← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 87

Sashe 59

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciyarta ta biya sunan sau biyu kafin wata murya a cikin kanta ta ™wallara kara, Ma'aruf? Me ya kawo Ma'aruf inda take? Me yazo yi a wajenta a wannan lokacin? Tsaya wane lokaci ne ma? Sannan a ina take tukunna? Tayi yunkurin bude idanunta amma kai tsaye sai wata zuciyar ta hane ta da hakan kai tsaye don haka ta fasa a daidai lokacin da muryar wata mace ke cewa.

"Gashin idonta yana motsi, da alama yanzu zata farka..."

"Tun Wazu abinda kike fada kenan, just go and call the Doctor."

Taji Ma'aruf ya sake fada yanayin muryarsa kamar a hasale.

"YallaSai na san aikina fa, idan da bukatar kiran likitan ai..."

"Ni zaki gayawa kin san aikin ki? Kin san aikin ki tun 8 kike zirga-zirga anan ta tashi ne?"

"B, Calm down ta san me take yi mana..."

Muryar Ishaq tayi saurin katse shi.

"Wannan tabe-taben banzan ne ta san abinda take yi Ishaq?"

Ya sake faWa muryarsa na cigaba da Wagawa cikin fushin dake fitowa karara, kuna matar bata yi shiru ba ta sake cewa.

"Amma dai ka san mu bamu isa mu tashe ta ba idan har..."

"I don't f*cking care! Idan har me?all I know is mun kawo ta nan ne don ta sami lafiya."

˜arar sakin wani abu ta cika iskar dakin kafin muryar matar ta sake cewa.

"Then ga ka nan gata ai, sai ka bata lafiyar."

Da haka taji matar ta juya karar takunta na yin nisa daga inda Kilishi take a kwance yayin da maganganun su Ishaq Win ke ™ara shiga kunnenta, sai dai ba su Hajiya Kilishi ke saurare a wannan lokacin ba, tunaninta yayi baya ne yana tarewa ga abinda ya faru jiya don ta fahimci abinda ke faruwa yanzu.

Abinda ya faru bayan Sadik ya kira mata lambar motar Ma'aruf a ™ofar gidan Awwalun, cewa tayi ya jira ta a wajen gata nan zuwa. Don a lokaci guda kwakwalarta ta gaya mata cewa tunda har ´ansanda suka zo neman Awwalu basu same shi ba, to tabbas dole ne ita ta fito su san yadda zasu yi su nemi inda Awwalun yake a wannan daren ita dashi don ta gama da babinsa kafin komai ya caSe mata.

Don haka tayi saurin yin transfer wasu kudade daga bankinta na ajiya zuwa na amfaninta da kowa ya sanshi da ita sannan ta debi kayan waWannan allurorin ta zuba a leda ta fita, ta fita a lokacin da kusan duk jama'ar gidan ke Sangaren Hajiya Maimuna na murnar dawowar Abdurrahim, ta fita babu wanda ya ganta don ko Maigadi bata samu a gate ba shima.

Da kafarta ta taka har bakin titi inda ta samu wani mai keke napep Win da ya sauke ta a shagon wani mai POS ta ciro dubu dari biyar daga account din ta zuba su a wannan ledar don ta riga ta gama shirya yin asarar ko nawa ne a jiyan don samun inda Awwalu yake.

Tana iya tuna yadda zuciyarta ta dinga bugawa a kirjinta a lokacin, tana iya tuna yadda ta kasa zama waje guda cikin keke napep Win zuciyarta na cikowa a ™irjinta,
har ™o™arin tsugunnawa tayi ta kuma yi ™o™arin tashi tsaye, daga baya ma taga kamar mutumin baya gudu sosai don haka tace dashi ya tsaya, ta sauka ta bashi kudinsa sannan ta tsaya neman wani, tana tsaye tsabar ruWewa da kuma yadda kanta yake juyawa sai taga kamar daya barin titin an fi samun keke napep Win da babu kowa.

