Sashe 81
Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har sai da ta kai Baffa da bakinsa watarana da suka yi waya ya bata shawarar cewa ta dinga saka lemon tsami a ruwan Wumi ta samu yasha kafin ya kwanta, yace mata hakan ba karamin abu bane dake wanke zuciyar Wan Adam...
Hajiya Maimuna kuwa tasa Munaya ta rubuto mata tarin addu'o'in wasu kuma tayi recording da muryarta tana tofawa a cikin ruwan shan sa, wani lokacin har ma da kayan da zai saka kafin ya fito daga wanka. Samirah ma ta sha kiran waya ta gaya mata abincin da ta san yana so tun asali wadanda idan anyi ransa ke jin dadi.
Kowa ya taimaka, kowa ya taimaka da iya abinda zai iya duk kuwa da halin da har yanzu zuciyioyinsu ke ciki, musamman su Samiran ´a´an Hajiya Kilishin da ko a idanunsu, ba™o zai shaida damuwar da suke cikinta har yanzu, amma har su Salma dake gudajensu suna kira su ji lafiyarsa.
Don haka duk da ta sani cewa ba da iya taimakonta kadai suka karaso matakin da Ma'aruf din yake a yanzu ba, matakin da take ganin kusan bashi da maraba da warkewarsa gabaWaya, duk da haka tana jin zata Wauki alhakin duk abinda zai biyo baya idan har aka samu wani akasi ga me e da lafiyar tasa.
Kowa yayi kewarsa a gidan nan, tarin kewar da take ganin kamar shine ruhin gidan nasu gabaWaya, don irin murnar data ji daga kowa a gidan a ranar da shi da kansa ya dauki waya ya kira su, wani abu ne da mizaninta ya kasa aunawa.
Tana tsaye daga baya bata ko jin me suke cewa, da amsoshinsa kadai take ayyana tarin murnar da har ™walla sai da ta saka ta, sai ta juya masa baya tana sharewa da tafin hannunta yayin da zuciyarta da ma duk wani abu mai hankali a cikin kanta ke ™ara tasbihi ga jalla wata'ala da ya takaita wahalarsa da ma tasu bakiWaya, don ko daga gidansu Amma tace kowa yayi kwanan farin ciki musamman ma Baba wanda ya matsu ya ga dawowarta.
Bayan hakan Ma'aruf da kansa ya yanke ranar da zasu koma Kanon bayan tarin abubuwan da suka ™ara gamsar da ita warkewarsa, don a yanzu har da Faruk suna waya game da harkokin kamfaninsu, yana gaya masa iri tsarin sababbin securities dn da Abdurrahim ke sakawa a kowanne bangare na kamfanin ta yadda babu wani mai wayon da ya isa ko yaga kaya ma idan za'a fitar dasu daga kamfanin balle kuma kuWi.
A yanzu haka ma kusan sati guda baya yini a gidan yana can fafutukar rufe asibitinsa MMB-6 da cewar zai mayar dashi can hida Kano inda shi da kansa zai dinga jagorantar komai... A yanzu kusan an gama komai ma kokarin samun masu siyan ginin kawai ake yi... Kuma sai ya zama fitar ma ta kara taimaka masa wajen sake warwarewa don ta sani akwai tarin abubuwan da a zaman gidan kadai zasu cigaba da tuno masa da Kilishi da kuma dukkanin abinda ya faru, amma bai taSa maganarta ba tunda ya farka, ko da Baffa ko kuma da Baba Usman Win da suke waya a kullum.
Sannan bayan tahowarsu Munaya ta gaya mata cewa cikin abinda bai fi sati hudu ba wata guda n canja tsarin gidan bakiWaya, Baffa ya saka an rushe bangaren Hajiya Kilishi, an haWe gidan baki Waya a waje Waya kuma ta kofa guda saboda su Samirah dama dukkanin al'ummar gidan da tabbas ganin Sangaren nata zai dinga tuna musu da ita a kodayaushe.
