faransancin tasan ta kade a hannun ta itama,don ta tabbatar aisa ta gaya mata abinda tace data bata labarin abinda ya hadosu da Jamaal.
Daidaita kanta tayi sannan ta juya tana komawa dakin.
"Wai don Allah bakiji toc toc namu ba?". Scarf dinta kawai ta dauka dake ajiye saman dressing mirror ta daure sassalkan gashinta.
"Biftuuuuuuu" Shehinaz ta sake qwala mata kiran da sai data dakata daga shiga toilet din ta waiwayo ta ware mata blue eyes dinta
"Ban bude bane Shehinaz?......Fiche-moi la paix(ki qyaleni don Allah)" Ta qarasa fadi kaman zata saki kuka. Bata doguwar magana ko hayaniya me yawan idan ta tashi a barci,dukkansu sun sani haka yanayinta yake,amma yanzun gasu sun sakata a gaba zasu addabeta,kuma ta fahimci plan ne.
Samu tayi ta wuce bandakin ta barsu a nan,a gurguje tayi tsarki ta daura alwala,tana mamakin baccin da tayi haka,har yayi nauyin da ko alarm dinta ma har yayi kuwwarsa ya gama bata ji ba,na qarshenne ma ta jishi kamar cikin mafarki,kuma ta miqa hannu ta kashe taci gaba da baccinta. Muddin ta gaji da yawa ko kuma ranta a bace yake to takanyi nauyin bacci,don haka ba kowanne guri take sakin jiki tayi bacci sosai ba.
Har ta fito ta shimfida abun sallah Shehinaz da aisa basa jin kawunan juna. A nutse ta bada faralin sallarta,wanda tana dab da idarwa kira ya shigo wayar Shehinaz din ta dauka,abinda ya kawo ragin karadinsu cikin dakin.
Zaune kawai tayi saman abun sallar itama,dakin sai ya zamana ba sautin kowa saina Shehinaz dake amsa waya can qasa qasa,don haka aisa ta jawo remote ta fara canza channel daga makekiyar tv din dake maqale a bango.
Sannu a hankali takai channel din iman. Wani program akeyi da wani matashin malami da a kallo daya zaka fahimci yadda ilimin addini ya ratsatashi. Ajjiye remote din aisa tayi tana maida hankalinta kan tambayoyin da akeyi masa. A hankali maganganunsa suka fara shiga kunnen akhnan,saita daga kai ta dubeshi sannan ta tabe baki.
"Zaki iya kashemin wannan tv din ko ki maidashi a bluetooth daidai kunneki?". Kai aisa ta dago ta zaro idanu waje tana kallon akhnan. Ta rasa wanne irin alaqa ke tsakaninta da duk wani matashi da zaiyi kamanceciya da malami ko me ilimi na addini kamar haka,karàtuttuka da lectures duka idan tana wani abun ka kunnashi a gabanta yana zame mata kamar takura ce.
"Baki da Imani........télé dinne zan sakawa Casque audio?" Kafada kadan ta daga cikin basarwa.
"Eh.....II semble que vous vouliez le regarder(naga kamar kinason kalla ne)".
"C'est intéressant(yana burgeni)" Ta amsa mata kanta tsaye. Maganar ta fusgi hankalin akhanan,har ta waiwayo da sauri tana duban aisa ba tare data shirya ba.
"Shi wa?" Ta qara tambayarta tana watsa mata manyan blue eyes dinta
"Shi malamin" Aisa ta fada kanta tsaye tana duban idanun akhanan dake bayyana zallar mamaki. Shuru ya ratsa tsakaninsu a dakin,har hakan ya dauki hankalin Shehinaz dake waya,sannu a hankali akhnan ta motsa ganinta akan aisa sannan tace.
"Kuma kina nufin abinda kika fada dinnan har zuciyarki?".
" Yes......har qasan zuciyata" Aisa ta furta tana bata tabbaci. Wani abune ya tsargawa akhnan har qasan zuciyarta,kamar ba zata dauke ido daga kallon aisa ba,kafin daga bisani ta janye duban nata tana rasa kalmar da zatayi magana da aisa da ita.
"Ki fahimci wani abu fa.......wani boyayyen sirri ne cikin soyayya da auren malami ko auren ma'abocin sanin ilimin addini........akwai wani alfanu da wani boyayyen sirri da sai wanda ya auresun kadai yake ganewa.......su na dabanne......."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kawai taji akhnan ta saki. Sosai mamakinta ya ninku sanda taji tana maimaitata ba tare data juyo kuma ta kalleta ba. Kalmar nada wani irin girma da nauyi a qirjin dukka musulmi,wannan ya sanya Shehinaz yanke wayar da takeyi ta dubesu tana rarraba ido a tsakaninsu adan rude.
"Lafiya?,Que se passe-t-il?(me yake faruwa?".
" Aisa zakiwa wannan tambayar,nikam tafi qarfina" Akhnan ta fada tana tsugunnawa ta kwashe abun sallarta tana zare kayan sallar jikinta. Harga Allah har zuciyarta takejin maganar aisa. Bata mata fata ko sha'awar auren irin mutanen nan sam sam,ba aisa kawai ba.....duk wada take qauna yake kuma tare da ita,don bata hangi komai a cikin hakan ba face wani gagarumin ci baya da koma baya,bataga kuma abinda za'a tsinta a cikin hakan ba.
