← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 97

Sashe 82

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In sha Allah.....saidai kada ka sanyani alqawarin yin ziyara a tsakaninmu saboda yanayin aiki" Dariya kadan mainassara ya saki yana jinjina kai

"Bazan sanyaka ba,har sai sanda ka gamsu da kanka,ko ni aka bani dama nazo" Kai haisam ya jinjina,ya kuma ja da baya da kansa yana rufewa mainassara qofar motar.

Tare suka taka da omari suna komawa ciki yana gayawa omari din wasu daga cikin abubuwan da omari xai iya sani.

"Mun kama hanya,inaji a jikina" Omari ya fadi,sai haisam ya gyada kanshi.

"In sha Allah,komai zai tafi daidai".

Lokaci ya duba sanda yake komawa daki,akwai sauran mintuna kafin ya fita agadez palace,don haka ya zauna ya soma lalubar number president na Ethiopia don bashi bayanan da suka dace,kafin nan kuma ya kira bobbo muhammad daud shima.

President Amaan Mikel andom wanda haisam yayi saving number dinsa da Mr amaan. Daya daga cikin tsayayyun shugannin qasa a tarihin Ethiopia da qasar ta samu,jajirtattu da sukayi tsaiwar daka a kanta.

Kasancewar masarautar jimma daya daga cikin masarautun dake da girma da qarfin iko.....kyakkyawan tsari na aiwatar da mulki da samarwa mutanenta ci gaba ya haifar ya kuma samar da kyakkyawan alaqa tsakanin gwamnatin qasar Ethiopia da masarautar. Uwa uba tsirowa da kuma samuwar jajirtaccen dan kishin qasa,qwararren ma'aikacin national intelligence and security service prinsii muhammad haisam cikin masarautar jimma,wannan ya qara zurfafa alaqa a tsakaninsu.

Samun irin haisam cikin hukumar abune me wahala,matashi me ji da gata fikira kyau uwa uba ga sarauta a gefe,amma hakan bai hanashi jin sha'awar taimakaw qasarsa da dukkan fikirar da Allah ya bashi ba.

Muhammad haisam din yayi ayyuka masu tarin yawa.....ayyuka masu zafi wadanda ba'a taba yin irin su a tarihin hukumar ba,wannan ya sanya sosai mr President Aamani yake ji dashi.

Tun ba'a wani jima ba yaso hadashi da d'iyarsa,shalelensa wadda ita daya ce 'ya mace daya haifa wato HAANA amma a hankali da kanshi ya fahimci hankalinsa baya ta gurin. Duk da hakan bai sanya ya janye qudurinsa ba,yaci gaba da qarfafa alaqar zumunci a tsakaninsa da haisam,a tsakaninsa da masarautar jimma ta dukkan hanyoyin da suka dace,yana sanya ran watarana alaqa me qarfi ta qullu tsakanin haisam din da haana.

*MOMMA*

Daga waccan ranar har kawo yanxun da take tsaye gaban closet dinta bayan ta ciro wata alkyabba da aka samar da ita daga wani silk material me tsadar gaske tana sakata a jikinta......hankalinta da tunaninta gaba daya bai sauka daga kan akhnan ba.

A kowanne rana tana sanyawa cikin sirri ana laluba mata halin da take ciki. Koda kebe kanta da tayi na wadannan kwanakin tana kwanciya ne ta kuma tashi da tunaninta ya take ciki?,me takeyi yanzu?,me yake gudana a kewayenta?.

Koda sau nawa akhnan zata aikata laifi.....koda meye zatayi batajin zuciyarta zatayi nesa da ita,zuciyarta zatayi nesa daga soyayyar da take mata,wanda wani bangarene kawai na soyayyar safeena da tayi fiffike ta sauka a kanta.

