Sashe 59
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna takawa zuwa masallacin dake layin,wanda qananun taku ne kawai zai sadaka dashi zuciyarsa na sake yi masa tariyar yadda al'amarin ya wakana. A lokacin ya gayawa kansa ne ba wannan ne ya kawoshi cikin masarautar ba.......ko meye zasuyi daidai da tsarinsu ne da rayuwarsu,aiki ya shigo yi,shi ya dameshi,kuma shi ya kamata ace ya kula dashi,amma baida jib'i da komai na rayuwarsu,sai gashi a yanzun yana jin kamar ba haka ba,abun yana neman tsaye masa a rai.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 49
___________________________
*_INA MASU BUQATAR QAWATA GIDAJENSU DA KALAR TSUNTSAYE DON ADO DA DEBE KEWA?_*
*_INA MASU BUQATAR FARA SANA'AR SAIDA TSINTSAYE.....SANA'A ME TARIN RIBA DA ALBARKA DA KUMA SIRRI A CIKINTA?_*
*HALY JASHERU VENTURES.*
munada tsuntsaye na kasashen waje masu kyau da daukar hankali kmn haka.
TATTABARU
French modain(Argentina)
Indian faintail (3in1)
indigo,opal,Andalu,Lahore,busa,Bukhara, indomie,Jacobin dasauransu.
KAJI.
Brahma,silkie,silver lace,coshine,dawisu, parrot (aku)dasauransu.
,
Munada kayan Islamic center.habbatus saudah,hulba,zaitun,qusdul Hindi,minannas,Rose water dasauransu,dangin garinsu ,mansu yayansu ,ganyensu. munada original Zuma,yar chad da mombila.
Munada kayan gwanjo masu kyau daga jariri zuwa babba,
Overall,Rumpers, bodysuit, sweaters,wanduna, tracksuit dasauransu,munada kaya masu kyau na bacchi na gwanjo.
Munada Ethiopian magic hair oil 🪔 Wanda yake Kara gashi,yayi tsaho laushi,yayi Baki drct daga Ethiopian muke kaisa ko Ina afadiin duniya.
Don Neman Karin bayani number waya
07046665338.
____________________________
*AKHNAN*
Ko kafin takai ga idar da sallar taji an mata knocking ya kusa sau biyar. Tana sallan amman ranta yana baci. Ba wanda take buqata yanxu haka a kusa da ita,ba wanda take buqatar tayi magana dashi,kebewa kawai take so,sai kuma jiran kiran sultane. Kiran da inda tana da dama tabbas da zata tsere masa ne,amma kuma tasan bata da damar hakan,hakan kuma bame yiwuwa bane. Dole ne ta amsa tambayoyin sultane,dole ta tsaya ta fuskanci sultane muddin tana neman 'yancinta,dole ta masa bayani ta yakice kowanne irin tsoro dake a ranta.
A hankali ya fado mata a rai sanda take zauke daidai saman daddumar,tafukan hannayenta akan saman fuskarta. Wancan lokacin da kalmar.
"Subhanallah" Ta fita a bakinsa,sanda take dab da shan qasa daga saman thunder dinta. Har yanxu wannan sautin yaqi barin kunnenta,har yanzu wannan sautin ya sha tashinta daga baccinta a darare masu yawa. Tasha sake ganin wannan abun daya faru yana sake maimaituwa a cikin baccinta.
Qamshinsa da har yanzu bata sake jin makamancinsa ba,har kwanan gobe tana iya hakaitoshi,saidai kuma da tarin wata irin matsananciyar tsana da kuma jin haushi.
Inda tana da hali,tana kuma da dama lallai da sai ta laluboshi a dukka inda yake a fadin duniya. Tana da wannan qudurin,amma kiran sultane da maganar da sukayi a jiya kawai ta warware duk wani karsashi da take dashi.
A yau kawai tsanarsa ta ninka a zuciyarta ninkin baninkin. Shine silar duka wani hukunci da sultane ya dauka a kanta. Shine sila,ta tabbatar wannan video clip din ya gani........ya kuma zame mata dalilin wannan horon da sultane yake shirin yi mata.
