← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 97

Sashe 57

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Silvouse plaît" Cak ta dakata,qirjinta yana wani irin luguden duka. A tsahon tarihin rayuwarta,idan ka cire sultane......babu wani d'a namiji guda daya da taba samun damar kama koda zaren da aka dinka tufafinta dashi,bare ya riqe mayafin dake yane a jikinta.

Baisan girman kuskuren da ya tafka ba,shi ya sanya yaci gaba da tsara mata kalaman da yake ganin zaisa ta fuskanceshi. Tsakanin buhaina birra da yalwa basusan waye yafi wani gigita ba da ganin irin kalar kuskuren da abood ramadan ya tafka ba,saidai dukkaninsu basu kai ga tantance abinda zai iya faruwa ba qarar saukar marin ya isa ga kunnuwan mutane da dama......cikinsu kuwa harda haisam da falaak wadda ta gaza motsi tun sanda akhnan ta fara magana da abood. Tun shigowar akhnan din tajishi saboda gurin daya ne,wasu tsararrun shukoko ne masu tsaho da kauri kawai suka banbamta gurin.

Cikin wani irin razana da tashin hankali falaak ta daga idanunta ta can qasa tana satar kallonsa sanda yake ci gaba da sauraron karatun Aafreen.

Ba wani yanayi dake fuskarsa daya canza. Bataga alamun ma yaji komai ba,abinda ya sanyata a dimbin dimauta da kuma kokwanto.

Babu ta yadda za'ayi yace baiji abinda ya faru ba,tun daga shigowar biftu gurin baqinta har kawo yanzu ba. Tayi imanin koda kana nesa da inda su suke karatun xaka ji komai ballanta a nan din inda suke zaune koda takun sauke qafafu saman ganyayyakin da suke zube a qasa kana iya jinsa.

To amma me yasa yayi kamar baiji ba?,me yasa yanayinsa ya nuna baiji komai ba?.

Qanqame hannuwanta da idanunta tayi sanda kalaman akhnan na qarshe cikin tsananin fushi suke fita.

"Idan kai mahaukaci ne ya kamata kasan guraren da zaka dinga gwada haukarka.........in bakayi wasa ba tabbas ba zaka fita daga masarautar agadez da qafafunka ba,zan ganar dakai kuskurenka.......ka gaggauta kwashe karnukanka ku fice mana a masarauta,domin nan din ba bariki bace"

"Me yasa yaa biftu?......me yasa?" Falaak ta fada can qasa tana jin jikinta yana daukan rawa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 47
__________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
____________________________

Ba ita aka mara ba amma tana jin saukar sautin marin har yanxu,tana jin takun akhnan da yalwa ke faman sanyayawa rai

"Allah ya huci zuciyarki shelelen sultane,.......Allah shi baki haquri......ya tafka kuskuren nan ne duk a rashin sanin wacece ke......ayi masa afuwa da gafara" Har taji takun nasu ya mata nisa alamun sun fice a wajen.

Da qyar ya iya riqe numfashinsa zuwa sanda Aafreen takai qarshen surar. Ya maida bangon qur'anin ya rufe yana qoqarin controlling hannunsa ya furta.

"Ma sha Allah" Yana miqa mata qur'anin.

"Yaaa falaak" Ta tsinci muryar Aafreen tana kiran sunanta,abinda ya dawo da ita hayyacinta kenan. Ta daga kanta da sauri sai suka hada idanu,ba shiri ta maida kanta qasa. Kusan sakanni goma bai sake cewa komai ba,kafin a nutse yace.

"Ki tabbatar kin ajiye komai daga bakin qofar nan kafin ki shigo aji,nafi buqatar koya karatu ga wanda yasan girman abinda nake koya masa din........na biyu jilbab,ki nema jilbab wadatattu da zaki dinga zuwa daukan karatu dashi......na uku....." Sai yadan dakata kadan yana daidaita numfashinsa.

"Ki nemi wadda zaku dinga zuwa karatu tare da ita,bazai yi ajinki ya zama ke daya bace" Ya fadi yana jin komai dole ya zama bisa tsari na shari'a. Baya taba yarda da batun kebewa koda wane muddin macace don kiyaye hukuncin Allah da haqqin addini.

Kai ta jinjina a hankali tana sake yin qasa da kanta,mamaki kuma yana sake kasheta. Dan siririn murmushi ya saki yana miqawa Aeera me shekaru hudu hannu.

"Ilallliqaaa" Ya furta da tataccen larabcinsa,sai yarinyar ta saki murmushi itama tana maida masa amsa.

"Liqa'ana bi khair" Duk da qarancin shekarunta tana jin yana burgeta,tana jinsa kamar wani abbanta ko yayanta.

"Yaa falaak.......an tashi fa" Aafreen ta fadi wadda ta miqawa ramma litattafanta ta tsugunna tana qoqarin sanya takalman qafarta.

"Zan taho yanzu" Tace dasu tana miqawa ramma litattafanta. A girmame ta amsa,taja hannun yaran suna wucewa.

Tsam ta miqe,ta zura lausasan takalmanta tana jin jikinta gaba daya ya sake,zuciyarta kuma tana cakuduwa da wani irin yanayi guda biyu.

