← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 97

Sashe 90

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ammm.......mammina ga muhammad nan,sabon d'anmu,kuma malaminsu falaak dake daukansu darasi duk yammaci" Sultane ya fada yana duba mammina din.

Wani irin numfashi ta fusgo,kafin kuma ta biya ta hado da aron murmushi daga wani loko can na zuciyarta,kafin kuma a nutse ta saci kallon yanayin zamansa da kuma saqar jubah din dake jikinsa,ta kuma dora da.

"Barka da warhaka sheikh,muna maka maraba da shigowa cikin da'irar ahalin sultane,haqiqa lallai ka taki babbar sa'a da har ka samu matsayin D'A sukutum daga sultane.......kinga daga yau biftu kin samu dan uwa ko?". Murmushin farinciki sultane ya saki,yana jin haisam kamar da gaske d'ansa ne har cikin jininsa.

Ido haisam din ya lumshe tare da budesu lokaci guda yana dan jinjina kai. Sautinta da yadda karin harshenta ke fita yake qoqarin harhadawa cikin kansa. Wani irin accent yakeji daga bakinta daban,accent din da yake ji daga bakinta kamar ya banbanta da sauran harsuna da yaji sunyi magana cikin agadez.

Idanunsa ya daga a hankali ya sauke kan mammina,wani kallo qwaya daya amma da aka yishi da tarin manufofin dake dauke da harsashe me zurfi.

Idanunta ta lumshe tana qoqarin daidaita wancan qamshin a hippodrome......wannan qamshin a ranar da ya saketa ta kusa faduwa kusa da dakin hutawar sultane......da kuma wannan lokacin a yanzu da qamshin ya mamaye ko ina da wani irin yanayi da taji yana harbawa har saman kanta yana kuna sake dawo mata da ranarsu ta hippodrome data yiwa laqabi da BAQAR RANA. Ranar da har ta koma ga mahaliccinta bata jin zata bace a kwanyarta.

A nutse mammina taci gaba da satar kallonsa qasa qasa,kowanne abu a jikinta daka iya bata signal akan komai yana motsa mata gami da ajiye mata wasu baqin yanayi a jikinta. Ba tambayar dake neman dakusar da nutsuwarta irin son sanin WAYE SHI?. Duk da cewa kunnuwanta sun jiye mata kuma kwanyarta ta ajiye mata batun MALAMINSU FALAAK ne. Sai takejin kamar sultane na zolayarsu ne......sai takejin kamar sultane na son tsokanarsu ko gwada hankalinsu ne. Ta aminta zai iya zama malaminne,saboda wani irin haske da ajiyayyen kwarjini da take hanga tattare dashi,amma ko da malaminne bawai malaminsu falaak ba,yafi kama da qasaitaccen malamin da gata da hutu suka huda jikinsa. Yaushe ma ya shigo masarautar amma bata samu labari ba?,yaushe ya soma rayuwa cikin ta ita bata taba sani ba?......hakan yana nufin tayi sakaci kenan?,hakan yana nuna akwai sauran qofofi data bari a bude wanda bata toshesu ta hanyar zuba masu bata masaniya ta wannan qofar ba.

"Akwai sauran gyaran daya ragemin" Ta fadawa kanta,tana jin bata da sukuni har sai tasan wayeshi. A tsarinta cikin lokaci me muhimmanci da tsada cikin rayuwarta irin wannan,bata buqatar baqon abu cikin masarautar agadez,mace ko namiji,yaro ko babba,don dukkan wani wanda yake rayuwa cikin masarautar tana da dukkan wani bayanansa,na rayuwa hali dabi'u yanayin aiki da sauransu,samun qarin wasu baqin zai zame mata kamar maida hannun agogonga baya ne.

