← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 97

Sashe 48

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zuciyar sultane ce.....diya qwara daya da sultane yake ji da ita,diyar kuma data zama wani abu mafi girman daraja da tsada da sultane yake dashi a duniya" Idanu haisam ya lumshe sannan kuma ya budesu,yana jin maganganun Maher din a wani muhalli da sam bai gane masa ba.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Idan kace ita daya ya mallaka bakayi laifi ba.....duk da a zahiri diyoyinshi guda biyu ne.......sangartacciyar 'yar gatar da ake tattalinta da dukka abinda takeso.......da kuma dukka abinda taga dama takeso ya wanzu a yadda take muradi. Tana hukunci tana alfarma,tana kuma zartarwa dukka a qarqashin nata ikon,saidai wani abun mamakin kuma.......ba wani wanda zai iya baka cikakken siffa da kamanninta,don ganinta ido da ido a gurin jama'ar yankin nan bai zama abu me sauqi ba".

Wani abu haisam ya hadiye a hankali yana qoqarin faffasa kalaman Maher,yanason kawo daidaito tsakanin maganganunsa dana Ousmane.

"Akwai maganganu da yawa a kanta ga wadanda ke rayuwa kusa dasu.......tana da wata irin izza girman kai da alfaharin daya zarta na mahaifinta.......tana da tsare tsare da dokokin da muddin zaka rayu tare da ita dole ka kiyayesu.......har ila yau......ita daya ce tilon macen da take iqirarin har a yanxu ba'a haifi nau'in namijin da zai dace da rayuwarta ba.......har yanzu babu namiji irin nau'in ajinta....." Idanu abdii ya waro yana duban haisam da gabansa kawai yake kalla,hankulansu suna rarrabuwa kashi kashi. Yanayin unguwar da suke tafiya a cikin ta,yanayin mutanen dake kai kawo jifa jifa,sai wani dan qaramin kaso na hankalin nasa daya miqa akan maganganun Maher. Dukkan alamu sun tabbatarwa abdii hankalin haisam baya kai dari bisa dari,sai ya janye idonsa daga kan haisam din ya mayar kan Maher yana mamakin me ya hana wannan baqon labarin da yasha banban da labaran da suka saba ji da gani su dauki hankalinsa?.

"Amma ita din wacce irin halitta ce ita?......yaya take?......wani irin launi gareta da dukka mazan duniya basu tsaya a mataki da cancantar samun aurenta ba?".

Sosai shima Maher yake da nutsuwa,irin nutsuwar da zai wahala ka fuskanci shi din daya daga cikin ma'aikatan NISS Ethiopia ne.

"Mutum ce kamar kowa......amma nasha jin hirarta a bakunan mutane a guri daban daban da lokuta daban daban.....mutum ce amma tasha banban da tarin Mata........tana da wani kyau kwarjini da kebantattun abubuwa da naji suns cewa ta cancanci zaben duk kalar mijin da takeso.....ko waye ko wanne iri ne......"

"Meye alaqar koya karatuna da yaran sarki da ita?" Yayi tambayar ta kai tsaye ba tare daya kalli Maher ba,don yanason banbamce wasu abubuwa da baiso su zama cikin qurataccen lokaci. Uwa uba ya gaji da jin soki burutsun bayanai a kanta......abu guda yakeson tantancewa shine.......ta kasance bata cikin mutanen da zasu fado hanya ko gonarshi.

Girman kai......izza da raina mutane,wasu dabi'u ne da yanzu yanzu suke raba tsakaninsa da kai. Wasu dabi'u ne da ya tsana yayi matuqar yin hannun riga dasu.

"Tana Niamey tana gudanar da kasuwancinta.......itace CEO na SAHEL COUTURE" A nutse haisam ya maimaita sunan kamfanin can qasan ransa.

Kalman CEO babbar muqami ne ko matsayi a kamfani. CEO yana tsaiwa akan komai da komai daya shafi cikin kamfanin dama wajensa......to amma ta yaya tana da wannan matsayin fuskarta ta zama wata boyayyar aba?.

"Zanso naga wannan......." Abdii ya soma fadi,saidai baikai ga qarasawa ba haisam din ya tari numfashinsa

"Abdii" Ya kirashi still idanunsa yana kan hanya.

"Obbo" Ya furta yana maida hankalinsa jikinsa.

Daga yanayin haisam Maher ya fuskanci baya buqatar hirar......hirar kuma bata dace da mode dinsa ba,don haka bai sake cewa komai akai ba,har zuwa sanda sukayi doguwar tafiya sosai.

"Ina buqatar qarin sani akan komai daya shafi cikin gidan......sauran zan bincika da kaina" Ya fadi yana tattara hankalinsa guri daya.

★★★Cikin girmamawa kowacce qofa ta gidan da masu tsaronta mataki mataki take motsawa tare da budewa don samun damar shigar motocin dake dauke da akhnan din cikin ainihin ginin gidan.

Basu tsaya ba har sai da sukakai gurin ajiyar motoci na musamman na cikin gidan,wanda ke dauke da tarin motocin sultane dana mammina da ragowar na akhnan din,harma dana morsa safiyya wanda ba kasafai ta fiya hawansu ba.

