← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 87

Sashe 67

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanda a sannan ne kuma Ma'aruf ya mi™e, babu wanda ya san inda za shi a lokacin  don shi bai maganshi ba sai da ta isa wajen kofar office Win, babu wanda yayi wa magana, babu alamun ma ya san da su zaune a wajen don baya tuna cewar ko bayan da suka shigo tare dasu Baffa ya Wago da kansa, su Abdurrahim ne kawai suka yi musu magana kafin tashin hankalin dake yawo a cikin Wakin ya ziyarce su.

Kuma babu wanda yayi tunanin su tsayar dashi a lokacin, babu wanda yayi tunanin komai sai bayan fitarsa da minti biyu sannan shi da yake zaune hankalinsa ya dawo jikinsa, ya fita da sauri ya bishi amma bai ga komai ba sai maigadi da ya hango daga can yana ™o™arin maida gate din wajen zai rufe... A lokacin ya san cewa dukkanin su sunyi babban kuskuren da zai shafi al'umma da yawa a wannan daren.

Ilai kuwa! ˜asa da minti talatin bayan hakan, a lokacin da Baffa ke ™o™arin kwantarwa dasu Hajiya dake can gida hankali, a lokacin  kiran DSP ya shigo wayarsa da sakon cewa Ma'aruf yayi wa mutane biyar jina-jina a asibiti ciki gar da ´ansandan sa guda biyu sannan kuma ya Wauki mara lafiyar da suke gadi wadda suke zarginta da ta'ammali da mugayen kwayoyi kuma ya har yayi nasarar fita da ita daga asibitin ba tare da an iya tsayar dashi ba.

Ishaq ya sani cewa idan za'a zaunar dashi zai kwana yana saka hannu a takardun da zasu bada tabbaci na cewar Baffa mutum ne jajirtacce irin wanda bai taSa gani ba a rayuwarsa, a iya abinda ya sani na tarihin rayuwarsa yana da lissafin tarin wasu abubuwan da ba kowa ne zai iya fuskantarsu a duniyar nan kuma rayuwarsa ta cigaba da tafiya daidai ba, amma Baffa ya fuskance su, yabi ta cikinsu ba tare da wani abu guda daya ya goce daga rayuwarsa ba, ko a iya harkar kamfaninsa kadai akwai tarin abubuwan da mutane da yawa zasu iya kasawa a bugu daya, amma da kafafunsa ya tsaya, ya jajirce, har komai ya kawo matsayin da yake a yanzu.

Amma a lokacin da DSP ya kira shi da wannan bayanin, a jiya cikin wannan daren faduwa yayi har kasa daga yadda yake mike bayan ya amsa wayar Hajiya Maimuna, babu wanda ya gani babu wanda ya lura, sai da ya kai har kasa wanda hakan shine kalubale na biyu da suke fuskanta, don tun jiyan bai farka ba, sun kwana dashi a asibiti bayan likitoci sunyi kokarin dawo da numfashinsa, amma tun a daren jiyan Hajiya Maimuna take magiyar a dawo dashi gida, don haka a dole likitan da ya kwana dasu a asibiti ya biyo su gida dab da sallar asubahi aka kwantar dashi a dakinsa tare da sauran hade-haden da akayi masa a asibitin.

Sunyi masa allurar bacci mai ™arfi da a™alla zata Wauke shi tsawon kwanaki biyu don likitan ya tabbatar da cewar idan har ya farka a yanayin da yake komai zai iya faruwa, saboda halin da zuciyarsa ta shiga.

A yanzu haka kuma cikin gidan ya koma tamkar gidan makoki ne don iya abinda suka ji ya tayar da hankalinsu mutuka, tunda dama tun a jiyan sun kwana ne a zaune.

Yanzu dashi da Baba Usman da kuma su Faruq suke ta fafutukar neman Ma'aruf da kuma Mamin ko ta wacce hanya, kuma hankalinau na tsaye ne kamar yadda suma suke a tsaye, Abdurrahim na kan Computer tun a daren jiyan yana kokarin gano signal din wata karamar waya mai Wauke da layin Ma'aruf din na biyu wadda ake tunanin cewa tana cikin motarsa, saboda ana ta kira ba'a dauka wani lokacin ma bata shiga.

Sai dai duk kokarinsa ya kasa kama signal din wayar har yanzu saboda matsalar Nigeria da ba koina ake samun service ba idan har ba mutane bane a wajen... Faruk kuwa yana can sunyi hanuar Kuran tare da ´an sandan, shima a yanzu dawowarsa daga asibiti kenan wajen mutanen da Ma'aruf Win yayi wa rauni a daren jiya, dole ana bukatar sa hannun wanda yake da alaka dashi ne a wadu takardu da za'a cike a asibitin don haka DSP din ya kira waya yace a tura wani.

"Su biyar din ne kamar yadda suka ce?"

Baba Usman ya tambaye shi bayan ya karaso cikin falon Baffan inda ya same shi, kuma shima bayan ya gama wayar da yake yi. Kansa a sunkuye ya daga shi.

"Eh, bayan ´ansandan biyu sai maigadin kofar wajen da aka ce yayi kokarin hana shi shiga,sai kuma wani Nurse guda Waya."

Baba Usman ya gyada kansa tare da ajiyar zuciya sannan yace.

"Nayi magana da sakataren IG Win, ina ga kamar ya karbi case din da muhimmanci don haka yace da zarar ya shigo office zai yi magana dashi a sake bamu wasu ma'aikatan."

Lebbensa a bushe kamar makogwaronsa Ishaq ya gyada kansa a hankali sannan yace.

