Sashe 75
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin sanyi qafafunta taji sunyi,tsoro taji ya shigeta,ga yanayin gurin daya soma lullumewa saboda gabatowar magariba. Me zai faru idan ya zamana aljanu sun fara wasa da hankalinta ne da tunaninta?. Tafin hannunta takai saman fuskarta da niyyar shafa don bawa kanta relief,saidai kuma wannan qamshin dai taji fes cikin hannuwan nata kamar an diga mata turaren ne a cikin su.
Da sauri ta janye hannun tana duban tsakiyar tafin hannun. Hannun dai nata ne,wannan lallausan tafin hannun da kowacce rana cikin wankeshi ake da nau'ikan mayukan wanke hannu,ta kuma shafeshi da ajiyayyen cream na musamman saboda hannun kawai,amma qamshin nasa ne......qamshinsa ne.
"Kina dab da rasa ganin sultane" Wata zuciyar ta yunquro mata da lamarin da ya sanyata takowa ganin sultane kai tsaye ba neman izini ba iso. Damqe tafin hannun nata tayi tana jin cewa wannan shine issue na gaba mafi muhimmanci a gareta. Ta tsani wanzuwar qamshin a tare da ita......amma a yanzun tana buqatarsa a hannunta zuwa awannin da zata kammala ganawa da sultane.
Tun a parlor din farko data hangi sultane din tsaye kowanne karsashi nata ya soma sulalewa. Wannan kwarjinin dake lullube da fuskarsa dama gangar jikinsa gaba daya suka soma dakushe nata kwarjinin dama jarumtarta,sai wani irin rauni ya fara sauko mata,irin raunin da d'a kanji a sanda yake neman alfarmar da ba wanda zaiyi masa shi sai iyaye,sai kuzarinta ya ragu,tayi qasa da kanta tana takowa zuwa gabansa,ta iso dab dashi sannan ta sulale saman gwiwarta tana kafe gwiwoyinta a qasa.
Wani abu qwaya daya da duk duniya sultane keda wannan girman da zatayi masa shi......wani aiki da a duniya banda mahaliccinta babu wata halitta data taba zubewa hakan a gabanta,sai ta saki siririn kukan da bata taba yarda ta yishi gaban kowa sai gaban mutum biyu SULTANE DA MAMMINA. Don koda cikin addu'a da salla batasan yadda ake kuka ba,bata zama doguwar addu'a saboda bata taba hasashen tana da wata buqata ba. Rayuwarta ta cike mata tako ina cif cif a nata idanun,bata da sauran abinda zata kuma roqa,rabbana Aatina fiddunya hasanatan wafil Aakhirati hasanatan wa qina azabannar kadai take iya maimaitawa.
Yana tsaye kawai goye da hannuwansa a qirji. Baice mata ci kanki ba,kaman yadda baice ta tafasa sauke ba. Indai akhnan ce......indai khadeejatu ce,indai kuma shine ya haifeta yasan tabbas zatazo. Ya shiryawa zuwan nata kuwa da kyau,ya kuma shiryawa ko meye zata ce,ya riga ya yanke hukuncin da ba abinda zai sanyashi maida hannun agogo baya. Lokacin aurar da AKHNAN daga masarautar agadez yana ji a jikinsa yayi,babu kuma abinda zai sauya wannan. To amma ta wani Fannin.....idan har yace kukanta baya taba ranshi......ko kuma kukanta bata mintsinin zuciyarsa yayi qarya. Kowanne iyaye akwai cikin 'ya'ya wanda Allah yake jarrabarsu dashi,shi kam ya amince da akhnan din aka jarabceshi. Baya iya dauke idanu daga dukkan wani ko wani abu da zai kusata da ita ya illatata ko ya cutar da ita.....bashi da juriya jumuri ko jarumta game da ita.....ba kuma wai haka kawai ta samu dukkan wadannan ba....Aah SAFEENA ce sila.
A duniyarsa ba wata halitta sama data safeena......ba wani mutum a jiya ko a yau shekaran jiya ko gobe da zai iya wafce matsayin safeena a rayuwarsa,har zuwa ranar da numfashinsa zaibar gangar jikinsa.
