← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 97

Sashe 89

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani zuzzurfan kallo ya masa guda daya daya dasa masa wani qaqqarfan zargi me girma a zuciyarsa game da mutumin da ko fuskarsa bai samu daman gani ba,bai kuma yarda yayi wani motsin da zai alamta masa tahowarsa ba,har sai daya isa saitin qofar parlor din,ya soma zame takalmin qafarsa ta hanyar yin amfani da dunduniyar daya qafar sannan ya saki wata taqaitacciyar gyaran murya mara amon sauti idanunsa kafe akan mutumin.

"Waaqa!(god!)" Ya fadi a razane sanda yake waiwayowa da hanzari cike da mamakin wanzuwar wani dan adam a gurin bayanshi.

"OROMIA?" Haisam ya furta can qasan ransa cike da zallar mamakin jin fitar yaren oromo daga bakin mutumin,mamakin da ya gaza boyuwa ya wanzu saman fuskarsa dama idanunsa,ya kuma kafe TAMIM da kallo duk da a lokacin bai kamata cikin tsarin aikinsa yayi hakan ba.

Idanunsa ya maida ga goshin tamim dake tsatstsafar da zufa,abinda ya sanya tamim wanda shima ya zubawa haisam idanu kai hannunsa ga goshinsa,ya kuma shafo gumin yana dubansa hannunsa.

Idanunsa ya sake maidawa kan fuskar haisam,zuciyarsa cike da wani irin madaukakin mamaki da kuma tarin tambayoyin

"Waye wannan?......waye shi?,yaushe ya wanzu cikin masarautar agadez?,a wanne lokaci ya samu matsayi irin wannan?,matsayin ketawa ta sassan sultane kanshi tsaye?. Ba dan rakiya?,ba iso?,ba tsarewa daga gurin masu tsaron sassan?.

So yake yaci gaba da kallon idanun haisam ko zai iya karanta ko sansano wani abu tattare dashi,amma wani irin kaifi da kwarjini dake fita daga idanun haisam din sun danne nashi. Kasa jurar ci gaba da kallon fararen manyan idanun haisam din yayi,sai ya janye nasa,yana maidasu wani sashen cikin Tsananin mamakin jin wani baqon abu tattare dashi.

A hankali haisam ya janye dubansa daga kan tamim din,ya tura sliding door din falon,abinda ya sanya tamim samun daman waiwayawa yana kallon haisam din a sanda ya fara takawa yana barin farfajiyar cikin jin wannan nauyin yana zartawa yana son murqushe zuciyarsa da duk wani karsashi nasa. Tashi guda kuma yana jin wani irin nauyi da wani abu me kama da tsoro yana son lullubeshi.

"Bappi....." Akhnan ta kira sunan sultane din da wani irin rauni daya cika muryarta,raunin da sultane din kadai ta yarda ya ganshi,raunin da bata taba yarda ta bayyanashi gaban kowa idan ba sultane din ko mammina ba.

"Bappi.......kayi haquri,kayimin alfarma bappi,ka janye maganan nan,bazan iya auren hakeem ba......ka yafemin bappi na roqeka" Ta fadi da sanyin da sai daya daki zuciyar sultane din,saboda abune da ya jima shi kansa bai ganshi ba a tattare da ita,saidai kuma tunawa da yayi cewa wani gatan zai sake yiwa rayuwarta,sai ya gayyato wannan jarumtar tasa ya aza saman ranshi. Wani kallo ya aje mata me nauyi,kallon daya soma ratsa duk wani jini dake yawo a jikinta da wani irin sarewa da lamarin sultane,kallon daya bata tabbacin yin nasararta abune me matuqar wahalar gaske.....hasashen daya kusa tarwatsa mata kwanya saboda razani,tayi qasa da kanta cikin jiran tsammani,abinda ya sanya lullubin saman kanta ya hadu da sassalkar sumar nan da tsananin kulawar da take samu ya maidata me sulbi,ya zame daga saman kanta zuw kafadunta.

Saidai kafin shi ko akhnan wani a cikinsu ya sake cewa komai amon muryarsa ya gauraya a parlor din.

