Sashe 75
Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yarda ta rasa Ma'aruf, ta rasa shi ta rasa kulawa da kuma ™aunarsa. Babu kalamansa ko a cikin kanta, ta ji su a lokacin da ya fade su kuma ta barsu a wajen, babu abinda ta dauko sai ciwo da kuma takaicin rasa shi da tayi ta wannan hanyar a raywarta, ta shirya dama, ta shirya barinsa don haka ta dade tana ywa zuciyar tata tanadi na wasu abubuwa da zasu dauke hankalinta bayan ta bar cikin rayuwarsu, amma da hakan ya faru a lokacin da bata shirya ba sai ya dake ta da tsananin tashin hankalin da bata ™ara ganin wani abu da ya tsorata ta ba bayan hakan ba.
Ko sanda ya danna kan motar suka tafi suka daki bishyar nan, bata ji tana tsoron mutuwa kamar tashin hankalin cewa an riga bude ainihin kammaninta a idanunsa ba.
Da kuma sanda ta kalli idanun su Baffa, Baba Usman, Ishaq, abokin Ma'ruf mai suna Faruq da kuma Abdurrahim... Ta kalli idanunsu ne tana jin zuciyar fayau yayin da tunaninta yake wasai, don tunda zuciyarta ta karSi tashin hankalin wajen Ma'aruf bata tunanin kuma akwai wani abu a duniyar nan da zuciyar tata zata sake rusunna masa, hatta Baffan kuwa, hatta shi din da ya zame mata tsani kuma hanya wajen aikata dukkan abinda ta wanzar a rayuwarta.
Tana kallon kowa ne kawai tana kuma jin abinda suke cewa, amma yadda bata furtawa Ma'aruf ko da kalma guda ba, haka babu abinda tace har wayewar garin yau, abu daya kawai take so ta yarda dashi shine cewar ba zata yi biyu babu ba, ba zata rasa Ma'aruf ta kunyata a idon duniya a rana guda ba sannan kuma ta rasa burin rayuwarta ba, ba zata taSa iyawa ba, ba zata yarda an zo gaSar da zata je ™asa ba kamar yadda ta shar'antawa kanta a baya ba, har yanzu tana da yardar cewar damarta bata ™are ba, dole ne ta fidda kanta kamar yadda ta sa ba.
Dan sandan yace bata da kowa a yanzu,ta yarda, ta yarda da hakan... Don tun da ta rasa yardar Ma'aruf ta sani cewa ko yardar ´a´an ta ba zata samu a yanzu ba, don haka ta yarda zata barsu, zata bar kowa nata sannan zata bar kowa da ta sani, abinda bata yarda ba shine da yace bata da komai, wannan ne zuciyarta bata amsa masa ba don ita ta san tana da abinda zata kare kanta ko a gaban wane alkali ne a duniyar nan.
Amma ba za'a kai nan ba ma, ba zata je gaban kowanne alkalin ba, zata yi nisane da kowa, zata yi nisa zuwa wani waje da zata kafa sabuwar rayuwarta, sabuwar rayuwar da ta san a cikin lokacin da zai ja mata... Dole ne yayanta zasu dawo gare ta, dole ne watarana zasu juyo su waiwaye ta, don meye yake raba ya'ya da uwarsu a duniyar nan?!
Sai kawai ta mika hannunta mai lafiyar ta janyo file din dake gaban Wan sanda, ya dago ya bita da kallo fuskarsa na shaida mamaki da kuma tunanin abinda take shirin yi, ta ajiye file din sannan ta sake mika hannunta alamun ya bata biron da yake rike dashi, sakan daya, biyu... Kamar ba zai bata ba sai kuma kawai ya mika ma tan, bayan ta karba yana kallon yadda yatsunta dama rubutun da take yi ke rawa, rawar dake shaida rikicewar da yanayinta ke Soyewa.
Lambobi ne, lambobi ta rubuta guda goma wanda ba sai ya tambaya ba ya san lambar asusun banki ne (account number), ta ajiye biron akan file din sannan ta sake turo masa shi gabansa.
Idonsa ya kalli lambobin sannan ya dago ya sake kallonta, a lokacin ne kuma tayi magana ta faWi abinda ba ga Wansandan ba kadai, har ga ita kanta ya tabbatar mata da cewar har yanzu tana nan a matsayin Kilishinta.... Tanan bata canja ba!
"Akwai kudi sama da miliyan dari huWu a cikin account din nan, ka taimake ni in fita daga wannan wajen, ka taimake ni inyi nisa daga dukkan wadannan matsalolin dake rubuce a cikin file dinka, ni kuma nayi alkawarin zan baka rabin kudin da nake dashi, zan gyara rayuwarka ta yadda har ka koma ga ubangijinka ba zaka taba sanin Wacin Babu ba!"
Ta kai karshe a lokacin da idanun Wan sandan ke kallonta da wani irin yanayi mai wuyar fassara a lokaci guda!
***
A cikin Wakin asibitin ba ka jin komai sai ™arar kaWawar iskar Acn da ya kaure ko'ina.
Hajiya Mardiyya ta girgiza kanta ri™e da wayar dake kare a kunnenta kafin tace.
