← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 97

Sashe 8

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki saka buhaina ta dubamin yiwuwar gabawa da sultane". Maganar tadan bawa armelle mamaki sosai. Baqon abune a wajenta ganin sultane ko kebanta dashi,musamman a irin wannan lokacin na yammaci......a kuma ranakun da yake samun yawaitar baqi qwarai fiye da kullum,amma sanin yanayin da ake ciki ya sanya bata tunasar da ita akan komai ba ta saka kai tana ficewa zuciyarta ita kanta cike da alhini da kuma dogon nazarin da taso ace momma ta tambayeta wani HASKE Ko ta shigo da ita ciki,to amma ita dimma tana tsaiwa ne kawai inda aka buqata,duk da dadewa da kuma tarin amincin dake tsakaninta da MORSA SAFIYYA(momma).

Cikin kowanne bugawa da jini da kuma zuciyarta sukeyi ba abinda takeji a cikin ruhinta sai wani irin tashin hankali. Khadeeja ce?,khadeejan juhaifanta......jinin JUHAIFA ne.....jinin juhaifa ne ake waannan wasan kuran dashi?......idan ta zuba idanu gudan jinin juhaifa qwaya data tallin tal data bari a duniya ya wulaqanta haka shin TAYI ADALCI?.......anya bata zama BUTULU ba?,anya batayi cin amana ba?. Jinin juhaifa ya zarcewa duk wata kima da martaba a gurinta da idanunta......zatayi dukkan wani yaqi......zatayi kuma duk me yuwuwa na ganin bai wofanta ba.

Ko sau daya ko kuma daidai da qiftawar idanu..........bata taba daukan iqirarin MAMMINA da wasa ba. Wani irin kalamai ne da suka yiwa zuciyarta kyakkyawan dashe,irin dashen da girgizarsa ko tabuwarsa ba abu bane mai sauqi. Ta aminta da dukkan zuciyarta wani babban yaqi ne ya shigo rayuwarta,tun a wancan lokacin ta sani.......jikinta kuma yake bata cewa akwai wani shiryayyen abu da zai iya faruwa,ko a kusa ko a nesa........sai gashi a nesan da bata taba kawo irin wannan nesan ba.

Duk yadda zuciyarta ke bata shawarar ta zauna ko zata hutar da qafafunta ko hakan zai kawo sassauci ciki rai da gangar jikinta amma ta kasa. Tana jin mintunan da aka diba kafin ta samu amsar yiwuwar ganin me martaba din kamar sunyi wani mugun tsahon da suka kusa daidaita da tarin watanni.

Kasa juriyar ci gaba da tsaiwa cikin falon tayi,don haka saita matsa da dan zafi zafin nama ta sanya lausasan takalmanta ta gyara lullubin dake saman kanta sannan ta soma fita a parlor din.

Barka da fitowa hadimanta suke mata cikin sadda kansu qasa,ta daure zuciyarta qwarai wajen ganin ta amsa musu yadda ta saba,duk da cewa ruhinta da gangar jikinta ba yana a tare dasu bane sam sam.

"A dubomin buhaina a duk inda take.........a gaya mata ta shaidawa sultane ina nan ina sauraron ganawarmu" Morsa safiyya ta fada tana hade tafukan hannayenta guri daya,cikin qoqarin controlling abinda takeji yana mata kaikawo a zuciya.

"An gama" Nanay ta fada,Daya daga cikin hadimanta dake da wani irin zafin isar da saqon morsa safiyya din.

Wata nannauyar ajiyar zuciyar ta sauke tana janye jikinta da idanunta daga jikin window din,wanda yake tuna mata da abubuwa masu tarin yawa da suka shude. Daidai lokacin da hadiman guda biyu ke shigowa buhaina da nanay.

Daga bayanta suka zube cikin girmamawa kamar yadda suka saba,sannan buhaina ta fara magana.

