← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 87

Sashe 12

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi Mami mun gama duk abinda zamu yi, munyi sallama lafiya kalau da shi har ma da wanda muka hadu dashi din, kowa ya hau mota muka rabu a wajen round about din nan, to ni nayo gaba kawai sai go slow ya tare ni kafin inyi nisa, anan naji wasu mashin da suka karaso suna hirar fadan da suka baro ana yi a baya, daya yana cewa wai ai ya san mai dukan sunansa Ma'aruf yana aiki tare damu a kamfani, naji yana bawa abokinsa labarin daya incident din a ya faru dashi da Daniel.

Da kyar na fita da go-slown nan na koma, kuma lokacin da naje ma har an raba su an dawo da Ma'aruf din motarsa mutane suna ta rike shi, ina masa magana amma kamar bai gane ni a lokacin ba, shine na kira Ishaq, sai da ya karaso sannan da kyar yasa shi ya yarda ya baro wajen, amma tunda naje abu daya yake ta fada wai a barshi ya karasa kashe mutumin yana da sakon da zai bashi."

Hajiya Kilishi tayi ajiyar zuciyar dake shaida tsananin damuwarta kafin tace.

"Kuma ko bayan fitar tasa ma munyi waya sai kuma na kira shi daga baya bai dauka ba."

"Ai Mami gabadaya wayoyin nasa ma da wallet da komai an kwashe, da yake bude motar kawai yayi ya fita a lokaci guda, to a wannan hayaniyar Sarayi suka samu dana suka kwashe komai, har mukullin motar sun tafi dashi, ita kanta motar ma don baza su iya dauka a lokacin bane."

"Tana ina yanzu?" Kai tsaye ta sake tambaya.

"Tana wajen, nasa wasu dai sun tura ta zuwa gefen titi, sannan na basu kudi su kwana a ciki saboda ban ma san inda za'a nemo spare key dinsa a dauke ta ba."

Duk wannan bayanin da Faruk ke yi, Amina dake zaune daga kujerar baya ta masu zaman jira a asibitin idanunta na manne ne da kayan Faruk din, farar shadda ce a jikinsa wadda gabadaya gabanta ya Saci da jini har zuwa kowanne hannun na rigar, zuciyarta na bugawa da motsin dake shaida girman laifinta da a yanzu take ganinsa karara, yayin da kalaman ke yawo a cikin kanta, tana yarda da kowacce kalma Waya bayan daya dake maimaitawa daga cikinsu.

Suna gaya mata cewa tabbas babu abinda dan adam zai samu a duniyar nan cikin sau™i, sannan kuma babu wani abu da mutum ya kamata ya fito yayi takama dashi a duniyar nan, don ana zuwa gabar da rayuwa ba zata baka zabi ba, zaka zo kayi wani abu da ko a mafarki ba zaka taSa tunanin aikata shi ba.

A baya zata rantse da Alkur'ani wajen karyata duk wanda zai zo ya shaida mata cewar zata iya aikata wani abu najamancin wannan, amma sai gashi a yanzu da hannunta ba tare da tursasawar kowa ba tayi abinda take jin tambarinsa ya Warfanu a zuciyarta ta hanyar da ba zai taba goguwa ba, don idan har za'a lissafa da sunanta a cikin wanda suke da kamasho a yau wajen faruwar wannan tashin hankalin, wajen zama sanadin da har mutane biyu ke kwance a asibiti, da kuma fitar jinin da take kallo har a jikin Faruk yanzu, to kuwa ta tabbata bata da kalaman da zasu wanke ta ko a gaban waye.

"Ka ce bai ji ciwon sosai ba ko?" Sai a wannan lokacin muryar Mamin ta shiga kunnenta, tana tambayar Faruk din da ya gama amsa wata waya wafda da alama fuk akan abinda ya shafi al'amarin ne.

Ya daga kansa sau daya.

"Ba sosai ba, na wancan mutumin ne yafi yawa, tun a can muke fatan Allah yasa bai fasa masa ido ba, don dukansa yayi tayi Mami, yana cewa a kyale shi ya kashe wai yana da sakon da zai bashi."

"Inalillahi wainna ilaihir raju'in... Bari na kira Baffa."

Ta faWa amon muryarta na fitowa da tsananin damuwar da babu wanda zai kasa shaida hakan, Amina ta bita da kallo baya ta juya ta bar wajen, kuma a wannan ya lokacin ne wata Nurse dake cikin Wakin da suke jira a kofarsa ta fito, hannunta dauke da farantin kayan dressing wanda ya cika fal da tarin auduga mai jini.

Idanun Amina ya sake bin hannunta da kallo har ta Sacewa ganinsu, abinda take ji a ranta yayi yawa a lokacin don haka sai kawai ta dam™e hannayenta biyu duka waje daya ta a shirin kore kwallar dake taruwa a idanunta. Munaya wadda suka taho tare da ita ta karaso daga fitar da tayi tana gama waya da Hajiya Maimunan da ta sake kira tana tambayar halin da ake ciki.

Taji sanda ta zauna a gefenta bayan tayi sallama da Hajiyan don haka ta juyo ta kalle ta.

"Za'a barmu mu ganshi yanzu?"

Sai ta girgiza kanta.

"Wallahi ban sani ba, amma ko sun ce ma ai inaga Mami ce kadai zata shiga."

Idon Amina ya nuna da mamaki kafin ta tambaya.

"Saboda me?"

"Saboda idan yana wannan yanayin bai kamata aje kusa dashi ba, Mami ta fada mana hakan tuntuni."

Bakin Amina ne ya bude a lokaci guda, mamakin dake idonta ya karu tana kallonta.

"Waye yake kula dashi kenan?"

