← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 97

Sashe 92

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

PAGE 78
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

Wankan ya sakeyi da ruwan zafin,sannan ya fita parlor din dake manne da bedroom din ya hada coffee cikin mini coffee maker din da aka ajiye masa saman dan wani qasaitaccen table aka zuba duk wani kayan buqata na hadawa da kuma shan coffee.

Sai daya sha cup daya sannan ya shimfida abun sallah. Wuturi daya rage masa yayi,ya zauna yayi tarin addu'o'insa sannan ya zame yana barin gurin.

Sai daya daidaita tsakiyar gadon bayan ya ajiye abokin hirarsa wato coffee a gefe,ya rage hasken wutar dakin duka,ba hasken da kake gani saina system din dake gabansa.

Cikin mintuna talatin ya kammala rubuta duk wani experience nashi na ranar,ya soke yatsunsa cikin na juna ya tallabi kumatunsa dasu ya zubawa rubutun idanu yana sake bibiyarsa.

"Akwai wani baqon kallo da emotions a tattare da ita,akwai wani reflection dake nuna connection tsakaninta da wanda ka kira da TAMIM. Connection na tsananin jituwa ko kuma na akasin hakan.....yaya akayi wannan bawan dake tsaye bakin window sunansu yazo daya da wanda ya shigo parlor din sultane?......indai har ba amintaccen sultane ko wani daga cikin mutum ukun dake ciki ba......mammina......ita akhnan din da tamim na biyu daya shigo ba.....bata yadda za'ayi da tarin masu tsaron dukka qofofin ya samu isa wannan gurin dake da matuqar tsaro.

Idan har kuma amintaccen ne na gaske,me ya hanashi qarasawa cikin kanshi tsaye?,me ya tsaya ji?,me ya tsaidashi cikin yanayin dake nuna zallar rashin gaskiya tattare dashi?.

Gumin fuskarsa a sanda yaji motsinsa......kallon dake cikin idanuwan mammina sanda ta ganshi,me yasa bata qaunar baqo da zafi irin haka?,bayan masarauta ce.....cike take da tsari da yanayi na amsar baqi a kowanne lokaci,cikin kuma kowanne yanayi?,me yasa yanayinta yake nuna zallar kishi?,kishin kada kowa ya kusanci sultane?,kishin kada kowa ya fita kusanci dashi?. Yaga haka a idanunta sanda akhnan ke yunqurin yin magana da mahaifinta......kallon data masa yasha banban da wanda ta yiwa tamim ME YASA?. Me yasa take matsa hannuwan akhnan a sanda take yunqurin roqar mahaifinta?.....me yasa ta hanata magana?,me yasa bazata barta ba?. Siririn tsaki yaja,yana tuhumar zuciya da kwanyarsa. Wannan din ba abinda ya shafeshi bane,abinda ya shafeshi kadai shine yayi binciken dukkan wani dake da alaqa da sultane dama masarautar......ya kula da motsi da takun kuwa,ya kuma zaqulo wanda suke nema muddin yana a cikin masarautar yana kuma rayuwa. Amma baya ga haka,dukkan wani abu da zai faru.....dukkan wata alaqa ba huruminsa bane shigarta.

"Tabbas akwai Oromian.......akwai Ethiopian cikin masarautar" Ya fadiwa kansa kai tsaye yana tuna lafazin mutumin daya fara gani a balcony.

Yaren oromo ne fes saman harshensa......da accent din da sai haifaffen yaren kawai zai iya lanqwasa harshensa izuwa wannan yanayin.

Idanunsa ya sake qanqancewa yana dawo da sautin muryoyinsu dukka cikin kansa. Akwai sautin mutum daya da harshen sa ya karye sosai.......ya kuma banbanta dana sauran mutum ukun dake wajen,lanqwasuwar harshen tasha banbam data saura.

"Nasrumminallah" Ya furta yana motsa labbansa masu glowing dinnan a hankali.

