← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 87

Sashe 42

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakinta ya furta sunan ba tare da ta san ma me ta fada ba, kuma kafin ya amsa sauran kalaman suka biyo baya, bi da bi, wani na tunkude wani akan lebbenta.

"I think we're pregnant....!"

( Ina tunanin muna da ciki...!)

****

*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
*Gidan Hajiya Salamatu.*

"Kar ki damu Hajiya, gobe-goben nan zan sako miki su a mota, an riga an haWa sun cika cif, laces guda talatin da biyu ne, atamfa arba'in, sai materials Win guda takwas Nylon da kuma cotton guda goma..."

A cikin wayar dake kare a kunnen Hajiya Salamatu take wannan bayanin, tana zaune ne a barandar gidanta, daga ™asan rumfar yayin da iskar yammar ke kadawa a kowanne Sangare na harabar gidan.

A gabanta akwai wani dan karamin tebur da ta ajiye jotter da kuma biron da take karanto adadin kayan da take lissafawa a ciki, bayan jotter akwai jug mai garai-garai yana Wauke da lemo kakar yalo tar da kuma kofinsa wanda aka zuba lemon a ciki.

Ta kai ™arshe a wayar tata, sannan ta sauke wayar, kuma kai tsaye hannunta ya lalubo nambar Hajiya Kilishi wadda taji shigowar nata kiran a lokacin da take waya.

"Ina tare da mutane na ne ranki ya daWe..."

Ta fada kai tsaye bayan Kilishin ta Wauki waya daga nata Sangaren.

"Na sani ai shi yasa ban takura ba... Saratu ta kira ni da safe take gaya min cewa zasu dawo kasar nan kunyi waya?"

Hajiya Salamatu ta gyaWa kanta tace.

"Mun yi tun jiya, nake cewa komai labari ne, yaushe take ta daga hankalinta akan ya™i tafiya da ita gashi har ya dauke ta da ´a´an nata kuma zasu zo hutu."

Hajiya Kilishi tayi murmushi mai kama da dariya kafin tace.

"Da ta biyo ta hanya ta ba, a baya ta tashi hankalinta a banza, amma da ta fahimce ni ta ja da baya ta zama macen kanta ba gashi yanzu komai ya dawo hannunta kishiyar tata ma ta kama gabanta ba."

"Wallahi kuwa..." cewar Hajiya Salamatun kafin ta canja zancenta da cewar.

"Kin samu kayan ne?"

Hajiya Salamatun ta tambaya tana kurbar lemon hannunta.

"Wai sai Jibi zasu iso, abinda nake ta tunani kenan Salamatu, karo na farko da zuciyata ta kasa kwanciya akan wani abu, haka kurum nake jin cewa kamar jibin nan ba zata karasa ba wani abu zai faru."

Hajiya Salamatu tayi dariya kafin tace.

"Ki kwantar da hankalinki Hajiya, kin san hausawa sun ce aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, gangarar kawai kika zo shi yasa kike jin haka, ban da abinki ma daga ni sai ke fa muka san wannan abin da kike shirin yiwa Awwalun nan, kuma ni dai kin san ko yanka ni akayi baza'a iya fitar da sirrinki daga cikina ba ko?"

Kilishi ta gyada kanta.

"Na sani Salamatu, kawai ban san me yasa ba bana gane komai ne a yanzu sai na fara gamawa da Awwalun nan, Wazu munyi waya da Maigaskiya yace min yana office abubuwwa sun yi masa yawa, bai ce min komai bayan hakan ba amma na fahimci kamar binciken nan suke yi kuma sun gano wani abu Salamatu, da ba Awwalu na dora akan harkar nan ba da na bari ko sau daya ne dun ganni da tuni inaga abubuwa sun canja kala daga yadda nake kallonsu."

Salamatun ta girgiza kanta itama.

"Ki daina wannan tunanin, ki fuskanci abinda ya rage kawai bayan Awwalun, zancen yarinyar nan tasa Hamida sai kuma mutuwar shi mai gidan naku da har yanzu baki tsara yadda zata kasance ba."

"Na tsara komai Salamatu, zan gaya miki da zarar mun hadu, a yanzu bayan wadannan biyun kuma ina so da Amina idan ta gama yi min aiki akan yarinyar in raba ta da mai gaskiya itama, a fuskokinsu kawai zaki gane kamar rayuwa na tafiyar musu daidai, ba zan iya basu wannan farin cikin ba Salamatu... Ba zan iya barin Ma'aruf da wani abu mai haske a rayuwarsa ba, so nake har ™arshen rayuwarsa ya dauwama yana tunanin ni kaWai ce haskensa."

Hajiya Salamatu ta taSe bakinta kaWan kafin tace.

"Ba zaki canja tunaninki akan yaron nan ba Kilishi, amma wannan Win ma daidai ne, ai bai Wara daga cikin aikin ki ba, sai dai tsaya... Wane tabbaci ma kike dashi cewa har i yanzu yarinyar nan bata Wauke da wata hamidar ko kuma Hamidu?"

Kilishi tayi murmushi mai fadi kafin tace.

"Na dade da bata magani Salamatu, kuma a yadda yarinyar nan ta yarda dani ba zata saba min alkawari ba, abinda zanyi musu ma idan ta gama yi min wannan aikin na Hamidan zai rufe musu ido ba zasu ga komai a rabuwar tasu ba daga iyayenta har ita din. Kuma yadda zan raba sun babu wuya, ni na san abinda zanyi, na san abinda zanyi yadda Mai gaskiya ba zai sake kallon yarinyar nan a duniya ba."

Hajiya Salamatu ta gyada kanta.

