Sashe 50
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Madarar da falaak din ke miqa mata tabi da kallo.
"Karki ce ba zaki sha ba.....kyauta ce daga 'yar uwa zuwa ga 'yar uwarta" Ta fadi tana narke murya da fuska kaman zata saki kuka. Sai bata sake cewa komai ba,ta saka hannu ta karba,ta kai bakinta ta soma sha.
Sak irin madarar da tafiso fiye da kowacce,tayi mamaki kadan na yadda akayi falaak din tasan haka,amma izzarta ta hanata ta tambaya. Abun baiwa falaak ciwo ba,tunda har gashi tana sha,tunda har gata a gabanta tana mata fira kuma tana saurarenta,hakan ya sanyawa falaak hope me yawa akan wataran komai zai canza kamar yadda momma keda buri da kuma fata.
"Momma nata kewarki......tunda akace kinzo taketa shirin tarbarki,tana ta duban hanya duk da batace komai ba,amma nasan tana jiran ganin shigowarki ne" Falaak din tayi qarfin halin fada.
Yadda taga fuskar akhnan din ta gimtse sai taji abun ya tabata,kafin kowannensu yakai ga cewa komai motsin mutum daga baki qofar yaja hankalinsu.
Mammina ce ke shigowa a nutse idanunta akan falaak,kafin ta janyesu ta maida kan akhnan sannan ta azasu akan cup din hannun akhnan din,kafin ta kuma saki murmushi tana cewa.
"Yauwa......gwara da kikazo ai......ta dalilinki tasha madara kenan?" Mammina ya fadi tana zama gefan akhnan din.
Kai falaak ta daga a sanyaye tana duban mammina din kafin ta maida idanunta akan akhnan wadda ta dora kanta a hankali saman kafadar mammina,abinda zai gaya maka zurfin shaquwar dake tsakaninsu.
Tsam falaak ta miqe tana ajiye cup din nata hannun.
"Zan qarasa ciki yaa biftu......me zance da momma?". Maganar ta saka mammina daga kai ta kalli falaak,shurun akhnan kuma ya zama kusan shine amsa ga falaak,sai mammina tayi murmushi.
"Tunda sultane yayi kiranta hankalinta yake a tashe,nayita fama da ita ta shiga ta gaidata amma taxo daki ta wani narke kaman wadda akace yankata zaiyi.....karki damu zasu iya haduwa yanxun nan,don naga jakadiya asabe ta tafi kiranta". Kai falaak ta jinjina a hankali sannan ta juya ta fice.
"Ki tashi ki shirya......sultane ya zauna" Maganar data saka akhnan daga kanta babu shiri tana duban mammina. Meye hadin kiranta da sultane yayi da kuma kiran momma da yayi?,hakan na nufin ganinta da zaiyi a gaban momma ne?.
Tsaf mammina ta karanci komai ta idanunta,saita girgiza mata kai.
"Banaso kiya wani ba daidai ba......banaso ki musanta duk wani abu da nace kiyi".
" Indai ni da sultane da ita ne......kiyi haquri mammina......bazan amsa kiran sultane ba" Tayi maganar wani zafi yana tasowa daga qasan zuciyarta. Murmushi mammina ta saki dan qarami.
"Harda ni...harni sultane ya kira" Maganar data bawa akhnan relief kenan.
Hannunta yana cikin na mammina din sanda suke shiga Qawatacciyar shiyyar sultane din dake da wani irin zubi da ado na daban. Cikin wata doguwar riga ruwan madara ta shirya,wadda qasanta yake a bude sosai yake kuma sharar qasa. Hawa biyu ne da ita,don haka ta saman gabanta a bude yake,saidai an mata wani irin Qawataccen aikin hannu.
Daidai bakin dakin hutawarsa jakadiya asabe ta dakata tana ja da baya gami da rusunar da kai,yayin da mammina sukaci gaba da takawa ciki ita da akhnan da takejin zuciyarta kamar zata fito.