A nutse ta waiwaya tana duban falaak data shigo dakin da sallama gami da amsa mata sallamar,rungume take da litattafanta,wani kwantaccen murmushi yana fita saman fuskarta. Idanunta ta lumshe ta kuma budesu duka lokaci guda,a kwanakin nan wani nutsuwa da tarin walwala momma take hanga shimfide saman fuskar falaak din. Ga wata irin nutsuwa data sake fahimtar tana shigar falaak din,duk da dama ita din bame hayaniya bace ko zafi surutu ko rawan kai,saidai tana da kuzari sosai da hira ga duk wanda ta aminta ta kuma saki jiki dashi.

Sake duban falaak din tayi,dukka yanayin dressing dinta yana sake canzawa,duk da dama can ita ba ma'abociyar shigar bayyana tsiraici bace,wannan din tarbiyyar hairaan ce......hairaan kuma rainonta ce,duk kuwa da cewa suna rayuwa cikin masu jajayen kunne,to amma wannan yanayin dake tattare da falaak na dabanne.

Har a cikin ranta,har kuma zuciyarta tana jin cewa inama ace biftu ce ta samu dukkan wannan kamalar?,inama ace biftu ce ta samu wannan nutsuwar?,inama ace biftu ce ta samu wannan walwalar?.

"Momma" Falaak ta furta a shagwabe,tana waving hannunta saitin fuskar morsa safiyya.

"Momma wannan kallon kamar bakisanni ba?" Ta sake fada a narke. Murmushi morsa safiyya tayi,tana qoqarin maida hankalinta jikinta gami da soma gyara rigar jikinta.

"Meye ne haka yake sauyamin ke falaak?,ko dukka karatunne?" Wani qawataccen murmushi daya qara bayyana kyan falaak din ya qwace mata,wata 'yar qaramar kunya da batasan me ya haddasata ba ta taso ta rufeta,saita matsa tana taya morsa safiyya gyara rigar jikin nata.

"Ko dadin karatun sheikh muhammad dinne?" Morsa ta sake fadi tana fatan samun wani haske da zuciyarta ta jima tana haska mata shi.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

Irin murmushin dazu ta kuma saki tana fara sawa morsa safiyya maballan rigar.

"Nima ban sani ba momma.....kawai dai ya iya karatu gaskiya,yana da wani irin fasahar koyar da karatu,bani ba hatta badeea tace bata taba jin dadin karatu irin nasa ba.....momma ilimin dake kanshi da fasahar dake harshensa yafi qarfin koya karatu a gida......jami'a ya kamata ya tafi cikin dubannan dalibai.....momma har yanzu mamaki nake,jikina yaqi gamsuwa da cewa shi din gama garin malami ne kamar kowa". Shuru morsa safiyya tayi,tana jin yadda falaak din ta tsinke da surutu har fiye da bayaninma da momma din ta tambayeta.

Murmushi ta saka me dan sauti,a hankali ta soma takawa.

"Nagartacce ne kenan?" Momma din ta fadi ba tare data waiwaya ta dubi falaak ba,don batason ta bata haske akan wani abu take zargi. Tasan falaak sarai,tana da wani irin alkunya,tsaf zata tsinke zaren zancan ba tare kuma da ita takai ga gaci ba.

Idanu falaak ta fidda waje tana qaramar dariya.

"Momma......idan nace miki har yau sau daya tak ya taba kallona zaki yarda?" Har cikin ranta momma din taji mamakin abun,amma sai tace

"Kaman yaya?,shi baya kallon mutane ne?".

" Momma.....bama kallo kawai ba,ko magana sau daya zuwa biyu take hadamu har a gama karatun,idan kinga yana sake fuska to da aaera ne,don ko da Aafreen ba sosai ba.....na fuskanci yana da tausasawa da tausayawa ga yara,yadda yakewa aeera karatu daban da yadda yakewa Aafreen,nima yadda yakemin daban da yadda yakewa Aafreen,wani irin qasaitaccen murmushi yakeyi momma,saika lura sosai kake iya banbancewa.......me kyau dashi momma".

"Halan ke tsira masa idanu kikeyi ko?,bayan shi kame ganinsa yake?" Maganan momma din kenan data dawo da ita hayyacinta.

Bakinta ta rufe tana dariya gami da girgiza kai,sai a sannan taga kaman maganganun data saka sunyi yawa.

