← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 97

Sashe 5

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai data zare jikinta daga na mammina sannan ta gyada kai. Qasan ranta kawai takeji wannan din bata lokaci ne da kuma bata bakinta kawai da mammina keyi din,gaba daya tsakanin jiya da yau tana jin kamar an bata mata awanninta ne kawai,tasota da sultane yasa akayi tun daga niamy......ya banbareta daga kan aikinta,ya barota daga ayyukan kamfaninta da take tsaye a kai,wani abu guda da bata taba gajiya dashi.......wata hidima qwaya daya da bata taba jin ta qosa da ita ba.......hidimar kamfaninta........kasuwancinta........kuma babbar kadarar da kaf cikin kadarorin sultane Muhammad hammud babu me kima da darajarta........wadda soyayyar da yake mata ya sanyata sallamar da ita ga AKHNAN din. Wannan din wani abu ne da yayi matuqar girgiza zukatan mutane da dama.........abune da ya bada mamaki ainun cikin masarautar gaba daya. Wani abune da ba'a taba hasashen faruwarsa ba tsahon zamanin,domin kamfanin ZUCIYA ce ta dukiyar sultane dama abinda ya mallaka.

Faruwar abin ya bude wasu qofofi da dama da a baya suke a rufe.....ya bude wasu qofofin da ba'a taba tsammanin budewarsu ba.......ya kuma qarasa bude wasu da motsi kadan suke jira su bude din. Yabar wasu irin tabbai.....da muhimman al'amura cikin zukatan mutane da yawa.......hakanan ya gadar da wani gagarumin shirin QUDURI da baisan zai zamewa rayuwar AKHNAN din BARAZANA BA......barazanar da take ci gaba da bibiyarta ba tare da idanun masu kallo nazari ko hasashe sunkai kai ba.

Da kanta mammina din ke biye da ita a baya tana kuma jeranta mata addu'o'in samun daidaito tsakaninta da altaab nu'uman,addu'ar da akhnan ke ji tana mata yawo akai da zuciya......tanason cewa mammina tabar addu'ar nan haka don bata tunanin zatayi amfani a wannan muhallin da gurbin,saidai miskilancinta dake a kusa ya hanata buda baki tace da mammina komai.

"Allah shi ja kwananki.........Allah shi karya maqiyanki". Kakkaurar muryar ta karade parlorn farko da mammina......wanda daga shi sai 'yar farfajiyar da zata fiddaka da sashen.

A nutse akhnan ta daga kanta tana ajiye dubanta daga sashen da take jiyo sautin. Tamim ne,mutumin da har yanzu ba zata iya tuna ko tantance lokacin daya samu kansa wanze cikin masarautar ba. Bama ita kadai ba,kusan duk wanda ke cikin masarautar bazaice ga sanda tamim ya zama halalin masarautar ba......ba wani wanda zai iya dorar da komai a kansa........an wayi gari yana rayuwa a masarautar kamar sauran al'ummar masarautar........kamar kuma yadda sauran hadiman cikinta ke rayuwarsu.

Yana da wani irin ladabi da ya siya masa kusanci da qauna me tarin yawa daga wajen mammina..........yana da wani irin biyayya da d'a sama da biyayyar bawan da ubangidansa ya zuba kudade masu kauri ya siyeshi........tamim din ya samu wani kusanci da sultane muhammad hammud ta hannun mammina din,wanda ha jima da zama dan gidanta.......kuma amintaccenta da ya kasance lamba na daya a bangaren maza hadimai na gidan. Yadda yake nuna qauna da kulawa ga akhnan........yadda yake nuna sadaukarwarsa akan duk wani sha'ani nata.......yadda yake nuna fansar ransa game da masarautar agadez dama duk wani lamari daya shafeta ya sanya ya sake samun shiga sosai wajen sultane muhammad,ya bashi yabo ya kuma bude masa wata qofa ta aminci yarda da kuma kusanci.

Tun kafin ta gama zama KHADEEJA take ganin irin wannan tsananin girmamawa daga tamim. Girmamawar da har qasan ranta duk da tarin izzarta da sarautar dake yawo a jininta takejin tafi qarfin nata girman. Ba zata taba iya tuna wata raba qwaya daya ba tun bayan data mallaki hankalin kanta da tamim ya taba tsaiwa a gabanta alhalin tana tsaye ba bare kuma a zaune,ba zata taba tuna wata rana guda daya da tamim ya hada idanu da ita ba ko ya gaidata yana sanya idanunshi cikin nata ba. Ire iren wadannan abubuwan suka sayawa tamim din wata 'yar daraja kadan daga gareta,duk kuwa da cewa ba zaka taba fahimtarta akan hakan ba koda da motsin yatsan hannunta ba.

Abu guda daya ne da har yanzun takeji game dashi,bai kuma taba gusawa ko motsawa daga ranta. Yanayin zubin halittarsa da qirarsa da idan ka kalla zakaga tasha banbam data sauran mazajen qasar agadez......hakanan kuma tayi banbanci da dukka qabilun dake qasar niger gaba daya. Idan kayi masa kallon farko aka ce maka

"Wannan din mutumin kirki ne" A karon farko zaka qaryata hakan,don babu wata siffa tashi guda daya dake nuna haka,saidai kuma mu'amalarsa sauqin kansa da kuma irin girman daya runguma yake basu gaba daya zai gaya maka gaskiyar abinda aka gaya maka da farko.

