← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 97

Sashe 40

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daidai imda tunaninta ya katse daidai sanda thunder din yaja wani irin birki daya kusa sakata fadowa ta gaba,bata kuma gama daidaituwa ba ya saki wata haniniya yana daga qafafuwansa na gaba sama,abinda ya sakata yin baya gaba daya ta tafi suuuu zata daki qasa.

"Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" Momma safiyya ta furta tana miqewa da wata irin razana......dukkan gabanta suka dauki rawa,zuciyarta na wani irin rawa itama kamar zata tsinke,yayin da falaak ta ruqunqume momma din da kyau wani irin tsoro yana cikata.

Yayi imanin idan har ta fado a irin wannan yanayin ba abinda zai hana qashin qugunta tabuwa koma ta rasa lakarta gaba daya........yana matuqar qyamatar taba koda yatsar daba halal bace......amma kuma indai ya bari ta hadu da matsala daya cikin biyunnan ya tabbatar yana da nashi laifin a gurin Allah,wannan ya masa qaimi,cikin wata irin azama kar cirar walqiya ya isa gurin yana tokare kansa da qafarsa dake cikin boot,ya kuma miqa hannunsa guda daya ta fado akai,ta mirgina gaba daya ta fado jikinsa da wani irin matsanancin bugun zuciya daya bayyana a dukka gabanta da suke rawa.

Iya qwayar idanunta kawai ya iya gani data fito ta tsakiyar helmet din kanta,ya zareta daga jikinsa da sauri yana tsaidata saman qafafunta gami da furta.

"Astagfirullah wa'atubu ilaih" Da sautin daya tsaya iya saman labbansa,yanajin istigfarin yana zarcewa har cikin zuciyarsa.

Tuni hadimanta suka fara bullowa da sauran ma'aikatan da hukumar wasan suna cika filin. A nutse yayi taku biyu baya sannan ya juya da zafin nama yana gyara zaman helmet dinsa yana takawa a zafafe da dukka kuzarinsa yana barin gurin.

Duk takunsa daya idanunta yana kanshi.......duk da yawan jama'ar dake gabanta,wanda dukkaninsu sun iso ne su sake tabbatar da saukarta lafiya qalau. Kowanne taku nasa daya sai ya tada qura saboda karsashi da energy din da yake dashi,sannu a hankali har ya saje cikin dubbannin mutane ya bacewa ganinta.

*MORSA*

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda momma kawai taci gaba da maimaitawa ta kasa barin bakinta. Har yanzu hannunta yana dafe a qirjinta,har yanzu kuma tsananin bugun da zuciyarta keyi bai sassauta ba ko ya dakata,tashin hankalin da takeji kadan ya sauka,daga kashi dari zuwa casa'in.

Me yakai akhnan jikin wani?.....me ma yakai akhnan filin tseren dawakai?,me ya sanyata a jerin 'yan wasa?,yaushe ta shiga?,yaushe ta fara?,bayan abubuwan da tasan tana yi a Niamey yaushe wannan din ya shiga cikin dabi'unta?.

Har yanzu falaak na lafe a jikinta cikin matuqar tsoro,itama qirjinta bugawar kawai yakeyi har yanzu,gefe daya wasu siraran hawaye masu dumi suna sauka a hankali a kuncinta.

Da gaske tana son 'yar uwarta......da gaske tana son biftu fiye da komai,tana da matsuguni me girma a zuciyarta,bata kuma sake gasgata hakan ba sai yanzu da wani mummunan abu ke daf da samunta. Batasan tana da girma da matsayi har haka a zuciyarta ba sai yanzu,shin menene a baya ya lullube girman wannan qaunar da take mata?,me yasa abaya bata fuskanci haka ba?.

Rashin tashi da rayuwa qarqashin mahaifiya daya?,ko rashin rayuwa ne qarqashin kulawa iri daya?,ko nisan zango da tazarar dake tsakaninsu ya haifar da haka?.

A mugun kasalance ta janye jikinta daga na momma din,sannan ta daga idanunta tana duban cikin idon momma. Maida kallonta itama momma din tayi a kanta,a nan falaak ta tsinci taruwar hawaye kwance cikin qwayar idanun momma din,wadda tayi murmushi wa falaak da zummar batar dasu,saidai maimakon su koma sai suka yiwa kansu hanya suka zubo.

Sosai falaak taji wani irin tashin hankali ya yanko mata. Momma kuka?,yau momma ce da kuka?. Matar dake da wani irin dakakkiyar zuciya?,matar dake da wani irin juriya da jajircewa akan dukkan wahala ko tsanani?.

"Momma....." Falaak ta fadi tana kai hannunta fuskar momma din. Riqe tsintsiyar hannun falaak tayi tana qin bari murmushin ya bace daga fuskarta.

"Na kasa falaak......na kasa komai akan rayuwar akhnan......ina gani ina kallo a gabana rayuwarta take tabarbarewa a hankali a hankali da wani irin mataccen salo da zai qarasa maida rayuwarta abar qyama......na kasa falaak" Ta fada da wani irin mugun karaya.

"Baki kasa ba momma......baki taba kasawa ba......a kullum ke din me nasara ce,a kullum cikin cin nasara kike kuma zakici gaba da cin nasara har abada......koda yaushe kina gayamin......akwai wani abu tattare da yaa biftu......akwai wani abu a rayuwarta......akwai abinda yake faruwa......su waye?.....meye a tattare da ita?" Falaak ta fada da mugun son jin komai a bayyana,kamar yadda ya zame mata dabi'a duk shekarun da suka shude.....tun daga shekarar da hankali ya fara zuwar mata zuwa yanzu,amsar da har yanzu batakai ga fahimtarta ba.

