← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 87

Sashe 9

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tunda Baffa ya bani kudin nan bake binsa da kallo, baice min komai ba amma na fahimci baya miki magana tun last week, kuma na tambaye shi amma bai bani amsa ba, bana son inyi komai akan zargi Mimi, ki gaya min abinda nake tunani haka ne?"

"Jamal..." Ta fada tana kallonsa.

"Dan Allah." Yayi saurin katse ta.

"Ki gaya min gaskiya, ki san gyarawa zanyi, kin san ba zanyi abinda bai dace ba."

Wucewar wasu sakanni kafin ta gyaWa kanta a hankali tana cigaba da kallonsa.

"Akan zancen zuwa hutun su Munaya ne a Abuja, yace bai yarda ba kuma suna son zuwa, shine nayi masa maganar cewa ta kanaya suje din, amma sai bai fahimta ba, sai laifin ya dawo kaina, yace sun fara girma sun fara raina maganganunsa ni kuma ina biye musu."

Ya kalle ta tsawon waucewar wasu mintuna kafin ya zura hannunsa cikin gashin kansa.

"Kiyi hakuri Mimi, insha Allah duk irin wadannan abubuwwan sun kusa zuwa karshe, na sha gaya miki akwai sa hannun wani a irin wadannan abubuwan dake faruwa tsakaninki da Baffa amma nq kusa gyara komai a gidan nan da yardar Allah, rayuwarmu ba zata cigaba da tafiya a haka ba."

Sai ta girgiza kanta.

"Nima na sha gaya msaka cewa ka daina irin wannan tunanin Jamal, ka daina saka zargi a zuciyarka, wannan matsala ce dake faruwa a kowanne irin aure ba wai wani abu ba, duk sanda kayi naka zaka fahimta kaima. Amma babu ruwan kowa a wannan al'amarin, kana gani dai ko Kilishi da muke kishoyoyi bata da matsalar komai to waye kuma zai saka mu a gaba? Akan me?"

Ya zura hannunsa daya cikin gashin kansa.

"Matsalar kenan Mimi, ba kya bari zuciyarki ta bude abinda yake kasan zuciyar mutane, shi yasa ba kya yarda dani a kodayaushe, amma insha Allah kwanan nan zan nuna miki wani abu da zaki san ba zargi nake yi ba Mimi, so nake kawai in tabbatar in dai ina raye komai ya kusa zuwa karshe insha Allahu."

Haka ya fada a lokacin, amma ita kallo sa kawai take yi tana son gaya masa cewa a wannan lokacin ba wannan ne fatanta ba, ba wannan ne buri ta ba, burinta bai wuce cewa yayi kokarin jawoata Ma'aruf zuwa kusa da ita ba, tana fatan hakan daga yadda take ganin alakarsu na tafiya, fon tun a wancan lokacin maganganun ´ ´anuwanta dun fara zama a zuciyarta, musamman a lokacin da Ma'aruf din ya kammala karatun secondry dinsa, tana ganin ma'anar kowacce kalma da suka sha fada mata game da ala™arta da Wan nata.

Sai gashi kwata-kwata awannin da hakan ya faru basu karfin na kwana guda ba, yace in dai
Ina raye... Kamar wani abu a lokacin na gaya masa cewar zai iya rasa ran nasa da wuri.

Tana jin kukan su Shukra da sauran jama'ar gidan daga wajen falon, tana jin tashin kukan kowanne a cikinsu yayin da mazan dake wurin ke ™o™arin basu baki, don an hana kowa shigowa a wannan lokacin, Baffa yace babu wanda zai ga gawar a wannan yanayin sai an shirya shi tukunna, itama ta shigo ne don ita mahaifiyarsa ce, babu wanda zai iya kallon idonta yace ba zata ganshi ba.

