Sashe 88
Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"In sha Allah.....ba zakayi dana sanin bamu lokacinka ba.....kuma nayi imanin zaka sauraremu da dukkan kunnuwanka masu cike da adalci da tausayawa na qasa dashi". Motsawa ya sakeyi kadan yana lanqwasa yatsunsa,already ya fahimci maganan data kawosu,to amma yana da wani irin nutsuwa da dattijantaka a jininsa,bazai hanasu magana ba,tunda ya riga ya gama yanke hukunci,baya tunanin kuma akwai abinda zai sauyashi.
Da qyar ta tattara duk wani qwarin gwiwarta,ta sauke qanta qasa,da wannan tattausar muryartata dake da wani irin amo me sanyi akhnan din tace.
"Barka da warhaka bappi". Kadan ya dubeta,cikin bagararwa kaman baiga wani canji tattare da ita ba yace.
" Barkanki,kina lafiya?" Tambayar da yayi mata saita tsinkar mata da zuciya. Sultane yana nufin shi baiga komai tattare da ita ba?,baiga girman tashin hankalin data shiga ba?,baiga yadda nutsuwarta ke neman wargajewa ba?,baiga yadda komai nata ya sauya ba?. Bama wadannan ba duka,ita din da idan tazo agadez,duk wani motsinta na wunin ranar......duk yadda sultane yakai ga yin busy,duk yadda itama takai ga shigewa wasu hidimomin.....koda sau daya ne a qalla a kowacce rana sai taxo sunci abinci tare,walau na safe ko na dare?,wasu lokutan ma idan ya samu sukunin ayyuka da kyau sukanci na rana ne tare.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tana zama ta sake sosai dashi fiye da yadda take sakewa da kowa,wani lokaci fiye ma da yadda zata sake da mammina.....sama da yadda zatayi hira da ita. Ya bata duk lokacinsa,ya saurareta,ya kuma bata shawarwari. Wasu shawarwarin sun shafi rayuwarta ne,wasu sun shafi sahel couture,wasu kuma fadakarwa ne da jan hankali dangane da rayuwa,amma yau duka sultane ya ruguza wadannan abubuwan don kawai yana so tayi aure?. Yafi kowa sanin auren nan ba wajibi bane......bai zama wajibi a kanta ba,amma ya matsanta ya daga hankalinsa,to ko sultane ya fara gajiya da ita ne?. Ta tambayi kanta da kanta,bata kuma kai ga lalubo amsar ba muryar mammina ta sauka a kunnenta.
"Ranka ya dade.......alfarma mukazo nema" Ta fada tana sake qanqan da kai. Kansa ya daga a nutse ya kalli mammina.
"Allah yasa zancan bame tsaho bane,don ina da baqo me muhimmanci da na gayyata zamuci abincin dare dashi" Ya qarasa maganan yana kallon katafaren agogon dake tsaye da qafafunsa wanda akayi da wani irin qarfe daya bada shape na gidan sarauta.
Wani irin bambarakwai sukaji maganar ta saukar musu,girman maganar a kunnuwansu ya sanya suka kalli juna a sanda idanun sultane yake kan agogon,kafin ya janyeshi a hankali ya maida dubansa kan mammina din.
"Wacce alfarma ce?,Allah yasa batafi qarfina ba......bata kuma shallake iyakoki na ba" Ya fada hankali kwance,yana barin kwanyar akhnan dama ta mammina da lisaafin wanne irin baqo ne haka me tsananin muhimmanci a gurin sultane?,har yana batun su gaggauta fadin buqatarsu don lokacinsa na baqonsa ne kenan?. Wani abu akhnan taji ya tsaye mata a wuya. A iya saninta,ita kadai ce,ita daya ce keda tarin wannan muhimmancin a gurin sultane,to amma waye haka ya samu nasara ya shammaceta,yake kuma neman daidaito kan matsayinta da ita kadai ta cancanci ta sameshi?.
