← Book details Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 97

Sashe 33

Luu Luu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba yadda zaa canzamin wannan b'eran?" Dariya taso kama muhammad dawud. Daga ganin idanun haisam da gaske yake fadi,ba tun yau ba ya sani,duk wani aiki da zai shiga ko zai jagoranta to ba shakka sai ya zabi mafiya nagarta wajen jarumta da qwarewa sannan yake aiwatar da aikin.

"Kasan dokar aikin mu haisam.......indai kasan wani abu a ciki ko akai......to ka shiga cikin aikin ko ka shirya ko baka shirya ba". Muhammad dawud ya fada yana danne dariyarsa ganin kallon da haisam ke jifan omari dashi. Idanun nasa ya dauke daga kan omari din,ya fara takawa zuwa qofar fita daga office din,yayi scanning card dinsa qofar ta bude masa,ya saka qafarsa daya a waje sannan yayi magana ba tare daya waiwayo ba.

"Kaja masa kunne.......ka sake karanta masa komai,bazan dauki sakaci ko ganganci ko wani tsoro ba.......mu ba mata bane......an haifemu don mu fita muyi farauta......an haifemu don mu zama garkuwa......bango majingina" Ya qarasa fada yana qarasa ficewa ya maida qofar.

Sanda yake saukowa daga escalator yayi mamakin hango abdii sosai. Tsaye yake a lobby din shi daya,cikin shigar qananun kaya. Hannayensa zube a aljihun wandonsa yana duba wayarsa.

"Abdi" Ya fada qasa qasa yana motsa labbansa idanunsa a kanshi. Baisan wanne irin qauna yaron yake masa ba......wannan qaunar ita ta sanya ya gutsira abdii kadan daga sirrinsa da ko nanay bata sani ba.

Boyayyen murmushi ya saki da bai bayyana akan fuskarsa ba. Ya sani zai wahala abdii ya iya zama sai ranar daya tsara zai dawo din,ya tabbatar tunda ya taho shima hankalinsa yayo addis ababa,yanzun kuma da zai tuhumeshi me yasa ya yanke hutunsa tun yana da ragowar lokaci zaice wani uzuri ne ya taso daga makaranta.

Kamar a jikinsa yaji haisam din yana wajen,sai ya daga idonsa a hankali ya sauke kan escalator din. Murmushi ya sakarwa haisam din yana maida wayarsa a aljihu,ya kuma matso a nutse bakin escalator din yana jiran qarasowarsa.

"Saurin na meye abdii?" Haisam din ya furta a nutse yana dauke idanunsa daga kan wata mace dake shigowa gurin wadda kafatanin hankalinta da idonta yake kansa.

Sumarshi ya shafa a hankali yana miqa hannu zai karba jakar wajen haisam din,wanda aiki ne na hadimansa da guards dinsa,wanda baisan me yasa wannan karon yake nesanta kanshi dasu ba.

"Uzurine daga makaranta obbo" Ya fada yana shafa qeyarsa. Dole a wannan karon wannan murmushin dake da gurin ajiya na musamman ya subucewa fuskar haisam,yadan lumshe kyawawan idanunsa yana kuma budesu duka akan abdii.

"Abdii......qaryafa tana cikin manyan zunubbai".

"Obbo mana......ba qarya nayi ba.......uzuri daga makaranta,kai din makaranta ne obbo.....akwai uzurin da yafi wani ya kasance dakai?.....hankalin mooti yaqi kwanciya kaman yadda nawa ya kasa kwanciya......shine kawai mukayi shawara dashi na biyoka......daga nan har AGADEZ " Idanunsa masu nauyin nan ya zubawa abdii,har sai da abdii din ya gaza jure kallon nasa,yaja baya kadan yana cewa

"Obbo.......your eyes obbo" Yadda yayi maganar da gaske kallon ya masa nauyi,sai haisam din ya janye idanun nasa ya soma takawa zuwa qofar da zata fiddashi daga gurin ba tare da yace da abdii komai ba. Qasan ransa yana juya yadda tafiya da abdii zata iya yiwuwa da kuma rashin yuwuwarta......duk da qiris ya rage abdii ya zama wani bangare na national intelligence agency a department dinsu.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

PAGE 28
__________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________

Driver dinsa da baisan sanda ya biyoshi ba shi ya bude masa qofar motar,ya shiga a nutse ya zauna yana sauke numfashi. Batun tafiyar da dukka maganganunsu shida muhammad dawud ke masa yawo,indai har zai gayawa mootii komai game da tafiyar......to bai kamata yabar nanay cikin duhu ba,yana jin ya kamata ko yaya ya haska mata,ya kuma buqaci addu'arta.

Abdii keta masa hira yana saurarensa kawai. Bai gaza ba don yafi kowa karantar yanayin haisam din a mabanbantan lokuta. Ya sake kallon agogonsa,yana jin omari yaja lokaci da yawa bai fito ba,mutum ne shi bai baza uzuri sosai......bayason kiran omarin,bai sani ba ko suna magana me muhimmanci da muhammad dawud ba......amma ya gaji,gida yakeso ya qarasa ya samu ya bawa kwanyarsa hutu.

