← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 87

Sashe 41

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai kaje gida ka huta, gobe early in the morning mu san ta inda zamu fara kafin mu sami bayani daga IT members din, zan taho da ´an bayanan da na hada sai mu gani."

Ma'aruf ya gyaWa kansa sau biyu kafin yace.

"Gobe Abdurrahim zai dawo and I think ni da Ishaq zamu dauko shi daga airport, but insha Allah zamu yi komai."

"Wow! Allah ya kawo shi lafiya..." Cewar Faruk Win kafin ya cigaba.

"Da safe kafin in kira ka, munyi magana da mutanen Rotel&co (kamfanin da zasu yi aiki dashi na gaba) na gaya musu ranar da muka yi fixing zamu zauna dasu... Amma yanzu da wannan abubuwan da suka taso, ina ji kamar a kira su mu ™ara Wagawa..."

Ma'aruf, ya sake girgiza kansa.

"Let them, zamu iya Insha Allah Faruk, kar ka manta duk wannan fafutukar da muke yi Baffa bai sani ba, so abinda kawai zai sani shine idan muka tsayar da aikin mu, har zuwa karshen shekarar nan fa bamu da wata kwangila a gaba, wannan ce damu kawai, may be idan muka yi aiki mai kyau, zamu iya sake wani contract da wasu."

"Haka ne."

Cewar Faruk Win kafin wayarsa ta fara ™ara, ya dauka ya kara a kunnensa ya shiga waya da makanikensa wanda zai zo ta dauki motarsa data mutu a ™ofar Prison din nan da suka fara zuwa.

"Canja ta zanyi kawai Aminu, kawai dai a fara gyarawa mu gani tukunna..."

Faruk Win ya  shiga magana, sai kawai ya dun™ule hannunsa guda dunkule akan bakinsa yayin da har a lokacin yake kallon titi.

Wani iri zuciyarsa ke masa, wani iri yake ji a dukkanin jikinsa gaba daya, kowannan tukin ymda yake yi ji yake kawai kanar a cikin wani zagaye yake tafiya da idan suka yi gaba suna sake, tunanimsa yq kasa hango masa waye wannan Awwalun da kuma dalilinsa na kassara su, yadda yake amfani da kwakwalwa dana kudinsa don ganin kawai ys tarwatsa su.

Zai rantse har da Allah dalilin wannan abin bai taru kawai akan kuWi ba, dole akwai wani labarin dake ™ar™ashin komai.

A haka har suka karasa kofar gidan Faruk din ya sauke shi.

"Ka huta sosai B dan Allah idan kaje gida, ka barwa gobe komai, let your mind rest."

Abinda Faruk din ya fada kenan bayan ya fita ya tsaya daga wajen motar, kuma da ya kalle shi sai yaga kamar yana kallon mudubi ne wanda ke hasko masa irin tarin gajiyar dake tattare dasu, idanun Faruk din kadai sun kada kamar nasa, don banda ruwan da suka siya bayan sunyi salkar La'asar babu wani abu da ya shiga cikinsu a tsayin ranar yau din.

Sai dai kafin ya buWe baki ya bashi amsa, kofar falon gidan daga can barandar dake fuskantarsu ta buWe, yara biyu mace da namiji suka fito da gudu suna ihun.

"Daddy! Daddy!"

Kafin matarsa ta baiyana itama ri™e da hannun karamin Wansu Aarif wanda ya fara tafiya, sai kawai yayi masa murmushi sannan ya ja motar zuwa can gate inda maigadin dake tsaye bai rufe ba kasancewar ya gaya masa yanzu zai iso. Da a yau bashi da inda zai je ya huta gajiyarsa kamar Faruk, baya jin zai iya hana ciwonsa tashi kotawacce hanya.

*

Siraran hannun Amina suka kwankwasa kofar bandakin a hankali, idanunta na kallon tiririn daje saman ™ofar inda wajen glass ne maimaikon katakon dake kasa.

