Sashe 72
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan bata manta ba,wannan hakeem dindai shine wanda mahaifinsa ke qorafin yaqi karatun boko.......wannan hakeem din shine dai wanda mahaifinsa ke qorafin ya zabi karantarwa,yaqi amsar dukka wata harkar business ko fita qasashen waje da mahaifinsa keyi sai qaninsa ya dora akai.....wannan hakeem din dai shine taji mahaifinsa na dariya yana fadin ya gaza zabar matar aure,kamar tsoron mata yakeji,ba kasafai yake tsaiwa da mace suyi doguwar magana ba......wannan hakeem din da shine yaqi kasuwanci duka ya miqa ragamar kula da komai nasa ga qaninsa.......wannan hakeem din da bai iya doguwar magana da French sai larabci kawai da asalin yarensu na zinder yaren mahaifi da mahaifiyarsa.......wannan lusarin HAKEEM din......wannan LUSARIN MIJIN shine sultane ya zaba mata?. Tana zaune a wani gefe daban na dakin hutawar sultane tana jira ya sallami baqonsa yayi mata signing din da zai mata taji dukka wadannan maganganun. Ta tabe baki tana maida hankalinta ga takardun gabanta,cike da mamakin failure irin ta wannan mutum da suke magana a kanshi cike da mamaki.
Ya shigo ya samesu a dakin hutawar.......maganganun da sukayi a kansa ya sanya ya daga idanu sau daya tak ta kalleshi don taga wanne irin mara sanin ciwon kaine wannan?,a sannan ta soma ganin fuskarsa. Tun a sannan taji baiyi mata ba,bawai don akwai wani abu daya faru ba.....a'ah,sai iya tattaunawar da taji su sultane sunayi a kansa,tun a sannan kuma ta laqaba masa sunan KASASHE a ranta.
Ya bace mata sam akai,don tun daga wancan ranar bata sake ma wani tuna abinda ya danganceshi ba,sai a yanxun da ta kalli fuskarsa komai ya dawo mata.
Sake jagulewa ranta yayi,ta sanya hannunta a goshi ta dafe kadan,sannan ta dauke yana yarfar da hannuwa,tana jin yadda gaba daya bacin rai ya cika nata qirjints,har tana jin babu wani space daya rage. Bacin ranta ya sake ninkuwa sanda take dubansa duba irin nakai tsayen nan ganin yadda ya gaza sanya idanunsa cikin nata. Abune me wahala ta kalli namiji irin haka,amma baqo dai irin HAKEEM rashin darajarsa ta zarta ta kowa a gurinta.
Tabbas tun daga sanda ta samu labarin morsa safiyya ta taka wata rawa a zuwan baqonta na yau tayi imanin babu wani alkhairi ko abun arziqi a ciki. Ba wani alkhairi kwata kwata da zaizo daga matar zuwa gareta,sharri ce ita!.......duk kuma wani abu daya danganceta din sharri ne.
Qoqarin gyara mata kujerar da zata zauna yayi,amma zafin naman da takeji yau a jikinta ya sanya ta rigashi aikata hakan
"Nasan za'a rina......daga yanayin gidan gaba daya jikina ya bani wani qasqantaccen ne yazo gareni........ashe arahata har takai haka?" Ta qarasa maganar idanunta na nuna zallar kaifin fushin dake cikin su,ta kuma dauki qafarta daya ta dorata saman daya cikin wani yanayin zama dake nuna zallar izzarta da kuma izgili ga hakeem dake zaune kawai yana dubanta ba tare daya motsa ba.
Idanunsa ya dan runtse,yaji zafin kalamanta,amma kuma tunawa da yayi itadin macace me raunin hankali sai yayi qoqarin basarwa.
"Sallama ya kamata ki fara yi koda ba zamu gaisa ba ko gimbiya?". Manyan fararen idanunta masu blue din qwayar idanu ta watsa masa,abinda ya sanya kwarjinin nan dake tattare da ita ya ratsashi.