Kuma a lokacin ne abin ya faru, a lokacin da tazo tsallakawar ne motar ta buge ta, taji lokacin da ta tashi sama, numfashinta na biyo ta sannan taji lokacin da ledar hannunta ta suSuce, tana gaya mata cewa  kuma abu na ™arshe da zata iya tunawa kafin numfashinta ya yanke shine taji hayaniya da kuma salatin mutane da yawa a saman kanta.

A yanzu a asibiti take kenan, asibiti ne daga maganganun da taji suna yi a saman kanta.... Salatin da bakinta ba zai iya ba shi zuciyarta ta karanto ta kuma sake karantowa, ina ledar dake hannunta ina kuma wayarta? Me yake shirin faruwa ne? Wane irin mummunan mafarki ne wannan? Ta yaya Allah zai jarabce ta da hadarin da har zai kai ga kwanciya a asibiti a wannan halin da take ciki? Ina ledar hannunta ina wayarta? Inalillahi wainna ilaihir raji'un... zuciyarta ta ambata tana sakewa, don abu na ™arshe da zata so yanzu shine ace ledar hannunta dama wayarta tana hannun da bai dace ba, hannun da zsi iya tona asirinta ba tare da wata wahala ba.

Tayi kokarin yin motsi kaWan, a lokacin ne taji yadda kanta ke juyawa kotawanne Sangare, jikinta yayi tsami kamar anyi mata duka.

"Har yanzu akwai ´an sanda a ™ofar?"

Taji muryar Ishaq ya tambaya, tambayar da ta haddasa dokawar ™irjinta a lokaci guda, bugawar da ta nemi dagargaza zuciyarta, bakinta ya sake karanto kalar wani salatin da bata taba sanin ta iya shi ba... ³an sanda? A ina?

"Suna nan baza su tafi ba ai, Baffa yace babu yadda baiyi  dasu ba, amma har sun tura maganar sama, don haka babu yadda za'ayi a rufe case din tunda shi DPO din da ya kade ta ma yaki saurarar Baffan su sake magana."

DPO? DPO'n ´an sanda ne ya kaWe ta? Kuma yaga abinda ke cikin ledar hannunta? Yaushe duniya ta tsuke har haka?

Muryar Ma'aruf ta fito da kaushi, kaushin dake shaida tsananin Sacin rai mai haWe da tashin hakalin da baya Suya. A cikin kanta ta kintaci cewa ya girgiza kansa kafin ya cigaba da cewa.

"There must be a mistake dole Ishaq, me Mami zata yi da allurar ™waya irin wannan? Sannan har da kudi five hundred thousand a cikin leda? Na yarda framing dinta kawai wasu ke ™o™arin yi tunda ko Baffa ma bai san da fitar ta ba... Kuma ban san me yasa ba amma jikina yana bani cewa wannan al'amarin yana da alaka da case Win da muke yi, shi yasa nake so ta farka tayi bayanin komai waWannan ´an i*kan su bamu waje."

A wannan lokacin ji tayi kamar ta mi™e zaune ta girgiza kanta, ta gaya musu cewa ba zai yiwu ace komai ya caSe mata a wannan lokacin ba...

Ba zai yiwu ba, tana da sauran lokaci,  damarta bata taba karewa ta sani, tsarinta kullum daidai yake tafiya don haka ko a yanzu da take iya jin tsananin damuwa daga muryar Ma'aruf ta sani zaren bai ™are mata ba, tana nan a Mamin da take a idanun kowa abunda ya rage kawai shine ta bude idanunta ta ture wannan ™alubalen ta cigaba daga inda suka tsaya... Zata san yadda zata yi ta fidda kanta ta sani... Sun ga ledar a hannunta amma hakan ba zai basu tabbacin komai ba tunda babu wayarta.

