← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 97

Sashe 1

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*FREE PAGE 1*
_______________________________

https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
_____________________________

_Bismillahir rahmanir raheem_

*_Shimfida_*

_Lu'ulu lu'ulunne dai ya yardar Allah,shimfidaddiya kuma miqaqqiyar tafiya dake dauke da wani sabon zubin labari_

_manyan qasashe guda biyu da taurarinmu zasu kasance mallakin qasashenne,wasu abubuwa da guraren zasu iya sabawa da yadda ainihin zubi tsari da kuma yanayin da qasar ke rayuwa akai_

_fatan shine cimma gaci.......fatan shine cimma anihin saqon da alqalamin HUGUMA ya sauka a kai_

_wani sabon salon labarine dake dauke da sarqaqiya.......boyayyun qulle qulle da ZARGE wanda bahaushe kewa kirari da mugun qulli_

_sarauta QASAITA DA IZZA ne zallarta take magana cikin wani irin salo me ban qayatarwa_

_karki bari.......karki sake......kada kuma ki yarda a baki labarin tafiyar nan ya kasance ba dake aka yita ba_

_Allah ya bamu sa'a,yadda muka fara yasa mu kammala a tare cikin qoshin lafiya arziqi da kuma wadata_

*AGADEZ*
*masarautar agadez*
*_Maison de i'emir_*

Masarutar agadez,babbar masarauta ce data kafu tsahon shekaru masu yawa. Ta samo asalin kafuwarta tun daga wani qarni can baya daya wuce,wanda aka samu rarrabuwar kawuna gurin masu buqatar mulkar yankin daga kowanne gida iyali da kuma dangi. Rashin samun hadin kan fidda mutum daya yayi sanadin yanke hukuncin tafiya zuwa ga daular musulunci ta istanbul,mahukuntan yankin agadez kuma suka nemi agaji wajen basu wanda zai zama shike mulki da yankin,wannan shine ya haifar da samuwar sarki na farko dan asalin daular turkiyya istanbul *MUHAMMAD AGGA_ABBA BIN MUHAMMAD ALMUBARAK*.

Sosai auratayya hulda na kasuwanci da cinikayya sukaci gaba da wanzuwa tsakanin qasashen nan guda biyu,wanda ta haifar da haihuwar mutanen da suka kasance *RUWA BIYU*. Wato halfcast inji bature.

*BUZAYE* na daya daga cikin qabilun da suke da yawa sosai cikin qasar agadez,wasu irin launin mutane dake da wani kyau na musamman daya zame musu tambari na daban,ya kuma sanya suka zama na musamman. A cikinsun SULTANE MUHAMMAD HAMUD ya fito.

Mahaifinsa buzu ne na asali,wanda jininsu ya gauraya da na turkawa,don kuwa mahaifiyar SULTANE MUHAMMAD HAMUD 'yar asalin garin istanbul ce......wannan ya sanya kyanshi ya zama wani irin nau'i na daban daya gadoshi daga bangare biyu wato UWA da UBA.

SULTANE MUHAMMAD HAMUD......qasaitaccen sarkin da yake mulkin qasar agadez a yanzu. Wata irin hamshaqiyar sarauta dake cike da izza qarfin mulki dana iko gaba daya. Sarkin da yasha banban da dukka sarakunan da sukayi mulkin kafin shi......sarkin daya kawo gagarumin sauyi ya canza qasar agadez gaba daya daga fuska yanayi da tsarin da take a baya,zuwa wata sabuwar duniya datasha banban da kowanne yake na qasar NIGER gaba daya.

AGADEZ din a yanzu ta zama wani yanki ko kuma gunduma ta musamman.......yankin daya fadada ta fuskar noma kasuwanci ilimi da sauransu. Wannan sauyin bai tsaya a iya yankin AGADEZ kawai ba......yayi mamaya har ya zuwa cikin ainihin gidan sarautar yankin. Komai ya canza daga inda yake zuwa wani bigire dake tafiya da zamani.....wani yanayi dake dauke da kowanne ci gaba na zamani,ya zamanantar da komai din da wani irin salo da dole kowa ya sallama. Cikin qauna ga sultane muhammad hamud da girmama duk wani motsi da aiki nasa suka bashi sunan ZAMANI GOMA.

Qasaitaccen sarki,ma'abocin izzar dake barazana tare da kad'a zukatan abokan burminsa.......qasaitaccen sarkin da kwarjinsa ya keta ta cikin kowanne hijabin BARAZANA......qasaitar data dasa shakka tsoro da kuma kokwanto akan zuciyar duk wani dake da zaton yakai ya tsaya gurbi guda dashi......kwarjinin daya zama wanzajjen abu dake ea matuqar tasiri,ya kuma sanya zukata da yawa sallamawa.......

Yana da wani irinn qualities yana da wata irin ZARRA yana da wata irin jajircewa.......saidai duk da hakan akwai wani RAUNINSA guda daya.......RAUNI ne da ba zai taba canzuwa ba.......bazai kuma taba shafewa cikin rubutacciyar qaddararsa ba. RUHINSA ce ita......wani bangare ce ta RAYUWARSA.......GUDAR TSOKA daga zuciya da kuma jikinsa.......ita din wani abune me muhimmanci da ta zama shaida ga kowa cewar.......ba wani abu me tsananin muhimmanci da idanu ke iya ganin ya MALLAKA kamar ita. *_khadeeja(AKHNAN)_*
*_Duk kuwa da tarin baiwar dake lullube da rayuwarsa......amma yana jin kamar daban TAKE cikin komai nasa. Tarin dukiya madararta,izzarsa......mulki da DAUKAKAR suna data mulkinsa wadda ta gangara cikin kowanne lungu da saqo na qasarsa.....qasashen africa GABA DAYA dama wasu daga cikin qasashen qetare_*