"Inda zaki sauqaqawa kanki khadeeja ki tashi hakanan,don babu abinda zai sauya wannan hukuncin......ZARTACCEN ABU NE kuma tabbatacce da ikon Allah......ban taba tunanin akwai lokaci da zaizo da zan iya zartar da haka ba a kanki......sai gashi yanayi yazo da bayanan da suke gwada hakan shine gata na qarshe da zan gwadawa rayuwarki......ki tafi ki fara shirye shirye......na baki watanni biyu kacal ki horas da kanki yadda zaki zauna da HAKEEM a mazaunin mijin aurenki na dindindin". Ya qarasa maganar yana soma barin wajen bayan ya dauki carbinsa da alkyabbarsa ya maida saman plain jallabiyyar jikinsa.
Tafi kowa sanin sultane bawai don tafi kowa doguwar rayuwa dashi ba......tafi kowa saninsa domin shi din jinin jikinta ne. Daga yadda ya nuna mata ta sake karaya da samun tabbacin hukuncin sultane na wannan karon BABU GUDU BABU JA DA BAYA!. Indai hakan ta kasance ta cika marar nasara.....tozartacciyar da zata auri namijin da yafi kowanne nau'in mazaje rauni da kuma rashin NASARA.
Namiji me ilimin arabiyya kadai?......koda yana da ilimin nasaara ba zabinta bane,hakeem da ire irensa dukka sun kasa .....namiji irin hakeem koda aisa ko shehnaz bare falaak ba zata yiwa fata ba.
Koda tana ra'ayi muradi ko burin aure......tsayayyen namiji.....jan zaki.....me budaddun idanun da suke iya hangen duniya a tafukan hannuwansa.......me iya sarrafa tunani dama abinda duniya ke ciki.....me idanu a kowanne fanni na rayuwa,gwarzo jarumin da ba abinda ke iya raunanar da zarrarsa......irin wannan ne WATAQILA......WATAQIL ta iya bashi dama cikin kaso daya cikin dari ya gwada sa'arsa.....sa'ar da idan ta tabbata wala'alla ta bashi daman ci gaba da nemanta har zuwa sanda zata iya jin cewa ita KHADEEJA MUHAMMAD HAMMUD zata iyayin aure a rayuwarta.
Sanda takai qarshen tunaninta sultane ya dade da bacewa ganinta. A hankali yakai yatsarta kan fuskarta tana taba dumin da taji yana gangaro mata. Duban yatsun ta sakeyi,hawaye ne......farare tas masu dumin da batasan sun sauko mata ba.
Kuka ba dabi'arta bace......amma akan sultane da hukuncinsa zata iyayin sama da kuka dinma.
★ "Me yasa ka nuna masa kana iya zama a gidan nan gaba?". Omari da ya zuba masa idanu yayi tambayar ga haisam din kai tsaye.
A hankali ya bude idanuwansa,duk da cewa bai motsa ba ko kadan daga yanayin yadda yayi relaxing cikin kujerar. A nutse yake duban omari,yana kuma son hotonta ya bace bat daga idanunsa.
Muryarsa can qasa,cike da gajiyar da yake ji cikin sassan jikinsa yace.
"A wannan karon...cikin jikina nakeji akwai wani abu cikin masarautar,da akwai wani abu cikin gidan,jikina ne kawai yake bani hakan,ba don ina da tabbaci ba.....komawata bata lokaci daya bace.....komawata zata zama kadan kadan ne har izuwa wani lokaci idan komawar ta tabbata gaba daya.......naji oromian language a muhallin da naga gilmawar tufafin hadiman cikin gidan.....tabbas dole yana kasancewa akwai alaqa ko sanayya ta juna tsakanin duk mutumin da kuke yare daya dashi.... Qabila daya a sanda kuka tsinci kanku a wata baquwar qasar da ba taku ba.... Tabbas akwai wannan zumuntar" Ya qarasa maganar yana jin tabbaci har cikin ransa. Shuru omari yayi yana jinjina kai,hasashe da maganganun haisam a bisa layi suke,baisan dalili ba,amma shima a jikinsa yake jin kamar nasara ce take tunkarosu.