Nutsuwa ko sau daya bata kusanceta ba,ta kwantar da wadannan idanun nata sosai tana qoqarin karantarsa a duk wani motsi nasa,cikin salon da ba kowa bane zai karanci haka kai tsaye. Saidai kuma cikin jikinsa yake jin akwai wani unusual kallo dake fita daga wani bangaren na dakin zuwa jikinsa. Bai motsa ba amma jikinsa ya gaya masa haka,yaci gaba da qoqarin maidawa beeno saqon gaggawa daya tura masa,yayin da wani sashen na kwanyarsa yaci gaba da aikin saita daga wanne sashe wannan kallon yake fitowa ba tare kuma daya daga kanshi ba ko sau daya.

Agogo sultane ya kalla sannan ya maida dubansa ga akhnan,cikin sautin nan nasa dake cike da nutsuwa da kamala yace.

"Ina saurarenki.....mene kike cewa kafin yanzu?". Maganar ba iya akhnan kawai ta daka ba,harda mammina. Ta dauka tunda baqo ya iso gurin,baquwar fuskar da babu ita cikin masarautar maganan ya wuce.

Blue eyes dinnan nata da sukayi wani irin jirkicewa ta daga ta kalli fuskar sultane,sai kuma ta maida kanta qasa ba tare data iya sake cewa komai ba. Ta yaya zata bari rauninta ya bayyana a idanun wani bare?,barenma da take qarfafa zargi me girman gaske a kansa.....wanda muddin wannan zargin nata ya tabbata,tayi rantsuwa da ubangijin sammai da qassai saita tozartashi mafi munin tozartarwa.
((Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Duk da wani sashe na zuciyarta yana mata tantamar haka. Ba wani kidahumin malami irin haka,da bai gama sanin kansa bama ballantana dabbobi ya iya sarrafa dawakai haka......ya iya hawa doki da dukkan qarfin izza da qwarewa irin haka,zuciyarta tana cika da tantama idan ta tuna wannan.....babu wani malamin addini dake da wannan zarrar,ba wani kidahumin malami da xai iya tunkararta har ya iya hada tsere da ita. Ko waye wanda yayi hakan,tana da imanin cewa akwai tsartuwar jinin jarumta a jikinsa. Akwai wani yarfi na izza tattare cikin jininsa,akwai kuma wani abu na daban ma tattare dashi da kaifin idanunsa suka kasa barinta a mafarkai mabanbanta.

Taga maza masu tarin yawan adadi a rayuwarta......masu tsananin zallar madarar kyau daga mabanbantan qabilu,cikinsu harda mazan qabilarta da sukayi fice a fanni na kyau a qasarta dama dukkan qasashen africa dama duniya gaba daya......mazan da suka yarda su sadaukar da komai nasu don ta aminta ta zama mallakinsu,amma babu wani namiji qwaya daya da wani abu nasa ya tsaye mata a rai,kuma wai har ya zama abokin mafarkanta sai a kansa.

A hankali cikin kuma hikima ta daga idonta ta aza akan haisam. Sam sam kamar ma ba a gurin yake ba,kamar ma baisan wani abu dake wanzuwa a gurin ba,ya bawa wayarsa nutsuwarsa da kuma dukka hankalinsa. Abinda ya sake sanyata cikin mamaki,ba wani mutum da zaizo gaban sultane yayi haka,gayyata daga sultane ba qaramin alfarma bace,a niger kake ko a maqwabtan qasashen africa,amma shi gashi gaban sultane kuma yana danna waya?. Ko data daga kanta kuma ta dauka zata tsinciki alamun karkatuwar hankalinsa akan sultane ko shiyyar da akhnan take,amma ga tarin mamakinta,da dukka iya zurfin nazarinta bata hangi wata alama koda qarama ba dake nuna haisam yana tare dasu
"Waye wannan?,wanne irin mutum ne shi?" Ta tambayi kanta da kanta,sai ta jinjina kan tana jin qarin wasu baqin dabi'u daban data hanga tattare dashi. Koda bataga alamun yana tare dasu ba,amma bataji yarda dashi ko kadan ba,ita din wata iri mutum ce da samun yarda daga gurin ta yake maka wahala,samun yarda daga gurinta yake daukarka dogon zango dogon lokaci da kuma dogon zamani. Sassauta murya tayi zuwa ga mafi qanqantar yanayi,yanayin da mammina keda yaqinin Haisam bazaiji ba tace.