Idanunsa ya maida ya lumshe,yayi relaxing bayansa jikin kujera,dakin yayi shuru kamar yadda ilahirin gidan ya dauki shuru,yayi relax sosai kaman me sauraren wani abu,saidai kuma baya iya jin komai daga shurun da gidan ya dauka,sai qananun qwari dake bada mabanbancin sauti,da kuma qananun sautukan na'urori na Ac da sauransu da basuyi qarfin da zasu takura kowa ba.

Nauyi idanunsa sukayi,kaman bacci yana son daukarsa,take duhuwar dake cikin idanunsa ta ingizo masa hotonta fes cikin gizanniya.

"Subhanallahil azeem" Ya furta da sauri da wani qaramin amo da iyakarsa qasan maqoshinsa kadai. Zama yayi sosai saman sofa din,ya sanya yatsansa babba da dan manuni yana matse idanunsa,tamkar wanda hakan zai taimaka masa wajen fidda hotonta daya gilma masa a idanunsa.

Ya dauki tsahon wasu mintunan a haka,sannna ya bude idanun nasa da suka kada suka sauya launi yanajin qirjinsa yana masa nauyi.

Yana da wani yanayi da dabi'a dake saurin shiga kansa. A duk sanda yaga gilmawar wani abu daya shafi mace yakan zauna masa wani lokaci cikin kansa,wannan ya sanya yake cire kansa gami da nesanta kan nasa daga dukkan wani lamari daya shafesu. To amma a wannan karon besan me yasa abun keson dadewa cikin kansa ba tare daya barshi ba.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ya fadi da cikakken nutsuwa yana qarasa kashe system din tasa,sai kawai ya dauki wayoyinsa ya zura bedroom slippers dinsa yana zarcewa dakin bacci.

★ *AKHNAN*

Kayan jikinta kawai ta cire ta sauyasu da kayan bacci. Pyjamas masu rigar data tsaya iya cinya me dogon hannu,silk ne me dogon wando daya zauna mata,ya fidda shape din jikinta tamkar bawai kayan bacci bane a jikinta.

Lamo kawai tayi saman gadonta,cikin jibgegen duvet dinta da tsabar laushinsa take sake nutsewa a dukka motsin da zatayi. Wani irin zafi zuciyarta keyi mata,a yau sultane yayi mata abinda bai taba yi mata ba,wanda ya soma jefa shakku a cikin ranta game dashi. Anya kuwa akwai wannan soyayyar?,akwai wannan qaunar?. Anya kuwa morsa safiyya bata shiga tsakiyar wannan alaqar ba?.

Furuci da kuma tsaiwar da sultane yayi akan hukuncinsa ba tare da nuna alamun samun sassauci daga gareshi ba,wani abune daya bata matuqar mamaki. Wani abu ne kuma daya zo mata a bazata,don bata taba kawowa da tsammatar hakan daga gareshi ba. Saidai a jikinta take jin koma yaya ne ba zata taba yarda ta zama mallakin wani hakeem ba,koda kuwa hakan zai sababba fushin sultane ko kuma daukan mataki daga gareshi,wannan ya sanya take jin abun kamar baikai nisan da hankalinta zai tashi sosai ba,duk da hankalin nata ya gaza kwanciya yadda ya dace ace ya kwanta din,duk da alwashi da maganan da sukayi da mammina bayan fitowarsu na qarshe.

"Kada ki damu ko kuma ki daga hankalinki,ni bazan gaji ba wajen nema maki da kuma sama miki farinciki da dukkan qarfina,da kuma dukkan iyawata muddin ina raye. Gobe ma zan koma,zan kebe da sultane,zan kuma tabbatar da cewa ban baro gurinsa ba saida labari me dadi".

Wannan issue din ya kamata ace yafi damunta fiye da komai,amma saita tsinci zuciyarta tafi jin zafi da qunci kan abinda sultane yayi mata a gaban BAQUWAR FUSKAR da har yanzu take ji a jikinta bawai baquwa bace......tana ji a jikinta tasan fuskar......tasan kuma idanun.

Maganganun da sultane ya fadi a kanta a gabansa ya dawo mata,qirjinta ya wani quntata guri daya,har a yanzu tana jin yadda ta wani muzanta,kaman a yanzu sultane keyi wadannan maganganun.