Cikin muryar nan tasa dake da wani irin zurfi da kuma amo ya yi cikakkiyar sallamar dake nuna yasan haqqinta yasan kuma cikakken ladan da ma'abota cika sallama suke samu.

"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Sultane ya maida martanin sallamar fuskarsa tana washewa da wata kwantacciyar fara'a,abinda ya d'arsa wani babban abu saman zuciyar mammina,tana kuma jin nauyin sautin muryar haisam har saman zuciyarta.

Waye wannan daya samu nasarar gusar da fusata da bacin rai daga zuciyar sultane da sallamarsa kadai?. Kaman sultane yasan me take tattaunawa da zuciyarta,cikin nutsuwa da girmamawa yace.

"Bismillah sheikh muhammad........kai da falon mahaifinka?".

" Mahaifi?" Mammina ta maimaita kalmar can qasan zuciyarta,tana kuma jinjina girma da nauyinta. Wannan kalmar da wannan furucin na sultane ya sanya zuciyarta cikin zaquwa da son sanin waye wannan?,abinda yaja hankalinta kenan ta zubawa qofar shigowa idanu don ganin bayyanarsa.

Cike da wannan cikakkiyar kamalar wadda ta cakuda da kaifin kwarjini da haibar jinin sarautar OROMIA dake jininsa ya sanya qafafunsa cikin parlor da cikakken nutsuwar nan tasa. Karon farko idanun mammina suka sauka a kansa,wata irin matsananciyar faduwar gaba ta saukar mata ba tare da tasan dalilinta ba.

Dukka idanunta ta zuba masa sanda yake ketowa cikin gurin,tana jin wani irin yanayi da batasan wanne iri bane yana ratsa jikinta har zuwa cikin b'argonta a hankali,kamar wadda ake fifitawa iska tsakiyar sanyin hunturu.

Kallonta ta maida kan sultane wanda ya miqe yana fadada fara'arshi.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Barka da zuwa sheikh......ga guri zauna na qarasa ganawa da me dakina" Ya fadi yana yiwa haisam din nuni da mazaunin dake daura dashi.

Iska ta sake shaqa a karo na uku tana jin kamar kwanyarta ta fara birkicewa,kaman komai ya soma dagule mata,kai kaman hauka ne ma yakeson kama ta?,ko kuma depression ne yake mata sallama?. Banda haka ta yaya?.....ta yaya a irin wannan lokacin?,a daidai lokacin da take tsaka da gwabza yaqin neman sauko da sultane daga kujerar naqin da yahau,kuma sannan a lokacinne wai hancinta zai dinga dauko wannan ajiyayyen qamshin yana kawo mata kusada hancinta?.....shin da wanne zataji?,da qoqarin soke auren hakeem a kanta ko kuma case din wancan mutumin?.

Mutumin da tun daga wancan ranar zuwa yau bata sake lafiyayyen bacci ba ita kadai?,mutumin da tun daga wancan ranar zuwa yau bata taba kwanciya ta tashi lafiya qalau ba tare da taga gilmawar wadannan idanun masu wani irin magnet cikin baccinta ba?,wannan idanun da take zargin ta sake ganinsu ko ganin irinsu a wancan ranar,a ranar data kawo kanta wajen sultane.

Kamshin wani irin ajiyayyen abune da kwanyarta da zuciyarta ta yiwa mugun ajiyar da koda cikin baccinta zata shaqeshi ta tabbatar saita farka,komai nisa ko nauyin baccin,koda zata manta komai daya shafi wancan ranar,ba shakka ba zata taba manta wadannan abubuwan biyu ne WADANNAN IDANUN da kuma WANNAN QAMSHIN da har yanzu ta kasa samar da irinsa domin hujja.

To ta yaya ma zata mance dasu?,bayan yana cikin manyan burikanta?. Bata da buri a yanzu days wuce zaqulo SHI. Wannan baqon da yaso tozartata ya tozarta nasararta da ajiyayyen tarihinta name tabbatacciyar nasara?. Muddin ta barshi ko ta haqura ko kuma ta manta ita din bata cika HALASTACCIYAR DIYAR SULTANE MUHAMMAD HAMMUD BA.