Don ko a lokacin da yayi general meeting tun kafin tahowarsu, ba ga ´an gidan kadai ba har da sauran yanuwa na da kuma na Hajiya Maimuna akan abubuwan da suka faru, yayi ta jaddada cewa dole ne kowa ya cire ta daga cikin zuciyarta saboda trin laifuka da kuma cutarwar duk da cewa an Soye wasu da yawa saboda Inna Danejo dake fama da rikicewar tsufa tun daga wannan daren da al'amarin ya faru.
A zahiri yanzu rayuwa ta fara komawa daidai, abubuwa suna tafiya kusan a daidai ga kowa don Baffa yana iya bakin kokarinsa wajen ganin ya daidaita rayuwar tasu ta koma kamar da, amma a cikin zuciyoyin kowa Amina ta sani cewa dole akwai wannnan digon bakin ciki da ba zai taba gogewa ba musaman ga su Samirah ´a´anta, wanda ko sau daya Baffa bai bari sunje sun ganta a can kurkukun da aka daure ta ba...
Munaya tace mata wasu daga cikin yanuwansa sunyi kokarin tausar sa akan hakan, amma babu wanda ya san cewa yayi nasa fushin sai a lokacin, don Ishaq ya kira ya zauna a gabansu sannan yace ya zama shaida zai yi shari'a da duk wanda ya ™ara kawo masa magana makamanciyar wannan. Shikenan! Sai zancen ya mutu ko su Samirah basu kara yunkurin hakan ba.
Gobe itace ranar da Ma'aruf ya yanke shawarar komawarsu, bata sani ba ma idan ya gama da zancen asibitin nan, amma ya tabbatar mata cewar zasu koma gida don tun jiya shi da Ishaq suka gama tsara komai, don haka itama tun a jiyan da kuma yau da safe ta gama shirya dukanin kayansu, akwati guda uku ne sai kuma wata jakar dake Wauke da yan kanan tarkacenta, ta tattare komai nasu hatta kayan da zasu saka ta fito dasu, na jikinsu idan sun cire ne kawai zata sama musu waje.
Kuma bata san me yasa ba haka kurum tun jiyan take jin wani iri don haka a yanzu da Amman tayi mata wannan tambayar sai kawai ta sake jin jikinta ya mutu, ta haWiye yawu a ma™ogwaronta kafin ta gyada kanta a hankali.
"Insha Allah Amma ba abinda zai faru, yaji sauki da gaske, kuma idan mun dawo Win ma zai ™ara tafiya can asibitin da ake duba shi kafin ma ya koma aiki insha Allah."
Daga cikin wayar, Amma ta yi tata ajiyar zuciyar a hankali.
"Shikenan, Allah ya kawo ku lafiya, Allah ya ™ara sauki. Maganar da nake son mu yi akan yadda zamanki zai cigaba a gidan nan ne... Na gaya miki Kilishi ba itace matsalarki ta ™arshe a duniya ba, zama yau da gobe tare da kowa a duniyar nan dole yana bukatar hakuri don watarana ma baka san lokacin da zaka batawa wani ba, kina gani ko sanda kina nan a tsakaninku yanuwa ma kuna samun sabani balle kuma a gidan surukai.
Don haka dole ne ki cigaba da yin taka tsan-tsan wajen kyautatawa kowannensu da kuma Wauke kai akan abinda bai shafe ki ba, wadannan abubuwan guda biyu Amina sune abinda mata da yawa suke kuskurensu shi yasa ba ga surukansu kadai ba har a wajen miji suna samun matsala, idan kin dawo zamu sake yin magana insha Allah."
Amina ta gyaWa kanta alamun ta fahimta ta kuma rike kamar dukkan sauran maganganun mahaifiyar tata kafin ta amsa.
"insha'Allah Amma, insha Allah."