"Na fahimci har yanzu da saura a harkar nan Kilishi, shi yasa kika ce zuciyarki ta kasa kwanciya... Amma kar ki damu, tunda kin iya da tarin abubuwan da kika shallake a baya waWannan ma ba zasu yi miki wahala ba, ki cigaba da tsarinki kawai, ina garin nan har sai kaya na sun ™are, don haka kar kiji komai."

Da haka wayar tasu ta ™are.

Hajiya Salamatu ta Wauki jotter da kuma bironta sannan ta mi™e tare da wayarta ta shiga ciki tana barin jug Win lemon anan, kuma shigarta kenan bata ko yi minti biyar ba, wata ´ar aikinta mai suna Sadiya ta shigo, ta durkusa har kasa tace.

"Hajiya kinyi ba™o, yace wai mai karbar kaya ne shi yasa maigadi ma ya barshi ya shigo."

Ta Wan kalle ta tsawon wasu sakanni tana son tuna wadanda suka yi alkawari dasu a yau cewa za'a zo a karSi kaya, bata tuna Win ba don haka sai kawai tace.

"Je ki shigo dashi."

Ta tashi ta juya ta fita, idonta yabi ta da kallo har ta fita daga ™ofar falon nata da yake na biyu a jerin tsarin gidan.

Minti guda bayan haka Sadiya ta dawo, biye da ita Wani ne da bata ga fuskarsa a karo na farko ba kasancewar ya saka riga irin ta sanyi mai hula ya rufe kusan rabin fuskar tasa, don haka bata sallami Sadiya ba ta tsaya tana kallonsa, idonta akan kofin lemonta wanda ta baro a waje dake rike a hannunsa yanzu, kuma kafin tayi magana yasa hannu ya cire hular zuwa baya, a lokaci guda fuskar Awwalu ta baiyana a gabanta.

Yana murmushi ya kai kofin bakinsa ya kurSa, sai kawai ta Wagawa Sadiya hannu alamun ta sallame ta, Sadiyar ta juya ta tafi shi kuma ya karaso ya zauna a kujerar dake gefen tata.

"Me ya kawo ka wajena Awwalu?"

Ta tambaya fuskarta a hade tana kallonsa, da murmurshi a fuskarsa ya sake kurbar lemon sannan ya taso ya fuskance ta sosai yana rike kofin da duka hannayensa biyu.

"Ni ba mutumin banza bane Hajiya, na san ™awarki, na san Kilishi tun bata da komai a duniyar nan sai ku biyu ke da Wayar da bata magana Saratu... Yau sati guda kenan Kilishi bata kira ni ba, tun bayan da na karbo mata wannan hodar a Lagos, don haka dole na san akwai abinda yake faruwa kuma na san ba zan sami bayani a ko'ina ba sai a wajenki ko kuma wajen wannan Wayar yarinyar da ta shigo da ita cikin al'amarin.

Don haka zuwa nayi ki gaya min ta inda Kilishi ke shirin kashe ni..."

Hajiya Salamatu ta kalle shi tsawon sakanni, cike da mamakin yadda akayi yasha jinin jikinsa game da Hajiya Kilishin tunda ta gaya mata cewa bata bashi wata dama da zaiyi tunanin cewa tana shirin juya masa baya ba... Kuma ko mutumin da ta saka ya kusance shi mai suna Sadik bai bada damar da zai zarge shi ba har yanzu. Sai kawai ta haWiye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta.

"Ban san komai ba Awwalu, ka tashi ka fitar min daga gida."

Ta ™arasa tana nuna masa hanyar kofa, sai kawai ya saje wani murmushin yana kallonta, ya girgiza kansa sannan ya sake kai kofin lemon bakinsa, wannan karon ya shanye shi tas! Sannan ya Wago ya sake kallonta.

"Na gaya miki ni ba mutumin banza ne bane Hajiya, ina da abinda zaki miko min Hajiya Kilishi yanzu ba sai anje koina ba."

"Me kenan?"

Ta tambaya tana kallonsa cikin ido. Ya sake wani murmushin yana kallonta cikin ido shima kafin bakinsa ya sake motsi.

"Kina da labarin inda Wanki yake?"

Mamaki ya bayyana tar a fuskarta, mamaki irin wanda ke sauka a fuskar mutum lokaci guda, ba shiri bakinta ya furta.

"Wane Wan nawa?"

Awwalu yana sake wani murmushin da shi kadai ya san ma'anarsa kafin yace.

"Šan da kika haifa tare da mijinki na farko, wanda ya mutu a asibiti ranar da kika haife shi!"

***

_Ku gaya min me yake shirin faruwa ne?_

_Me Awwalu ke shirin haddasawa tsakanin aminan guda biyu?_

_Me ya faru a wancan lokacin?_

_Me Amma ke shiryawa game da tsarin Hamida?_

_Su Ma'aruf zasu sami Awwalu kuwa?_

_Ta yaya kuke tunanin faWowar Kilishi zata fara?_

_Gashi tana ta lisaafo wasu sababbin tsarikan...=ØÞ_

_And yes! BabyDoll think they are Pregnant!=ØÞ.... Ta yaya ake Soye ciki ne wai=ØÞ?_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:56 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©ýÿAYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*15*

*Ina mika ta'aziyyata ga al'ummar musulmi na rashin babban malamin da muka rasa a yau, Dr Ahmad Bamba BUK. Allah ya jimansa ya kyautata namu zuwa Ameen.*

~~~~

Awwalu ya cije lebbensa, kansa yana gyadawa... Gyadawar da shi kansa bai san yana yi ba, idanunsa sun canja, dun cika kuma sun yi fayau, suna tsaye akan fasashshen gilashin kofin dake gabansa, kofin da ya tarwatse tun daga lokacin da Hajiya Salamatu ta feWe masa biri har wutsiyarsa game da dukkanin shirin Kilishi akansa.
Chapter 42 · 0% Book details