← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 97

Sashe 71

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan qasaitaccen qamshin da a jiya ya sanyata laluben kalar turaruka da dama ko zata samu wanda qamshinsa yayi daidai dashi shi ya fara marabtarta,shine kuma ya shaida mata wanzuwarsa a gurin,sai ta daga kai tana jin wata irin fargaba qwayar idanunta qasa qasa tana dubansa,kafin ta zame idanun nata can qasa daga barin kallonsa gudun kada ya ganta,sai takalman da suke qafarsa kawai take iya kalla.

Idanu ta zubawa takalmin tana son tuna wani abu. Tsahon wasu sakanni sannan ta tuna. Irin takalmin sak da morsa ta taba siyawa me martaba cikin kayan gift da takan hada masa a duk shekara na barka da sallah. Kudi ne masu nauyi da har falaak ta dinga cewa.

"Sultane dan gatan morsa,Allah sarki ni auta falaak,morsa nan na kawo na dubu dari biyar kikace yayi tsada da yawa,ni din macace da zanje gidan wani,ba lallai komai na samu a gidanmu ba na sameshi a gidan mijina......amma ga sultane da takalmin......" Daquwa morsa ta watsa mata tana jifanta da harara,saita saki dariya,ta dauki takalmin kawai tana juyashi,don sosai ya tafi da ita.

Idanunta ta janye a hankali tana laluben fuskarsa,kallon fuskar daya sake tsananta bugun zuciyarta. Wani washewa fuskar tasa tayi sosai cikin lullubin da yakanyi ya suturta habatsa har zuwa karan hancinsa,wanda hakan ba kasafai yake bada daman ganin fuskarsa gaba daya ba. Fuskarsa ta yalwata da sakewar da ba zaka kirata murmushi ba,yana riqe hannun Aeeda sarkin saurin sabo da mutane,wadda kuma ko sau daya mutum yayi mata me rabata dashi dai Allah. Aeeda irin yaran nan ne masu shiga rai,ba ruwanta da baka yinta ko kana yinta,itadai indai kayi mata shikenan,sauran matsalar taka ce.

Tana ankare dashi,da salon takunsa dinnan dake nuna lallai akwai digo na jinin sarauta a jikinsa ya qaraso section din su Aeeda,ya zare takalman socks yayi saura a qafarsa,yahau saman tattausar kujerar da tafi zubi da ni'imtacciyar shimfida me tudu,ba kuma tare daya daga ido ko sau daya ya kalli sashen da suke zaune ita da badee'a ba

Yanayin zamansa kawai sultane mahaifinta ya haska mata,ire iren xamansa kenan a fada ko a cikin gida. Wani zama ne na musamman dake sake fidda kwarjini sosai ga sarakuna,sai ta zuqi wani irin numfashi,kafin kuma ta ajiye badee'a ta rigata magana.

"Hodijam.......yanzun wannan malami ne me koyarwa?" Ta jefawa falaak tambayar tana me mantawa da girman tazarar dake tsakaninsu. Tun dawowarta jininsu yazo daya da badee'a,kuma morsa ta sanyata cikin hadimanta na kusa,don ta yarda da hankali tarbiyya da kamun kan badee'a din. Bugu da qari falaak tana buqatar wani a kusa da yayi rayuwa sosai cikin agadez......cikin masarautar agadez da zai dinga kwatanta mata yadda abubuwan gidan suke,don ta jima rabonta da qasar,tun batafi shekaru bakwai kacal a duniya ba.

"Me kika gani?" Falaak ta tamabayi badee'a tana dubanta a hankali.

"Allah ya huci ranki idan har nayi maganan da ya sabawa tarbiyya da kamata. Kwarjininsa da kyansa ba na irin gama garin mutane bane,zamansa uwar dakina kadai yana alamta ba mutum bane irin kowa......baiyi kama sam da jinsinmu ba.......duk da yana zubi da kamanni da buzaye.......amma akwai banbancin launi a tattare dashi" Tayi maganar qasa qasa,saboda yadda jikinta yake bata kaman zaiyi kaifin jin magana.

