← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 97

Sashe 49

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akwai sauran lokaci,ki wanka ki huta kadan,don sultane ya fita,amma a gida yace zaiyi sallar isha'i,kafin sannan saiki shirya ki shiga ki gaida mommanki". Duban mammina tayi,tana jin ranta yana baci yanzun nan.

" Momma na?" Rai mammina ta hade tana kuma daga mata kai alamun eh. Yadda yanayin mammina din ya canza ya hanata sake cewa komai,sai ta miqe kawai ta soma zare kayan jikinta. Ta kammala tsaf ta barsu a zube a gurin ta daura towel tana wucewa bathroom din dake da sassa biyu,toilet da bathroom din kansa.

★A nutse sanye kuma da budaddiyar abayar data rufe ilahirin jikinta ta kuma sake qawata shigar tata da dan qaramin Malaysian hijab take qarasowa inda morsa safiyya take.

Kebantaccen guri ne da ta ajjiyeshi kawai saboda ibada,ko da tsakiyar dare,ko bayan sallar magariba ko bayan sallar asuba.

Daga kai tayi tana duban falaak din sanda take zama a gabanta,takai qarshen addu'ar dake bakinta sannan tace.

"Ya akayi?". Kadan tadan yamutsa fuskarta.

"Tun dazun akace tazo.....amma banga ta shigo gaidaki ba momma" Sosai morsa safiyya ta zubawa falaak idanu,tsoro yana neman yin tasiri a ranta. Tsoron wani abu takeyi,tana tsoron faruwar wani abu.....wannan abun kuma da idan ya farun zai sake jaddadawa zaitun nasararta.

Wannan jarumar zuciyar tata ce ta motsa,ta kuma mamaye duk wata fargaba tata. Murmushi ta saki tana ajiye dan qaramin littafin azkar din dake hannunta.

"Annabin rahama S A W yana cewa:- duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira,ya girmama baqonsa.....biftu a yau da kuma kwanakin da zatayi tabar gidan nan duka baquwarmu ce.....ke me kikayi don girmamata a matsayinta na wadda take gaba dake?" Morsa safiyya takai qarshen maganar tana duban idanun falaak. Idanu falaak din ta zubawa momman tata,so take ta bambance kariya momma take bawa akhnan ko kuma dai tana fadin abinda da gaske haka ya kamata ya kasance?.

Ta karanci hakan a tattare da ita.......ta kuma gane me takeson karantowa,don haka ta sake lullubeta.

"Kin manta?,kinmin alqawarin kusantar da kanki da ita?,kinmin alqawarin zaki tayani ta koma kamar yadda nakeso?,ina wannan alqawarin falaak?". A hankali sai fuskar falaak din ta washe daga wani kaso zuwa qasa da hakan.

"Na sani,nice nayi alqawarin,kuma zan cikashi momma" Dubanta morsa safiyya keyi tana jinjina kai. Koda falaak bata daukota a komai ba,amma ta dauko dabi'arta ta cika alqawari......ta dauko halayyarta ta cika magana muddin ta fadi zatayi,don haka ta bita da murmushi.

"Naji dadin hakan,Allah yayi miki albarka,ya kuma baki damar cikawa kaman yadda kika dauka".

"Ina zuwa" Falaak din ta fadi tana miqewa a nutse da zummar ficewa a dakin,sai hakan ya tunawa da morsa maganan da sukayi da ustaz Ousmane dazu.

"Gobe bayan sallar la'asar sabon malaminku zaizo,zaku dinga zama karatu juma'a da asabar,qarfe hudu da rabi na yamma zuwa shida,awa daya da rabi zai dinga yi ba kaman ustaz Ousmane ba da yake awa biyu ba harda rabi......yana da qa'idojinsa,bayaso kuma a karya masa su". Fadin qa'idojin ya sanya falaak dakatawa,ta kuma waiwayo sosai tana duban momma fuskarta na yamutsewa.

Fata take kada dokokinsa su zamana masu tsauri kuma masu takura......don muddin hakan ya kasance bata jin tafiyarsu zatayi tsaho. Ta sani,ba wani hukunci da zai musu momma ta qalubalanceshi,duk dama bata tunanin koda kallon banza akwai malamin da zai iyayi musu ballantana kuma takai ga hukuntawa.

"Dole ku dinga rigashi isa gurin karatun kafin ya qaraso.....idan ya rigaku isa har sati uku a jere akwai hukunci" Momma ta fadi murmushi yana subuce mata. Haka kawai takejin abun da malamin yana burgeta. Ba abu bane me sauqi don zaka koyar da yaran masarauta......masarautarma diyoyin cikin sultanr ka rattaba musu dokoki hankalinka kwance,bin dokokin kuma shine damarsu ta daukan karatu a wajenka.

"Momma......baisan......"

"Ya sani,kada ma ki tambayeni,amma hakan shine daidai,kuma a raina naji cewa sai yanxu kuka samu malami irin malamin da nakeso,duk da ban sanshi ido da ido ba.......girmama karatu akan dalibi dashi.....kasan girma da martabar abinda ake koya maka,kin manta ne?". Kai falaak ta jinjina,duk da haka tana jin kamar ya cika jaye jaye da yawa.

"Allah ya kaimu" Ta fadi kawai tana juyawa tana fita a dakin,a qasan ranta kuma tana juya wanne irin malami ne wannan?.

