Sashe 61
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zamewa kadan akhnan tayi daga riqon mammina.
"Me kikeyi na ba daidai bane?,ko yaushe baki iya ba?,ko yaushe kome zaki mata ba daidai bane?" Akhnan ta fadi a zafafe.
Fes ya fahimci wannan fushin,wannan taurin kanne ya motsa,saita riqeta sosai
"Indai na isa dake muje kawai" Ta fada tana duban tsakiyar idanunta.
Wani sauka taji ta soma yi,ba musu ta juya a hankali tana takawa mammina na take mata baya.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Qasa da kanta morsa safiyya tayi,don taji dukkan abinda akhnan din ke fadi. Wani irin d'aci ke zarcewa maqogoronta tun daga saman harshenta,kalar d'acin da jinsa ya zame mata jiki,amma har yanxu ta kasa daina jinsa.
"Safiyya" Sultane ya kirata a tausashe yana tsareta da ido.
"Allah ya taimakeka" Ta furta a nutse tana motsa labbanta da tun dazun taji sunyi mata nauyi. Sarqafewa idanuwansu sukayi guri daya ita dashi,kafin ya janye nata idanun zuwa wani sashe na daban.
Ya sani,shurun safiyya yana nufin abubuwa da dama,duk da cewa ba komai take iya yiwa shurun ba,ba kuma komai take iya ajiyarsa a ranta ba......amma muddin akace tayi shuru,to tayi shurunne,ba kuma zata qara magantuwa akan komai ba.
Ta sani baiji duk abinda akhnan ke fadi ba,don sautinta bame qarfi bane duk iyakar inda takai ga yin magana cikin bacin rai,a daidai lokacin kuma hankalinsa ya tafi sosai akan wayarsa da batasan me ya janye masa hankali akan wayar haka karon farko ba.
"In sha Allah......zan tabbatar da zamana mahaifi kaman kowanne uba.......in sha Allah" Ya fada yanason karanto wani abu ko yaya dake ranta. Sake daga kanta tayi tana sakin murmushi a hankali kafin tace.
"Allah ya baka iko.....ya qarfafeka a dukka lamuranka" Idonsa ya lunshe shima yana gyada kai.
"Ameen..........yaghana ta dawo.......yanzun nan suna filin jirgi". Wani murmushi ne ya subuce mata,wanda sam bata ma shirya fitarsa ba.
"Alhamdulillah" Ta fada a fili walwalarta tana qaruwa. Watanni bakwai da sati shida kenan da barin yaghana masarautar agadez,watanni bakwai din da suka dinga zuwarma morsa safiyya da wani irin tsanani,bata taba zaton yaghana tana da wani muhimmanci me girma haka a rayuwarta ba sai sanda tayi nesa dasu. Duk da kusan cikin kowanne motsi da kai kawo a masarautar tana tare dasu,amma wannan nisan dai bai canza daga yadda yake ba.
Yaji dadin yadda karon farko albishir dinsa ya saukar mata da fara'a d walwala,ya gusar da wannan yanayin daga fuskarta,sai yadan tsokaneta kadan.
"Yanzu zami fara cike takardu kafin samun damar ganinki kenan,tunda yaghana ta dawo?" Murmushi tayi tana girgiza kai.
"Duk muhimmanci da yaghana ke dashi,bana tunanin ta kama qafar naka". Shuru ya danyi yana jinjina kai,duk da yana kokwanto a maganarta.
" Yanzu sai ina kenan?" Ya tambayi safiyya dake gyara babbar rigar da take ta'ammali da ita a duk sanda zata baro sassanta don sake suturce jikinta.
"Ba wanda ya gayawa isowarta yau,ina tunanin harkai......dole akwai buqatar shirin gaggawa" Ta kammala fada tana rufe jikinta ruf zagayayyar fuskarta dake yawan tuna masa da safeena ta bayyana. Sai yaja numfashar cikin hunhunsa sannan yace.