Idanunta na kallon gawar da tayi kaca-kaca da jini, kirjinsa ya dagargaje, ance bishiyar da suka daka shi ta soke don a saitinsa take, kuma har a yanzu ma akwai wasu kananun itacenta da suka hade da jikinsa da aka kasa cire su, jini yana malalowa a hankali har yanzu daga jikin gawar yana jika kayanta a lokacin, don tana tsugunne a gabansa, sanye da wani tsadadden leshinta da tayi shirin zuwa biki dashi a ranar.

Tana jin yadda danshin jinin nan ke ji™a kayanta, yana gaya mata cewa jinin Jamal ne, Wanta guda na farko a duniya, Wan dake mutukar sonta fiye da komai a duniya, Wan da tun yana karaminsa zuciyarta ke cin buri akansa, wannan kyakkyawan Jamal Win da kowa ke yabawa, kyakkyawan Wan da take alfahari dashi a kowacce, a yanzu vabu wannan kyan, babu kamanninsa ma ko kadan, dogon hancinsa ne kawai ake iya ganewa a cikin kumburar da fuskarsa tayi ba. A cikin kunnenta muryarsa kawai take ji yana ce mata...

_Zafi nake jin Mimi, ko'ina a jikina ciwo yake yi..._

Haka yake ce mata duk lokacin da bashi da lafiya a makaranta idan suka yi waya.

"Limamin ya iso."

Taji wani a cikin mazan dake bayanta yana faWa, sannan taji muryar Baba Usman yana cewa.

"An kira waya yanzu, ance an shiga da Ma'aruf din tiyata, likitocin sun ce anyi sa'a babu internal bleeding."

Sannan taji wani a cikin mutanen na tambayar su waye a wajensa.

"Mami ta tafi tun dazu."

Amsar da ta fito daga bakin wani, itace a amsar da tun a wannan lokacin ta bawa Hajiya Maimuna wani tabbaci na cewar shikenan tayi biyu babu.... babu Jamal Win kuma babu Ma'aruf din! Don bata jin bayan addu'a tana da wani sauran fata a duniyar nan na dawowar Ma'aruf wajenta.

***

*Present Day.*

Tun da Munaya ta shigo tace da Hajiya Maimuna wai Ma'aruf ne ke zaune a falo yana jiranta hannayenta ke rawa wajen shiryawa, karfe goma sha Waya na safiya a lokacin sai kallon agogo take tana karawa.

A tarin shekarun da lissafinta ba zai iya ta tancewa ba, ta manta yaushe rabon da ta sanya idanunta a cikin na Ma'aruf din a wannan lokacin, iyakarta dashi bayan tsawon wasu kwanaki ne da zai shigo ya gaishe ta kawai, zuciyarta ta daWe da ha™ura dashi game da wasu abubuwa da ta san cewar hakan ne ya kamata, ta dade da Waga kasan ruhinta ta binne dukkan wasu al'amuransa, shi yasa har a yanzu dukkan maganganun ´anuwanta game da hakan basa damunta sosai.

Sai dai duk da dauriyarta, ta sani cewa bata isa ta canja cewar ita uwa ce ba, bata isa ta daure wannan kewar da zuciyarta ke ciki shekara da shekaru game dashi ba. Basu saba ba, Wawainiyarsa kaWan ta sani, abinda take gayawa kanta kenan a kullum wajen tausar kanta, amma ta sani cewar babu wani abu a duniyar nan da zai yi daidai da dawainiyar rainon cikinsa da kuma haihuwar sa da tayi, shi yasa har abada a duniya uwa Waya ce, kuma babu girman wani abu da ya isa ya canja matsayinta.

A zaune a falon kuwa ta same shi baysn ta fito, hannunsa rike da wani dan karamin kwano mai kyau, yayin da idonsa ke manne da Tvn dake nuna tashar CNN.

Ya juyo ya kalle ta daidai lokacin da ta karaso hannunta yana danna buttun Win tsayawa jikin keken tayar.

"Barka da safiya."

