← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 97

Sashe 65

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin cikakken ado take,wanda yake bayyana tsantsar dacewar sunan da ita wato GIWA. Wani irin yadi ne me alfarma da asalin tsada dan asalin qasar turkey da aka yiwa adon da ba jikin kowacce basarakiya zaka ganshi ba.

Daga mayafin jikinta har qawatacciyar lallausan socks din qafarta data lullube ainihin qafarta daban suke.

"Wa'alaikumussalam......maraba" Nannie ta fadi sanda mammina ke qarasowa parlor din.

A hankali ta sulale a qasan carpet din,cikin tsananin ban girma,fuskarta kwance da murmushi ta soma fadin

"Ayimin afuwa......bani da kowanne labari na dawowarki Nannie,sai da asubahin yau......jiya na yini cikin hidimar masu bukukuwan aure......sai can dare na samu kaina......da asubahin yau din kuma yayi wuri a tasheki". Qaramin murmushi Nannie ta saki.

"Hidima bata qare miki zaituna,tunda ban ganki ba nasan akwai abinda ya faru,amma safiyya tasa anyi komai daya dace.......ina fatan na sameku lafiya". A hankali ta hadiye wani abu,ta kuma ci gaba da tabbatar da fuskarta a yanayin da take.

"Komai lafiya alhamdulillah"

"Ma sha Allah" Ta fada tana jinjina kai.

"Ga kayan barka da sauka nan,ina fata basuzo a makare ba" Mammina ta fadi tana dan rusunar da kanta.

Wajen Nannie ta waiwaya ta kalla tana murmushi,batasan me yasa kirkin mammina yake neman yayi yawa ba,bata gajiya da hidimarta da hidimar duk wanda ya jibanci sultane.

"Wannan kayan ba iya ni fatimatou kawai ba......harda dukkan wani wanda yake qarqashin bangaren fatimatou ne......kin kawo sanda wadannan 'yan buruntun suke kusa" Ta fadi tana nuna aisa da baki.

Waiwayawa tayi yana murmushi ta dubi aisa,tunda safen aisa ta shiga sun gaisa ita shehnaz,saidai akwai wani dan abu data karanta dangane da mode din yaran. Ta nazarcesu tsaf,dukkan abinda ta hanga din kaifin idanu dana zuciyarta ne suka tsinko mata shi,amma sam su kansu basu sanya shi a mizanin da yanayin yadda idanuwa zasu iya gani ba.

Kaifin ganinta da tsinkayenta ya zarta yadda mutum zaiyi hasashe,ita kanta tasan wannan yana cikin baiwarwakinta da take alfahari dasu,tasan kuma suna cikin abubuwan da suka tabbatar da nasarar rayuwarta a matakin da take kai yanzu.

Murmushi ta sakarwa aisa din kamar yadda itama ta sakar Mata,sai mammina din ta maida dubanta kan Nannie.

"Mammina" Akhnan ta fada da wani irin yanayi dake nuna zallar sakewa daya sake fidda quruciyarta,ya sake daukan shekarunta kuma ya maida can baya,zamanin da quruciyar zalla ke cikin jikinta sosai,saita matsa zuwa jikin mammina din sosai ta zauna.

Hannuta mammina ta riqo tana dubanta.

"Na biya ta sashenki,kamar bakici abinci da safennan ba yadda ya kamata,me ya hana hakan biftu?" Ta fada a tausashe tana duban idanunta cikin nuna zallar kulawa.

"Biftu din dake dosar shekaru ashirin da biyar akewa haka.......zaituna kam bansan sai yaushe zaki daina kallon khadeeja har yanzu a mizanin yarinya ba" Nannie ta fadi tana dubansu da kyau.

Murmushi ta danyi,saidai kuma cikin nata kakkaifan hangen.....cikin nazarin nan nata takeji a jikinta ya kamata ta fara magana,ita ya kamata ta fara cewa wani abu ba Nannie ba......akwai wani harsashin daya kamata ta kafashi a irin wannan gurin,a irin wannan lokacin,don haka tayi qasa da kanta kadan.

"Nace ba......idan ba damuwa,idan kuma da lokacin da za'a iya bani,inaso muyi magana". A nutse Nannie ke dubanta,yadda zaituna ke bata girma yana kamanceceniya da yadda take bawa sultane. Bata dubanta sam a mazaunin qanwar MIJI girma take bata irin na YAYAR MIJI.

