← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 87

Sashe 62

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana faWin haka yayi wani guntun murmushi sannan yaronsa ya rufe kofar motar ya zagaya zuwa gaba ya shige, cikin abinda yake kasa da minti guda motar ta tashi... Suka bar wajen suna tayar da ™urar da ta bade fuskar Awwalu baki Waya.

Sai dai wannan ba shine abinda ya dame shi ba, ba shine tunaninsa ba... tunaninsa Waya ne, he's free at last! Don haka ta ina zai fara??

***

_Ta ina kuke tunanin kowa a wannan babin zai fara?_

_Ta ina Kilishi zata fara?_

_Ta ina Jawad zai fara?_

_Ta ina Hajiya Salamatu zata fara?_

_Sannan ta ina Awwalu zai fara?_=ØÞ

_Wai ina Rukayya ne??_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:58 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©ýÿAYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*21*

_Sin makes its own hell, and goodness its own heaven.-Mary Baker Eddy_

~~~~~~

˜arar tashin jirgin ta ragu a cikin kunnen Jawad, yana jin yadda tafiyar jirgin ke ™o™arin daidaita a sararin samaniya, yana jin kamar kafafunsa na bin gudun jirgin ne zuwa garin da suke dosa, yana jin yadda tasirin tazararsa da Kaduna ke yagewa a jikinshi, zaren na yin tsawon da bai san ta yaya zai kwatanta shi da wani sunan ba face cewar yana barin Zainab ne a baya, yana barinta a cikin halin da bai sani, halin da bai ko iya ganin fuskarta ba balle ya iya kintata halin da take ciki.

Sai kawai ya koma da baya ya rufe idanunsa, yayin da a hankali bi da bi abinda ya faru awannin da suka wuce tsakaninsa da Nura ya shiga dawowa cikin kansa.

*

"Karya yake..."

Abinda Nura ya fada kenan yana kallonsa a lokacin da yake tsaye a gabansa. Shi din da ya dawo ya sake nemansa lokaci kadan bayan rabuwarsu, don a tunaninsa tun bayan lokacin da suka sauke shi sun dade da barin garin, sai gashi cikin abinda yake kasa da awa guda kiransa ya sake shigowa wayarsa da tambayar yana ina? Kuma bai bata lokaci ba ya shaida masa inda taken duk da mamakin da ya kama shi, wajen da cikin abinda yake kasa da minti goma yazo ya same shi.

Tun kafin ya tsaya ya hango motar don haka ya taho ya iske shi a daidai jikinta bayan ya fito.

A wannan lokacin Nura zai rantse da Allah duk da ya dade da sanin halin mahaifinsa ba karamin mamaki ne ya sake lulluSe zuciyarsa ba lokacin da Jawad din ya shaida masa abinda ke faruwa.

Farko, yayi mamaki sosai da ya kasance yarinyar ta zama Zainab Win da ya sani cewar a kwanakin nanýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹ŒŽ‘’“”•–—˜™š›œžŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿ an rasa zaman lafiyar gidansu saboda ita, ya san ya kalle ta a lokacin da ya fara haduwa dasu amma baiyi mata kallon da zai gane wacece ita ba don a tunaninsa matarsa ce, matar aure ce, matar da babu dalilin da zai sa shi kare mata kallo, don duk buWewar idanunsa duk irin tarin zunuban da yatsunsa zasu lissafa ya aikata a rayuwarsa babu harkar mata a cikinsu, a kodayaushe a kowanne hali yana daraja mata, yana basu ™ima da kuma darajar da ya san Allah ya halitta su da ita, don haka mace ko wace iri ce ba saka ta a ransa.

Mamakinsa na biyu akan mahaifinsa ne, mamakin yadda kai tsaye ya haWa ™arya irin wannan don kawai ya kore alkhairin da ya san cewa ba zai shafe shi ba... Don halin da yake ciki bashi da alaka da zuwan Jawad ko rashinsa kwata-kwata, kawai yayi hakan ne don son zuciya da kuma ™o™arin kuntatawa yarinyar da ko maraicinta ba zai kalla ba don ya sassautawa rayuwarta.

Satin sa biyu da dawowa garin lokacin da mahaifiyarta ta rasu... Ya dawo ya tarar bata da lafiya kuma zai rantse kafin mutuwar tata akwai ranar da kunnensa yaji tana ro™on mahaifin nasa akan ya dawo mata da ´arta don tayi jinyarta, wanda sai a sannan shi ya tuna cewa ma tana da ´a guda daya da tsohon mijinta, kuma a lokacin ne ya fahimci inda yarinyar take don da kunnensa yaji mahaifin nasa na gaya mata cewa idan yarinyar ta dawo bai san kuma da wanne kudi za'a dinga samu ana siyo mata magunguna ba don shi bashi da shi.

Rigimar da ake ciki kuma a gidan ta fara ne tun bayan rasuwar mahaifiyar tata inda yanuwanta da suka zo suka nemi yarinyar kai tsaye kuwa sauran matan kuma suka shaida musu cewa ai mahaifin nasa ya kai ta can birni aikatau.

Saboda haka tun kafin a kai ga share makoki aka fara sa'in sa a tsakaninsu, suka tsaya akan cewar sai ya dawo musu da yarinyar, da kyar aka sulhunta wajen bashi wasu kwanaki da cewar ya dawo da ita, kuma basu ko tsaya an kai kwanaki bakwai ba ana share makoki da kwana uku gabakidayansu suka koma kauyensu.