"Gaisuwa......ko sallama,dukkaninsu ana yinsu ne ga mutumin madaukaki me daraja........wanne gangancinne yakai ka gabatar da qudurinka a kaina?......har ka nemi ganawa dani?" Ta masa tambayar tana tsareshi da idanu kaman yadda uwa kewa d'anta.
Murmushin qarfin hali ya saki a hankali. Ya sani,tunda har bada son ranta bane,zai iya fuskantar kowanne qalubale da kuma turjiya kafin ya samo kanta.
"Qauna ce.....da kuma son kasancewa mijinki in sha Allah". Idanunta ta janye,wani dariya data maida gurbinsa da murmushi ya subuce mata,abinda ya sake fidda zallar ainihin kyanta,kyan daya daki zuciyar hakeem kai tsaye.
Sakanni kusan biyar sannan ta gyara zamanta tana zube masa idanunta.
"Kai yanzun a naka ganin akhnan ta dace da maqasqancin mutum irinka?" Ta furta da wani irin kaifi a muryarta da idanunta,kamar ta bashi damar bata amsa ne,kafin kuma ta sake cewa
".....Na yarda......cikin nau'in mutanen da sukafi kowa son zuciya......tsaurin ido da kai kai inda Allah bai kaisu ba irinka ne.......mutanen dake iqirarin ilimin sanin Allah da annabi.........maha'inta masu ci da addini........inaso ka sani.......cikin nau'in mutanen da na tsana.......bazan kuma taba iya aurensu ba koda NI DASU KADAI MUKA RAGE A DUNIYA sune gidadawan masu ci da addini da sanya rawani a kansu da daukan litattafai da sunan su din malamai ne......"
Ba ita daya ba,hatta da badee'a ta fahimci karatun yana shigarta sosai,don itama ta sake nutsuwa,ta kuma tattara dukkan hankalinta guri guda. Saidai a sanda muryar akhnan da hakeem ta fara ratsowa inda suke sai dukka hankalinta ya soma rarrabuwa gida biyu,da wani irin nauyi da kunyar yau kuma me zata ce da hakeem?.......yauma yana jin abinda take furtawa ko kaman jiya ne?.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 62
A nutse ya sanya hannunsa ya maida bangon littafin ya rufeshi,bawai don sun gama karatun ba ko kuma yakai inda ya kamata ya tsaya ba. Tun daga sanda ta fara magana da hakeem yake gayawa zuciyarsa ba huruminsa bane........ba abinda ya shafeshi bane,wani sha'ani ne da bai shafeshi ba.......bai kuma hada dashi ba sam.......saidai kuma wani irin suka kalamanta suka fara yi suna sauka saman qahon zuciyarsa daya bayan daya da wani irin kaifi,duk kuwa da cewa bada shi take ba,batasan ma da wanzuwarsa a gurin ba.
Shuru gurin ya dauka,kaman yadda baiyi motsi ba haka ba wanda ya motsa tsakanin ita da badee'a.
Ko ina jikin falaak rawa yake,takaici da tashin hankali yana cikata. Koda baiyi kowanne motsi ba ta tabbatar a yadda gurin yayi shuru,dukkanin maganganun da Akhnan taci gaba da jifan Hakeem dasu suna sauka yadda ya kamata cikin kunnuwasa.
Shurunsa na nufin abubuwa da dama,ya dunqule hannunsa guri guda yana jin zafin kalamanta tamkar shi take gayawa. Me hakeem yakeyi?,me hakeem yaci gaba da tsaiwa yana yi har ta samu daman ci gaba da zuba masa wulaqantattun kalamai haka?.
Mutum nutsatse irin hakeem din,wanda yake da quality din daya tabbatar yafi nata duk da taqamar sarautar da takeyi?!. Har abada babu wata daraja ko matsayi da zaiyi daidai dana mutumin da yake dauke da ilimin addini a kwanyarsa!......me hakeem yakeyi?!. Ya sake tambayar kansa yana jin yadda jijiyar kansa ta fara tashi,kowanne kafa na jikinsa ya soma fidda gumin da hakan yake bashi tabbacin lallai ransa ya soma baci.