Wayarta, babu wayarta, basu same ta ba, don haka ba shiri ta haWiye wani abu a ma™ogwaronta, komai da sauki, komai zai zo da sauki kenan, ba'a kama Sadik ba, tana da sauran fata ta san yadda zata yi komai ya tafi daidai, ta sani.... Ita Kilishi ce kuma ko a wani hali tana da mafita...

"Ka cire tunanin wadannan mutanen a ranka B, babu inda zasu je idan har ba umarni aka basu daga can ba."

Ishaq ya faWa daidai lokacin da ya daga wayarsa kuma ba sai yayi wani bayani ba daga gaisuwa kawai Kilishi ta fahimci cewa da Hajiya Maimuna yake magani.

"Mami baza su barku ku shigo ba, mu ma da I.D cards Winmu muka yi amfani, yanzu ma so muke mu samu ta farka watakila komai zaiyi sauki..."

A lokaci guda hankalin Kilishi ya dugunzuma ya ™ara tashi, ak'amarin ya kai har a hana nakusantan ta ziyartar ta? innalilahi wa'inna ilaihir raji'un! Ta ina zata fara neman mafita idan har al'amarin ya kai haka? Me zata fara kamawa a yanzu? Ta ina zata fara bayanin inda ta samu allurar da kuma wajen da zata je? Wannan wane irin mummunan tashin hankali ne? Me yasa komai zai Sare a lokacin da bata shirya ba? Me yasa sai a wannan nisan sannan ™alubalenta zai zo? Don ta yarda har yanzu wannan ™alubale ne, babu ta yadda za'ayi ace wannan shi zai kawo ™arshen ta, tana da mafita a komai na rayuwarta, tana da ita ta sani! Kawai zata fuskanci wahala ne kafin ta daidaita komai.

"Hajiya ce, wai su Samirah ne har da kuka zasu taho..."

Taji Ishaq ya faWa bayan ya ajiye wayar da yake yi.

"Babu wanda zai zo, su bari mu san me ake ciki ma tukunna, idan sun zo me zasu yi?..."

Cewar Ma'aruf yana jin tasirin abinda ke zuciyarsa na yin yawa, kuma Ishaq din bai ce konai ba, shiru ya ratsa dakin kafin wayarsa tayi kara, kuma yana jin ya dauka  ya fara waya zuwa office Winsu, sai kawai ya mi™e, ya mi™e tsaye ya nufi kofar Wakin, kuma bai kira komsi ba ya kama hanya ya fita.

Missed call Win Faruk guda biyar ne, duka bai san lokacin da ya kira ba sai kuma na Amina guda biyu.

Amina ya fara kira kafin Faruk Win, kuma sautin muryarta, wannan sassanyar muryar tata, shine abu na farko da ya tuna masa da irin tarin wahala da kuma gajiyar dake jikinsa, wanka kawai yayi a jiya lokacin da Baffa ya kira shi da zance mafi tashin hankalin da hafi ba zagayen halin da yake ciki, cewar wani dan sanda ya kira shi da cewar ya kade Mami akan titin hanyar gidan Gwamna, sannan sun tsinci wasu miyagun kwayoyi a cikin ledar dake hannunta.

Yana iya tuna magiyar da ta dinga yi masa a lokacin, magiyar cewar ya fada mata abinda ke faruwa, amma bai iya ba din,rigar da take miko masa a lokacin ya karSa kawai ya zura a jikinsa sannan ba tare da ya damu da taje barbajajjen gashin kansa ba ko kuma ya shafa mai ya dauki mukullin motarsa kawai ya fito, ya fito ya barta ita da Hamidan dake binsa a baya da nata tambayoyin da kuma kwanukan tuwon nan da yaci burin huce gajiyarsa dashi kamar me...

"Babydoll...."

Muryarsa ta fito a hankali bayan ya shige cikin motarsa. Kuma maimakon ta amsa sai tace.
Chapter 59 · 0% Book details