← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 97

Sashe 78

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dama kana tunanin kyanka iya kalamanka ko wani quality dana tabbatar baka dako daya ne zaisa ta soka ta aureka?.......a matsayinka na qasqantacce maras daraja?!.....ni zaituna ni zan sanya akhnan ta aureka ba tare data shirya hakan ba......ni zan tsara yadda zata mallaka maka zuciyarta bawai qoqarinka nakeso kayi wajen faruwar hakan ba......kawai kayi qoqarin daidaita kamalarka da hankalinka......kayi qoqarin zama BASARAKE kayi wanka da ruwan da 'ya'yan sarakuna keyi......ka siffantu da IZZA wadda ita daya ce makamin daka iya janye hankalin biftu akan d'a namiji. Izza gadonta ce......izza wani abu ne a jininta,so dole taso namiji ME IZZA ba tare da tasan da wannan abun cikin ranta ba" Takai qarshen tana nuna qirjinta.

IZZA da mammina ke maimaitawa ta sanya yaji ya kwadaitu dason ganinta. Shima a jininsa ne......mace me izza tana burgeshi.....ba mace ba koda namiji ne me izza hakan yana qawatar dashi,to amma dole ne kaman yadda ta buqata ya saisaita nutsuwarsa. Zata iya hangen finsa samun alfanun komai......to amma kuma shi yana hangen alfanun da zai samu saiya ninka nata.

"Dole kayi nisa da dukkan wani nau'in kayan maye......dole ka haqura dasu na wasu watanni......kana iya ci gaba bayan komai ya saitu ya kammala......amma yanzu kyanka da hankalinka mukafi buqata" Ta fadi da sautin dake nuna da gaske kowacce kalma ke fita a bakinta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 67
____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

Idanunta ta juyar zuwa ga tamim tana maida kallonta a kansa. Bai zaci zata maida dubanta a kansa haka da wuri ba,sai yayi saurin sake sadda kansa qasa saboda nuna tsantsar biyayya.....saidai kuma,can qasan ransa da zuciyarsa wata iri nau'in wuta ce me zafi take tartsatsi.

"Nutsuwarsa tana hannunka........a duk lokacin daya sake fita daga saitinsa laifin baya wuyan kowa saikai.......zansan yadda za'a rage maka ayyuka da nauye nauye a masarauta......don ka samu cikakken lokacin tarbiyyantar dashi da al'adu da yanayin sarauta ta yadda zatabi jininsa........abu na qarshe daga yau.......daga kuma sanda zai fara fita don sajewa da mutane da shiga masarauta,sunansa ya sauya daga almaz......sunansa ya koma FARRE ABBA JALAAL sunansa dana mahaifi". Jinjina kai tamim yayi da wani irin nauyin dake gwada ya karbi dukkanin umarninta,ta miqe a hankali tana takawa.

"Zan aiko da yalwa da wasu CFA din da dukkan adadin nauyin da kuke buqata....."

"Godiya nake uwar gijiyata" Ya fadi yana tattara dukka qarfin halinsa ya miqe,daidai sanda almaz ya karkace ya koma saman lalallausar sofa din yayi kwanciyarsa yana ji a ransa duk duniya bai taba jin abu me laushi kaman gadonsa na can dakin ba da kuma wannan kujerar.

*AKHNAN*

Da qyar takai kanta daya daga cikin bedrooms dinta,ta kuma samu ta zube saman gadon da yake shimfide da wata shimfidar alfarma tana tura kanta cikin comforter din dake saman gadon tana jiran a buqaci amfani da ita.

Batasan yaya ba......bata kuma san daga ina ba,dukkan wani qwarin gwiwarta ya soma kwaranyewa. Dukkan wata jarumta tata ta soma sulalewa tana barinta da iya zallar halinta,abinda ya sanya wani irin kuka tsinke mata,a karo na farko tun bayan data mallaki hankalin kanta da kuka me nauyi irin wannna me cike da kadaici ya tsinke mata. Wani irin kadaici kawai takeji yana ratsata,tana maimaita kiran sunan mammina. Ina mammina ta tafi ta barta a irin wannan yanayin?,a irin wannan lokacin da tafi buqatarta sama da ko yaushe?,a irin wannan lokacin da komai yake shirin jagule mata?.