"Come in..."

Muryar Ma'aruf ta faWa daga ciki, sautinta ya fito lazily kamar yadda yanayinsa yake tun lokacin da ya shigo, ta tsaya kamar ba zata bude ba sai kuma tasa hannunta daya da baya ri™e da Wan karamin towel din da ta ri™o, ta murda handle din a hankali, kofar ta rabu da wata ´ar siririyar hanya amma sai ta kasa karasa buWewa, ta tsaya rike da handle din kawai tana shakar daddadan dimin dake fitowa hade da ™anshin sabulunsu.

Baifi sakanni biyar ba Ma'aruf yaja kofar daga ciki ya buWe ta gabadaya, yana tsaye daga shi sai towel din dake jikinsa na wankan da yayi, gashin kansa a jike yake gabadaya ya barbaje wasu kuma sun manne da fatarsa, tana kallon idanunsa da suke a lumshe sosai don kusan rabinsu je kawai a buWe kanar mai jin bacci, sai kawai ta karaso ta rufe takun biyun dake tsakaninsu, tasa towel din hannunta akansa sannan ta shiga goge masa gashin a hankali da duka hannunta biyu.

Ya rufe idanunsa duka biyun a lokaci guda da hannayensa suka zagaye ™ugunta yana rike ta sosai a jikinsa... Yana jin yadda siraran yatsunta ke motsi a cikin gashin nasa ta jikin towel Win. Sai kawai tayi Wage da kafafunta ta ™ara tsawo daidai shi sannan ta dora goshinta akan nasa, ta janyo hannayenta daga saman towel din ta zura su ta kasan sa, numfashinsa ya kara nauyi akan fuskarta sanda yatsun nata suka shiga cikin gashinsa gabaWaya, tana jin yadda ya ™ara ri™e ta a jikinsa, Wumin jikin nasa da kuma ™amshin sabulun na mamaye ta gabaWaya.

"Are you feeling better?"

Muryarta ta fito a hankali, a hankalin da shi kansa da yake jikinta can kasa yaji ta sosai.

"Abinda nake ji yafi karfin Better Babydoll, you are healing me..."

Kalaman suka sata murmushi, suka kuma bata kwarin gwiwar yin Wage da kafafunta a hankali kafin tayi kissing dinsa, bai ce komai ba da farko sai da yaji da gaske take sannan bakinsa ya furta.

"Damn it!"

Da haka ya sake ri™e ta sosai a jikinsa yana tuna mata da banbancin dake tsakanin abinda zata iya da kuma wanda shi zai yi, tsawon mintuna kafin ta janye zuwa baya a hankali tana kallonsa.

"I love you." Muryarta ta fito kamar wadda ta tsaya a tsakiyar gudu.

"I love you too Noor."

Ya fada tasa muryar hankali kwance. Sai tayi murmushi mai fadi jin sabon sunan da ta samu kafin a hankali ta janye towel din daga kansa ya fado zuwa wuyansa sannan ta saka hannunta na dama ta shiga gyara gashinsa zuwa baya a hankali.

"Da zan iya tsaida lokaci zan tsayar da wannan daren yayi ta sake faruwa Sugar, har sai ka dawo daidai, sai na tafiyar da gajiya da kuma damuwarka gabadaya, this is our own happy place, ni da kai kawai."

Ta fada idanunta na kan gashin nasa da kuma yadda take gyara shi, ya sake rike ta a hannunsa kafin ya gyada kansa a hankali sannan muryarsa ta fito.

"Nima haka BabyDoll, I wanna see the sun rise on your skin kullum, amma kar ki damu da nayi settling abubuwan da ke gabana we're going on a honeymoon, somewhere far away, just me and you." (Da na gama da abubuwan da dake gabana zamu tafi yawon amarci, wani waje mai nisa daga ni sai ke kawai.)

Ta gyada kanta tana kallonsa da murmurshi a fuskarta, sai ya sake cewa.