Tun kafin motocin su kammala tsaiwa take iya hangen mammina din. Tsaye cikin adon nan nata da kowanne lokaci yake qara nuna ita din matar sarki ce.....matar babban mutum me alfarma ta daya sultane muhammad hammud. Iya suturar dake jikinta kawai wani babban jarinne a gurin dubbunnan mutane,daga bayanta kuma hadimanta ne su biyar,ciki harda yalwa ta hannun damanta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 40
___________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*👘🥻

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana goma KACAL!✌🏽*

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*🙌🏽
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________

Dauke idonta tayi tana sauke ajiyar zuciya,jikinta duka a mace yake kuma a sanyaye,saboda har yanzu bata da tabbaci ko tartibin abinda zai faru da ita.

Alamun bude mata murfin motar ne ya dawo da hankalinta jikinta,ta fidda numfashi me nauyi tana jin yadda zagin gidan yaketa wasata

"Gaba salamun baya salamun......barka da isowa zuciyar sultane.....tauraruwar qasar agadez......me alfarma 'yar masu alfarma,wallahi ganinki kadai ya ishi bawa alkhairi,zamanki tare da mutum alfarma ce,qarin daraja a wajensa,sukari me farin alkhairi,bango majinginar bayi........me kyauta da hannun damanta hagunta bata sani ba,me darajar da babu ta biyunta.....ga khadijatul kubra". Sau tari yadda zagin ya iya tsara da jero kalamai a kanta abun yana matuqar burgeta,uwa uba kuma ba wanda yakewa sai ita daya,koda sultane kuwa baya yiwa,ita kadai ya tsayawa yake yiwa,shi yasa sosai take sakar masa kudi.

Mutum ce ita me amana,meson kuma mutum me amana. Wannan ya sanya zai wahala kayi magana da ita ma ka jita a gurin koda su aisa ne,amanarta da zallar miskilanci da izzarta ma ba zasu bari ba. Amma a yau din sai takejin kirarin nata yana damunta har cikin kanta. Ta daga ido tana duban wanda ya bude mata motar,mammina ce da kanta,ta miqa mata hannu kuma tana sakin mata murmushi,take taji zuciyarta ta karye,wani qaunar matar yana sake ratsata,qauna tsantsa mara algus a ciki.

Rungumeta tayi a jikinta tana fadin.

"Sannu da zuwa......sultane ya sakamin ke a gaba gashi ya jawo miki tafiyar mota,Allah ya rabaki da ciwon jiki". Ido kawai ta lumshe,tana jin dadin yadda mammina ke kula da ita,tana jin dadin yadda mammina ta damu da damuwarta,suna raba farinciki da kuma baqinciki tare da mammina din......suna raba samu da asara a tare,suna raba ciwo da lalura dukka idan suka sameta,wasu abubuwa kenan da bata taba hangensu ba ga matar da ake faman kira UWA a gareta.

To wai ta yaya ma zata iya raba wannan qaunar?,wannan soyayyar?,da wannan kulawar?. Batasan ta inda zata fara azasu akan mizani guda daya ba sam sam sam.

A hankali ta daga kanta daga jikin mammina din tana dubanta.

"Kinsan dalilin kiran sultane a gareni?" Ta fada da muryarta me laushinnan wadda ta qara sirancewa. Murmushi mammina ta saki tana kai hannunta fuskar akhnan din.

"Na fiki son insan dalilin da yasa ya kirakin tun kafin ki iso" Ta furta wanda har a qasan zuciyarta hakan take nufi,saidai kuma ta lullube da wani bayanin.

"Don bana qaunar abinda zai taba farincikin wannan halitta komai qanqantarsa.......koma meye ni nasan bazai taba yin abinda zai cutar dake ba,koda ace fushi yayi........amma koda irin hakan zata iya faruwa,ni ina bayanki,ina kuma tare dake a duk wani hukunci da sultane zaice zai yanke". Wannan tsadadden murmushin nata ta saki,ta dora hannunta saman hannun mammina dake fuskarta,labbanta dake da pink color ya motsa a nutse tana furta kalmar.

"Na gode" . Inda akwai wani matsayi a duniya da yafi matsayin mahaifiya,tabbas da zata bawa mammina shi,don ta cancanci hakan.

"Ku kai mata su sassanta,zamu wuce ciki da ita" Mammina ta juya cikin isa tana bawa su buhaina umarni,wadanda suke dauke da handbag din akhnan wayoyinta da wata 'yar qaramar jakarta guda daya data saka suka zuba mata abubuwanta masu muhimmanci da zata iya buqatarsu,saita riqe hannun akhnan sosai cikin nata suna wucewa zuwa sassanta tana qoqarin sako mata labaran da zasu dauke hankalinta.

Sosai akhnan ta cika da mamakin tarbar da mammina ta shirya mata,tamkar wadda tayi wata tafiya ta shekara da shekaru bata nan. Kalolin abinci da abubuwan sha iri daban daban,gyara na musamman tasa aka yiwa dakinta dake sassan mammina din,wanda a baya cikinsa take rayuwar quruciya harta zama budurwa sanda aka wareta daga sassansu. Ta ajiye mata abubuwa masu yawa da tasan tana sonsu,sai akhnan din ta tsaya kawai tana kallon komai kamar almara,kafin ta mayar da dubanta kan mammina din.

Girarta dukka guda biyun ta dage mata alamun yes,sai kawai akhnan din ta fada jikinta tana sakin shagwababben kukanta.

"Ya isa mana babyn sultane" Ta fadi da wani salo can baya da ake kiranta dashi. Janyeta tayi saman wata tattausar qaramat Royal chair dake dakin tana qoqarin kwantar mata da hankali,bata bar dakin ba sai data tabbatar ta samu nutsuwa.
Chapter 48 · 0% Book details