← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 97

Sashe 15

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 10
____________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________

Da kallo morsa safiyya ta bita,tana jin wani abu yana taba zuciyarta sosai,wani irin qaqqarfan abu me matuqar tasiri a zuciya.

"Allah ya tsare hanya......ya bada sa'a,ki kula da kanki,ki kula da mutuncinki..........ki kuma tsare martabar gidanku data mahafinki" Kusan kowanne lokaci wadannan sune kalamanta kuma maganganunta a kanta a duk sanda ta samu sukunin yi mata sallama. Bata ce komai da ita ba taci gaba da takawa tana fita......hakan kuma bai hana morsa safiyya binta da idanuwa ba har sai data bacewa ganinta.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana jin sassan jikinta suna yin wani irin sanyi. Koda wasa akace mata irin haka zai taba gwada faruwa tsakaninta da jinin safeena ba shakka zata qaryata. Da gaske rayuwa wani mafarki ne na daban. Wani mafarki ne da zuciyoyi da ruhi keyi ba tare da samun yaqinin tabbatuwarsu a sanda ake kan ginasu ba. Safeenarta.......halitta mafi soyuwa a ruhinta dama kafatanin rayuwarta gaba daya......yanzun dama akwai sanda lokaci zaizo da irin wannan yanayin tsakaninta da jinin SAFEENA?.

Taja siririn tsaki aqalla ya kusa sau biyar kafin ta isa sassan mammina. Tarin hadiman dake sassan suka shiga marabtarta cikin matsanancin ban girma,saidai ba wanda ta samu amsawa. Hakan ba baqon abu bane a wajensu,musamman idan tana jin 'yan izzarta a kusa,ko kuma 'yan miskilancin suka motsa mata. Ko baya ga haka kuma dama ita din muryarta kamar wani abune me daraja a tare da ita da ba kowanne guri take sakinta ba.

"Ki gafarceni.......uwar daki tana cikin muhimmiyar ganawa......bata kuma bada izinin shigar kowa ba har sai bayan ta kammala" . Bayanan tafisu ta yiwa akhnan kenan,wadda ta isa direct ga qofar kebantaccen parlor din hajiya zaitun da tasan a lokaci irin wannan anfi samunta a can.

Wani irin kallo akhnan ta dago ta watsawa tafisu,tana mata wani duba na qanqanci da kuma zallar mamaki.

"Hala wani abunne a kanki?.......kinsan dawa kike magana kuwa?" Akhnan ta furta cikin izzar nan tata dake bayyana cikin kowanne motsi nata.

Rawa jikin tafisu ya dauka,kwarjinin akhnan din sosai ya daketa,ya kuma tarwatsa duk wata juriya da takejin tana da ita na tsaida akhnan din.

"Zaki fuskanci hukunci.......tabbas zaki fuskanci hukuncin tsaidani da kuma batamin lokaci da kikayi" Ta qarasa maganar tana tura qofar,daidai sanda tafisu ta zube muryarta da jikinta dukka suna rawa.

"Tuba nake.......afuwa nake nema ki yafeni......kiyimin rai".

Bata ko saurareta ba ta sanya kai cikin parlor dake da qofofi biyu na musamman,ta cikin gidan da kuma wata qofar daban ta bayan ainihin ginin.

"Yaya sunanshi?......." Kalaman mammina kenan da taji wanda bata ko ta kansu ba ta motsa bakinta a izzace ta saki siririyar sallama tana sauke idanunta ga faffadan mutumin dake duqe a gabanta kamar me neman gafara.

"Sunan......." Ya buda baki da nufin bada amsa tambayar da akayi masa,saidai amsa sallamar da yaji mammina tana yi ya dakatar dashi,ya kuma daga kansa da hanzari yana duban me shigowar. Sam baiji motsi ko sallamar kowa ba......don haka baisan da shigowar kowa din ba.

Idanu mammina ta kafeta dashi na sakannin da suka kusa biyar kafin ta sakar mata murmushi.

"Karkicemin sai tafiya?" Ta fadi tana marabtarta da hannayenta,abinda ya sanyata qarasowa cikin hanzari ta zauna jikin mammina din sosai tana aza kanta saman kafadarta.

"Maraba da isowa........tuba nake.... .Allah ya qara miki nisan kwana......ubangiji ya kauda maqiyanki daga duniyarn......"

"Ya isa haka" Mammina ta dakatar dashi tana sanya hannunta cikin na akhnan.

"Ka bamu guri haka nan......zan gana da diyata......zan nemaka wani lokaci"

"An gama Allah shi biya miki" Ya furta yana miqewa da dukka tsahonsa,sannan ya sanya kai yana fita ta qofar da zata fitar dashi ta bayan sassan mammina din.

Sai data tabbatar da gushewarsa a wajen,ba tare da wani motsi nasa ba sannan ta dubi akhnan.

"Tun daga yanzu na fara kewar wannan diyar tawa,daya daga cikin abinda ke jefani tunanin yadda rayuwa zata kasancemin bayan na kaita gidan mijinta". Wani murmushi ya subuce ma akhnan din,murmushi nan nata me tsadar da zai wahala kayi mu'amala da ita na wasu taqaitattun lokuta ka samu ganinsa. Koda yaushe fuskarta a tsuke take,zaka dauka kaf rayuwarta batasan wani abu waishi farinciki ba.

Hannunta ta zura ta bayan mammina ta rungumeta sosai.