"Kar ku damu Khadija, ki bawa su Innan ma hakuri, tahowarmu ba zata wuce gobe zuwa jibi ba insha Allah, ni ban san haka wannan asibitin yake ba da muka dauko ta wancan na gwamnatin muka kawo ta nan, su bamu refferal kawai abu na neman gagara... Ashraf dai yace yayi magana da likitan dazu, ni ko bai yarda ba zan dauko ta ne kawai mu dawo ba zan jira ba."
Ta gyada kanta sannan ta sake cewa.
"Eh, Ahmad ne ya taho yau, da asuba ya kira ni yace Babansu yace yazo ya kawo min sa™o... Amma shi kadai ya taho banda sauran."
Wadda suke wayar a ciki ta amsa kafin ta ta lashe wayar tana ajiye ta a gefen bedside drawer dake kusa da gadon, kusa da gadon da Rukayya ke kwance idanunta a rufe.
Kusan awa guda kenan da ta samu bacci, awa guda bayan ta farka da tarin surutan da a ciki basa iya gane komai sai sunan Hamida ´arta da kuma Hajiyan Sudan da take ambata, Ashraf yace zai iya yiwuwa shine abu na ™arshe da ta dinga fada lokacin da hatsarin ya faru, ta ga Hajiyan Sudan din a wancan asibitin na farko da suka je dauko Rukyya, ita bata ganta ba kuma bata bari ta ganta din ba, babu kowa a wajenta kafafunta na karye duka biyun an nade su da bandeji an kuma dage su zuwa sama.
Tana ji wata Nurse na faWan cewar har yanzu ba'a sami wani danuwanta da zai zo ya biya kudin treatment da akayi mata ba... Bata ce komai ba suka biya kudin Rukayyan kawai suka karbi sallama suka juyo.
Don abu na karshe da zata yi a rashin hankalinta shine ta nuna wata mu'amala tsakaninta da Hajiyan Sudan Win a gaban Ashraf, ta sani kashinta ne zai bushe idan har mijinta ya san da hakan... Ya san abinda ta tura Rukayyan yi a Niger kuma tare da ™awarta. Don haka bata ce komai ba har suka bar asibitin suka kawo ta wannan.
To a yanzu Ashraf din ya dame ta da tambayar wacece Hajiyan Sudan din da Rukayyan ke kira, ta gaya masa cewa itama bata san ta ba amma kallon da yayi mata bayan ta gaya masa hakan ta san ba na yarda bane.
Ta sake kallon Rukayyan, ciwonta da sauki ba kamar yadda suka zata a farko ba, mild stroke ne mutuwar barin jiki wanda likitoci suka tabbatar masu da cewar ba zai dauki lokaci ba zata warke ta koma daidai idan har za'a bi dokin da da kuma kaidojin da suka dace... Ita ta sani dama, ta san Allah ba zai jarraba su ta wannan hanyar ba, kyawun yarta haWe kuma kyawun jikinta wani abu ne da ba zai nakasa ba.
Don haka hankalinta ya dan kwanta ta yadda bata hango komai sai komawarsu Nigeria don su cigaba da jinyarta acan ba tare da asirinta ya tonu ba.
Lokaci ya nuna karfe biyu daidai yana tuna mata da sallar azahar din da bata yi ba, don haka ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala sannan ta shimfida slaya a gefen gadon ta tayar, zuciyarta cike da fatan kafin idarwar tata, Ashraf ya dawo tare da Ahmad din da yaje daukowa daga airpot.
Ai kuwa sai fatan nata ya karbu don a sallamar raka'a ta karshe su ma suka yi sallama suka shigo dakin.
Ta amsamusu a lokaci guda da ta fahimci rashin fara'ar dake kwance akan fuskarsu... Ahmad din ne ke gaishe ta yayin da Ashraf ya samu kujera ya zauna fuskarsa na numa tsananin bacin ran da ta dade rabon da ta ganshi a fuskarsa.
"Me ya faru? Wani abu ne ya faru kuma?"
Ta tambaya tana kallon dukkanninsu... Kuma Ahmad din dake gabanta bai ce komai ba sai kawai yasa hannu ya ciro wata takarda daga aljihunsa ya dora akan sallayar da take kai.
"Sakon da Daddy yace in kawo miki ne."
A lokaci guda zuciyarta ta buga a kirjinta, bata san meye a cikn takardar ba, bama tayi tunanin menene din ba, amma daga yanayin fuskokin yayan nata kadai ta san ba abu ne wanda zata so shi ba, dn hak ta yankewa kanta nisan taraddadin, ta mika hannunta a hankali wanda ke rawa ta dauki takardar, kuma tun kafin ta kai ga buWe ta, taji kwalla ta na neman cika idanunta yayin da kwakwalar ke gaya mata cewa ita ta riga ta karbi sakon tun kafin ma ya iso.
A rubuce a ciki, Hajiya Nafisa ta tadda kalaman da sune abu na karshe da kunnen kowacce mace zai so yaji su daga sautin mutumin da take raba rayuwarta tare dashi!
***
_˜addarar dake jiran labarin nan a gaba ya danganta ga amsar da Hajiya Kilishi zata samu daga bakin Wansandan nan...._
_Me kuke tunani?..._
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/22/22, 19:33 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*25*
_They tell you to be grateful for what you have, but you are also allowed to be sad for what you have lost..._
~~~~~
*Bayan watanni Shida.*
**
*Kano.*
*Central Prison.*
*03:00pm*