Wani abu me qarfi mammina ta hadiye tana qoqarin saisaita muryarta,tare da bad da tunanin dake neman yin wasa da kalaman data tanada saboda lokaci irin wannan.
"Ba wata buqata da zatafi qarfinka Allah ya baka yawan rai......komai yana biyayya ne ga umarninka......haka nan jin qanka......ya ta'allaqa ne akan kowa,ballantana kuma kan iyalinka da kuma shalelenka" Takai qarshen maganan tana nuni da akhnan dake zaune bata ko qwaqwaqwaran motsi.
"Karki damu da dukka wadannan bayanan,jeki kai tsaye ga bayananki" Ya fadi yana qara nesanta fuskarsa da dukkan wata fara'a.
"Me martaba......muna neman kayi mana rai.....kayi mana alfarma,ka janye zancan hakeem daga kanmu.......ka dubi......."
"Zaituna" Kiran da sultane yayi mata kenan,wanda ya sanya gabanta wani muguwar faduwa. Sautin daya kirata dashi,da kuma kiran da yayi mata kai tsaye ba sakayawa ya tabbatar mata cewa.....lamarin yayi wani irin zama cikin zuciyarsa......hukuncin ya samu dukkan tabbatuwar da babu alamun janyewa.
"Zaituna......daga yau daga kuma yanxu.......inaso ki janye kanki daga cikin wannan batun.....bama ke ba,inason duk wani wanda yakeson ya tsira daga fushina ya cire hannunsa.....wannan din hukuncina ne......wannan din zartarwa tace da babu wani abu da zai canzashi. A wannan shekarar,zan aurar da diyata ga wanda na gamsu na kuma nutsu da addininsa tarbiyyarsa da nasabarsa,zan aurar da diyata kamar yadda musulinci ya baawa uba daman zabawa diyarsa budurwa miji......saidai idan zata nuna masa iyakarsa ne.......zan aurar da khadeeja kamar yadda kuma musulunci ya tsara......ba shawara nake nema ba bare a kawomin mabanbantan ra'ayi". Ya fadi da wani irin yanayi dake nuna babu sassauci ko canzawa a maganarsa.
Wani irin kalar tashin hankali ta dinga ji yana sauko mata. Ba abinda ke gilmawa a idanunta a sannan sai gata an daura mata igiyar auren HAKEEM. Gata a qarqashin inuwar bagidajen mutum irin hakeem din,tana karba daga umarninsa,tana kuma gaza yin komai da haninsa.
Wani abu ya harba cikin kanta,taji kamar an samu allura ne an soka mata. Taji wani energy a jikinta da yake bata cewa......tayi dukkan me yuwuwa wajen nunawa sultane batason auren HAKEEM,tayi dukkan abinda zatayi don tabbatarwa da sultane qudurinta da kuma ra'ayinta,ba tare da jiran shawara ta biyu ba ta miqe.
Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki kai tsaye ta zarce tana takawa zuwa inda sultane yake zaune. Da mammina da sultane din binta sukayi gaba dayansu da kallo,ta qarasa,sai ta sulale a hankali tana zubewa a gabansa kaman me neman gafara. Ta sadda kanta qasa,zuciyarta na tsananin bugawa da yadda taga sultane ya zube mata dukka idanunsa.
Wasu zafafan hawaye ne suka subuce mata a sanda bata shiryawa zubarsu ba,kawai sai taji bata da wani sauran jarumtar boyesu ko hanasu zuba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 76
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_________________________
*SHEIK HAISAM*
★★Wani sashe ne na musamman cikin gidan dashi kansa tsarinsa ya burgeshi. Na musamman din da zai sake tabbatar maka da hakan saboda kalar masu tsaron dake kowacce qofa da kusurwa da zai taka ya wuce.
