← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 87

Sashe 49

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matar nan da kanta ta gaya mata cewa lokacin sallah yayi, ta buWe mata banWakin cikin office Win ta shiga tayi alwala sannan bayan ta fito ta shimfida Wankwalinta akan carpet din wajen tayi sallah, haka ta zauna idanunta na cigaba da zarewa har sanda ya dawo, kuma a lokacin kallonsa kawai tayi taji shakuwar Wazu ta dawo, haka ta dinga yinta tana kokarin boyewa har suka koma motar kuma ya sake miko mata wani robar ruwan ba tare da yace komai ba, wani abu da duk rikicewarta sai da ya saka ta murmushi a lokacin.

Sun dawo gidan jikinta na rawa kamar yadda zuciyarta ke yi na tarin abinda ta san zata tarar, abinda ke jiranta wanda kwakwalarta ta kasa hasaso mata shi, amma bai ko bari tayi hanyar wajensu ba yace ta biyo shi bangarensa.

Kafafunta sai da suka tsaya cak jin hakan yayin da wani shiru ya ratsa ta tana jin yadda komai ya Wauke a cikin kanta amma bayan yayi gaba ya sake juyowa ya kalle ta da wadannan idanun nasa sai kawai ta kasa cewa komai ta biyo bayan nasa suka shigo har bangarensa, ya buWe mata kofar wannan dakin ya bata ledar kayan dake hannunta a yanzu yace ta shiga ta shirya.

Ta shirya. Shiryawar da bata san ma'anarta ba har yanzu, kallon Wakin kawai take yi kamar a cikinsa zata samo amsoshin da take nema.

Ta tsugunna a hankali har ™asa, ta buWe ledar hannunta ta zaro kayan ciki, wata farar riga ce mai tsawo da kuma laushi, akwai wani dogon wando kakar adon jikinta pink, sannan da hijabi fari tas wanda ta san zai kai mata ne har ™asa, mamakin inda ya samo kayan ya kamata, Allah ya sani bata san me yake nufi ba, bata gane komai ba har yanzu, so take kawai ya barta ta fita ta samu Hajiya Mardiyya ta gaya mata duk abinda ya faru ta kuma ro™e ta gafara, don ™wakwalarta na shaida mata cewa itace gatanta ba Jawad da al'amarinsa ba.

Kusan minti talatin tana zaune a kasan carpet Win Wakin ta jingina bayanta da jikin gadon yayin da kwakwalwarta ke ta faman lissafin wucewar lokaci tana jira yazo ya sallame ta tafi, kuma saboda gajiya da kuma zazzaSin da bai gama barinta ba har a lokacin, sai ta fara gyangyadi zaune a wajen har zuwa sanda aka kwaknkwasa kofar dakin, sau biyu kawai kafin kofar ta buWe.

Idonta ya sauka akansa tana ™o™arin wartsakewa, yana tsaye sanye da wata jallabiya ba™a, hasken fatarsa ya ™ara fitowa sosai alamun wanka yayi, yayi shirin da ita bata yi ba.

Jawad ya tako har ciki yana kallonta, da alama inda ta tsaya bayan ya barta a dakin a wajen ma ta zauna, Babu alamun ta matsa ko'ina, me yasa take so ne ta kara masa matsala bayan tarin abubuwan da yake fuskanta?

Shi kaWai ya san yadda ya daurewa kansa yayi aiki a office yau, zai rantse da Allah bai taSa ganin tsoro a idanun kowacce mace a duniyar nan ba kamar yadda ya gani a nata lokacin da ya tambaye ta idan zata aure shi, shi yasa ko da ya barta a Office din Aunty Mary, sau biyu yana kiranta yaji idan tana nan bata gudu ba, wannan shakuwar kaWai da ta dinga yi tayi yawo a cikin kansa ta yadda da ™yar ya goge ta yayi aikin dake gabansa.

Da gaske yake, da gaske yana ganin zai iya aurenta shi yasa har ya tambaya, don bai taba jin wani abu da ba zai taSa kasancewa ba sai a lokaci da Mamah ta gaya masa cewar wai aure iyayenta zasu yi mata, ya sani bashi da iko akanta fiye dasu ko ma wani a duniyar nan, amma a lokaci guda yaji cewar babu mahalukin da ya isa yasa hakan ta kasance, babu wanda zai bari yayi nasarar dauke ta daga gabansa, shi yasa a lokaci gudan ya yanke shawarar tambayarta idan har zata aure shi.

Don a wannan lokacin yana ji kamar idan ta amsa shikenan komai ya tabbata, shikenan ta zama tasa sun kaucewa dukkan wasu abubuwa.

Burinsa kawai ya cigaba da wayar kowacce safiya yana ganinta a gefensa ko da ba zai iya taSa ko yatsanta ba, ya riga ya fahimci a yanzu rauninta yake so, shine babban abinda ke jan hankalinsa akanta, wannan rauni da kuma rikicewarta da suke banbanta masa ita da Rukayya, Rukayya mai ji da kanta da kuma ta™amar tsayawa da kafayrta a kodayaushe, komai nata yayi hannun riga da Zainab, shi yasa tun a farko zuciyarsa ta fara tsayawa akanta don yana neman duk wani abu ne da zai sa ya manta da Rukayya a lokacin.

Da lokaci ya cigaba da tafiya kuma sai yake jin zuciyarsa ta saba da wannan banbancin sabon da baya jin a karo na biyu kuma zai bari ya sake rasa wani abu irin haka a rayuwarsa.

Tun kafin ya karasa shigowa Wakin ta mi™e hannayenta na ™o™arin fara rawa ri™e da rigar da ta Wauko a cikin ledar, ya cije lebbensa kaWan yana daurewa abinda ke ™o™arin tasowa daga zuciyarsa.