"Allah shi riqa miki.......me martaba sultane yana cikin baqi masu yawa.........duk da kusan da yawa ya sallamesu........amma gajiya bana tunanin zata barshi ya ganki a dai.........". Wani irin suka maganarta ta yiwa zuciyar morsa safiyya,zafin daya ratsa zuciyarta ainun. Ba al'adarta bace ganin sultane barkatai irin haka ba........hasalima ita da sultane din akan dauki kwanaki uku ba tare data sanyashi a idanunta ba,duk kuwa da cewa miji yake a gareta kamar yadda mammina take mata a wajensa. Lokuta da dama a duk sanda zata buqaci ganinsa a irin wannan yanayin,tana yin hakanne bawai don buqatar kanta ko wani kebantaccen abu da ya shafeta ba,kusan dukka buqatar ta mutum daya ce wato akhnan,duk da cewa a idanu da zuciyoyinsu basa kallon hakan akan buqatar kansu face buqatar qashin kai.

"Daga wanne lokaci zai iya shiga lokacin taqaitaccen hutu?". Saida buhaina tayi qasa da kanta sannan ta amsa mata.

"Nan da mintina biyar zuwa goma ranki ya dade".

"A daukomin rigar waje" Tayi umarnin tana soma takawa a hankali tana nufar qofa,abinda ya gaya musu cewa tana da buqatar fita kenan.

Ba jimawa mariya ta dawo da rigar da sassarfa,ta rusuna tana yafa mata,yayin da morsa safiyya ta qarasa sakawa sannan ta qarasa lullube jikinta da wani irin yanayi dake nuna zafin da takeji a zuciyarta dama jikinta gaba daya,suka fara takawa suna ficewa ita da mutum uku cikin hadimanta.

Duk taku daya da takeyi tana fuskantar sassan sultane zuciyarta qara zafi take mata. Kusan bayyanarta a wajen a irin wannan lokacin wani irin baqon abune da ba'a saba da ganinsa ba. Mutum ce ita da zaka dauki dogon zama cikin masarautar baka sanyata cikin idanunka ba......mutum ce da zaka jima a cikin masarautar bakaji tace komai dangane da komai ba.......idan nace komai ina nufin umarni hani ko kuma zartaswa. Kaf ta tattara hankalinta da rayuwarta ne dama duk wani ikonta a kan gidanta KADAI. takan fadi lokuta da dama idan ta zauna hira da hadimanta.

"Ba kowanne abu bane yake da buqatar kayi magana sharhi ko tsokaci akai ba. Wasu abubuwan zaifi kyau kayi shuru a kansu,domin shurun yafi zame maka ado kima da Kuma kwarjini hadi da cikar kamalarka a rayuwa". A tare da ita sun koyi abubuwa masu yawan gaske,a tare da ita sun dauki wani irin darasi da babu shi a kowanne sashe na duniyarsu.

Kanta tsaye ba kuma tare da jiran umarni daga dogarawan dake da wani irin shiga tsari da horo na musamman ba,wadanda ke tsaron qofar da zata sadaka da kebantacciyan parlor da yafi kama da wata fada me zaman kanta ta doshi qofar kai tsaye,abinda ya tilastawa duk wani wanda yake gurin janye ganinsa kame kansa da killace ganinsa daga kanta.

Koda ita din ba daya daga cikin matan dake da daraja ta farko cikin qasar agadez ce ba.......ita din ta musamman ce,da wata irin kamala da kwarjini da sassanyar nutsuwa suka yiwa tufafi. Tana da wani irin girma a zukata da kuma idanunsu.......tana da wani irin matsayi da KAME KAI da tsame baki daga dukkan al'amuran da basu shafe ka ba dama wadanda suka shafekan suke siyawa dan adam.

Ba su kadai ba.......su buhaina dukka da ta taho dasu suma nan din shine qarshen inda aka lamuncewa takawarsu,don haka ita kadai ta tsoma qafa a palace din da ta kebanta ga sultane muhammad hammud da kuma iyalinshi a halinsa.

Hankali kwance,cike kuma da wani irin nutsuwa ta fidda kayan jikinta ta musanyasu da wasu kaya da birra ta ajiye mata. Dogon wando ne leggings me bin jiki sosai,sai gown dinsa me dogon hannu data zauna das a jikinta ta kuma bude sosai daga qasa. Birra tasan zabinta,kusan tana cikin mutum na uku data gama sanin komai da take so,duk da har yanzun ita kanta tasan tabar birra dinne kawai ta san abinda taso ta sani din.