"Ranka ya dade......ina ganin wannan maganar bai kamata a yita ba a gaban baqo kuma bare......abune daya shafi iyali". Murmushin qasan rai haisam yayi,yana da wata irin baiwa ta kaifin ji matuqar gaske,kaifin jin da ya dinga bawa nanay tsoro. Ko yaya akayi magana,komai nisa muddin nisan yana kewaye da inda yake zai iya jinta. Daga idanunsa yayi ya kalleta,sannan a hankali yakai hannunsa ya riqo hannun haisam,sai a sannan din haisam ya daga kanshi yana duban sultane dake riqe da tsintsiyar hannunsa.

"Nayi zaton daga yadda ya shigo ya riskemu zaki fahimci cewa daga yau SHI DIN D'ANA NE.....na dauka iya wannan zai gaya miki yana da girman matsayin da komai baza'a boye masa ba,na dauka kin karanci cewa ya zama DAYA DAGA CIKIN AHALINA.....komai na iyalina......komai na ahalina yana ciki,ba wani sauran abu da za'a boye masa". Girman bugunsu da maganan tayi ya sanya saida akhnan ta sake daga idanunta a karo na biyu ya saukesu kan haisam ba tare data shiryawa hakan ba. Ga mamakinta har a wannan lokacin sam bai dubi koda gefen inda take zaune ba,hakanan yanayin fuskarta bai nuna mata abinda take zaton gani ba.

Farinciki murna da walwala take saka ran ganin kan fuskarsa,madaukakin farincikin da samun damar shigewa jikin me martaba haka ta farat daya,samun qazaitacciyar damar da ba wanda ya taba samun kwatankwacinta,tun daga sanda sultane ya zama magajin muhammad agga har zuwa yau din. Saidai a maimakon hakan,ba wani sauyi da yanayinsa ya nuna. Wannan fuskar me tarin kwarjini,wannan fuskar dake cike da wani irin kwantaccen kyau me daukan hankali.......wannan ran dake cike da wani izza ta sarauta cike yake da nutsuwar da zaka fahimta a karan kanka......hankalinsa sam sam baya tare da maganganunsu.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 78
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

Wadannan idanun dai sune da suka sake haske saboda da hasken screen din wayarsa dake shiga ta ciki.

"Zaiyi wahala ya kasance bashi bane wannan mutumin" Zuciyarta ta gaya mata kai tsaye ba kwana kwana,da kuma irin yanayin da indai ta d'arsa mata abu dashi to daga qarshe hakance take tabbata.

Wani irin mahaukaciyar tsanarsa tayi gangamin gayya ta sauka saman zuciyarta,ta qanqance idanunta zuwa can ciki da wani irin kallo,tana fata koda sau daya ne ya kalli cikin idanunta ta soma ajiye masa saqon farko,amma hakan bata samu ba.

Bata iya hadiye fushi ba,ba kuma kasafai ta fiya ajiye abu a ranta idan yana damunta ba,tana cikin jerin sahun mutanen da fadar abu yake zame musu sauqi da rangwame cikin rayuwarsu,hakanan nunawa a aikace ya zame musu dabi'an da bata canzawa.

"To amma shi din ba kowa bane bappi.......bai rayu damu ba,baisan ya rayuwarmu take ciki ba.......hasalima ko cikakken magana da yaren abzinawa baya fita a bakinsa yadda ya kamata,ta yaya zai zama wani yanki daga ahalinmu?,waye shi?" Ta furta maganan Kai tsaye tana duban sultane.
Chapter 90 · 0% Book details