Takawa ta dinga yi a hankali,har ta zagaya ainihin masaukin baqin akhnan din. Wasai yake babu kowa,alamun an gama,kuma kowa ya kama gabansa. Da wani irin mutuwar jiki ta qarasa ta zauna saman daya daga cikin kujerun dake a wajen ta zauna.

Wai meke damun yaa biftu ne?......mari?,marin ma a fuskar namiji me cikakken hankali da kuma shekaru?. Ta yaya har take da zarra da qarfin halin d'a namiji?. Yaushe zatayi aure?,yaushe zata fahimci aure yana zama wajibi akan mace irinta?,sai yaushe zata daina raina maza har haka?.

Yadda qarar marin ya riskesu ya dawo mata,takai hannunta fuskarta tana shafawa. Me yasa yayi kamar baiji komai ba?,me yasa yayi kamar baiji abinda yake faruwa ba?. Ta tambayi kanta bugun zuciyarta na qara gudu da iya tunawar da tayi kadai da fuskar sa.

"Saboda bai shafeshi ba,ba huruminsa bane" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa nakai tsaye,amsar data sanya murmushi subucewa daga fuskarta duk da ba a yanayin take ba.

Wannan shine kalar saurayin da yake burgeta,wanda ba ruwansa da shishshigi.....kalar mutumin da sam baya shiga sabgar da ba tashi ba.....MISKILI NE kenan da gaske?" Ta yiwa kanta tambayar tana rungume hannayenta a qirji.

Daga kanta tayi sama,duhu ya fara raguwa sosai,alamun dake nuna magariba tana dab da qarasowa,saita miqe a nutse tana sake harde hannayenta a qirji tana kuma takawa don ficewa a gurin.

Saidai har yanzu murmushi yaqi barin saman fuskarta,tana ta jimami tanata kokwanton ba zasu samu kaman oustaz Ousmane ba........sai ga wani da yasha banban dashi ta kowacce fuska. Ba karatu yayi mata ba yau din,yau din ta cika ne kawai da tarin tambayoyi,amma yanayin tsarin da ya aza nasa karatun ya bata gamsuwar dari bisa dari shi na musamman ne.

Amma ya cika izza da yawa,kaman akwai tasirin sarauta a jininsa,dukka motsinsa da yanayinsa ya mata kama da wani basarake ko masarauci,saidai ba wata qwaqwarar shaida daya nuna hakan,ta yaya karatun zai kasance?" Ajiyar zuciya ta saki nannauya tana kai tafukan hannuwanta ta shafi fuskarta.

"A hankali falaak,wannan dogon tunanin duka na meye haka?" Ta tambayi kanta da kanta,tambayar data sakata sakin murmushin dole.

"Tsarinsa ne da yanayinsa kawai yayimin" Ta bawa kanta da kanta amsa,batasan ko tayi daidai ba ko batayi ba,iya amsar da takejin zata iya fita daga zuciyarta kenan a daidai wannan lokacin.

*AKHNAN*

Ko sassan mammina batayi sha'awar komawa ba ta dakatar dasu yalwa tun daga farfajiyar data raba sassan sannna ta wuce sashenta. Tun a falukan farko ta dakatar da kowa,tace dukkan wani motsi bata sonshi,kowa yayi nesa da inda take ta wuce kai tsaye zuwa dakinta.

Da kanta ta dinga zare kayan jikinta tana watsarwa,tana jin tsanar suturar tana mamayarta.

Irin abinda take gudu sultane yake shirin jawo mata?,wannan din shine mutum na goma sha biyu cif da sultane ya tilasta haduwarta dashi,yanzu har yakai?,har yana da zarrar kama gefan mayafinta?.

Kuka take so tayi,amma sai takejin bashi da martaba da darajar da zata zubda masa hawaye. Bashi da wannan alfarmar da hawaye zasu zuba a idanunta ta dalilinsa,kawai abu daya takeji......kaman ya kamata hukuncinsa yafi marin da tayi masa.

Toilet ta shiga,ta sake wanka gaba daya,tana jin kamar ya samu nasarar taba jikinta ne ba mayafinta ba. Ta wanke jikinta sosai tana jin kamar ta sauya fatar jikinta,ta fito daure da towel fuskar nan cike da wani irin fushi.

Ta jima zaune tana jira ruwan jikinta ya tsane da kansa,don ko samun damar gogeshi batayi ba,zuwa sannan kuma har ta jiyo kiraye kirayen sallar magariba,don haka ta miqe a kasalance ta shige closet dinta tana laluben kayan sawa,abinda bata saba bata ma iya ba,wannan ya sanyata kafin ta kammala ciro wani up and down skirt da blouse dinsa da dan madaidaicin scarfs dinsu taji ta gaji tubus.

Gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta,har yanzu zafin abun takeji har cikin fuskarta. Ba wanda zata nema,ba wanda zatayi magana dashi har sai sun nemeta da kansu.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

Wani irin kyau kayan sukayi mata,sun fiddata kamar 'yar qasat turkiyya din,ta aza abayar sallarta a sama ta tayar da sallah.

*MAMMINA*

Tunda suka fita da yalwa tana zaune daga bakin babban window din da yafi kama da qofa,wanda ya bada wani irin yanayi me kyau da take iya hangen lambun dake liqe da sassanta.

Wayarta na a hannunta tana duba fuskar wayar lokaci bayan lokaci,yayin da gabanta ke shaqe da nau'ikan kayan ciye ciye na kayan marmari.
Chapter 57 · 0% Book details