Sassan nata babu motsin kowa,domin kuwa sanannen abu ne.......mutum ce ita ba koda yaushe take da buqatar mutane a kusa da ita ba,wannan ya sanya dukka hadimanta suke tsananin kiyayewa da dukkan abinda suka san bata so,domin ita din zuciyar SULTANE ce,HASKEN AGADEZ kuma.

Hankali kwance ta zaba ta kuma nutse cikin jerin sofas din dake parlor din,sai a lokacin hankalinta ya koma kan wayarta,don tayi imanin wannan matsalar ta gama da ita kuma. Ta sani......bawai abun ya qare bane......bawai za'a tsaya iya haka bane.......amma har cikin zuciyarta take gayawa kanta da kanta zata yiwa tufkar hanci.....zata kuma daqile afkuwar hakan a nan gaba.

Ta gaji da ganin fuskokin mazan da suke nuna kansu a gabanta. Mazan da zuwa yanzu ba zata iya riqe lissafin adadinsu ba,har yanzu tana ji a ranta BASU KAI BA,wannan alfarmar tata har yanzu ba wani DA NAMIJI da ya samu nasarar taka koda matakin farko na samunta.

Sashen adana lambobi ta nufa(contact),taci gaba da dubawa a nutse da wani irin aji daya zame mata dabi'a koda ita daya ce a waje.

Haleesha shine sunan data tsaya akai,ta kuma danna kira sannan ta sanya wayar a handsfree tana ajiyeta a hannun kujerar kamar yadda kusan dabi'arta ce hakan. Ba kasafai take sanya waya a kunne ba......muddin hakan ta faru lallai duk wanda take magana dashi din wani mutum ne muhimmanci qwarai da gaske a wajenta,kamar sultane mammina aisa shehinaz da ire irensu.

Bugu biyu rak aka daga wayar daga daya sashen,saboda sanin illa barin kiran ya zama miscall da zai iya jawowa mamallakiyar number.

"Barka da yammaci Madame......" Aka fadi da sautin dake nuna tsananin girmamawa. Sai da taja fasali tana duba dogayen yatsunta,ta lumshe idanunta sannan ta budesu kafin tace

"Ya kike haleesha?"

"Ina lafiya Madame" Ta amsa cikin jin dadin nuna qanqanuwar kulawarta a kanta.

"Yayi........an kammala karbar designs din?"

"Eh Madame......ke kadai ke jira". Kai ta jinjina,tana jin zuciyarta da hankalinta gaba daya ya koma niamy

"Wannan tafiyar ce ta kawomin tsaiko......amma ina hanya gobe in sha Allah". Kai haleesha ta jinjina tana mamakin dawowarta da wuri.

"Allah ya kaimu Madame.....don sosai kasuwa take buqatar kayanmu".

"Tout se passeda bien in sha Allah(komai zai daidaita in sha Allah,zan kum duba demande(request) da kika turawa enterprisé".

"Je vouse remercie Madame(na gode madam)" Haleesha ta fada cike da farinciki.

Bata sake cewa komai ba ta gintse wayar,ta maido hankalinta cikin falon tana furzar da siririyar iska daga bakinta.

Ita kanta tana mamakin yadda take jin qirjinta wasai,duk da lokaci lokaci tana dan jin tunanin yadda sultane zai tunkareta da batun hambarar da lamarin altaab da tayi,duk cewa tasan bata da wata matsala ko damuwa game da sultane....don duk abinda takeso shine cikar muradinsa......amma ita din bataso ta sanyashi ko yaya yaji ba dadi akan wani mutum da bata jin darajarsa da d'ara ko ina ballantana ya zama silar sosuwar ran sultane.

Irin so takewa sultane da mammina.......wani irin tattalin muradi da kuma farincikinsu takeyi. Murdinta na cika burinsu akan duk abinda suka sanya interest akai daban yake a zuciyarta......sai kuma akayi katari su din suka kasance mutane ne masu fifita maslaharta da muradinta akan nasu.

Waya ta jawo,ta saka wasu taqaitattun lambobi don yin kira bangaren hadimai da bayi,wanda cikin qasa da mintina biyar birra ta bayyana.
Chapter 8 · 0% Book details