"Idan ya kasance shine ne na hippodrome fa?" Zuciyarta ta jefa mata tambayar data tilasta mata ture bargon da take ciki,ta kuma miqe zumbur ta zauna saman tattausan gadon nata,kafin kuma ta janyo jikinta a hankali tana sauka daga saman gadon,tare da bin makunnin fitilar dakin ta sake kunnata.

Ta yaya zata bari wani mutum qwaya daya ya gagareta a rayuwa?,abinda kaf cikin tarihin rayuwarta bata taba samun hakan ba?....ta yaya wani dan adam zai shigo qasar da mahaifinta ke mulki da ita ya dasa mata abubuwan da zasu tattare dukka nutsuwarta suyi gaba da ita?......ta yaya zata bari hakan ta kasance?,wanda kamar 'yar manuniya ce ta cewa ya raina girman izza da matsayin da take dashi,daidai da daga mata yatsa saitin idanunta.

After dress dinta dake fidda sassanyan qamshinta daya kama duk wata sutura tata ta sanya,ta yane kanta da siririn mayafinta,ta murda qofar ta fito zuwa parlor din farko.

Kai tsaye ta isa ga landline,ta kumayi kira zuwa dakin birra. Cike da mamaki birra ta daga kiran ta saka a kunnenta,bata kuma barta tace komai ba ta aza mata umarnin dalilin kiran.

Ki dubomin tamim duk inda yake......ki kuma shaida masa ina buqatar ganinsa yanzu yanzu".

"An gama" Ta fada a ladabce amma cike da tarin mamaki.

Wayar ta mayar ta ajiye,saita sake takowa zuwa parlor na biyu. Duk girman gurin ba digon tsoro a tare da ita,kasancewar ta sani kewaye take da tsaron daba wani dan adam indai ba aljani ba daya isa ya iske inda take. Cikken motsi kawai mai qarfi ya isa ya kawo masu tsaron qofofinta zuwa inda take.

Da wani irin yanayi take kaiwa tana kawowa cikin kebantaccen gurin data saba ganawa da tamim din. Cikin lokacin ba abinda take ji take kuma gani sai mugun dadewa da yalwa tayi,wadda ta aika ta kira mata tamim a duk inda yake.

Duk da cewa a zahiri bawai dadewa yalwa tayi ba,to amma qaguwa da ganinsa a gabanta ya sanya take gani kamar jiran yayi tsaho da yawa.

Wani irin zafi takeji a jikinta da zuciyarta gaba daya idan ta tuna cewa MATSALA zata iya kunno kai. Tana jin kamar akwai abinda yake ba daidai ba,akwai abinda yake buqatar ta sanshi ko ta gyara zamansa ya zamana a daidai.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Sallamar tamim ta sanyata Waiwayawa da sauri,bata kuma tsaya amsa sallamarsa ba tace.

"Shigo.....qaraso ciki". Cikin sakanni ya bayyana,idanunsa cikin na mammina. Kanta ta jinjina a hankali tana hango wani abu cikin idanun tamim din. Ba haka ta saba ganin fuskarsa dama yanayinsa ba gaba daya,sai take hango kamar akwai wani abu daya taba ranshi.

"Waye shi?" Ta jefawa tamim tambayar kai tsaye,kaman tana da tabbaci da masaniyar cikakken sanin tamim gareshi.

Kai tamim ya jinjina,ya kuma matsa gefe yana neman gurin zama. Tun daga sanda ya baro gurin sultane bai samu zama ba ya shiga laluben wayeshi?. Ya sani tabbas zata buqaci sanin hakan,daga ganin irin kallon dake fitowa daga idanunta a kansa yasan hakan zata kasance. Haka kawai shima yaji wanzuwar matashin a gurin ya sauya yanayin gurin dana jikinsa ma gaba daya. Babban abinda ya fara fusgar hankalinsa shine.......kwarjinin da yaji ya masa,ya kuma cike gurin gaba daya duk da cewa a qalla zai bawa matashin shekaru kusan ashirin,amma sai yakejin wani irin girma nasa cikin idanunsa. Uwa uba......abu mafi girma shine wanzuwarsa cikin masarautar ba tare da shi ya sani ba.
Chapter 92 · 0% Book details