*EMIRE PALACE*
_Palais de i'emir_

Wani bafaransen gine ne ko kuma mu kirata DUNIYA ta musamman dake zaman kanta tsakiyar bagargajiyen ginin masarautar AGADEZ din. Gini ne da dake tsakiyar manyan katangun masarautar agadez dake qara nuna qarfin iko dana izzar da masarautar ke dashi. Zaka tadda gine gine iri daban daban dake nuna gargajiya da kuma ainihin al'adar gidan sarautar dake bisa tsari da kuma zamani......zamanin da bai sanya alamu ko burbushin gargajiyar bacewa ba saidai ya gyarata daga ainihin asalin GARGAJIYAR zuwa GARGAJIYARZAMANI.

Wani taswira ce da aka tsamota kacokam daga qasar France,qasar da a baya ta zama uwa kuma uwar goyo ga qasar ta nijer,aka kawoshi aka ajiye cikin gidan sarautar sultane muhammd hamud. Katafaren VILLA ce wadda ita ke zama mafaka kuma mazauni ga iyalan SULTANE MUHAMMAD HAMUD. Duk kuwa da cewa matanshi na auren biyu ne........amma kuma villa din na dauke da sassa guda shida ne.

Sassa uku dake cikin villa din tafi kowanne sassa na ginin girma kyau fadi tsaho da kuma tsaruwa,biyu na matansa ne daya mallakin me alfarma sultane muhammad hamud,sauran an ajiyesu ne saboda baqi da kuma hadimai. Duk sashe daya yakai girman wani mansion House na mutum guda,wannan ya sanya akwai tazara sosai tsakanin wane da wane,kuma kowa yake rayuwarsa ba tare da damuwa ko takura daga dan uwansa ba.

Bata baki ne kawai a gareka a wannan rana ta juma'a tsaiwa tambayar wani
"Akwai wani gagarumin taro ne da zai gudana?" Domin kuwa tun daga gate din farko da zai fara kawowa farfajiyar farko da zata kaika farfajiya ta biyu wadda zata sadaka da villa din mai alfarma sultane idanunka zasu iya ganin komai. Yawaitar zirga zirgar hadimai maza da mata.........canje canje da sauye sauyen da akewa wash flowers da sauran kayan alatun da suka zama cikar ado da qawar villa din,duk kuwa da cewa wannan din ba baqon abu bane,kusan koda yaushe wannan villa din cikin tsari take da kuma gyara bisa kulawar manyan jakadun guda biyu da villa din ke dasu *AYAANA* da kuma *ME WADA*.

A qarqashin ayaana da me wada kuwa tarin bayi ne.......dogarai da kuma ma'aikatan da kowanne yake jagoranci da rarrabuwa ayyuka iri daban daban,wadanda sune suke tafi da kowacce rana da wuni na villa din. Iyakar nan dinne kawai tasu iyakar da hurumin,kaman yadda kowanne dogari da bawa yake da nashi iyakar da hurumin cikin gidan.

Duk da yawan canzawar motsi da kai kawo dake wanzuwa a villa din harma da gidan gaba daya,hakan bazai hanaka ganin daga bangaren da wannan motsin yafi yawa ba.

Sashe ne da yake mallakin hajiya *ZAITUN* uwar gidan me alfarma sultane hummad hummad wanda ke amsa sunan *UWA* ga *AKHNAN*. Duk kuwa cewa ba itace matar farko ga sultane muhammd hummad ba.......amma a yanzun sunan uwar gidan ya zama shine TAMBARINTA........uwa ce ga AKHNAN amma akwai wani dalili daya hanata amsa sunan MAHAIFIYA. Dukka wadannan dalilai hakan bai samu qarfin iko dana dantsen togacewa ko rabata da wadannan *LAQABI* guda biyu ba da take matuqar ji dasu.....fiye da yadda uwa ke ji da jaririnta sabuwar haihuwa UWARGIDAN SULTANE kuma UWAR AKHNAN.

Wani qasaitaccen gine ne dake qunshe da dukkan wani kaya na qasaita da kuma alfarma,wanda iya su kadai sun isa gaya maka lallai QASAITA da kuma MULKI ne suke magana.

Zaka wuce faluka bayan faluka,gurabe masu yawa kafin ka samu isa bangare ZUCIYAR MASARAUTAR kuma SHALELEN SULTANE take.

Wani irin ni'imtaccen parlor ne dake da wani irin girma da kuma tsari......irin tsarin da yake zamewa abun kallo a idanun mutane masu yawa,saboda ba tsari ne da aka saba ganinsa ko ina ba......ba kuma tsari bane da aka saba ganinsa koda yaushe ba.

Komai na parlor din ya kasance ruby red color and gold,tun daga kan lafiyayyun curtain na kamfanin NICETOWN dan qasar France,har zuwa Italian royal chairs da parlor din ya laqume har set biyu. Lausasan carpet dake nuna zallar alfarma da qasaitar falon dama dukkan abinda ya mallaka dake cikinsa......wasu irin qananun side tables mulmulallu dake daukan idanu wanda suke mahadi da Italian royal chairs din dake parlor din. Gypsum ceiling ne lullube saman parlor din,wanda aka qawata da wasu kyawawan fitilu da kuma crystal Chandelier daga tsakiyarsa. Iya su kadai abun kallo ne da zai daukeka shudewar wasu daqiqu kana mamakin yadda aka baje fasahar samar da ceiling na musamman irin wannan.
Chapter 1 · 0% Book details