"Kune kuka takura......ku kuka matsa mammina......me nake da buqata a rayuwata bayan kun yimin komai.....kun gama min komai......sannan kun mallakamin komai". Kai ta girgiza a hankali.

"Yaro yaro ne......yaro man kaza......baa nan gizo ke saqar ba.......amma na gaba kadan zaki fahimta......akwai wani abun da kike buqatar ki tafi dashi Niamey?.....bayi hadimai ma'aikata ko wani abu na buqatar rayuwa?". Manyan idanunta ta lumshe,tana jin dadin yadda take nuna damuwa da komai daya shafi rayuwarta,tana jin dadin yadda take kula da dukka buqatunta.......tasha banban da nisan tazara me tarin yawa tsakaninta da momma safiyya.........tazarar da bata jin a nan kusa akwai wani abu da zatayi wanda zai sanya ta taddota.

"Babu......babu komai mammina.......saidai zanyi kewarku" Ta qarasa fada tana sake dora kanta saman kafadarta.

"Muma zamuyi kewarki biftu.......amma zamu kasance ta cikin waya.........dole ne ya zame miki nauyi da kuma wajibi bawa kamfani kulawar da dukka ta dace........shine zuciyar duk wata kadara da dukiyarki akhnan........bake kadai ba.......hatta da me martaba ma". Kai ta jinjina,sannan a hankali ta zame kanta daga kafadar mammina din sannan ta miqe.

Da kanta ta bude mata seat din baya,mazauni na musamman dake gareta cikin lafiyayyar motar qirar BMW X5 fara qal wadda tasha banban da kalolin sauran motoci ukun dake dauke da masu tsaronta da kanyi mata rakiya zuwa Niamey,wasu su zauna a can,nacan din kuma su dawo nan agadez sai tayi wani zuwan sai a sake canza mata da wasu cikin amintattun hadiman da masarautar agadez ta aminta dasu.

"Allah ya tsaremin ke......ya kawar da dukkan wani abunqi"

"Ameen mammina". Ta fada a narke kaman yarinyar qarama. Matsawa mammina din tayi tayi kissing hannun akhnan din,sannan ta maida dubanta ga aisa.

" Aisa" Ta kirata kai tsaye da yanayin daba kasafai ta fiya kiranta ba.

"Naam mammina"

"Ki kulamin da diyata" Ta furta da yanayin dake nuna mata da gaske take. Kai kawai ta jinjinawa mammina din tana dauke kanta zuwa wani sashe na daban,kafin mammina ta matsa da baya ta rufe musu motar,suka fara motsawa kuma suna fara fita daga masarautar agadez. Duk inda zasu gifta da motocin tun daga cikin gidan har zuwa wajen gidan sai kowa ya bada hankalinsa,ya kuma matsa baya cikin girmamawa yana yi mata addu'ar sauka lafiya da wani irin ladabi tamkar tana ganinsu.

Shuru motar ta dauka sanda suke nufar mano dayak international airport(AJY),inda ta saba tashi a nan,sauran hadimanta kuma su juya subi ta hanya zuwa Niamey din.

Kowa da tunanin da yakeyi a ransa,saidai duk da haka waya ce a hannun aisa tana danne dannenta,wanda fiye da rabi chart takeyi ita da shehinaz da take bata tabbacin yau din ko gobe itama zata baro zinder ta shigo Niamey din. Akhnan kuwa idanunta nakan hanyoyi da shimfidaddun tituna kyawawa da suke wucewa. Cikin ranta take sake jinjinawa mahaifinta da mulkinsa,ya jawowa qasar agadez ci gaba masu tarin yawa,irin ci gaban da koda wadanda suka jima saman karagar mulkin basu samar da koda rabin rabin hakan ba.

Duk da wannan nazarin da takeyi hakan bai hana zuciyarta fadawa cikin tunani ba.....abubuwa da dama dake cunkushe a kwanyarta,tana kuma tunanin hanyar warwaresu.

Qaramin tsaki taja ciki ciki,a yanzu tana jin energy dinta dukka na aikinta......bata buqatar sulalar dashi da kwaranyar dashi akan wani abu can da bashi da cikakken muhimmanci ga rayuwarta,don haka saita fidda daya daga cikin wayoyinta tana jin bari ta duba sashen saqonnin email dinta ta rage yawan saqonnin da suke jiranta.

Saqo na farko na biyu......ana uku idanunta suka sauka ga adireshin saqon da ya sanyata jan wani qaqqarfan tsaki da yaja hankalin aisa. Daga kanta tayi tana duban akhnan da taqi koda duban sashen da aisa din take,har yanzun idanunta nakan wayar,don haka itama aisa din saita bagarar taci gaba dayin abinda take.

Tsaki na biyun data sake ja shi ya sanya aisa yin magana wannan karon,ta aje wayarta saman cinyarta ta soke yatsunta guri guda tana dubanta.

"Wanda bai kashe zomon ba.....kuma ko ratayar zomonma ba'a bashi ba......na meye zaa cika masa kunnuwa?" Tayi maganar tana tsuke fuskarta guri guda.

Sau daya tak ta daga kai ta kalli aisa da almond shape eyes dinnan nata dake gayawa aisa ta tara maganganu ne da yawa qasan ranta amma miskilanci ya hanata fada,sai tayi abinda aisa din tafi tsana wato maida kanta kan wayarta.
Chapter 15 · 0% Book details