Bata iya yin sallama ba,sai sallamar mammina data wakilci tata. Cikin muryar sultane ta tsinci muryar momma din,wadda ke zaune daura da tuntum din da sultane ya dora hannunsa dake dauke da ayabar da momma ta bare masa tana kuma yanka abarba taba ajiyewa a plate din dake tsakaninsu.
Janye idanunta momma tayi,bata fiya son kallon mammina a tare da akhnan ba,yawan kallon yana qoqarin wargaza mata duk wani kafiya da cijewarta da kuma tsarinta na shekara da shekaru da take tafiya kuma take aiki a kai.
"Sannu da aiki" Mammina ta fadi tana zama daura da momma din cikin sakakkiyar fuska me nuna kulawa da damuwa da mutum.
"Yauwa" Ta fada tana dauraye hannunta adan wani qoqo na zamani dake gefe ba tare dako ta kalli fuskar mammina ba.
Janye ido akhnan tayi daga kansu. Har abada morsa safiyya bata da wani buri illa ta wulaqanta mammina?,akan meye ne?,me mammina tayi mata haka?. Me yasa mammina ba zatayi zuciya ba?,me yasa ba zata haqura ba ta daina damuwa da dukka lamuranta ba?. Tunaninta ya tuqe sanda ta zube gaban sultane tana fadin.
"Barka da warhaka bappi.....barka da wannan lokacin"
"Yauwa barkanki" Ya fadi a yana dubanta kafin ya janye idonsa daga kanta ransa yana motsawa.
"Barka da dare" Akhnan ta fadi tana waiwayawa sashen da momma ke zaune ba tare data kalleta da idanunta ba.
Murmushi sosai ya wadata a fuskar momma din,cikin sakakkiyar murya dake nuna kulawa ta amsa.
"Barka kade biftu,ina fatan kina lafiya?"
"Alhmdulillah". Ta fadi har qasan ranta bataji ita ko kulawarta suna burgeta.
"Ya baku taho dukkaninku ba?.....kamata yayi ace dasu aisa din kukazo ai ko?" Ta qarasa maganar tana maida dubanta ga sultane.
"Ba buqata,hakanma ba laifi" Ya furta yana turawa akhnan plate din kayan marmarin.
Maganar morsa safiyya qwaya daya tak ta d'arsa wani abu saman zuciyar mammina. Nazartarta takeyi kaman yadda zargi me girma ya d'arsu a zuciyar akhnan. Taji a jikinta duk wani kira da sauran b'urbushin fushi da take gani daga fuskar sultane yana da alaqa da momma din.
Wai me yasa har abada matar ba zata daina bata ciwon kai ba?,me yasa ba zata daina zama silar bacin rayukanta ba?. A hakanne zata dauki duk wani karatu akan girma da martabarta kaman yadda mammina da sultane sukeso ta dauka?.
Abinda ya qara birkita mata tunani shine......hira da sultane ya fara yi shida momma din. Wani abu ya motsawa mammina,ta gyara zamanta cikin sakin murmushi tana jefa bakinta cikin hirar tasu.
Bata taba yarda ta zama saniyar ware a gaban sultane,bata kuma yarda da kowanne irin abu yayi mata shamaki ko katanga tsakaninta dashi ba......kamar yadda bata laminci ki na second daya hankalinsa ya juya daga kanta ba.
Cikin second biyar kacal sultane din ya jefa tambayar data saka kowacce jijiya tsinkewa daga jikin mammina da akhnan.
"Me yasa ba'a shaidamin shirya tseren dawakai guda biyu ba da aka gabatar a Niamey cikin satittika biyu da suka wuce?" Yayi tambayar yana aza idanunsa akan fuskar mammina,tambayar data fita daga bakinsa cikin wani irin calmness hankali kwance,ba alamun fushi fada ko bacin rai,amma kuma cikin qasa da second uku tambayar ta huda qirjinta ta kuma soma yaga bangarorin zuciyar akhnan da tsoro.
Maganar tazo mata da wani irin ba zata,ba zatar da bata taba hasashe ba. Cikin ranta taji wannan din shiryayyen abune......wani abu ne da aka shirya faruwarsa,don bataga ta inda maude zai fidda labarin nan ba koda dambunsa za'a yi.
