← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 87

Sashe 10

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami tasha yi masa addu'a, kala-kala ma, har da wadanda idan ta fada zai kara kallontasau biyu kafin ya amsa, amma Allah ya sani ya dade baiji addu'ar da ta shiga har cikin zuciyarsa ta tabo wani abu da bai san da zamansa ba irin wannan. Kalaman Mami daban ne da irin wadannan, yawanci addu'arta tana tsayawa akansa ne kadai babu wani a gefe da ya shafe shi, don haka tmya sani tun bayan lokacin daurin aure sa da Baffa da kuma Baba Usman suka yi musu makamanciyar wannan addu'ar, zai lissafa wannan a karo na biyu da yaji irin wannan addu'ar daga bakin wani.

Makogwaronsa ya bushe a lokaci guda, amma yayi kokarin hadiyr wani abu a hankali kafin ya amsa sannan ya tsugunnna yana yi mata sallama, bai kara iya kallonta ba itama kuma baya jin ta sake kallon nasa, don wata™ila suna raba abu iri Waya ne a zuciyarsu daga shi har itan.

Kuma karo na farko a wannan ranar bayan ya shiga wajen Hajiya Kilishi yaji haka kurum baya son dadewa don ransa bai gana daidaita ba har a lokacin, yaji hirar da take yi masa ba fahimta yake yi sosai ba, don haka yayi mata sallama ya fito, sai dai kafin ya bar cikin dakinsai da yayi mata wata tambaya dake yawo a cikin kansa tun bayan lokacin sa Amina ta bashi robar zogalen nan.

"Mami kina son zogale kuwa?"

Ta kalle shi kamar tana son gano wani abun kafin tayi murmushi tace.

"Haba ka manta ne Mai gaskiya, amma bana son zogale tun asali."

Sai ya gyaWa kansa kawai sannan ya ™ara yi mata sallama.

_"Dan Allah zaka mi™awa Hajiya wannan? Zogale ne na bayan gidan nan tsinko na dafa, Munaya tace min Hajiya tana so, amma Mami ita bai dame ta ba."_

Haka ta gaya masa lokacin da ta tsaya a gabansa rike da robar tana ta juya ta a hannunta. Wani abu ne ya faru smdashi bai gama gabe masa ba har yanzu, ya san dai kawai ba laifi suka yiwa Mamin ba amma kuma duk da haka yana jin wani iri.

Ya zaro wayarsa ya duba bayan ya shiga mota, sakon da ya shigo dazu ba daga Faruk bane, daga mutane kamfanin RTL ne da suka yi dasu akan cewar gobe zasu je shi da wasu daga cikin board trustees Winsu su karbo kudin da suka siya dilolin kaya a hannunsu, haka kurum wanna karon ya yanke shawar cewa baza su karbi kudi ta account ba gwara su karbi cash kawai, tunda an cuce su wancan karon kuma har yanzu basu gama da gano matsalar ba.

Sakon yana bayani ne kan wajen da zasu hadun da kuma lokaci da sauran abubuwa, ya kashe wayar ya tada motar daidai lokacin da kiran Faruk ke shigowa, ya san ya riga shi isa wajen kenan kuma yanzu zai dame shi, don haka ya danna motar ya nufi hanyar titi daidai lokacin da idonsa ya kai kan robar zobo mai sanyin da Amina ta ajiye masa daga kasan dashboard din motar wajen da akayi musamman don ajiye roba dama.

Babu shiri wani murmushi ya subuce a bakinsa, yana da plan dama tarin tsaruka na ydda zai saita rayuwarsa tare da yarinyar nan, don tabbas ya gama yarda cewa ita din alkhairi ce a rayuwarsa, kuma mafi dadin abin shine ya same ta ne a lokacin da ba nema yake ba.

Wani abu da alokacin bai sani ba shine kwance a cikin zobon nan, sinadirin kwayoyin maganin Hajiya Kilishi ne ke yawo tun daga sama har kasa.

****

*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*

A cikin ™aton falon, baka jin komai sai ™arar A.cn dake hurawa ta kowanne bangare na falon, akwai manya-manyan royal chairs set uku da aka rarraba falon zuwa waje uku dasu. Jawad yana zaune daga kujerun gefe masu kalar ruwan madara, gajeran wando ne a jikinsa kuma wata t-shirt kalar ruwan kasa, a gabansa wani tebur ne da aka cima da kayan abincin safiya, hannunsa na rike da kofin mug yana kuSar shayin ciki yayin da mahaifiyarsa dake gefe Hajiya Mardiyya ke kallonsa tana sake maimaita maganganun da ba jinsu yake yi ba.

"Yanzu Babana ko don wadannan makiran matan mahaifin naka ba zaka saurare ni ko sau daya a rayuwarka ba? Kana ganin irin banbancin da ake nuna mana a gidan nan, kuma da nayi magana sai kace dani ba zaka yi ba babu kyau, bayan shi kansa mahaifin naku ai ya san abinda su Suraj din ke yi, kawai bai damu bane kuma yana sane yake barinsu. Kowa na diban kason sa amma kai so kake mu mu tashi a tutar babu? Ba don ma Perm Sec. ya shiga zancen mahaifin naku ba kai ka sani da yanzu bama kan wannan kujerar.

Wallahi idan na shiga lissafo maka kadarorin da matan nan suka tara yanzu zaka rike baki Jawad, amma ni gida uku fa kawai nake dashi har yanzu, ba don nayi fafutuka ta ma ba da bana jin ina da ko daya ai, kai kuwa banda motarka bana jin ka tara wani abu, karfi da yaji ka maida mu talakawa alhali muna iyo a cikin kudi Jawad?"