"Me yasa baki shirya ba?"

Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, ta girgiza kanta da sauri kafin tace.

"Ba komai, so nake in koma Wakinmu dama sai in shirya acan."

"You are not going back to that place..."

Idanunta suka tsaya akansa da kallon rashin gane abinda ya faWa duk kuwa da yadda take a tsorace, sai ya Wan kalli gefe alamun mantawa da hakan sannan ya sake juyowa.

"Anan zaki zauna, ba zaki koma can ba,idan akwai abinda kike bukata a cikin kayanki sai ki saka a dauko miki.."

Ai tun kafin ya ™arasa kwalla ta cika idanunta ta shiga girgirza kanta da sauri.

"Dan Allah kayi hakuri ka barni in tafi, wallahi Hajiya faWa zata yi min, yau ma tace za'a mai da ni gida kuma..."

"Babu inda zaki, idan kin warke zan kai ki gidan ki gansu sai mu dawo."

Ya fada yana sawa ta tsaya cak tana kallonsa, don hatta kwallar data taru a idanunta bata zubo ba.

"Ba dawowa zanyi ba idan na..."

"Dawowa zaki yi, 'Coz babu inda zaki je ki zauna a duniyar nan da ya wuce nan."

Ya faWi hakan kamar cikin tursasawa don har yanzu a tsaye take cak tana kallonsa, sai kawai ya shafo kansa da duka hannayesa biyu shima yana kallonta, yayi kokarin saita kansa sannan muryarsa ta saje fitowa.

"Babu abinda zanyi miki Zainab, wallahi babu abinda zanyi miki, baki ga har hijabi na siyo miki ba? I just want to feel you close to me... So nake kawai in dinga jinki a kusa dani. Shi yasa na tambayeki idan zaki aure ni saboda zan je har wajen iyayenki ne in nemi aurenki, babu ruwana idan ma akwai wanda suka tsara zasu baki Zainab, ko shari'a zan iya yi da kowa idan akace za'a hana ni aurenki..."

Ya faWa yana kallon yadda take kallonsa har a lokacin, a tsaye kyam amma kuma idanunta na haskawa da dukkan wata ma'anar tsoro na duniya kamar ma bata fahimce shi va, ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yace.

"Ko ke baki da zaSi yanzu Zainab, zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni."

Yana faWin haka ya juya yayi hanyar kofar dakin, sai dai taku huWu kawai ya tsayar da kafafunsa kafin ya ™arasa, ya juyo ya sake kallonta, tana tsaye yadda take har yanzu kamar tana jira ne wani ya taSa ta ta faWi, sai ya juyo ya dawo da saurihar gabanta, kuma bai jira komai ba ya janye hijabin kanta zuwa ™asa, gashin kanta da akayi wa wasu manyan kitso mai suna 'Doka' guda uku suka baiyana da jelarsu ´ar gajeriya a baya.

Sai dai shi ba ta su yake ba ma, hannyensa yasa duka biyu a wuyanta, yatsunsa dukkansu suka zagaye dan siririn wuyan nata har zuwa baya, dumin jikinta ya ratsa zuwa tasa fatar a lokaci guda da ta rufe idanunta gabaWaya, wannan kwallar da ta taru tana samun damar zubowa. 

Dukkaninsu suka sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya a tare yayin da Jawad ke kallon fuskarta yana ji kamar ya ™arasa da tasa ya haWe goshinsu waje daya, amma ya daurewa kansa ya haWiye wani abu a kirjinsa sannan muryarsa ta fito, a hankali cikin sautin da baiyi kama da wanda ya gama magana dashi yanzu ba.

"Maganin ki yana wajen dining, ki ci abinci ki sha, zan je wajen Maamah yanzu zan dawo, kinji?"

Kuma ga mamakinsa sai kawai ta Waga kanta sau Waya bata ™ara ba kuma har yanzu idanunta a rufe suke, ya cigaba da kallon fuskarta na tsawon sakanni idonsa na sauka akan siraran leSSenta yana jin yadda kwakwalar sa ke kokarin saita kansa daga abinda yake tunani kafin ya zare yatsunsa daga wuyanta a hankali.

Kuma bai ™ara cewa komai ba ya juya ya nufi hanyar kofa fitar, zuciyarsa na goge hoton ta da na mahaifiyarsa a cikin idonsa, Hajiya Mardiyya... missed call dinta ne a wayarsa kusan goma sha biyar, bayan wayar da suka yi sau hudu yana gaya mata inda suke da kuma sanda zasu dawo, yanzu ma ya tabbata bata ji shigowar motarsa bane da tuni ya ganta tazo.

"Jawad dan ub*nka a matsayin me ka dauki yarinyar nan ka kaita har wajen aikin ka?"

Haka take gaya masa lokacin da yace mata suna office tare.

Bata taba zaginsa ba, zai rantse bai ma taSa jin kalmar zagi a bakinta ba, sunansa kadai akan shafe watanni bata furta ba, a kullum kuma a gaban kowa shi baban ta ne, amma yau da girman sunan da take ji da komai ta haWa ta zage gabadaya.

Ya hadiye wani abu a ma™ogwaronsa lokacin da ya fita zuwa  waje gabadaya, haka kawai yake jin kamar ko ita bata isa ta shiga tsakaninsa da yarinyar nan ba.

Yana isa Sangaren nata kannenta ya fara tararwa tare da wasu cousins dinsu sun zo gidan, sun haWu akan wani katon tray da suka dafa wata tarin indomie da kifi a ciki, kowacce ta tattare kayanta sun baje suna ci ga wasu manyan-manyan jugs na zoSo a gabansu.
Chapter 49 · 0% Book details