"Aah fa momma.....idan zanyi tambaya ne ko shi ya tambaya wani abun,ko idan yana yiwa su Aaera karatu......"

"Sai kita qare masa kallo kafin azo kanki kenan ko?". Wata qaramar tsawar kunya ce ta buga cikin kan falaak,kaman zata nutse a wajen. Ya akayi momma ta gano ainihin gaskiyar qarshen zancan?.....da gaske ne,tana yawan satar kallonsa idan suna karatu dasu Aafreen kafin ya sallamesu yazo kansu,amma daga nan bata iya sake kallonsa,saboda wani mugun mahaukacin kwarjini yakeyi mata,idan yazo musu karatu duk sai taji ya cika gurin da kwarjininsa,wannan qamshin da bata taba jin makamancinsa ba,hannunta har rawa yakanyi wasu lokutan,tana samun lalubo nutsuwar ta ne da zarar ta gama biya karatun jiya baice komai akai ba,alamun ta iya ba gyara ba kuskure.

"Saura awa daya ku shiga aji,kinsan dokarsa ai ko?" Momma ta fada tana takawa don ficewa daga dakin,ganin falaak ta daskare a wajen ta kasa cewa komai.

Saida tayi nisa sosai da gurin sannan murmushi ya kubcewa momma din. Ta soma tariyo maganganun falaak da kuma yanayinta. Tun daga sanda taga irin yabon da sultane yayi masa,da kuma daukansa a mazaunin mashawarcinsa na musamman taji dari bisa dari ta yarda dashi. Ballantan Aeera da kowanne lokaci cikin hirarsa take?.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

Page 71
_____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________

Ajiyar zuciya ta sauke me nauyi,fatanta da mafarkinta a kullum shine,Falaak da akhnan suyi auren isa da qasaita.......idan tace hakan bawai tana nufin qasaitaccen namiji me kudi ba.....aah qasaitaccen namiji tsayayye isashe ma'abocin sanin haqqoqin matarsa akansa. Wanda zai tausayawa ainihin rauninsu na diya mace......zai riqesu bisa gaskiya da tsantsar amana.....koda rayuwa tazo da juyin da duk wani abu me daraja a tare dasu zai tafi ya barsu,kyau ne mulki nasaba ko dukiya?. Wanda bazai wulaqantasu ba bayan sun rasa dukkan wadannan abubuwan,wanda zai zame musu mijin HUCE HAUSHI......namijin kerewa sa'a da nunawa duniya gurin samun kulawa kariya da kuma riritawa.

GARKUWA take nema musu a sanda duniya zata iya harar rayuwarsu.......DIRKA take nema musu a sanda duniya ke neman ruftowa saman kawunansu.......MAFAKA a sanda rayuwa zata iya kadasu kota hargitsa su.

Indai ya zamana wani al'amari ya darsu a zuciyar falaak game da sheikh muhammad haisam.......lallai zatayu bacci cikin nutsuwa cikin rayuwarta,zatayi bacci harda minshari bisa samun tabbaci da yaqinin kyakkyawan zabin da falaak ta yiwa rayuwarta,saidai fatan ta samu kwatankwacin abinda take tare dashi daga gareshi.

Amma can qasan zuciyarta zataso ace dukkan hakan ta kasance da akhnan. Hakeem kusan yana da wasu daga cikin qualities din daya sanya taji ta aminta da hadinta dame martaba......amma akwai abu daya da har yanzu yake tantama a kansa. Hakeem bashi da ZAFI bashi da ZARRA baida TSAIWAR DAKAN da take tunanin ita kadai ce zata bashi daman juya akhnan......ita daya ce zata bashi daman tafi da ita a sunan matar aurensa. Har a qasan ranta takejin kamar shi din BA JAJIRTACCE BANE.....irin jajircewar da take buqata take fatan ta kasance cikin jini halayya da dabi'un dukka mijin da zai zama mallakin akhnan din,domin sune abokan tafiyar iya zama da wannan TAURIN KAN nata,sune abokan tafiyar wannan KAFIYAR TATA.
Chapter 82 · 0% Book details