Ta gota tamim da taku kusan uku,amma haka kawai taji kamar an fusgi hankalinta. Ta waiwaya kadan ta saci kallon inda yake duqe har a sannan kanshi a qasa,mammina kuma na tsaye a gabansa ta dakata daga tattakin da take musu.

"Wanne irin yarda da aminci ya samu daga wajen mammina ne?,har yake iya ruskar inda take kai tsaye?,baya ga tarin dogarawan dake gadin sassan?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar dake yawo qasan ranta.

"Yana da kirki da sauqin kai,amma har yanzu na kasa sabawa da ganinsa,sai na dinga jin shi dabanne a cikinmu" Akhnan ta furta a hankali da yanayin daya sanya aisa waiwayowa ta kalleta. Maida dubanta gabanta aisa tayi sannan a hankali tace.

"Komai naki ya bambanta dana mutane akhnan.....ki yawaita addu'ar daidaituwar dabi'unki dana kowa......kirkinsa shine abun dubawa ba wani abu na daban ba" .

Shuru tayi maganganun aisa suna dawo mata. Ita ta sani a karan kanta ba kowa bane yake iya fahimtarta ba,ba kowa bane yake iya karanta badinin halayenta ba,shi yasanya sau tari takan zabi yin shuru akan yin wasu bayanan........takan zabi yin shuru akan yin wasu maganganun.

*MOMMA*

Kamala gami da haiba ne suke magana da kansu a dukkan wani taku qwaya daya da zatayi zuwa kebantaccen parlor dinta da takan gana da baqin da suka kasance na musamman a wajen ta.

Doguwace irin tsahon da zaa kirashi da tsaka tsaki,irin tsahon da yake qarawa mace kyau kawai bawai don ya sanyata cikin jerin sahun kyawawan mata ba.

Sanye take cikin tufafin al'ada na cikakkun buzaye,tufafin da aka zamanantar dashi da wani irin sakakken dinki daya suturce jikinta gaba daya ya kuma qara mata kwarjini da cika idanu.

Ko ba'a gaya maka ba kana kallonta kaga buzuwa..........irin buzuwar da ko a cikin qabilarsu da yaren nasu ma ta musamman ce ita. Farace qal kamar zaka ita hangen jijiyoyin dake kai saqon jini a jikinta.........hannuwanta da qafafunta sunsha qunshin jan lallen da ba'a masa kowanne irin ado ba,an qunsa ne bisa siga da yanayin gargajiyar da aka saba. Koda kanta yake a lullube amma hakan bazai hanaka ganin tudun sumarta dake daure cikin lallausan farin mayafin data yane kanta dashi ba. Lokacin da qafarta kuma ta taka matakale qarshe mata biyun dake tsaye a gurin kamar masu jiran isowarta suka fara gaidata.

"Barka da saukowa......barka da fitowa".

"Barka kade.......sannunku da hidima mamo sannunku samia" Ta amsa musu cikin kulawa da yanayin nan nata na girmama dan adam koda wayeshi.

"Armelle ta iso?" Ta sake tambayarsu tana takawa a tsanake ga hanyar da zata kaita parlor din.

"Ta qaraso......tadan jima tana tsimayinki ma". Wadda aka kira da mamo ta fada tana kama stairs din saman nata,don ita da samia suke kula da tsaftar makwancinta.

"Yayi kyau" Ta amsa tana dokin isa ga armelle din.

"A fito lafiya" Samia ta fada tana bin bayan mamo zuwa saman.

"Allah yasa" Ta amsa su tana buda qofar da zata kaita ga parlor din.

Babbar macace zaune cikin parlor din saman tattausan kilishin dake mamaye a parlor din. Wani irin ni'imtaccen muhalli ne maras hayaniya wanda ke dauke da kalolin peach da coffe light,tare da wani lallausan qamshin apple freshner daya wadatu dashi.

Baqa ce kakkaura,wadda kana kallonta kasan ta fito ne daga qabilar Agadasawa. Sanye take da wasu irin tufafi tamkar na saqi ruwan bula me turuwa sosai da har ya sanya suka kasance masu duhu kadan. Akwai wani haske na nutsuwa saman fuskarta,tare da wata kamala da bata rasa nasaba da riqon ibada.

"Barka da fitowa" Ta furta tana miqewa da ganin fitowar momma.

"Barka kade armelle........zauna" Ta fadi kafin ita din takai ga zama tana mata nuni da kusa da ita.

Zamewa tayi ta zauna satin qafafunta sosai tana tattara nutsuwarta.

"Allah shi taya miki......"

"Ya ake ciki armelle?" Ta tambayeta qagauta da jin bayanan daga bakin armelle din yana sake fitowa sosai saman fuskarta.

"Altaab nu'uman ya iso masarutar nan" Armelle din ta fada a taqaice.

"Alhamdulillah" Momma ta samu kanta da furtawa,kalmar data fito hade da wani nannauyan numfashi,saita maida bayanta ta jinginar ga jikin kujerar da take kai alamun samun rangwame daga duk abinda takeson ji din yana zagwanye daga fuskarta.

"Armelle" Ta kirata a nutse.

"Ranki shi dade".

"Ina buqatar cikakken rohoto game da yadda komai zai wakana,ina kumce sauraron jin daddadan labari".

*Zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*MYNITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*
Chapter 5 · 0% Book details