"Amma da French yake magana......saidai bayan wannan bansan ko yana magana da wani yaren ba na daban". Falaak ta fada tana neman qarin haske daga gurin badee'a.

Kamar ruwa ya cisu haka sauran kalaman dake bakin kowannensu ya dauke tsaf saboda daga idonsa da yayi ya kallesu sau daya,cikin qasa da second biyu kuma ya sauke kansa qasa yana duba ayyukan Aafreen.

Dukka suka rufe babin maganar,don daga ita har badee'a ba wanda ya qara cikakken motsi ma,har mintuna ashirin nasu Aafreen ya cika,Aafreen din kuma ta tako tayi kiransu rungume da books dinta.

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 61

Daga ita har badee'a cikin nutsuwarsu suka qara wajen,suka zare takalmansu suna zama saman shimfidar da aka raba littattafai gurin zaman mutum biyu. Koda baiyi magana ba falaak ta gama fuskanta,litattafan da zasu fara karantawa ne ya basu ba tare da tambaya ko bin ba'asin sun siya ba?.

Wani irin burgeta taji yayi,ta buda baki ta soma gaidashi da harshen faransanci,ya amsa a taqaice,gaisuwar badee'a ma ta biyo baya.

"Ga litattafan da zamu fara nan.....amma bana karatun banza,kowanne rana kafin mu dora sabon karatu zaku maimaitamin abinda muka karanta jiya don nasan abinda nakeyi din ba wahala bane" Ya fada cikin nutsuwarsa da kamewarsa data qara masa wani irin kwarjini. Da gaske ko zakayi wasa da komai amma kada ka yarda kayi masa wasa da karatu,baya daukan wannan kusan tsakaninsu hussam rumaisa noory dama dukkan 'yan uwansa sunsan da wannan.

"In sha Allah" Falaak ta fadi tana daukar littafin da yace dashi zasu fara.

Iska ta shaqa sosai tana zuqar daddadan qamshinsa har cikin hunhunta. Iya riqe littafin kawai da tayi ba tare data matso dashi kusa da hancinta ba tana iya jin fitar wannan qamshin nasa na musamman daga jikin litattafan. Ta tattara dukka nutsuwarta tana sauraren muryarsa dake fita da wani irin nutsuwar da dole kaso karatunsa......dole kuma ka fahimta ko don irin taushin da amon sautinsa yake bayarwa.

*AKHNAN*

A qasaicenta take takowa zuwa gurin daya zame mata na al'ada gurin ganawa da baqin da suka zamewa rayuwarta alaqaqai,cikin fata da sanya ran a yau wannan din ya zama shine baqo na qarshe da zata gani a gabanta. Duk kuwa da irin yadda zuciyarta ke sake nanata mata cewa,hukuncin sultane fa wani abu ne da babu wanda ya isa ya tayar dashi,duk da zuciyarta na d'arsa mata,lokaci bayan lokaci cewa.......tana taku ne zuwa ga muhallin da zata gana da mijin da sultane ya zaba mata......final choice kuma da take dashi,amma zuciyarta na gaya mata cewa wani abu ne da ba tabbatacce ba.....wani abu ne da bazai tabbata ba,sultane bazai taba aikata hakan ba,ya fadi ne kawai don ya tsoratar da zuciyarta zuwa ga karkata ga aikata abinda yakeso.

Haka kawai ya samu kansa cikin fargabar da baisan dalili ba.......lokacin da ya dauka yana jiranta sai yaji ya masa tsaho. Sau daya tak ya taba samun damar ganinta,amma kuma zuciyarsa ta jarabtu da sonta sau babu adadin da baisan yawan da zai qayyade masa ba.