Babban abinda yake bashi mamaki shine,ta yadda kowacce qofa yazo zai wuce da hanzari suke janye masa ya ratsa ya wuce abinsa,wanda a binciken da yayi iyalin sarki ne kadai.ko 'ya'yan cikinsa ko wanda yake da mugun kusanci dashi ya isa ya ratsa wadannan qofofin kansa tsaye,va tare da wata zazzafar tuhuma ba,har kuma ya tsinci kansa kyakyawar harabar da yake takawa a yanxu,wanda tafi zubu da makadeden tsakar gida na alfarma,wanda daga nan yake iya hango kyakyawar balcony din dake lullube da shuke shuke,balcony din da ita zata sadaka kai tsaye da qofar makadeden parlor din me martaba.
Guri ne da muddin ka iskoshi baka buqatar iso game martaba,dukka shingen daka tsallaka ka wuce suka baka daman isowa ga nan din sun gama tantanceka,don haka kai tsaye ya dinga takawa yana nufar balcony din.
Sanye yake da wata jubah me sulbi kalan gray color kalar data haska ta kuma fidda tsananin kyan fatarsa na asalin qabilar oromo me hasken kala data dara ta sauran asalin qabilar. Daga wuyan jubah jallabiyyar da hannuwanta wasu irin maballai ne masu tsananin kyau da daukan hankali.
Kansa kuwa hiram ne me kyau daya masa wani irin nadi da mafi yawan matasan larabawa 'yan birni keyi masa,shi ba yafashi yayi ba,amma yafi shigen kama da daurin dankwali da aka saki jelarsa ta baya,wata kuma ya sauko da ita kafadar hagunsa.
Tattausan unique scent dinnan nasa ke fita,iska tana kadashi gami da kwasarsa tana watsashi sassanni daban daban na sashen me martaba dama kewayensa,qamshin da yakan jimma manne a guri bar tafi ba,yakan dauki kwana uku ma musamman idan har haisam ya zauna a gurin ne na wasu awanni.
Qafarsa wani lafiyayyen farin takalmin fata ne,wanda ya dace da torches din jikin amama din kanshi(hirami) da kalarsa ta kasance gray da torches na white. Koda sau daya ka aza idanu a kansa lallai zai burgeka,komai nasa yana nuna tsantsar ilimin addini daya cakuda da wayewa ta fannin sanin duniya da abinda ke cikinta. Wata irin wayayyar siffa ce dake kwance cikin duk wani motsinsa,wadda ta cakuda da tasirin addini da wani iri kamala da kwarjini da alqur'ani yake zubawa dan adam.
Can qasan maqoshinsa yayi bismillah a sanda yake dora qafarsa saman step din farki na balcony din,bismillah din da adams apple dinsa ne kawai ya motsa,wanda ya fito sosai daga saman maqoshinsa kaman idan ka sanya hannu zaka iya ciroshi.
Manyan idanun nan nashi da shigowar dare ya sanya suka rusuna kadan ya ware a hankali,yana duban mutumin da baya iya ganin fuskarsa sai faffadan bayansa,yana maqale sosai da wani irin salon tsaiwa jikin tafkeken window din dake kai iskar tsirrai me sanyi dake busawa a gurin zuwa cikin ainihin parlor din.
Kaman yadda ci gaba da takawan da yakeyi bai hanashi ci gaba da kallon bayan mutumin ba......wanda da ganinsa basai an gaya maka ba qaqqarfa ne......hakanan takunsa bai dauke hankalinsa ko na mutumin daga tsaiwar da yakeyi ba. Qasan takalminsa yana da laushi kaman yadda saman takalmin keda laushi,wannan ya sanya hankalinsa ya gaza daukowa don da alama bayajin kowanne irin sauti,sai sake maqalewa da yakeyi jikin window din sosai,da alama akwai abinda yake tsananin buqatar yaji,abun kuma daya kasance me muhimmanci qwarai da gaske a tare dashi.
Sannu a hankali mamaki ya soma wanzuwa qasan zuciyar haisam,ya kuma katse duk wani nazari da yakewa katangun dake kewaye da sassan sultane din ya maidashi kacokam kan mutumin.