Sam ko kusa ko alama bai lura da ita ba,har sai zuwa sanda ya tako da zummar zama inda sultane din yayi masa tayin zaman.

Kanta yana qasa,abinda ya sanya wannan kyakkyawar sumar me kyau da daukan hankali bayyana sosai fiye da fuskarta. A hankali kuma cikin ba zata idanunsa sauka saman sumar tata,ya janye qwayoyin idon nasa da wani irin sauri yana canza direction dinsa zuwa wata shiyyar ta daban. Wani irin abune ya tsarga masa tun daga saman kansa zuwa tafin qafafunsa.

"Subhanallah" Ya fadi can qasan maqoshinsa,adams apples dinsa suna yin sama da qasa duka lokaci daya.

Gashin mace yana daya daga cikin al'aura a jikin mace,zai iya cewa tsahon girmansa bazaice ga randa yaga wani sashe na jikin mace haka ba,don hatta dasu Anani suna da doka a kansu kai tsaye daga gareshi,bai yarda dayin kowacce shiga da sukaga dama ba muddin ba'a cikin dakinsu bane,don haka zaiyi wuya ka samesu kansu a waje ko wani sashen jikinsu muddin ba'a dakinsu suke ba.

"Bismillah muhammad.......nan dukka na gida ne,kaima kuma ka zama dan gida......ga mamarka nan zaituna........ga qanwarka kuma babbar diyata khadeeja akhnan".

Sosai ta zuqi qamshin da qarshen harafin sunanta da sultane ya furta. Sake cika gurin da qamshin da yakeyi da kuma yadda wani ya samu darajar da zai shigo a sanda take ganawa da mahaifinta,har kuma sultane ya ajiye komai......ya tsaidata ya kuma tsaida uzurinta da hanzarinta,ya tsaya saurarensa da dukka girmamawarsa.......daga qarshe ya dinga hada dangantaka tsakaninta dashi,irin dangantakar ma ta YAYA da QANWARSA.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 77
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________

Dukka wadannan tunane tunanen suka harzuqata,ta daga fusatattun idanunta da taketa qoqarin controlling fushinta da bacin ranta da zummae saukewa koma waye wulaqantaccen kallon da zai sanya ya fahimci iya darajarsa,saidai kuma a sanda idanunta suka fada saman fuskarsa da take yau full opened......suka sauka kan wadannan kewayayyun idanun da suka shiga rayuwarta,suka kuma shiga dukka mafarkanta sukayi kane kane,sai dukkan komai ya kwance mata.

Wani irin lallausan murmushi ya sakewa sultane daya qara masa haiba,ya canza gurin zaman daya tabbatar zai sake nesantashi da ganin wani sashe na surar gashinta,yana qoqarin maida idanunsa kan wayarsa dake hannunsa wadda tayi blinking har sau biyu,alamun shigowar saqonni a jere.

"Allah yasa buqatata bata takura ka ba". Miskilin murmushin nan daya qarawa idanunsa wani irin sheqi ya saki,ya motsa labban nan nasa dake wani irin glowing su kadai,saika zargi ma ya shafa musu lip gloss ne.

"Gayyata irin wannan girmamawa ce sultane........"

"Bappi......zanfi son ka kirani da sunan,don sunan da diyoyina ke kirana dashi kenan" Ya qarasa fada yana maida dubansa kan akhnan.

Da qyar ta jefa hannunta baya ta jawo mayafinta,cike da tsammani da kuma yaqinin haisam din zai maido dubansa kanta,saidai a maimakon hakan kai ya jinjinawa sultane kawai ya maida wadannan idanun mash kaifi da nauyi saman wayarsa yana qoqarin sanya ta a silent yana kuma furta

"Barka da dare".

"Barka kade yarona......ya qoqari?,Allah ya dafa ya saka da mafificin alkhairi"

"Ameen ameen" Ya sake fadi cikin girmamawa.
Chapter 89 · 0% Book details