Tsam momma ta miqe......har a ranta tana sake jin wata sabuwar qwarin gwiwa da iya kalaman falaak kawai.....kalaman da kullum suke shige dana hairaan,kalaman da sune kadai qwarin gwiwarta,sune kuma suke riqe da duk wani motsinta har kawo yanzu,har izuwa yau.

"Akwai wani lokaci yana zuwa......akwai wani zamani tafe da za'ayi kyakkyawar farar walqiya.......a lokacin fuskokinsu da ayyukansu zasu bayyana.....inajin hakan a jikina falaak......amma me zai hana ne?,me kuma ya hana sultane tsaiwa a tsagina?.....ya tsaya a gefe na?"

"Ni zan tayaki momma......ni zan tsaya a tsaginki" Falaak data dora hannunta a bayan mahaifiyarta ta fada,tana jin yaqinin da dukka zuciyarta kan abinda ta fada din.

"Zan kusanci ya biftu kaman yadda kikeso.....zan samu kusanci da yaa akhnan kamar yadda kika tsara......zan zama a kusa da rayuwarta momma,na miki wannan alqawarin". A hankali a nutse kuma momma ta waiwayo tana duban falaak da dukka idanunta. Irin wannan nutsuwar......irin wannna kamalar....irin wannan dabi'un taso su zama rigar akhnan,irinsu taso ta siffantu dasu,koda falaak din ce zata kasance kamar akhnan a yanzu.....indai akhnan ta kasance kamar yadda falaak take a yanzun bata damu ba.

(08187255862 lu'u lu'u paying)

Jawo falaak tayi cikin jikinta tayi mata kyakkyawar runguma tana fadin

"Allah yayi miki albarka......Allah ya hadamin kawunanku.......Allah ya baku dukkan kariya da tsari irin tasa".

*AKHNAN*

Runtse idanunta tayi tana me lafewa sosai cikin kujerun motar. Tun daga nan gurin.....tun kuma a sannan ta fara jin faduwa da muzanta sosai tana zagaye duk ilahirin jikinta. Daga sanda tayoyin motocinta suka fara dagawa suna barin gurin......mic din dake zagaye da gurin ya karade da sautin neman wanda yayi nasarar......kwatankwacin abinda ya faru a wancan satin da ita.

First winner da suke kira a yanxu.....wanda da alama basu da cikakken sunansa,a wancan satin war haka sunanta ake kira......sunanta ne ya karade ilahirin amsa kuwwar ana nemanta a matsayin wadda tazo ta farko da gagarumar nasarar zubda maza sha daya,shin a yanzun meye ya canza wannan labarin?,meye ya canza wannan nasarar tata?.....WAYE SHI?.

Wannan tambayar ita ta zame mata tambaya mafi muni kuma mafi barazana.......FADUWA RASHIN NASARA kalmomin da tafi tsana.....kalmomin da tayi nisan nesa dasu tsahon wasu shekaru yau gasu a kanta.

Ta sani.....babu abinda zai canza wannan tarihin......babu abinda zai gogeshi.......babu abinda xai sauya sai idan har ta sake gwabza wani wasan ne tayi masa ninkin kayin da yayi mata.

Ya cinye wasan......ya kuma zama shine wanda ya ceceta daga hannun thunder?,wanne irin asara ce wannan har haka a gareta?.

Namiji ya kubutar da ita?,duk da tarin matan dake wajen?,bayan ya jawo mata asarar bacin suna?,anya kuwa har abada tana da maqiyi sama da wannan?

Tafin hannunta takai kan dantsenta,har yanzu tana jin shati da alamun yatsunsa a gurin,har yanzu tana jin yatsunsa da irin tsautsarar riqon da yayi mata sanda take fadowa. Wani malolo yazo ya tokare mata a wuya,daga haihuwarta zuwa yanzu,babu wani d'a namiji da ya taba riqe koda farcenta ma bare yatsa ballantana kuma akai ga dantsenta. Sultane kadai.....sultane kawai a mazaunin mahaifinta shine ya taba samun wannan damar a dukka fadin rayuwarta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 34
____________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*👘🥻

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana goma KACAL!✌🏽*

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*🙌🏽
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
___________________________

An haifeta abar riritawa......abar yiwa tattali.....abar gatantawa da shagabawa,abu mafi girman daraja da tsada da agadez ke qunshe dashi.......wannan ya sanya ta zama abar kaffa kaffa da bawa kulawa. Ganinta koda a cikin gidan ma wani abune da ya zamana babbar sa'a ga duk wanda ya samu hakan.......bayan ta girma kuma,wannan jinin na sarauta ya fara motsawa a jikinta,wannan izzar isar taqamar da qasaitar da sarauta ke saukarwa ta sake mamaye jininta da kyau. A hankali ta fahimci irin tsadarta......ta gane darajarta,ta kuma karanci tattalin da ake mata,saita sake sawa ranta da gaske ita din ta musamman ce.....da gaske tasha bamban da dukka mata.....harta 'yar uwarta dake da daraja kwatankwacin tata wato FALAAK. Tana ji a ranta ita da falaak ba daya suke ba......akwai wasu tarin banbamce babance da darajoji data dara falaak din dashi nesa ba kusa ba.
Chapter 40 · 0% Book details