← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 87

Sashe 39

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tun daga ranar da ya kawo min hodar nan daga lagos bai sake ce min komai ba nima kuma ban kira shi ba, dukkan abinda yake ciki ina jinsa ne ta hanyar wannan Sadik din dana tura ya zama abokinsa a kwanakin baya, saboda haka na riga na daWe da gama shirya masa, yanzu jira kawai nake yi ya nunawa Sadik inda ya tara Cd's din da yake Waukar muryarta, ya riga ya ganoinda computers din suke, da mun samu Cd's din, zan sa ya ™ona komai ne gabaWaya sannan inje in fuskance shi.

Zan gaya masa dukkan shirinsa da na san yana yi da kuma yadda akayi na kama shi, kafin in aiwatar da nufi na akansa."

"Me zaki yi masa?"

Kai tsaye Salsmatun ta tambaya tana wulli da wani leshi dake kan cinyarta zuwa cikin kayan dake baje a dakin.

"Haukata shi zanyi Salamatu, ba zan kashe shi ba, Haukata Awwalu zanyi ta yadda zai kare rayuwarsa yana biyan bashin cutar da yaso yayi min."

Salamatu ta gyada kanta tana taSe baki kafin tace.

"Shi kuma Sadik din fa?"

Kilishi tayi shiru tana nazari kafin tace.

"Sadik irin mutanen da basu da ra'ayin kansu ne Salamatu, kuma daga Ghana yake kin sani saboda haka wani kaso kawai zan bashi ya koma kasar su, da ya koma ya cigaba da shaye-shayensa shikenan bani da wata matsala dashi na sani."

Salamatu ta gyada kanta tana murmushi sannan ta sake cewa."

"Victoria Island dai na can na jiranki Kilishi, kafin ki kammala komai na tabbata an gama gine-ginen nan."

Girgiza kanta kawai Kilishi tayi kafin tace.

"Bar wannan zancen tukunna yanzu Salamatu, jikina ya bani cewar Ma'aruf ya dage akan binciken kamfanin nan nasu, bai ce dani komai ba amma na fahimci hakan ne kawai, shi yasa na tsayar da komai nake son inyi in gama da Awwalu akan kari.

Tunda kin san indai har sun sami mutanen nan duk abinda zasu samo zai kaisu ne kawai ga Awwalun tunda shi kadai suka sani, kin ga idan na kammala abinda zanyi dashi kafin su nemo shi, zasu je su same shi ne a haukace, haukan da ba zai taSa warkewa ba. Daga nan sai in dawo in fuskanci batun yarinyar nan da kuma Baffa, yadda zan tsara mutuwarsa a ranar da kudi na gaba zasu shigo kamfanin."

Dariyar da Hajiya Salamatu ta kyalkyale da ita tana debo wani zagi wata iriyar dariya ce da babu shiri Kilishin ta shiga taya ta itama, muryoyinsu suka karaWe falon cikin wani irin amo mai Wauke da tsananin nishadi da kuma ta™ama, ta™amar da a cikinta Kilishin ke jin kanta zuwa wani mataki da take jin cewa bata da takwara a duniyar nan.

Abinda bata sani ba shine, al™alami ya riga ya bushe akan wata ™adddara da zata wanzu cikin kwanakin da take lissafawa kanta da wani labari da yasha banban da wasi™ar da zuciyarta ke biya mata!

Kuma zaren labarin ya fara ne a daidai wannan lokacin kuma a cikin wannan dakin!

***

_Wanne irin sirri kuke tunanin Hajiya Mardiyya na Soyewa akan Jawad? Kuna tunanin sirrin yana da alaka da halayyarsa?_

_Sannan ta ina kuke tunanin labarin Jawad da Zainab yana da ala™a da Sangaren su Kilishi?_=ØÞ

_Ma'aruf ya tattaro kowanne Sangare na matsalarsa, kuna tunanin ya fara taka matakin nasara?_

_Ga kuma tsarin da Hajiya Kilishi ke yi tun kafin su kai ga ™arshen binciken nasu, matar nan A ce!_=ØÞ

_Amma ya kuke tunanin hakan zai kaya??_

_Ina gaya muku BabyDoll din Sugar ta tanadar mana wani surprise mai daWi a babi na gaba._ýÿýÿ>ØpÝ>ØpÝ

_Muje zuwa!_=ØÞ

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:56 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*14*

*Tarin Addu'o'in ku da kuma fatanku na alkhairi na Waya daga cikin abinda ya farfaWo dani, bani da bakin da zan ce Nagode, don ina ji kamar kalmar tayi kadan in dora ta a mizanin goriyar tawa... sai dai ince Allahu ya saka muku da alkhairi ya kyautata rayuwarku ta duniya da kuma lahira.*