Koma dai menene ita din har kullum tana juyawa ne da tsalle a tsakanin lissafinta,bata taba bari wata lamba ko gido qwaya daya ya bacewa ganinta ballantana lissafinta ya shiga rudu. A gaban sultane take,qasqanci kuwa muddin a gabansa ne tayi imanin DAUKAKA ce da kuma cimma nasara me yawan gaske,don haka ta sadda kanta,da muryar ta da tayi matuqar laushi ta fara magana.
"Tuba nake......tuba nakeyi ranka ya dade......akwai dalilai da suka......" Hannu ya daga mata.
"Ta wuce zaitun....ta wuce,amma akwai na gaba da wala'alla basuzo ba bare su wuce" Sai ya maida dubansa ga akhnan. A lokacin tana jinta ne kamar an tsomata a Kogin qanqara,sai takejin ta gwammace ko wanne hukunci ne sultane ya fadeshi,wataqila ta iya jureshi,wataqila ta samu sassucin fargabar da takeji.
"Akwai cikin masu son aurenki da zaki iya gabatarmin dashi a gobe?". Wani gigitaccen abu taji ya dira tsakiyar kanta,ta daga idanunta a birkice tana kallon sultane. Tayi zaton idan ya mata magana zata samu relief ne,ta dauka komai zai soma sassauta,amma sai taji har gwara shurunsa,har gwara baice komai ba.
Kai take girgizawa da sauri tana jin wani tashin hankali. Ko kalar wannan tambayar bata shirya amsawa ba bare ita kanta tambayar.
"Akwai?" Sultane ya sake tambayarta cikin dakewa yana dage dukka girarsa sama. Ta kasa cewa komai sai kai da take girgizawa. Zamansa ya gyara sosai yana fuskantarta,abu guda daya dake tabbatar mata magana zaiyi kenan da dukka gaskiyarsa.
"Ba damuwa bace......ni ina da wanda zan gabatar miki........a gobe ne kuma zaizo......bawai zaizo don ki gane yayi miki ko baiyi miki ba......zaizo ne don ki shaida fuskarsa,ki kuma sakashi cikin mafarkanki na shine mijin aurenki,mijin rayuwarki na dindindin,daga lokacin kina da damar yin tseren dokuna iya dukka adadin gudun da kikeso idan har shi ya lamunce miki".
Bata taba yarda zama zai iya gagarar mutum ba sai a sannan. Tana daga zaunen amma neman abinda zata dafa takeyi don ji take faduwa zatayi.
"Bappp....." Ta kasa furtawa saboda kallon daya aje mata,saita waiwaya tana duban mammina wadda takejin ita daya ce ta rage mata,itace kawai damarta ya qarshe.
Cikin rashin sa'a saita samu mammina din kanta yana a qasa ne tun sanda tayi magana ta farko,kuma har yanzun bata dago ba.
Abinda bata sani ba,maganganun sultanate akan akhnan din sune suka qara mata nauyin da takejin kamar ma bazata iya daga kan nata ba har sai an taimaka mata. Wani irin kalar tashin hankali takeji yana sakko mata yana lullube kowanne sashe na jiki da zuciyarta
Iya sautinsa,iya kuma yanayinsa kadai ya gaya mata,ko duka duniya zasu taru basu isa su sanya sultane yanjanye hukuncinsa ba a dadai wannan lokacin. Inda kuma akhnan zata fuskanci hakan data hutar da kanta,da bata bata bakinta ba gurin kiran.
"Momma......ki taimaka min". Har qasan zuciyarta takejin tausayinta yana narke mata,to amma wata soyayyar wani nuna tausayin wa yaro bashi da wani rana,bashi da wani muhimmanci face jagula komai da yake sakeyi.
"Kiyi haquri akhnan......darajarki kenan......mahaifinka bazai taba iya cutar dake ba" Ta furta tana lanqwasa muryarta da zummar ganar da akhnan din,saidai a maimakon ta gane din,sai wani matsanancin jin haushi da jin tsanar momma din ta saukar mata.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*