"Meye sunan yarinyar da ka hadani race da ita?". Haisam yayi tambayar sanda yake miqewa tsaye,sanye da wata fara qal din shirt cotton sosai me gajeran hannu da round neck,abinda ya bayyana cikakkun muscles dinsa da suke gayawa duk wanda ya kalla yanayin qarfi da yawan motsa jikin da yake dashi. Hannunsa zube a aljihun wandonsa da bai sauka har qasa ba.
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 65
Daga kai omari yayi yana dubansa yana kuma d'an jin mamakin tambayar,don ko a wancan karon haisam din baima tsaya sauraren kowanne bayani akan race din ba,abinda yafi maida hankali kawai shine yadda wasan zai qare,su kuma samu daman shigewa cikin agadez a sirrance.
"Princess akhnan muhammad hammud.......qasaitacciyar d'iyar sarki muhammad hammud......bansan ya zata kasance ba duk ranar da tasan cewa kaine silar faduwar nasararta" Omari yayi maganar yana sakin murmushi idanunsa akan haisam. Ya san halin haisam din,yana da sauqin kai ta bangarori da dama.... Yana da bala'in bada girma daraja da martabawa ga dukkan wanda yake sama da shekarunsa........amma fa bashi da dadi a wasu lokutan......yana da wata irin zuciya da muddin aka tabota......sauketa yana zama abu me wahala......ba kowanne irin hali da dabi'u yake tolerating daga waninsa ba......akwai wasu halaye da dabi'u da muddin kana dasu kada kayi kuskuren sha'awar yin rayuwa dashi. Yana da girmamawa don haka bayason raini,bai fiya daukan kansa da girma ba......amma kuma baya daukan raini wulaqanci ko qasqanci. Yana da dokoki......yana da iyakoki.......yana da layuka da yakam shata akan kowanne mutum da zaiyi rayuwa dashi.
RESPECT wani abu ne muhimmanci a tare dashi........baya wasa dashi baya yiwa wani wasa da mutuncinsa. Miskili ne irin miskilancin da idan ya motsa masa zaka jima kana rayuwa dashi baka gama fahimtar ya sound na muryarsa yake ba. Zai iya wuni guda kuna hira yana maqale da littafi abinsa,ko kunnensa ba zaku samu ba ballantana hankalinsa. Murmushi yafi zame masa amsa akan ya furta da bakinsa,dariyarsa tana da qaranci qwarai da ba kowa yasan launinta ba.......saidai duk da wadannan yana da zuciya me taushi......yana da wani irin kyakyawar zuciya me cike da dimbin alkhairi..... Irin alkhairin nan me sanyi da saka zuciya a mamakin mallakin zuciya me tarin alkhairi irin wannan.
"Na fahimci abubuwa da dama a tattare da ita a fitata da nakeyi cikin mutanen ta" Omari ya dora da fadi ganin ya samu daman hiran da yakeso yayi da haisam din. Taku biyu haisam din ya qarayi gaba,abinda ya tabbatarwa omari idan bai hanzarta ba haisam yana iya tafiya abinsa.
"Bata yana faduwa ba a dukkan komai.......itace gaba a kowanne abu da zai taso,ta tsani faduwa.......tana da wata irin izza da take rayuwa sama da izzar da sultane mahaifinta yake da ita. Ba kowa bane yasan fuskarta,ba kowa bane yasan muryarta,ba kuma kowa bane yasan ainihin kamanninta koda kuwa wadanda suke rayuwa cikin gidan.......a cewarsu har yanzu ba'a halicci mijinta.....su a karan kansu sunsan babu wata halitta data dace da princess akhnan hammud..........kaima kuma tana neman dukkan wata hanya da zata sake tsere da kai.....hakan kuma nasan baya rasa nasaba da faduwarta daka zama sila" Omari yakai qarshe yana miqa masa wayarsa bayan ya bude wani abu yana miqa masa.
Taku biyu haisam yayi ya dawo baya,ya kalli wayar da lumsassun manyan idanunsa kafin ya miqa hannu ya karba yana dubawa. Har yanzu murmushi ne shimfide saman fuskar omari,ya dade yana neman wannan damar da zaiwa haisam magana........yanason yaga dambarwar ya zata kaya. Yana ganin yawan saqonni daga hippodrome suna neman cikakken bayanai a kansa,da kuma yawan adadin request da suke sake turawa na shirya sabon race da zai zama globally gaba daya.