Ya daga ido da zummar yin magana ya hango omari din,sai kawai ya gyara zamansa yana jiran isowarsa.

Ko cikin mota shuru ya zabi yayi,don yayi doguwar maganar da shuru yafi buqata din a yanzu. Yawan magana ko doguwar magana wani abune da suke sanyawa yanzu yanzu qirjinsa ya fara zafi,ballantana kuma akai ga hayaniya,sam basa shirginsa.

Sau tari idan suka hadu dukka dasu taarik,hira da rudu irin na abokai shikam nashi baya nisa. Ba yanzu ba,tun a makaranta sanda suke tsakanin shekaru goma sha biyar zuwa sama. Littafi kawai zai dauka yayi maka wannan dogon zango,ya jima yana karantashi ba tare daya gaji ba......hakanan qur'ani da zai jima zaune shi kadai a kebantaccen guri yana tilawa abinsa.

Susan ya yanayi da dabi'arsa take,wannan ya sanya sau tari idan sukaga yayi shuru irin haka ko ya kebe kansa basu fiya damunsa ba.

Ba jimawa suka isa kazanchis layout,unguwar dake cike da wata irin nutsuwa da kullum take qarawa haisam son zama a cikinta.

"Mu sauka muyi sallah kafin mu.....shi ya qarasa gida da motar" Haisam ya furta. Dukkansu sun aminta da hakan,don ba wanda ba'a gajiye yake a cikinsu ba.

A babban masallacin unguwar suka qarasa ciki bayan sunyi alwala,tuni har an daidaita sahu,saidai shigowarsa ya sanya limamin neman ja da baya don bawa haisam daman jan sallar. Hannu ya daga masa yana girgiza kai,don ba kasafai ya fiya son haka ba. Yanajin kamar an aza masa nauyi ne an kuma banbamtashi da sauran mutane.

Basu jima ba suka baro masallacin. Tare suke takowa su ukun,duk da abdii ya danyi gaba dasu dasu kadan bai jera kafada dasu ba.

"Haisam" Omari ya kirashi a hankali.

"Na'am" Ya amsa masa,don dama tun dazun ya fahimci akwai maganar dake bakin omari din,yanayinsa daya gani na rashin son hayaniya ya hanashi cewa dashi komai.

"Baka hango kowanne illa da hadarukan dake cikin aikinnan?......me zai hana ka haqura a aika wani?" Omari ya fadi da sigar dake nuna daga zuciyarsa maganar ta fito. Bai zabi ya amsawa omari da wuri ba,har sai bayan shudewar wasu sakanni.

Tsaiwar da dakatawar da haisam yayi da tafiya shi ya sanya omari shima tsaiwa. Manyan zagayayyun idanunsa ya zube akan fuskar omari.......muryarsa d alamun gajiya sosai,gajiyar da bata hana jarumtarsa bayyana cikin muryar tasa ba yace.

"Bana tunanin akwai wanda ya fini cancantar aikin nan........abu daya ka sani......ajani amintaccen mooti ne.......amma kasan cewa mooti ABUN FARAUTA NE?!" Da wani bahaguwar ma'ana maganar ta saukarwa omari a sanda baiyi zaton jinta ba,wannan ya sanyashi bude idanunsa sosai saman fuskar haisam yana kallonshi.

Koda omari baice bai gane ba......koda omari baice qarin bayani yake nema ba.....amma iya kallonsa kadai da yakeyi ya fahimtar dashi hakan.

"Eh.....ina nufin abinda na fada omari.....mooti abun farautarsu ne da suka gaza cimmasa........suna raye kosu waye suka aikata wannan aikin......jikina yana bani ba mission na mutum daya bane......ba kuma sashe daya bane yake farautar MOOTI.....kasan sau nawa a cikin shekaru goman nan na tare yunqurin kaiwa mooti hari ba tare dashi kansa ya sani ba?". Sake dukan omari maganar tayi......ta dakeshi da wani irin yanayi da har sai daya kamo hannun haisam.

"Mooti kuma......meye hadin mooti da wannan case din har na tsahon shekaru goma?"

"Abota da dangantakarsa da ajani" Haisam ya furta wani abu yana motsawa qasan zuciyarsa.......wani abun daya motsa bacin ran dake qasan ransa ya kuma tuna masa da yadda yayita daqile yunqurin isa ga mooti din ba tare da ya bari ya sani ba,don samar masa da cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankalin da zaiyi sarautarsa ya sauke haqqi da nauyin al'ummarsa.

"Mooti shine abun harinsu.......a shekaru gomar nan ba wani abu daya sauya........ta yaya zanyi bacci yadda nakeso?.....ta yaya zanyi rayuwa yadda nakeso bayan ni daya nasan da wannan yunqurin?......ka taba tunanin me yasa nake rasa sukuni duk qarshen sati idan banzo jimma ba?" Ya qarasa maganar yana zube idanunsa masu nauyi akan omari. A hankali omari ya girgiza kansa mamaki yana sake narkar dashi,da gaske kenan hasashen da yasha yi gaskiya ne.......har yanzu bai gama sanin haisam ba da gasken haka take.
Chapter 33 · 0% Book details