" A sauka lafiya"
"Godiya nake" Ta furta cikin rusunawa ta juya tana takawa da wannan nutsuwar tata da ba abinda ya banbantata data safeena.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 51
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________
*AKHNAN*
"Tayi nasara.......tayi nasara mammina......tayi nasarar shiga tsakanina da mahaifina,ki gayamin mammina.......wai da gaske ne?,da gaske ne wannan alaqar da kike cewa akwai a tsakaninmu?,da gaske ita din uwace a gurina?". Akhnan da Fuskarta ta sauya launi zuwa pink da sirki sirkin red ta fada tana takowa cikin izza ta tsaya a gaban mammina kai tsaye tana dubanta.
Hannunta mammina din ta kama,a tausashe ta jata ta ajjiyeta saman sofa bed,sannan ta jawo ottoman ta zauna akai tana dubanta.
"Babu wani kuskure ko qarya a cikin abinda kika sani,abinda kika sani din dai shine xan yita maimaita miki.......biftu,ba buqatar ki damu da kowa a duniya muddin mammina dinki na tare dake.......ba buqatar damuwa da kulawar kowa indai mammina na nan..........maganan sultane ta gobe kada ta razanaki.......kada tasa ki rasa wannan izzar taki.......kar tasa ki manta matsayinki,kada kuma tasa ki manta ke wacece..........idan bakisonshi shima,hakance zataci gaba da tabbata,ba wanda zai canza ko ya kaiki bigiren da bai dace da ra'ayinki da tsarinki ba......ki daina dimauta.......ki nutsu kici gaba da tuna matsayinki......ki nutsu kici gaba da riqe wace ke a ranki". Wani ajiyar zuciya ta sauke tana son ta koma saitinta kamar yadda mammina ke buqata,saita harde hannayenta a qirjinta,tana zuqar iska tana fesarwa a hankali tanason saisaita zafin da zuciyarta takeyi.
"Da kyau......." Mammina ta fada tana sake riqe hannunta da kyau.
"Babu wani da zai canza wannan soyayyar......ba wanda yake da qarfin jirkitata koda morsa safiyya ce" Ta sake fadi cikin son bawa akhnan din dukka qwarin gwiwa.
*HAISAM*
Ba dabi'arsa bace kaiwa nisan dare har haka kafin yaci abinci,amma a ranar sai a qalla kusan tara na dare ya zauna cin abincin dare.
Addisaleem ne tsaye gaban table din,ya bude dukka warmer din dake dauke da nau'in abinci kala biyu,abun sha guda daya sai coffee,sai kuma hadin salad guda biyu,don qa'idarsa ne,ko meye zaici sai ya tabbatar akwai ganye da fruit a kusa dashi.
Duka nau'in abincin dake kan table din kalar abincin yaren oromo ne da haisam din yafi so. Addisaleem ya qarasa shirya komai,yaja baya cikin girmamawa ya basu guri shida omari.
Shuru gurin yayi,don ba kasafai yake magana ba idan yana tsaka da cin abincin. Ruwa omari ya dauka yasha ya ajiye,ya kasa haquri kuma ya kasa shuru jin baice dashi komai ba,sai yayi dan gyaran murya kadan.
"Ya ranar farko ta kasance cikin masarautar agadez?" Yayi tambayar yana kai lomar abinci bakinsa.
Zagayayyun almond eyes dinsa ya daga ya dubi omari,sai ya lumshesu hadi da janyesu,ya kuma nunawa Omari plate dinsa kawai ba tare da yace komai ba,yaci gaba da cin abincinsa a nutse.
Murmushi Omari ya saki yana maida hankalinsa ga abincinsa. Alamu dukka sun nuna yau mutanen ne a kusa,'yan miskilanci,shi kuma labari yakeson ji. Yanason yaji ya nasu gidan sarautar yake?,meye banbamcinsa dana jimma?.....dame yafi nasu,bazai qyaleshi ba kuwa sai yaji.
Bai samu wannan damar ba hussam yayi kiran haisam din a waya,sai ya ture abincin kadan,ya daga wayar ya karata a kunnensa
"Hello" Hussam ya fadi yana tattara hankalinsa a jikinsa.