Sake juya qaramin littafin hannunsa yayi,yana karantawa ne kawai don ragewa kansa lokaci,amma ba don yana fahimtar me yake karantawar ba,sai ya sake budewa yana ci gaba da dubawa ko hakan zai taimaka masa ya sake rage yawan lokutan data barshi a zaune.

Akwai wani yanayi a wajen wanda zata iya cewa baqo ne a idanunta. Batasan wanne irin baqo bane yazo gurinta,amma babu wannan securities din masu yawa......baqin fuskokin da suke alamta cewa dukkaninsu hadimai ne kuma ma'aikata ga baqonta.

Mamaki ya sake cikata.....wanne irin baqo ne yazo gurinta?,wanda babu wani kwarjini a tare dashi?,babu wannan haibar da cikar yawan adadin 'yan rakiyar da suke nuna matsayin da yake dashi.

"Waye shi birra?" Ta tambayi birra dake biye da ita kai tsaye ba tare data waiwaya ta dubeta ba,saidai ta xubawa qofar data rage da zata sadata da ainihin gurin da kuma inda yake.

K'asa birra tayi da kanta,har cikin ranta tana jin fargabar sanar mata wayeshi?. Ba iya yau ko jiya ba take tare da uwar dakinnata ba,tasan dukkan wasu zabuka nata,tasan dukkan wani buri nata......ta kuma san wanne irin nau'in miji take lissafi?.

"Ke nake saurara" Akhnan din ta fadi tana sake ragi karsashi tafiyarta,duk da dama tana takawa ne da salon tafiyar nan tata me kama da tafiyar dawisu.

"Tilon d'a guda daya ga limamin babban masallacin juma'a na zinder........." Birra ta fada cikin sanyin jiki. A sukwane ta waiwayo ta zubewa birra din wani irin kallo. Dan limamin babban masallacin juma'a?......limami kuma?......ita khadeeja sultane muhammad?,ita biftu?.....ita din mamallkiyar hamshaqin kamfanin da kaf fadin africa babu yashi?......ita din diya tilo ga sultane muhammad?.

Abubuwa da yawa ne suke mata kai kawo,bayan tarin tulin tambayoyin da take dasu,saidai kuma GIRMA wani abune dake yawo a jininta......hadimanta kuma har kullum hadimanta ne,kusanci ko mu'amalar yau da gobe ba zata sauya wannan ba,don haka birra ba abokiyar wannan maganar bace.......ba kuma huruminta bane.

"Ki jirani a nan" Ta furta tana juyawa a nutse da qasaitaccen takunta tana sanya kai.

Tun daga nesa ta zuba masa idanu,cikin wannan salon nata da ba kasafai kake iya karantar kai take kalla kai tsaye ba. Fuskarsa ta mata kama da fuskar data taba gani,amma ta manta a ina?,wayeshi?,kasancewarta wadda bame shiga hada hadar jama'a ba. Uwa uba dukka wani abu daya hada da maza a ciki bata sanya kanta cikin sha'aninsu,saboda jin martabarta da izzarta.

A hankali ya rage kaifin kallon da yake mata yana kiran sunan Allah har labbansa suna motsawa.

Da gaske.......kaman yadda ta tsaye masa a rai tun a gani guda daya tak daya taba yi mata a zahiri muraran haka take. Yadda zuciyarsa ta shagaltu da tunani da kuma imagination nata har abun yafi gaban haka a zahiri......da gaske d'aya ce tak cikin mata.....duk kuwa da cewa ba ma'abocin kallon mata bane shi.

HAKEEM sunan yazo kanta dab da zata isa inda yake. D'a ga limamin babban masallacin juma'a na zinder. Tabbas wannan shine wannan hakeem din,wannan hakeem din da sultane suka taba ganawa da mahaifinsa a satin da zata bar agadez ta koma Niamey don kula da kamfanin da sultane din ya mallaka mata sukutum.
Chapter 71 · 0% Book details