Baya jin zai iya ci gaba da zama a gurin kunnuwasa suna jin furucinta da daidai yake da zagin kowanne mutum me kamanceceniya da hakeem din
"Subhanakallahumma wabi hamdik,ashahadu an la'ilaha illa ant,astagfiruka wa'a tubu ilaik" Kawai ya rufe da ita yana qoqarin saisaita muryarsa da yakejin yanayin fitar sautinta ya sauya,ya miqe a nutse yana sanya takalminsa,wanda yayi daidai da isowar daya daga cikin hadiman me martaba.
"Sheikh......me martaba yace a shaida maka......yana buqatar ganinka idan an bashi dama". Idanu yadan xuba masa yana mamakin fitar kalar furucin daga bakinsa. Ya sani,ba yaren kowanne basarake bane hakan......ya nema izini daga wajen wanda yake ganin yana rayuwa ne a qasansa,umarni na kai tsaye shi sukafi ganewa,amma shi din izini yake nema ayi masa.
Wanne irin uba ne wannan da baiyi sa'ar diya ba?,wanne irin uba ne wannan wanda sam bai fidda iri me kyau ba?.
Kai kawai ya gyada masa,yana jin daukewar sautukanta masu zafi,wanda yake tunanin numfasawa ta tsaya yi,ko kuma ta kammala fadin dukka abinda yazo bakin nata ne.
"Idan burinka ko mafarkinka shine aure na......ina me shaida maka.....ni Akhnan nafi qarfinka har abada......zaka mutu kuma da wannan burin naka ne" Ta qarashe maganar sanda ta miqe tsaye,sannan ta juya da dan hanzari tana takawa don barin gurin.
A yadda takejin zuciyarta a sannan kuka kawai take da buqatar yi,banda kukan ba wani abu daya kamaceta........saboda zafin da takeji a ranta ya zarta ta iya cinyeshi kota hadiyeshi. Saidai kuma babbar faduwa ce a tare da ita wani daban yaga hawayenta......wanin da ba sultane ko mammina ba......koda morsa sai ya zamana dole ne take bari ta hangi fitar hawaye a fuskarta.
Tana ji a ranta a wannan karon itama a shirye take ta bijirewa umarnin sultane,a shirye take tayi fito na fito da umarninsa....... Gwaraba tariyo mata dukkan mazan da suka taba takowa domin nemanta......sultane ya zaba mata koma waye a cikinsu akan hakeem .
Hakeem fa?,hakeem din da rana ta farko data fara saninsa a rayuwa tayi masa laqabi da lusarin namiji.......hakeem din da bata tunanin ko digo qwara daya yahau cikin kaso dari na kalar zabin da take dashi idan har ya zama dole ma sai ta rayu da d'a namiji......hakeem din daya kasance malami,wanda baida kowanne irin experience na rayuwa........baida kowacce irin gogewa a rayuwa,baisan ma me duniya take ciki ba. Banda littafi rawani da zaman karantarwa ba wani abu daya sani.
Kai tsaye taji ba inda ya dace ta nufa sai gurin mammina.......ita daya ce ita kadaice kuma fatanta,ta tabbatar zata cika mata alqawarin data dauka na tsaiwa a gefanta da kuma tsaiwa a bayanta a duk sadda irin hakan ta faru.
*MAMMINA*
Ci gaba tayi da irgen mintuna daqiqu da kuma sakanni,tana jin ba wata kujera cikin parlor din da zata iya dauke nauyin abinda ke saman ruhi da zuciyarta ballantana ta zauna a kai. Wannan jiran ya zame mata wani irin jira na daban,irin jiran da yake da tsaho da kuma tsauri duk da fata da take dashi cikakke da kuma tarin yaqini.
Ta riga ta d'ana ta kuma dasa gami da harba komai......wanda abune me wahalan gaske wadannan shingunan.....wadannan turakun dukkaninsu ace an shuresu.