"Yaya Ishaq ne, yawanci ma ba anan suke zama ba, akwai asibitin da yake ganin likita a London, can suke tafiya sai ya sami sauki tukunna. Amma lokaci kadan ne, da mood din nasa ya dawo zaki ga koma daidai."

A lokaci guda sai taji hankalinta ya kasa Waukan maganganu da Munayan ke faWa, kallonta kawai take yi yayin da take jin kamar kwakwalwarta na washewa, komai yana gogewa, don bata san yadda zata dauki wannan al'amarin ta ™ara akan sauran tarin abubuwan dake kanta ba.

Tunaninta ya kasa lissafa wace irin zuciya ce da Hajiya Kilishi, a kowanne irin ma'auni na duniya ta rasa a wanne iri za'a dora zuciya irin ta Kilishi tayi kama da ta mutane... Abubuwan da ta aikata a rayuwarta kaf idan za'a tara su waje Waya bata jin duk raunin imanin mutum a duniyar nan za'a sami wanda zai kalla bai ji zuciyarsa ta motsa ba.

Ta shigo cikin rayuwar mutanen nan da ™arfi da yaji, ta gurgunta mahaifiyarsa, ta ™wace shi daga gare ta, ta shuka tarin ™ananun abubuwa a cikin rayuwarsu da watakila ita kanta ba zata iya lissafawa ba, kuma duk da bata sani ba tana tunanin wata™ila itace sanadin ciwon nasa ma amma duk wannan bai ishe ta ba sai ta da™ile shi kuma a dukkan Sangare na kulawa irin wannan.

Bata san irin ciwon Ma'aruf ba, bata san komai game dashi ba, amma tayi imani cewar babu wani ciwo a duniyar nan da baya bukatar kulawa, ko da na hauka ne kuwa, to ta yaya za'a ce ayi nesa dashi a lokacin da yake tsananin bukatar kulawa?

Farkon zuwanta gidan tana ganin komai ne daidai, tana sha'awar mu'malarsu da komai sha™uwarsu na mata yawo a ido kodayaushe, amma sai a yanzu take ganin tarin ramukan dake gewaye dasu, sai yanzu take fahimtar cewa ba daidai komai yake tafiya ba kamar tunaninta.

Mutane ne su masu hankali, ´an boko kuma masu ilimi, amma Kilishi ta dauke su gabaWaya ta sanya a wani rami da babu mai iya haurowa, tana daga sama sai iya amon muryarta da kuma umarninta kawai suke ji, suna yin dukkan abinda ta furta ba tare da sun sani ba, ba tare da sun san ma me saka su ba. Taji zuciyarta ta matse a lokaci guda wani abu a cikin kanta yana gaya mata cewa wannnan yana daya daga cikin abubuwan da zata fara canjawa.

Tana jin Munayan na cigaba da waya da wata classmate dinta a lokacin, tana jin suna tattauna wani abu da ita ba fahimta take yi ba har sanda Mamin ta dawo, ta shiga gayawa Faruk da ya dawo cewar yaje gida ya canja kayansa, don mutanen dake wajen duk wanda zai wuce sai ya kalle shi, amma yace mata bari likitan ya fito tukunna su ji abinda zai ce, don har ga Allah baya jin zai iya tafiya ba tare da ya san halin da ma'aruf ke ciki ba.

Zuciyarsa ta yage har karshe tun daga lokacin da yaga yadda yake rike Ma'aruf a wajen nan yana yi madmsa magana amma babu alamun ya a gane shi alhsli yanzu-yanzun nan suka rabu lafiya, lokacin da al'smarin Daniel din nan ya faru a Office zuciyarsa tana bada wani kamashon laifin ga Daniel din, yana ganin har da laifinsa wajen tunzura Na'aruf din, amma abinda ya gani yau, yafi karfin dukkan wani tunaninsa.

Don haka yana tsaye har lokacin da Ishaq ya bude kofar wajen ya fito, kayan jikinsa kalar maroon ne amma duk da haka ana ganin inda ya samu nasa rabon Sacin jinin shima.

"Ishaq me ake ciki? Me suka ce?"

Mami ce ta fara jero tambayoyin cikin za™uwa. Kuma da muryarsa a hankali  kamar kodayaushe yace.

"Mami ki kwantar da hankalinki, ciwonsa ne dai ya tashi, dama munyi sa'a ne kwana biyu mood din nasa ya saisaita, kuma ban san me ya tada shi yanzu haka a lokaci guda ba. Sai dai na yi musu duk bayanin da suka bukata kuma sun bude file sun rubuta hakan, yanzu an bashi alluran bacci yana hutawa."

"Abinda zasu iya yi masa kenan?" Ta tambaya.

Ya gyada kansa.

"Mami ai ko irin magungunan nasa na basu dasu anan, guda daya kawai aka samu, so na gaya musu zamu taho da na wajenmu zuwa gobe su kara duba su tukunna, ina tunanin insha Allah iya nan komai zai tsaya, ba sai mun koma  London ba. Don allurar da suka yi masa ma iya ta zuwa gobe ce."

Hajiya Kilishi ta gyaWa kanta alamun fahimta sannan ta sake furta kalmar inalillahi wainna ilaihir raji'un fuskarta na nunaea da abinda za'a kashe wani akansa cewar damuwa ce.

"Likitan ya fita, yanzu zasu kaishi Wakin da zai huta, sunce nambar dakin C0-9."

Mamin ta gyaWa kanta.

"Zamu je mu ganshi kafin mu tafi...."

"Mami zan zauna."

Babu zato muryar Amina ta katse abinda Hajiyan Kilishin ke shirin fada. Dukkaninsu suka juyo suka kalle ta a lokaci guda, wani guntun mamaki ya haska a fuskar Hajiya Kilishi kafin tayi saurin kore shi da murmushi.
Chapter 12 · 0% Book details