Dif haisam yayi masa yana shafa sumarsa gami da dan lumshe idonsa,duk da ya bashi alama da zata saka ya fahimci yana jinsa.
"am dhiifama(ina bada haquri),assalamu alaikum warahmatullah" Hussam ya gane kuskurensa da kansa ya kuma gyara. Ya manta sam haisam din baya daukar dabi'ar hello,kusan dukkaninsu sun saba da fara furta sallama a waya kafin komai,kuma duk ta dalilinsa ne hakan.
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Ya amsa masa da muryarsa data sake wani irin sanyi,yana jin dukka gabbansa sun gaji,duk da ba wani abun azo a gani yau din yayi ba.
"Kana lafiya obbo?"
"Alhamdulillah.........ya nanay take?" Ya tambayi hussam din. Yaso kiran nanay yaji lafiyarta,yau duka basuyi waya ba,to amma bayason yayi magana da ita lallai zata ji muryarsa ba yadda ta saba ji ba,kuma yasan halinta sarai akan duk abinda ya shafi yaranta,yanxun nan zata shiga damuwa.
"Tana lafiya obbo.......yanzun muka gama magana da Mr Hambaa......."
"Tole(alright)........ina jinka".
"An fidda ribar turaruka na kamfanin SHEBA SCENT da SELAM PERFUMES......."
"Uhmmm" Haisam ya fada a nutse yana sauraren hussam. Qaramin dariya hussam ya saki.
"The amount is incredible obboo......wannan shekaran ya kamata kayi aure " Ya furta yana dan danne murmushinsa. Bayaso haisam yaji,yana kuma son ya fahimci da gaske yake maganan.
"Hussam......are we age mate?" Ya fadi da seniority dinnan nasa da wani lokaci yakanyi amfani dashi akan hussam din,don hussam din ya cika wasa.
"Dhiifama" Ya fada yana gyara mode dinsa.
Zamansa haisam din ya gyara yana duban wayar.
"Ka zauna lallai a qarasa sauran lissafin daya company din,a fidda zakka da sauran kudaden da aka saba fitarwa,ragowan ka saka a account din nanay". Idanu hassam ya zaro dukka waje.
" Account din nanay obbo?". Ido ya lumshe sannan ya bude.
"Bakaji bane na maimaita?". Kansa hussam ya sosa.
"Naji captain......amma kuma,the amount is too large obboo".
"Nikam hussam......akwai wata shawara da nace ina nema daga gareka ne?" Kai ya girgiza da sauri,don tuni ya fahimci inda haisam ya dosa,bai sake cewa komai ba,har haisam din ya zare wayar ya kasheta yana fesar da iska.
"Baka ce komai ba har yanzu?.....ko akwai wani abu da ba daidai ba?" Muryar Omari yaji daga bayansa yana tahowa.
"Ya salam" Ya fadi a fili,abinda ya bawa Omari qaramar dariya kenan,ya dawo gabansa ya zauna.
Idanunsa da suka shanye kaman wanda bacci ya fara kamawa ya zubawa Omari,kallon daya sanya Omari fahimtar yau dai akwai abinda ya taba masa rai.
"Ba wani labari Omar,idan akwai zakaji" Ya fadi yana miqewa gami da kwasar wayoyinsa.
"halkan gaarii(goodnight)" Omari ya fadi cikin sauqaqewa kansa yana miqe bayansa cikin sofa din gurin,ya fidda wayarsa don rage wani aikin.
Bazai tsaya jayayya da haisam ko damuwar sai yaji komai ba,yasan halinsa shima ya iya hutsancewa wasu lokutan,musamman akan abinda bai shiryawa yi ba,shi yasa ya sauqaqewa kansa wahala na barinsa ya tafi.
Duk wani haske na dakinsa ya rage yabar na gefan gadonsa. Littafi biyar yana daukowa yana sauyawa amma duka yau sai yaji bayajin karsashin karatun,sai kawai ya miqe yana zura lausasan slippers dinsa,ya dauki wayoyinsa ya sauka a hankali zuwa library.
*MAMMINA*