Ta sake yadda abun shiryayye ne,dama ya shirya ne kawai don yaci mutuncinta ya kuma ci zarafinta. Tunda ga shaida da alamu dukka ta gani,ta tura musu request tana son a sake shirya wasan,amma sun maido mata amsar wannan dan wasan isn't available.......amma idan tana da sha'awar sake yin wasa,akwai tarin 'yan wasa available da zata iya karawa dasu.
Bata da buqatar ko daya a cikinsu,tana buqatar karawa da shine don cire masa dukkan wani abu da yakeji a kanta......don cire masa tunaninsa na yayi nasara akan akhnan muhammad hammud..........da wannan tunanin ta wayi gari,saidai a yanzu sultane na shirin dakushe wannan shirin,ya kuma maida akalar tunaninta kan wani abu na daban.
A karo na uku da aka buga qofar saita miqe a fusace ta isa qofan da kanta maimakon tayi amfani da remote ta bude. Cikin ranta tana me cin alwashin ko waye saita wanke masa fuska da zafafan mari tukunna,ko waye.....koda falaak ce,saidai kuma tana bude qofar sai taci karo da fuskar da tafi qarfin mari a gurinta.
Mammina ce a tsaye yana fuskantar qofar dakin. Dukka wani yanayi na alhini rashin jin dadi da kuma damuwa gashinan kwance saman fuskarta. Jiki a sanyaye ta saki qofar tana komawa ciki,mammina ta biyo bayanta.
"Don meye zaki kulle kanki akhnan?,bakya tsoron lafiyarki?,ko bakya tsoron wani abun ya sameki?" Ta fada tana riqo dukka hannayenta cikin tsantsar kulawa.
Blue eyes dinta da suka rusuna ta waiwayo yana zubewa mammina su,tana ji a ranta har tsakiyar zuciyarta.......bata da wani sauran gata daya rage mata a duniya bisa dukkan alamu idan ba mammina din ba......sultane ne taqamarta na farko,to amma kuma alamu sun nuna kamar sultane din ya fara yi mata nisa,ya fara nisa da muradinta. Ba zatace ga a abinda yake faruwa ba kai tsaye,amma tana da yaqinin zai wahala idan ba MORSA bace ke shirin rusa wannan kyakkyawar alaqar ba.
Duk wasu halaye da sultane ke gwada mata a yanzun baqi ne a tare da ita,tunda ta mallaki hankalin kanta bata taba ganinsa da wadannan dabi'un ba.
Ci gaba tayi da kallon mammina kawai,abinda ya bawa mammina damar karantar abinda yake kai kawo a zuciyarta.
"Tsoron me kike biftu?,kin manta alqawari na?......kina zaton idan sultane zai iya manta alqawarin dake tsakaninku ni zaituna zan iya mantawa?......duk runtsi duk tsanani ina tare dake akhnan" Sosai maganganun mammina suka karya mata zuciya. Bataso tayi kuka,don batajin ya kamata zuwa yanzu ta fara samun rauni har haka a zuciyarta,amma kuma tana buqatar kafadar da zata jingina da ita don samun sassaucin abinda takeji,don haka ta qara taku biyu,ta aza kanta saman kafadar mammina din.
Hannunta ta dora saman sassalkar sumar akhnan dake da tsaho santsi da kuma sheqin baqi tana shafawa a hankali,kaman yadda uwa keyi ga qaramin yaronta da sigar lallashi.
"Indai ina raye ba wanda zan bari ya aurar dake ga mijin da baki aminta dashi ba......ko baki fada ba yalwa ta gayamin.......sultane mahaifinki ne......indai ba zugashi akayi ba,bazai taba aurar dake ga mijin da baiyi miki ba......" Saita daga kan akhnan daga kafadarta tana riqe hannayenta dukka biyun.
"Ki sa a ranki da mahaifinki kike magana.......ki bude bakinki ki gaya masa bai miki ba!". Ta qarasa maganar da wani sauti dake nuna akwai wani abu daban daya taba zuciyarta.
Shuru akhnan tayi tana duban tsakiyar qwayar idanunta,irin duban da a yawan lokuta da dama yake qarfafa mata gwiwa tun daga yarintarta. Kallon idanun mammina din na bata wani irin qwarin zuciya tare da bata qarfin gwiwar aikata abinda take ganin bame yuwuwa bane ko ba zata iya ba.