Ko da imagination ba zata ita hakaito hakeem a mazaunin mijinta ba......koda zata rasa soyayyar sultane ba zata iya aminta da hakeem a mazaunin mijinta ba.

Hakeem fa?,mutumin da yafi dukkan mazan da suka taba zuwa don ganawa da ita qansqanci?,mutumin da shine mafi qaranci matsayi......daukaka.....wayewa da sanin ilimin zamani dame duniya take ciki?. Ba hakeem ba......koda wanda ya fishi komai.....koda wanda zai iya cika sharudda ya kuma hada qualities din da takeso bata jin zai samu amsa cikakken sunan miji a gareta,ballantana hakeem din da ko cikin 'yan uwanta na jini ba zata lamunce masa ya samu ba.

Malamin addini fa?,me qarancin wayewa?,banda bai iya boko ba sam.....wanda baisan komai ba sai karantarwa......baisan komai ba sai wa'azi?,bazai taba iya tsaiwa a guraren data tsaya ba a duniya,cikin dubban yaruka.....cikin dubban masu jajayen kunne......cikin qwarrarrun doctors masana masu tsananin wayewa. Tana running company irin sahel couture taje ina da malamin addini?,tana zuwa taruka na duniya da qasashen da suka isa,ta tsaya gabansu tayi magana da salon harshen da yake burge kowa ya kuma girgiza kowa,ya daga darajarta......ina zataje da malamin addinin da baisan kowacce kalar wayewa ba?.

Me yasa sultane bazai fahimta ba?,me yasa bazai gane babu kima ko guda daya game da wannan tunanin nasa ba?.

Hankali kwance take takowa cikin gidan,a nutse kuma tana karantar akwai wani abu daya canza tattare da gidan. Motsi da karsashin da kowa keyi yadan ja baya kadan,abinda ya alamta mata akwai abinda ya faru tabbas da gaske kuma.

Sanda qafafunta suka taka sassanta yalwa ta hange tsaye tana jiran isowarta,wanda ganin shigowarta ya sanya yalwa matsowa cikin girmamawa.

"Allah shi baki yawan rai......ina tunanin akwai matsala yau cikin gidan nan,akwai damuwa" Yalwa tayi maganan da sautin da zai sanya ka tsammaci batasan komai ba,bata da masaniyar komai daya faru.

"Me ya faru?" Mammina ta fadi tana zame takalmanta,daya daga cikin hadimanta ta tsugunna tana kwashesu gami da ajiye mata wasu masu sauqi ta soma zura qafafunta a ciki.

"Gimbiya akhnan ce.....ta shigo dazu a birkice tana nemanki,kiran sunanki kawai takeyi". Sosai fuska da yanayin mammina ya sauya yana juyawa zuwa yanayi na razana.

"Me ya faru da ita?,me ya sameta?,me yasa ba wanda ya sanarmin?,wanne irin sakaci ne wannan da rashin sanin martaba da muhimmancinta?,hakan yana nuna kenan ko bayan babu raina babu wanda zai iya kula da ita?,ba wanda zai iya kula da damuwarta?,ina morsa safiyya?,me yasa batayi komai akai ba?" Tayi maganganun cikin fadan daya sanya kowa ya sake rissinar da kansa,suna jin tabbas su masu laifi ne,jikinsu kuma yana sake yin sanyi. Dukkaninsu sunsan cewa akhnan din wata halitta ce me matuqar muhimmanci a garesu......ita din wata halitta ce da damuwarta taba ta ko shiga rayuwarta kayi mata wani abu na ba daidai ba babban kuskure ne a tare da kai.

"Muje na ganta" Mammina ta fadi tana sauya akalar tafiyarta zuwa kebantacciyar hanyar da zata sadata da sassan akhnan.