Sai dai shi tun daga kan haka bai kara bi ta kan zancen ba yaji inda aka tsaya ya shiga harkokinsa, don haka a yanzu da ya riski wannan labarin daga bakin Jawad, har da kuma sunansa da zancen cewar shi zai auri yarinyar dashi ko kammaninta ba zai iya zanawa a zuciyarsa ba, kafafunsa sunyi mutuwar tsaye ne na wucin gadi yayin da zuciyarsa ke maimaita kowanne batu Waya bayan Waya kafin ya girgiza kansa a hankali yana kallon Jawad Win.

"˜arya yake, wannan zancen ba haka yake ba, a gaskiya babu wani alkawarin aure tsakani na da yarinyar nan, ya faWa maka hakan ne don ka rabu da ita kawai..."

Wadannan maganganun su Nura ya faWa masa bayan ya ™are masa dukkan wani bayani, kuna sune magan ganun da a lokaci guda suka ciccibo shi daga wata duniyar suka dawo dashi wata, yaji kamar ya saka hannu ne ya sauke masa wani tarin nauyi da yake yawo dashi a kirjinsa. Yana kallonsa lokacin da ya cigaba da fayyace masa komai...

"Ka gane... Da shi da mahaifinta abokan juna ne, to bayan rasuwar mahaifinta nata ne sai ya auri mahaifiyarta, a lokacin kamar daga ita har yanuwanta sunyi tunanin zata samu sauki ne a wajensa ko kuma sun ga cewa sun sanshi ne sai kawai suka amince, to ni ban san me yake faruwa ba bsyan na tafi amma dai na fahimci bata jin dadin auren, kuma da ya tashi tura yarinyar aikatau ya hana ta gayawa yanuwanta kamar dole yayi musu ne ya tura ta irin yadda yake yiwa sauran ´a´an nasa.

To sai bayan rasuwarta ne a yanzu sannan suka dage akan cewar ya dawo musu da ita, sai kuma gashi yanzu kun zo, to ina tabbatar maka da cewar yanzu can wajen yan uwan mahaifiyar tata zai maida ita, kai kuma ya kore ka ne don ya san da zarar ya mayar da ita ba zai amfana da kai ba shi yasa yayi amfana da wani abu naka ba, shi yasa yayi amfani da sunana ya gaya maka wannan labarin amma ina tabbatar maka duk abinda ya faWa babu gaskiya a ciki, don ni yanzu ma babu batun aure a gabana."

Tun daga farkon bayanin har zuwa karshe ya saurare shi ne da dukkan nutsuwarsa, da dukkan hankalinsa da kuma tunaninsa wajen tantance gaskiya ko kuma akasin kalaman nasa, sai dai duk iya nisan da hasashensa ke kaiwa, dawowa yake yi wajen gaskata shi da kuma yarda dashi, idan aka cire muryarsa a idanunsa kaWai yana ganin tabbacin kowacce kalma da yake furtawa.

Yana jin yadda zuciyarsa da kuma kowanne abu mai hankali a jikinsa ke yarda dashi, don haka a lokacin da ya kai karshe, bai Sata lokaci ba ya shaida masa abinda yake son yayi masa bayan Nuran ya shaida masa cewa mutumin ba zai Wauki lokaci ba wajen sa wa a maida ita wajen yanuwan nata tunda har an riga an ™aiyade masa wasu kwanaki da sharaWin ya dawo da ita.

"So nake kayi kokarin da zai mayar da ita wajen yanuwan nata da wuri, sannan ka bi su har can ka gano ™auyen sai ka kira ni ka gaya min, zan biya ka ko nawa ne Nura..."

Yana tuna alkawarin da Nuran yayi masa, tarin alkawarin cewa komai zai tafi daidai kuma bai san me yasa ba haka kurum ya yarda dashi, ya Webo adadin wasu kudade daga cikin wanda ya fito dasu a cikin dashboard Winsa ya bashi da cewar ya kula da ita har zuwa lokacin da komai zai daidaita, kuma bai sake bukatar komai ba ya juya motarsa ya bar ™auyen, ya riga ya fahimci cewa gaggawa shine mataki na farko da zai bata hanyar mafitarsa.

Bashi da wani ™arfi ko kuma wani iko akan mutumin nan ya sani, babu yadda zai iya dashi a yanzu tunda har Zainab ta riga ta shiga hannunsa, don haka zai bi shawarar Nuran, zaiyi hakuri har zuwa lokacin da zata bar cikin ikon nasa, wanda yake saka ran saka ran hakan da wuri kamar yadda ya gaya masa, shi yasa bai ko damu ba a yanzu kafin tasowarsa da Nuran ya sake kiransa a waya ya shaida masa cewar mahaifin nasa ya ajiye Zainab ne a can cikin dakin uwargidansa inda ba zai iya zuwa ba don haka ba zai iya hada shi da ita a waya ba kamar yadda suka yi kafin rabuwarsu.

Wani abu ya wuce ta makogwaronsa a hankali yayin daya tuna babban al'amari na biyu dake shirin faruwa da rayuwarsa, bai san takaimaimai me zai faru ba, bai san na abinda zai je ya tarar a garin Kanon da yake nufa a yanzu ba, abinda ya sani kawai shine, tun kafin haduwarsa da Nura, bayan ya baro kofar gidan mutumin nan, kira ya shigo wayarsa da wannan lambar da aka bashi,lambar da yake saka ran ko yaya ne zata bashi hanya ta kuma saukaka masa wahalar tafiya neman abinda ya fito dashi har hakan ya shafi rayuwar Zainab.
Chapter 62 · 0% Book details