"Yaya kika bar su Amma?"

Su Amma, sunan ya tuna mata da gida da kuma dukkan abinda ya faru a can, sai taga kamar taje wata duniya ne ta dawo, rayuwarta a can da kuma a wannan gidan tana da tarin banbanci, a gidansu a gaban iyayenta da kuma ´anuwanta, ita Amina ce, Aminar da kowa ya sani Aminar da ita kanta ta san kanta a ita, amma idan ta dawo gidan nan sai taji ta koma wata daban, wata suruka a gidan ´an gayu da kuma Wan gayun mijin dake sawa taji kamar sune ma'aurata mafi sa'a a duniya, bata jin kanta a komai sai a matsayin Babydoll din da yake kiranta. Fuskar Hajiya Kilishi ce kawai mai ruguzo da ita tana tuna mata cewa ba'a aljanar duniya take ba.

Amma kuma bayan hakan a yanzu, karo na farko sai taji cewa kamar an ™ulla wani zare ne da ya haWe waccan duniyar tata da wannan, kalaman Amma, bata tabbatar ba, ba wai bata yarda ba... Kawai kokwanto ne a cikin kanta har yanzu...

Kokwanton da ta kasance a cikinsa tun daga wancan lokacin, don bata sake cewa Amma komai ba, basu sake maganar ba gar suka taho, kawai dai kowa ya san yanayinta ya canja, tunanin ya cika kanta, tunanin da a cikinsa babu komai sai na yadda zata gayawa Ma'aruf hakan, fon a tsarin da tayi, a tsarin da tayi na kokarin boyewa kowa, kowan da Hajiya Kilishi ta zamo sila babu Ma'aruf, hasalima shine daya hannun da zai talkafa mata wajen cimma dukkan abinda ta tsara din, tsarin da ko Amma bata san shi ba...

Amma kuma tun kafin tazo gaban nasa, sai ta rasa ta yadda ta yadda zata iya harhado kalaman da zasu tashi ma'anar da zata gaya masa, ta kasa tunanin konai, tana jin kwakwalarta dama zuciyarta fayau, don haka ko a yanzun babu abinda ta iya cewa sai kawai ta shiga bashi labarin gidan nasu da kuma yadda Hamida ta sake da ´anuwanta.

Har ya shirya suka koma falo inda ya cika cikinsa da abincinta kafin Hamida ta cika kansa da nata surutun, har suka yi bacci, tana rungume a jikinsa tana jin numfashinsa a hankali kafin ya koma mai nauyi alamun gajiyar dake jikinsa tafi ™arfinsa.

Har Asuba da tayi, ya fita masallaci ya dawo ya same ta akan tata sallayar, tana zaune gaban Mahaliccin data idar da ibadarta yayin da zuciyarta ke karanto tarin addu'o'in da basu da ™arshe.

Daga bayanta ya tsugunna akan gwiyoyinsa, sannan ya zuro hannayensa duma biyu ya kara su a bayan nata, ya tsayar dasu yadda ta yi wa nata wajen addu'ar sannan ya Wora haSarsa a saman kanta.

Tayi murmushi a hankali tana jin ™amshin sabon turaren da ya fesa a jikin sallayarta na shigar mata har cikin kai, ™amshin mai sanyi ne, amma ita tana jin ™arfinsa har cikin kanta, ta kai ™arshe a addu'ar kuma yana ganin ta motsa hannunsa ya haWe su da nasa gabaWaya suka tafi kan fuskar tata.

"Ameen ya Allah Noor."

Ya faWa daga saman kan nata sannan ya juyo da ita gabaWaya tana fuskantarsa, a lokacin ne ta rasa dukkan wani tunanin kanta, yadda yake kallonta a cikin duhun dakin ya warware dukkan wani lissafinta,  a lokacin ne bakinta ya furta abinda ya zama mafarin bude wata sabuwar rayuwa a tsakaninsu.

"Ma'aruf..."
Chapter 41 · 0% Book details