Muryarsa ta gaishe ta ba tare da wata inkiya ba kamar yadda yake yi kullum, kuma a wannan lokacin dai taji hakan bai dame ta ba kamar yadda take ji a baya, ganinsa kadai a wannan lokacin ma ya isa ya mamaye dukkan tarin abubuwan da take lissafawa a kansa.

"Barkanmu dai, kun tashi lafiya?"

Ta amsa farin cikin dake zuciyarta na nunawa akan fuskarta.

"Lafiya kalau, ya ™arfin jiki?"

"Alhamdulilhi mun gode Allah."

Har yanzu idanunsa na ™asa bai dago ya kalle ta ba, kuma tayi zaton iya abinda zaice kenan kamar yadda suka saba a kodayaushe, amma sai kawai taga ya dago ya kalle ta sannan yace.

"Kwanaki Baffa yace mun Abdurrahim ya kusa dawowa ko?"

Ba shiri ta daga kanta da murmushi.

"Eh, nan da sati biyu insha Allah."

"Ashe har ya tsayar da rana, the last time da muka yi magana yace mun bai saka rana ba tukunna."

Mamaki ya shiga cinye ta a yadda take zaune, amma sai ta daure tace

"Yanzu ya kammala komai ai, don ma baya son taro ne amma ni da nayi niyyar wasu suje masa convocation din."

Sai ya gyada kansa.

"Haka yace mun nima, har Ishaq ma ya tambaye shi amma sai yace masa wai ba wani abu za'ayi ba."

Ta sake yin murmushi.

"Rigimarsa tafi shi ai, nace masa ko kewar mu baya yi."

Shima murmushin yayi ba tare da ya sake magana ba, yana tausayin kannin nasa ya sani, duk sanda suke magana ta hanyar text idan ya tuna cewar ba zai taba iya kiransa ba yana jin wani iri a ransa. Wani iri kamar yadda yake ji a yanzu da yake zaune gaban mahaifiyar tasa yana hira da ita, hirar da ba zai iya tara shekarun da aka rufa kafin ta iya tuna lokaci na karshe da suka zauna irin haka ba.

Kai tsaye yaji wani Sangare na zuciyarsa ya shiga godewa Amina da tayi sanadin zuwan nasa, don yadda ta kalli idanunsa ta ro™e shi da Allah ya san ba zai taba iya kin ce mata A'a ba.

Kuma a wannan lokacin ba kallon Hajiya Maimunan yake yi ba amma sai jikinsa ya bashi cewa robar dake hannunsa take kallo, kuma yaji shigowar sako a cikin wayar dake aljihunsa, ya san Faruq ne, shi yake jiransa don haduwarsu da Yakubu (mutumin da zasu tura nemo musu Mr. Okafor.)

Don haka sai yayi saurin tasowa ya miko mata robar dake hannun nasa.

"Wai zogale ne na bayan gidan ta tsinko ta dafa shine tace in kawo miki Munaya tace mata kina so."

Yadda shiru ke ratsawa waje a lokaci guda ya kashe ™arar komai haka Hajiya Maimuna taji a cikin kanta lokacin da ta karbi robar, kalaman suka shiga cikin kanta amma suka tsaya cak! Ta riga ta fahimci wa yaje nufi da itan ba sai ya fassara ba, amma hakan wani abu ne da bata taba tunanin faruwarsa a cikin lissafinta ba.

Ta kalli robar ta sake kallonta, ba wani abu ne mai yawa ba, amma wannan lokacin tana jin kamar nauyin zogalen nan daje ciki yafi girman dukkan wata kadara da take shi, kwalla ta cika ramin idanunta a lokaci guda, don haka bata Wago ba sai kawai ta daga kanta a hankali.

"Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi Ma'aruf, Allah ya ™ara haWa kanku, Allah ya baku zaman lafiya, ya kade dukkan sharrin da zai shiga tsakaninku, Allah ya baku zuri'a dayyiba."
Chapter 9 · 0% Book details