Duk da takan shiga kitchen lokaci bayan lokaci,don girki yana daya daga cikin abubuwan da sukan bata nishadi,amma sosai a yau ma'aikatan dakin girkin sukayi mamakin shigowarta da kanta. Sun sani,tana da sauqin kai irin wanda sam ba zaka hadashi da na 'yar uwarta ba.....tana da sassauqar mu'amala da kowa ma zata iya mu'amalanta.

"A hadamin duk wani abu me muhimmanci da akasan yaa biftu tana son ci yanzun nan......nimra ki zubasu a kwando zamu wuce sassan mammina".

Sak kowa yayi cikin kitchen din,har ita da kanta ta karanci haka,saita dakata da zabar inibin da aka shigo dashi yanzu cikin kwando me yawa ta kalli fuskokinsu.

"Lafiya dai?" Ta tambaya tana son jin amsa.

"Ai ranki ya dade.......ba wanda yasan abincin da tafiso taci kaf gidan nan......inajin illa mutum uku,giwa mammina......buhaina sai birra" Girarta tadan yamutsa abun yana daure mata kai. Wasu abubuwan idan aka fadesu a kanta sai taji tamkar ita ke mulkin bawai sultane ba. Tayi shuru tana nazari kafin ta sake cewa

"Koda dan wani abu qanqani da tafiso ba wanda yasan satar amsarsa?" Shuru kitchen din ya sake dauka,kaman ba za'a samu me magana ba kafin nimra tace

"Abu daya zuwa biyu na gani......ana yawan kai madara sashenta,sannan ana yawan shiga da kayan itatuwa,duk da ba kowanne nau'i naga ana shiga dashi ba" Kai falaak ke jinjinawa.

"A shirya iya wadannan ababen.......a hada da kilishi da zuma,in kin kammala nimra ki sameni a bakin mararraba".

"An gama Allah ya taimakeki" Ta amsa cikin girmamawa hadi da rusunawa sannan ta juya tana komawa can cikin kitchen din,ita kuma falaak din ta fice.

Da mutum uku suke nufar sassan mammina din. Duk da dare ne amma kowacce qofa kowanne taku cike yake da dakarun dake tsaron sassan. Duk inda tazo giftawa gaisuwa suke kaiwa sannan su bude mata hanya ita dasu nimra su wuce zuwa ciki.

Daidai lokacin da akhnan din ke zaune cikin dakin nata,tana saman wata armchair. Ta dora habarta kai hannunta riqe da wayarta tana scrolling a hankali. Wani statistics na company neesha ta aiko mata take dubawa. A zahiri tana kallo ne kawai,amma a badini ba abinda take fahimta,tana dakon jiran kira ne kawai daga sultane,daga ina kiran zaizo?,me kuma zai biyo bayan kiran?.

Da sallama a bakin falaak ta tura qofar dakin tana shiga. Bata dago ba akhnan din bata kuma juyo ta dubi me shigowar ba. Kawai tana son gane waye ya keta mata doka ya shigo mata daki haka Kai tsaye a sanda ta buqaci kowa yayi nisa da ita?.

"Yaa biftu" Sunan da aka kira din ya kawo mata zaton falaak din ce,saita miqe ta zauna sosai tana kuma waiwayowa ga falaak din.

Idanunsu ne suka gauraya dana juna,dukkaninsu kowa abu na daban na sauka qasan ransa.

Ta dauka zata rufe falaak da fada ne kaman yadda ta qudirta a ranta sanda ta miqe ta zauna,amma sai taji wannan qudurin yana zagwanyewa sanda falaak din ke qarasowa cikin dakin bayan ta ajiye kwando na biyu data amso daga hannunsu buhaina da iyakacinsu wancan parlor din na farkon farko.

Har yanzu da wannan murmushin akan fuskarta,saita tako kanta tsaye ta qaraso gabanta ta zauna tana tura mata kwandon.

"Naji kinzo......tun daxun banga motsinki ba,nace bari na shigo mu gaisa na karbi tsarabata kuma" Tayi maganar da irin yanayin daya sanya take akhnan din taji girma ya motsa mata. Irin girman da yaya takeji akan qannenta,irin girman da yake tuna maka akwai wasu 'yan uwa qasa da kai qasa da naka shekarun.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 41
___________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*👘🥻

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana goma KACAL!✌🏽*

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*🙌🏽
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
___________________________

"Ni ga tawa tsarabar......Niamey nasan basu da wani abu na musamman da za'a iya tahowa agadez dashi" Ta fadi ba tare data tsaya duba ko tunanin batace komai da ita ba har yanxu.

Madarar ta bude ta fiddo wasu qawatattun cups guda biyu ta zuba,sannan a gefan ta saka wani plate din ta shirya fruit din da dukkaninsu take kyautata zaton zabin akhnan ne.

Ido ta zubawa plate din sanda falaak ke ajiyeshi kusa da ita. Sai data gansu ta tuna rabonta da abinci tun madarar da tasha da safe a Niamey. Duk wani kayan alatu na ciye ciye da mammina tasa aka bata dare zuwa safiya ana shirya mata ta gaza cin komai.

Sultane har abada sultane ne.....akwai shaquwa qauna da soyayya me girma tsakaninta dashi,amma hakan bai canza wayeshi ba,bai canza wannan tsananin nasa da kafiya ba.....bai canza qwarewa wajen iya hukunta mutum ba idan yayi ba daidai ba. Duk da tasani,a yawan lokuta tana cin albarkacin qaunar da yake mata......tana sanyashi ya runtse idanu ya sakar mata abubuwa masu yawa.....Amman haka baya hana wanzuwar d'aci saman harshenta a duk sanda ya murde ya kuma yi wani hukunci.
Chapter 49 · 0% Book details