Ya lumshe idanunsa a hankali lokacin da ta kai karshe sannan ya juyo ya kalle ta.

"Mamah amsata ba zata canja ba kema kin sani,abinda nake gaya miki kullum shi zan kara gaya miki a yanzu, ba zan saci kudin mahaifina ba ba zan dauki abinda ba nawa ba, shi yasa nake aiki kin sani, su sauran matan nasa da yayansu ke zuwa su debo musu ai basu suka saka su a gaba suka roke su ba, kowa ganin damarsa ce tasa shi yin hakan, don haka me yasa ni zaki takura min, ba ga su Khairat nan ba? ( Kannensa mata biyu) Ki koya musu wata hanyar da zasu samo miki mana, ai ba maza ne kadai suka iya samowa ba."

Ya ajiye kofin hannunsa sannan ya mike tsaye, sannan yace

"Zanyi bako anjima, Dan Allah Mamah ki sa ayi mana abinci, wadannan duk basu yi min ba."

Ya fada yana nufin tarin cimar dake kan teburin daya tsallake, kuma bai jira abinda zata ce ba yayi gaba, ya zaro wayarsa ya kira Haron da suka yi akan lallai ya shigo Abujan don ta nan ne zasu hau jirgi zuwa Kano, ya gaya masa shi ba zai yi tafiyar mota ba.

Kuma awa guda bayan hakan sai gashi ya iso, suka zauna daga falon kasa na Sangarensu yayin da Haron ke ta mita akan tason shi da yayi babu shiri.

"Kaifa kake bukatar abin nan J, amma ni ka takurawa na taho rana tsaka, ina ga dole mu maida harkar nan ma taciniki don na fahimci ni zan sha wuya a banza."

"Ko nawa ne ka san zan biya ka, I never regret anything indai akan Rukayya ne ka sani."

Haron ya kalle shi lokacin da ya tsiyaya wani lemo mai sanyi a daya daga cikin tambulan Win da aka kawo musu sannan yace.

"Shi yasa ni kuma nake iya kokarina don inga na ciro ka daga wannan masifar, Haba ka kalli fa inda kake rayuwa, ni ban ma san kun canja wannan gidan ba, amma ka kallafa ranka akan wannan shashashar yarinyar, in the first place ni ban san ma me yasa zaka neme ta ba idan har ka san aurenta zaka yi."

Jawad ya gyada kansa alamun ya fahimta yana kallonsa sannan yace.

"Ina ga duk mun wuce wannan stage din Haro, mun karaso wajen da kace zaka taimake ni, ni kuma nake jiran inji ta hanyar da zaka taimake ni din."

Cike da takaici Haron yana kallonsa kafin ya buWe briefcase din da yazo da ita a gefensa sannan ya zaro wasu hotuna guda uku ya miko masa, ba tare da bata lokaci ba kuwa Hawad yasa hannu ya karba.

Hotunan mutum daya ne a mabanbantan llokuta har guda uku, na farko kamar ranar daurin aure ne, don a cikin jama'a yake sanye kuma da kaya masu babbar riga, na biyu kamar hoton wajen aiki ne, yana sanye da suit da kuma sumar gashinsa wadda aka gyara cikin wani style mai kyau, sai na karshe a bakin titi ne yana waya, hoton yayi kama da cewar a boye aka dauke shi sosai.

Kuma ba sai Haron ya sake yi masa bayani ba, ya riga ya fahimci waye tun da wuri, don idan zai iya tunawa ma ya tabacganinsa sau daya a wani taron harkar kasuwanci da ya halarta shekara guda baya, idonsa ya manne akan fuskar sa yana son ya gano banbancin dake tsakaninsa dashi, wannan banbancin da yasa Rukayya ta juya masa baya, banbancin da yasa ta rufe idanunta akan tarin kyautatawar da yayi wa rayuwarta ta kasa ganin kokarinsa, ko ma rabewar da zuciyarsa ke yi a lokacin da take gaya masa cewa bata dauke shi komai ba face abin wasa kawai, abin wasanta!

"Na gama samun duk wani background information akan gayen, ashe har aure ma ya sake yi..."

"What?"

A lokaci guda ya katse Haron da ke kokarin fara bayaninsa. Fuskarsa na kallonsa da tsananin mamakin da ya kasa tantance daga ina yake fitowa yana shiga jikinsa.

"Yes, ya sake aure ´an kwanakin bayan nan, amma naji ance kamar bashi matar kawai akayi don tare akayi auren dana sauran yanuwansa."

Sai kawai ya gyada kansa a hankali ba tare da ya san me zai ce ba, hakan yasa Haron ya cigaba da maganarsa.

"Ka san ni bana sanya a al'amarina, so na samu labari ance min zai hadu da wasu mutane gobe, na samu details Win da komai daga bangarensu, so kawai zamu yi masa aiki ne a lokacin."

Jawad ya dago ya kalle shi."

"Aiki? Wane irin aiki?"

"Plan dina shine mu kama shi for now, kar ka tambaye ni me zai faru bayan nan, mu fara gama wannan din tukunna."

Jawad ya kalle shi tsawo sakanni biyu.

"Ba zan tambaye ka ba, amma ka sani cewa I wont sign for any shit, idan har kashe shi ne plan dinka..."
Chapter 10 · 0% Book details