"Mun yi waya da Faruk Baba, yace min sun wuce Kura ma yanzu wai wani manomi yace musu yaga shatin tayar mota a cikin gonarsa kafin ya fito, don haka zan bi bayansu..."

Idan ka kalle su a wannan lokacin daga Baba Usman din ha Ishaq din ka san kawai kowanne yana amsa sunansa ne na 'Namiji' amma bayan hakan babu abinda zai hana su fitar da tarin hawauen dake kwance a cikin kirjinsu, kuma a wannan lokacin ne, kafin Baba Usman Win ya buWe baki ya bashi amsa suka jiyo wani sabon kukan daga cikin gida wanda kafin ya iso inda suke Hajiya Madina matar Baba Usman ta kira shi da cewar Amina ta faWi!

***

_Komai dai yazo ™arshe, ina kuke tunanin Ma'aruf ya tafi da Kilishi?_

_Me zai faru?_

_Me zai faru?_

_Masu iya magana kan ce a lokacin da ba™i ciki ke samun waje da kuma bigiren yaWuwa a lokacin ne kuma a wani wajen, farin ciki ke kafa tasa tutar..._

_Wasu zuciyoyin na bushewa ne yayin da ruwan damina mai danshi ke mamaye wasu zukatan..._

_Kuna tunanin gangarar nan zata zama mai dadi ga kowanne bangare?_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:58 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©ýÿAYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*23*

_And those who burdened muslim men and women, without them doing anything (wrong) hsve burdened themselves with false accusations and open sin.- Surah Al-ahzab, Ayah 58._

~~~~~~

"Anan wajen ya mutu Mami..."

Ma'aruf ya faWa da sautin muryar dashi kansa ya sani baiyi kama da nasa ba, a zaune yake a cikin motar idanunsa a manne da wata katuwar bishiyar dake gabansu, daga bayan motar, kujerar baya Hajiya Kilishi ce zaune kanta a sunkuye yayin da idanunta suka yi jawur da tsananin tashin hankalin da baya mata kama da zahirin da mutane ke rayuwa.

Tashin hankalin da ya canja kamanninta, ya mayar da lissafin kammanin ta wani irin da da wuya ne ka gane ta a lokaci guda, don hatta jikinta ya canja a cikin kwanaki biyu kaWai! Ta rame ta sirrance sannan tsufa da kuma shekaru ta da a kullum kwalliya da murmushin ta ke Soye su sun baiyana tar!

"Anan wajen ya mutu bayan ya gaya min kar na kashe... Shine abu na karshe da ya gaya min Mami bamu sake magana bayan hakan ba, yana amsa waya lokacin da kaddarar da kika halitta mana ta faru... I was driving safely, na sani cewa tun a wancan lokacin banyi wani abu ba daidai ba.

Kawai naji sitiyarin ya ™wace daga hannuna ne sannan naga motar tana wullawa akan titin, ina jin salatin da yake yi a wannan lokacin Mami, sannan ina ganin hannunsa yana ta kokarin ya kama sitiyarin amma juyin da motar ke yi yasa buguwa kawai muke yi kotawanne bangare, lokacin da motar ta taho cikin dajin nan, daga ni har shi babu wanda yaga wannan bishiyar dake gabanmu har motar ta dake ta, ta dake ta daidai saitin inda wani reshenta yake a karye sannan daidai saitin inda Jamal yake da karfin da yasa reshen ya faso ta cikin gilashin ya soke shi a ko'ina na kirjinsa...."

Muryarsa tayi ™o™arin sha™ewa amma ya cigaba.

"... Ya rasu yana kallona Mami, idanunsa akaina suka tsaya har lokacin da jama'a suka karaso suka rufe motar ana kokarin fito damu, kuma ba'a iya fito dashi ba sai da aka sare reshen bishiyar nan daga jikinta, aka fita dashi dasu a jikinsa.... Har akayi masa wanka aka kaishi kabarinsa da itacen bishiyar nan a jikin sa Mami.

Kina tare dani a asibiti a lokacin, kin san wannan ranar itace sanadiyar samun ciwo na, ciwon da ya tauye tarin abubuwa da yawa a rayuwarta, kin san dukkan wahalar da na sha Mami, kusan haukacewa nayi kin sani, bana gane komai bana fahimtar komai, wannan ranar kadai ke maimaitawa a cikin kaina, tun daga safiyar da na ganshi zaiyi tafiyar, har tahowarmu mu, da maganganun da muka yi da kuma yadda hatsarin ya faru...

Na dade inabincike Mami, na daWe ina bincike fara bincike akan al'amarin, sai da na shekara uku ina bin wannan hanyar ina tuntubar mutane kafin na samu wasu mutum biyu da suka tabbatar min cewa wasu mutane ne suka harbi tayar motar mu a lokacin da nake tu™in nan, na gane cewa da silencer suka yi amfani a bindigar ta yadda babu wanda yaji wata ™ara sai kawai ta fashewar tayar.

Bayan nan, nayi iya binciken da zan iya don gano mutanen da suka yi wannan aikin amma har aka zo gaSar da hankalina ya karkata ga aikin kamfani da kuma binciken wata Sarakar da kike haifarwa acan ban sami komai ba Mami, duk hanyar da na bi bata Sullewa kamar yadda a binciken kamfanin ma bana samun komai, kawai ina ™arewa ne da tarin bacin ran dake sawa ciwona ya tashi, komai ya sake tsayawa a rayuwata ta yadda bana jin ina son komai sai tsananin yadda zan iya wanke kaina a wajen Jamal, in kuna kawo ™arshen komai, wanda hakan shi ke kara baki dukkan wata dama da kike kassaramu da ita...."
Chapter 67 · 0% Book details