"Ba wani lokaci da ba zaki sameshi ba zaituna.......bismillah" Tayi maganar daidai sanda aisa ta miqe a karo na biyu,sai itama akhnan ta yunqura zata miqe

"Zauna......maganan ke ya shafa kai tsaye" Yadda sautin ya fita daga bakin mammina din ya sanya akhnan daga kai tadan kalleta. Akwai dan kaurarawa kadan cikin muryar mammina din,ba kamar lokutan data saba yin magana da ita ba.

"Gata nan Nannie......kiyi mata fada ko ke zataji naki" Mammina ta fada cikin wata sassanyar murya gami da yin qasa da kanta.

Duban akhnan Nannie tayi,kaman yadda akhnan ta daga kai ta dubeta itama. Tsahon wasu sakanni sannan kowa ya dauke kallonsa daga kan dan uwansa.

"Yau kuma?......ni fatimatou?,qarar biftu?" Nannie ta fadi cikin mamakin daya kasa bayyanuwa hatta a saman fuskarta.

Kai mammina ta girgiza tana duban Nannie a nutse.

"Kamawa takeyi Nannie.......yau ta kama na kawo miki qararta.......saboda tana neman hana zaman lafiya tsakanina da morsa safiyya". Iya furta sunan morsa safiyyan kadai ya qarawa akhnan zafi a zuciyarta. Taja wani numfashi tana qoqarin calming kanta.

Girman matsalolin morsa safiyya cikin rayuwarta har yakai mammina ta kawo qararta saboda ita?,abinda bata taba aikatawa ba?.

"Ina jinki" Nannie ta fadi tana gyara zamanta gami da sake tattara hankalinta akan mammina.

"Nannie.......komai da akhnan zatayi koda bada sanin zaituna ba morsa safiyya na azashi akan mizanin NICE SILA.....nike da alhakin yin komai da akhnan zatayi ko tayi.......dukkan iya bakin qoqarina wajen samar da kyakkyawar alaqa da kuma fahimtar juna ina yinsa,ina qarar da dukka qarfina da tunanina wajen ganin akhnan ta fahimci girman alaqar dake tsakaninta da morsa........amma duk yadda nakai ga nuna mata hakan wasu lokutan sai tayi burus,inda a take kuma morsa safiyya ke aza alhakin hakan a kaina......kaman matsalolin dake faruwa kwana kwanan nan.......duk duniya bani da mafita a idanun morsa safiyya......kwana da wuni nake wajen bata lokacin fahimtar da akhnan muhimmancin bin umarnin sultane......darajar kowacce mace gidan aure kaman yadda aure ne itama ya haifeta,saidai na gaya mata ina tsaginta......ina kuma bayanta,bazan mara baya ayi mata auren dole ko aure da wanda bai cancanta ba......amma fidda miji da cika umarnin sultane ya zama wajibi a kanta......ki tayani fahimtar da ita don Allah Nannie......inaso mu zauna lafiya da morsa safiyya.......inaso muyi zama na zumunci da qaunar juna da ita.......amma na gagara samun hakan tsahon shekaru ashirin ina abu daya!" Ta qarashe maganar cikin sautin muryarta yana nuna wani abu ya taba rai da zuciyarta sosai da gasken gaske.

Dakatawa tayi tana maida numfashi,idanunta yana wani irin narai narai kaman hawaye ne kwance a cikinsu.

"Inaso mu zauna lafiya......inason ta fahimce ni,inaso ta gane cewa inason jininsu har zuciyata......ba laifina bane kome daya faru,tsarin Allah ne,kaman yadda na dauki tawa qaddarar a baya,daga baya Allah yayi ikonsa....ya kamata itama ta fahimci hakan,ta yarda da hakan,mu rayu cikin aminci da salama,mu samawa sultane nutsuwa a mulkinsa ta hanyar hada kawunanmu guri daya......na gaza fahimtar da ita hakan" Ta qarasa fada tana yin qasa da kanta da wani irin rauni.

Sosai abun ya taba ran Nannie,iya zamanta da mammina a duka shekarun nan ba zata ce ga wani halinta mara kyau guda daya ba.......ba zata ce ga wani abu guda daya mummuna da taba taba tsinkaya daga gurinta ba. Ko abubuwan da suka shude a shekarun baya.....a shekarun da dukkaninsu quruciya ke zagaya a jininsu ta jingina hakan da sabanin fahimta da aka samu akan mammina zaituna din......wanda daga baya ta wanke dukkan komai daga zuciyar kowa.....har kawo yau kuma ba wani me mummunar shaida ko abun ala wadai a kanta.