Daga yanda taga dukka hadimanta a cure a guri daya ta tabbatar lallai abun babbane,hankalinta ya tashi hankalin kowa ma a gidan ta tabbatar sai ya tashi. Da alama ta shiga wannan yanayin nata na tsananin fushi da fusata,tasan kowa dole yaji a jikinsa,komai nata kuma zai canza. Tako ina gaisuwa suke saukewa mammina din,suna kuma sake rusunawa zuwa qasa.

"Me kukeyi a nan?,meye amfaninku da kuka barta ita daya a ciki kuka dawo nan?!" Ta jefa musu tambayar a tsawace tana dubansu.

"Allah ya huci zuciyar giwa.......ita ta buqaci hakan,dole ne cika umarnin gimbiya akhnan,mun nisanceta ne bawai don haka yake muradinmu ba" Birra ta fadi cikin tsantsar ladabi. Shuru tayi dake nuna alamun tana calming fushinta,sannan ta juya a hankali tana wucewa qofar farko da zata fara sadaka da sitting room da falukan alfarma kafin kakai ga isa ainihin shiyyar bedrooms dinta.

Dan qaramin murmushi ta sauke,duka falukan ba gilmawar kowa sai na'urori daketa aiki abinsu suna bada qara mara sauti sosai wadda bata da damuwa sam. Ta dora hannunta kan qofar dakin data gani a bankade ko.maidata ta rufe bata samu daman yi ba,ta tura da sallama,sannna ta lalubi makunnin hasken dakin ta kunna,take haske ya gauraye dakin,daidai kuma sanda ta miqe daga saman gadon sukayi ido hudu da mammina din.

Da sauri ta ture comforter din kuka yana sake narke mata,ta sauko da sassarfa ta nufo mammina tana jin duk duniya damuwarta ta yaye da ganin mammina kadai da tayi.

"Meye haka biftu?......me ya sameki?,waye ya sakaki kuka?" Dukka mammina ta hada tambayoyin ta jefa mata su tana ware hannayenta akhnan din ta shige ciki tana sakin wani kukan.

"Sultane ne mammina......sultane ne" Ta qarasa maganan da yanyin da zai gaya maka zallar sakalci da gata data samu a dukkanin rayuwarta.

"Subhanallah......sultane dai kuma?,me kikayi masa?" Ta tambaya tana dan bubbuga bayanta alamun lallashi.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Don na sallami hakeem......bana sonshi mammina baiyimin ba,malamin addini ne fa mara wayewa sam sam.....yanxu kina ganin irin wannan mijin ya dace da d'iyarki?" Ta fada tana jin cewa matsalarta tazo qarshe. Ko kowa bai fahimceta ba mammina tana fahimtarta,ko kowa bai kawo mata mafita cikin matsalolinta ba mammina tana kawo mata,ko kowa bai goyi bayanta ba mammina tana goya,tsanani.....wahala ko dadi basa sanyawa mammina ta janye mata ko ta daina goyuwa da bayanta.

Wannan karon ga mamakinta sai taji mammina na zameta daga jikinta,abinda ya tilasta mata daga kanta a hankali tana duban mammina din cikin zallar mamaki.

Mamakin ya sake ninkuwa yadda taga mammina na dubanta da wani irin kallo,wannan tausayin.....wannan tausasawar.....wannan laushin dukka babu su. A hankali mammina ta soma girgiza mata kai.

"Wannan karon.....idan har kin bijirewa maganan sultane,idan har kin kasa biyayya wa umarnin sultane,to tabbas bana tare dake......". Mamaki ya tsayar da kukan akhnan gami da wani dan siririn firgici daya ratsata.

"Mammina......ke kikamin alqawari fa". Kai ta daga a hankali tana takawa da baya.

"Nice akhnan......saidai akwai abubuwa da dama da suka tilastamin tunanin janye wannan alqawarin........morsa safiyya,nice mutum ta farko da zata kalla wadda ta zigaki ta kuma doraki akan turbar bijirewa maganan sultane....."
Chapter 78 · 0% Book details