Tana jinta tana yiwa Shehinaz bayani da dukkan gaskiyarta,kawai saita koma ta zauna saman Beanbag chair ta zauna tana zurawa lausasan qafafunta socks saboda sanyin marbles din da takeji suna shigarta. A gefe daya tana ci gaba da jin maganganun aisa dake qara kare muradinta da kuma hujjojinta,saidai daga ita har Shehinaz ba wanda yace komai,batasan dalilin Shehinaz nayin shuru ba.......amma tata hujjar takaici ne da baqinciki kawai fal qasan ranta,sai kawai taja wayarta ta kira birra tace ta shigo mata sa fruit zata sha,ta maida jikinta cikin bean bag chair din ta kwantar abinta ba tare data sake tankawa kowa ba har birra ta shigo da nau'ikan fruit din da tasan akhnan din na ta'ammali dasu saman wani kyakkyawan tray. A yayyanke suke cikin wani irin yanayi da tsarin da zai baka sha'awa matuqa. Kusan dukka sun haddace wani tsari nata dama abinda tafiso tafi kuma muradi.
"Za'a dora dîner........ko kina da buqatar a dora miki wani abun daban?" Kai ta girgiza a hankali tana karbar spoon da pork din hannunta dake nade cikin fararen papers.
"Ku dafa iya cikinku......" Kai ta gyada,tunda taji ta fadi haka hakan yana nufin ba'a gida zataci abincin dare ba,ko kuma ba zataci abincin daren bama duka. Duka tana iya yiwuwa,wani lokaci tana fita French restaurant taci French cuisine,musamman irin taste da aroma nasu da tayi missing. Tayi zaman French na shekaru biyar,don haka da yawa wasu abubuwan nasu ya zauna mata,tana kuma wasu abubuwan irin nasu.
"Kin fahimci dalilai na ko?" Aisa ta jefawa akhnan tambayar. Tsaida kankanar data dauko da pork tayi ta daga idanu tana dubanta.
"Wa?"
"Ke mana" Aisa ta fada tana dariya qasa qasa,da alama akwai manufa a dukka abinda tayin.
"Bansan ma magana kikeyi ba ai bare na samu lokacin saurara,Ce que je sais,c'est....(abinda na sani shine),yaranki saisun tsine miki sunyi Allah wadai da uwarsu data rasa uban da zata zaba musu sai kidahumin uba" Baki aisa ta bude,yayin da Shehinaz ta miqe da wayarta a hannu kawai tayi qofa.
"Biftu......Es-tu sain d'esprit?(kina cikin hankalinki kuwa).......kinsan su waye kikewa kallon kidahumai.......?"
"Continuez(ci gaba)" Ta fadi tana miqewa tsam itama ta dauki farantin ta fita duk da batayi niyya ba,saidai ba abinda maganar aisa ke saka mata sai bacin rai. Idan taso jan musu aisa ta iyashi,idan taso jan magana ma haka,saidai ka sakar mata ko ka biye mata kuyita yi,abinda kuma ita sam bata iyaba kenan,wannan sai ita sa Shehinaz. Wani lokaci idan suka fara harji takeji kamar kanta zai dauki ciwo,bata iya dogon magana bata kuma iya bada haquri ba,saidai ta tattare 'yan kayanta kawai tabar musu gurin,idan sun qoshi don kansu sai su bari.
"Dadina dake mugunta.......baki iya raba husuma ko gardama ba ko za'a yi kisa ko?" Shehinaz kan fadi tana jifanta da harara,hararar da yawancin lokutama batasan tanayi ba,don ba kasafai take daga kanta ko ta bata hankalinta ba. Wani lokacinne idan 'yan maganar suna kusa takance
"Tunda ni na sakaku dole na tashi hankalina wajen hanaku" Daga wannan sai taja bakinta ta qara bamewa.
Itakam duk duniya idan kanaso kaga nutsuwarta da bada dukka attention dinta kan abu to abinda ya shafi aikin kamfaninta da office dinta ne.....wannan kam zata iya kashe masa ko awa nawa ne......sallah kawai ke tashinta.
"Ina da baqo gobe.......na kira ana na gaya mata......sannan na gayawa baba soulaimane shima" Shehinaz ta fada tana qoqarin saka wayarta a charge.
"Allah ya kaimu.....zaki baro,Allez-vous quitte le bureau tôt(zaki bar office da wuri?)" Kai ta jinjina
"C'est Exactement ce que je pense(haka nake tunani)" Ta amsa mata tana kulle wayar gami da nufar hanyar kitchen don ita din mutum ce meson girke girke. Zai wahala ayi wani girki bada ita ba,wannan ya sanya ta iya girke girke da yawa,aisa ke biye mata wani lokaci itama tana kwaikwayar wani abun,takance.
"Bari mu dinga pratique......naga mazan yanzun sun baci don girki". Sau da dama tana gefe tana aikin office abinta. Itakam koyon girkin yana cikin abu na sahun qarshe da bata taba tunanoshi hasasoshi ko kawoshi cikin rayuwarta ba. Tana ganin meye hadinta da girki?,ba girki kadai ba,kitchen dinma in general bata da wata alaqa dashi. Ba zata iya tuna lokaci na qarshe data taba koda dora ruwan zafi da kanta ba balle ayi maganar girki. Duk wata hidima da zatayi ko zata taso mata tana da masuyi mata,so ko a hasashe.......ko a mafarki bata taba kawo girki cikin agendas na rayuwarta ba.
★★★
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*