"Shirya muje.....ya aiko a kiraki,ni zan tsaya miki koda hakan yana nufin yin baqin jini,baqin jini a idanun sultane.......baqin jini a idanun morsa safiyyah".
Zame hannunta tayi daga na mammina,iya Kiran sunan morsa safiyyah kadai ya sake harzuqa zuciyarta,sai ta juya da baya da sauri,ta kai hannunta kawai kan dogayen rigunan dake zube saman gadonta,wadanda dukkaninsu sabbi ne,birra ta soma gyarasu zata zuba mata a closet dinta tace ta barsu ta fice ta bata guri.
Duk yadda take jin zuciyarta ta tsayu amma sai fargaba ta fara ratsata sanda suke nufar sassan sultane din. Tsinkewa kawai takeji zuciyarta tanayi zuwa pieces a cikin qirjinta.
Ta fahimci hakan mammina.......saita damqe hannunta da suke cikin nata tana magana qasa qasa.
"Karkiji tsoro......ina tare dake" Maganar data sake saukar da wani dan guntun sassauci kenan cikin ranta.
To amma daga sanda mammina tayi sallama cikin parlor din sultane din,ta kuma hangi morsa safiyyah zaune a gefansa tana sake tsiyaya masa ruwan markadaddiyar apple sai taji tana neman rasa duk wani qwarin gwiwar tata saboda abubuwa biyu.
Abu na farko yanayin fuskar sultane din. Wani baqon yanayi ne da sai me zuzzurfan kusanci dashi......me zuzzurfan hangen nesa da tsinkaye kuma shine zai iya karantar kwantaccen bacin ran dake kai kawo saman fuskar tasa. Duk da cewa ga me gajeran nazari wanda ba wata zuzzurfar alaqa Taakaninsa da sultane din zai dauka yanayi ne kawai irin na yau da gobe.
Morsa safiyyah. ....wanzuwarta a gurin gabanin zuwansu ya sake rusa mata duk wani kyakkyawan zaton da ta shigo dashi.
Ko sau daya......koda lokaci qwaya daya bata taba saqa alkhairi akan matar ba. Da yawan dagulewar al'amuranta tana alaqantashi da morsa safiyya din,alkhairi bai taba gifta mata ba muddin tana a gurin.
Idanunta ta dauke a hankali tana lumshesu,tana kuma takawa zuwa ga sultane din bisa qwarin gwiwar mammina da kalaman da take gaya mata qasa qasa. Kalaman da ba lallai kai dake kallonsu kai tsaye ka dauka wani magana takeyi da ita.
Cikin qasa da second uku wata irin shimfidaddiyar fara'a ta wanzu a fuskar mammina,idanunta tsakanin sultane da morsa safiyya.
"Sannu da hidima" Tace da morsa safiyya dake qoqarin rufe tambulan din lemon data gama zubawa sultane.
"Kece da sannu zaituna....." Ta amsa mata da salon daya sanya mammina jin wani iri. Kasancewarta mace me wata irin halitta da tasha banban data mata da yawa,irin matan nan da sukan iya shanye komai su kuma jure jin komai daga bakin wanda sukaso,saita maida mata da martanin murmushin,ta kuma qarasa a nutse daura da sultane tana yiwa akhnan mazauni daura dashi din,daidai sanda take cewa.
"Muna neman sassauci da afuwa ranka ya dade........na shigo ba tare da ka nema haka daga gurina ba......zuciyar d'iyata cike take da fargaba da kuma zullumi,bata da qwarin gwiwar tunkarar mahaifinta sam a wannan ranar" Takai qarshen zancan tana zame yatsunta daga cikin na akhnan,ta kuma ja baya kadan alamun dake nuna tafiya zatayi.
"Ina zuwa?" Sultane din ya tambaya kanshi tsaye yana ajiye tambulan din hannunsa.
Duk da yadda morsa taqi jinin yadda dukkan wata kebantacciyar alaqa ko dangantaka data shafesu mammina ke ciki tsulum tsulum,amma ita kanta a yau din tafi buqatar zaman mammina akan fitarta.