Zuciyar Nannie tayi rauni,tausayin mammina ya kamata,kaman yadda akhnan taji zuciyarta tana tafasa akan hawayen data gani yana shirin zuba da idanun mammina din. Ta kasa jurewa da wannan gajeran haqurin nata.......ta gaza danne wannan zuciyartata da fushi ke yawan mata tasiri,ta matsa baya tana jingina da kujera cikin bacin rai.

"Da wannan kalar bacin ran da take dasa mata?.....da wannan kalar dabi'un nata?,ta yaya zanji qaunarta a zuciyata?......ta yaya?.....har abada Nannie.....karkice zakice wani abu dani,taci gaba da amsa wannan sunan,taci gaba da riqe wannan sunan,amma ba zata taba samun komai daga gurina ba,sai wannan tursasawar kadai da zata yita ganinta a idanu na da ayyukana" Tana kaiwa nan ta miqe tana tattare rigarta.

"Kada kice na zauna Nannie......tafiya zanyi"

"Dole ki zauna akhnan......" Nannie ta fada a kausashe. Blue eyes dinta ta daga ta zubawa Nannie,sai dukka kamanninta da sultane suka sake fita baro baro,take taji kamar da sultane take magana,don haka ta sulale a nutse tana jin zuciyarta kamar zata fashe.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Ko baki gyara batacciyar alaqar dake tsakanin mammina da morsa ba......dole ki karbi baqonki na yau da mutunci da karramawa......baqonki na yau daidai yake da mutuncin sultane......daidai yake da martabar mammina......daidai yake da kima ta ni fatimatou hammud!". Har tsakiyar kanta taji saukar maganganun Nannie.

"Waye wannan?" Ta tambayi kanta da wani irin hautsinannen yanayi. Waye wannan da a yau yake karbar kakkausar kashedi data jima bata ji irinsa ba kaf cikin rayuwarta a kansa?.

Duka sauran abinda Nannie ke fadi ma bata ji ba bare ta fahimta,ta miqe kawai a hankali tana takawa ta fita a sassan zuwa sassanta kai tsaye.

Tun a gate na biyu na sassanta ta shaida birra bata buqatar kowa kusa da inda take,tun daga nan bata baiwa kowa damar wanzuwa a gurin ba ballantana akai ga qofar da zata sadaka da kashi kashin faluka da dakunan hutawarta har yakai ga bedroom dinta da yake number na uku cikin dakunan baccinta.

Takan jima bata shiga dakin ba,saboda yawan zamanta a Niamey daya rinjayi adadin zamanta a nan agadez. Takai ta kawo har batasan adadi ba,tunaninta yana sake tsere da son kamo wani abu.

Daga yadda Nannie ke magana a kansa.......daga yadda Nannie ke maimaita mata batunsa tabbas akwai wani abu.....wani abu da zataso ta fuskanta komai qanqantarsa.

Abu guda ta sani.......a yanzu,a wannan lokacin bata shirya auren kowanne d'a namiji ba bare ya sanya rai zata rayu qasan dokokinsa da kuna juyawarsa akan al'amuranta cikin kowanne yanayi da yaso.

Shawara ta sauya,ta jawo wayar dake dakin wadda ke bata daman kiran kowanne sashe na sassan gidan nata dama sauran sassansu mammina.

Wadda take buqata ita ta fara daukan wayar wato birra.

"Ki qaraso ciki yanzun nan" Ta furta tana maida wayar ta ajiye,sannan ta miqe tana rage tazarar nisan da tayi da falukan nata.

"Tashi" Akhnan tace da birra kai tsaye a sanda birra din ke shirin rusuna mata. Duk da cewa ta miqe din amma ta kasa tsaiwa sosai,don tana ganin kamar zata hada tsahonta ne dana akhnan.

"Ki zabi mutum shida......inason su sanya min idanu cikin masarautar agadez da kewayenta,komai qanqantar labari daga baqon yau da zaizo gurina ina da buqatarsa,ina buqatar kowanne bayani daya shafeshi" Ta fadi ba tare da tako dubi birra ba.
Chapter 65 · 0% Book details