"Kice muna gaishe shi, sai goben idan zaku taho kya kira mu."
"Toh zai ji insha Allah."
Har Amman na shirin katse wayar tayi saurin sake magana.
"Maryam tana kusa dake? Zan tambaye ta wani abu ne..."
"A'a bata nan amma ga Adam nan, bari ya kai mata."
"Toh Allah ya bamu alkhairi."
Amman ta amsa kafin ta mika wayar a hannun Adam dake zaune yana game a wayar Aminu, ya mike da sauri zuwa tsakar gida inda Maryam Win ke kitchen tana sake zubawa su Hafsa da suka tsira mata idanu abinci tana faWin kar su shigar mata daki su bata mata.
Ta karSi wayar bayan hakan sannan suka shiga tasu hirar akan wasu Winkunan kaya da ta barwa Maryam Win ta kai mata kafin tafiyarsu, Winkunan da take sa ran su zata yi amfani dasu a bikin Munaya da Ishaq wanda aka saka rana watanni biyu masu zuwa... Watakila lokacin da zata haihu da kwanaki kaWan. Ko can gidan a yanzu shirye-shiryen kawai da ake yi kenan, shine babban abinda ke dan dauke hankalinsu daga al'amarin da ya faru, musamnan su Samirah da Munsyan ke gaya mata cewa suma sun kara sakewa sosai a yanzu.
Aminu ya shigo kafin su ™arasa eayar da Maryam, yana shirin fita zuwa wajen aikinsa da ya cigaba da zuwa sakamakon saukin da kafarsa tayi. ya karSi wayar daga hannun Maryam suka shiga tasu hirar kamar kodayaushe yana gaya mata cewa ya cika akwati na uku ya buWe na huWu da kayan Baby.
***
Daga kan matattakalar benen dake saukowa cikin falon gidan, Ma'aruf ya sauko, kafafunsa na biyo matattakalar a hankali yayin da yanayin hasken falon ke shaida masa yanayin tafiyar da lokaci yayi don har ya kammala shiryawa da komai bai kalli agogo ba tunda wayarsa ma a falon ya barta tun jiya.
Iskar dake faman kadawa a falon kasancewar bude windows da akayi ta shoga kada shi kotawanne Sangare yayin da idonsa ya sauka akan Amina dake tsaye daga can wajen kitchen tana zuba fulawa a cikin wani kwano.
Numfashinsa ya tsaya a kirjinsa a lokaci guda ganin kayan daje jikinta, rigarsa ce... Wata loose T-shirt dinsa da yawanci idan zaiyi ball yake saka ta... Fara ce ™al, ta tattare dogwayen hannunta zuwa can sama, kanta babu dankwali yayin da girman cikinta ya fito sosai a saman rigar... Kafafunta, wadannan siraran kafafun nata da a yanzu suka kumbura ™aWan suna yawo ta kasan dan karamin wandon da ta saka wanda bai kai gwiwa ba.
Ba wai yau ya fara ganinta da irin wannan shigar ba, kusan kullum ne, amma kusan kullum din sai zuciyarsa ta cika da wani irin abu mara misaltuwar da yake ganin kamar idan ya kira shi da sunan farin ciki kaWai bai yi masa adalci ba... a lissafinsa itace duniyarsa a yanzu, ita kadai ce wani abu da har cikin ransa yake ganinta a cikin rayuwarsa a matsayin wani abu da yake so har cikin zuciyarsa ba wani abu da ya karba a matsayin maye gurbi ko kuma don babu yadda zai yi ba.
Yana sonta ta sani, yana sonta saboda kyawawan halayenta, yana sonta saboda kyautatawar ta, sannan yana sonta saboda taimakonta wanda a kullum a kodayaushe yake ™ara ganinsa... Musamman a yanzu da yake ganin wata irin kulawarta wadda duk yadda zuciyarsa ke da tauri a yanzu kai tsaye take wucewa tana taSowa har can ™arshe.