*Nagode da tarin ™auna.*

~~~~~~

_I'll hold you when things go wrong..._
_I'll be with you from dusk till dawn..._
_Baby, I'm right here... -ZaynMalik & Sia._

***

Hannun Inna dake ri™e da cokali ya juya wani kwadon zogalen da yaji kuli-kuli da kuma su tumatir daga can tsakar gida inda take zaune yayin da a lokaci guda da Amina dake zaune a gWaki ta sauke wayar hannunta daga kunnenta.

Idonta ya tsaya akan Amman yayin da kalamanta na yau suka shiga dawowa cikin kanta. A dazu bayan fitar Baba, sun fi ™arfin awa guda suna magana, magana sosai irin wadda tun bayan tafiyarta basu yi irinta ba kasancewar wannan ba'a waya bane ba, sun sake tattauna tarin abubuwan da suka gudana a baya sannan ta gaya mata cewar ta cigaba da rike Hamida hannu biyu kafin ta ga abinda su Rukayya ke shirin sake shiryawa, wanda har a yanzu ta jaddada mata da cewar kar ta bari Ma'aruf ya sani.

"... Ki cigaba da tafiyar da al'amarin gidanki kan turba mai kyau Amina, daga shi har yarinyar kar ki basu kokwanton wani abu yana faruwa daban tare dake, ki barshi yaji da matsalar wajen aikinsa da yake fuskanta yanzu, kuma kar ki taSa tambayarsa wani abu idan har ba shi ya gaya miki ba, don tambaya hanya ce mai ce mi™ak™iya ga zargi... Don haka ki kyale shi da dukkan wata tambaya da ta shafi binciken da yake yi, kwanciyar hankali shi yafi bu™ata daga gare ki yanzu, idan har muna bu™atar wani bayanin, akwai hanyar da zamu samu abinda muke nema daga gare shi, zai faWa miki duk abinda kike so ba sai ma kin tambaya ba."

Tana tuna yadda ta dinga juya maganganun a lokacin, yadda Amma ta gata mata dukksn hanyoyin da mace zata bi idan har tana son samun amsar wani abu daga wajen mijinta, ba tare da shi kansa ya fahimci tambayar tata da kuma abinda take nema ba.

"Rayuwar mace gabaWaya dabara ce da kuma kissa Amina, idan da har bayan ibada kowacce mace zata Wauki waWannan abubuwan guda biyu ta ri™e su a kowanne fanni na rayuwarta, da tabbas mata da yawa zasu sami rabin aljanarsu ta duniya."

"Kin san ranar nan kuwa Jamila tazo nemanki?"

Maryam dake zaune a gefenta ri™e da Hamida wadda ta Wane kan cinyarta tana zana mata fulawa da abin Rani ja kan fararen hannunta ta fada.

Amina ta kalle ta, tana tuno Jamilan da take fada, wata ™awarta ce da a islamiyya ce da babu gaira ba dalili ta tsiri daina yi mata magana, har Amma sai da ta shiga cikin al'amarin a lokacin wajen tambayarta abinda ya faru amma tace babu komai.

"Da gaske? Me tace kuma?"

"Wai taji labari ance kinyi aure ne shine tazo yin murna, wai a rakata inda kike ku gaisa."

Amina tayi murmushi tabya jinjina kanta alamun mamaki kafin Maryam din ta cigaba.

"Amma tace wai ai sai ta saka rana tazo a raka ta, shine ta karbi nambar wayar Amman wai zata kira, ni kuwa na bata wrong number, ranar da ta gaji ta tako ™afarta tazo, kwanciya zanyi ince bani da lafiya?"

"Saboda me?" Amina ta tambaya tana dariya.

"Dan Allah ki rako ta ko kuma ki bata namba ta, kinga ai a kawo karshen gabar tata."

Maryam ta girgiza kanta tace.

"Wallahi Yaya wannan yarinyar ba mutunci ne da ita ba, haka kurum taje ta jawo miki wata matsalar..."

"Haba dai, ai bata isa ta jawo min wani abu da yafi karfin wanda nake ciki ba Maryam, tunaninta bai isa yafi na mutanen da nake tare dasu ba."

Ta fadi hakan fuskar Kilishi na haskawa a cikin kanta.

"Bata sake yi kiranki ba har yanzu?"

A dazu da suke magana da Amma haka ta tambaye ta, ta girgiza kanta kafin tace.

"Bata sake yi min magaba ba tun daga lokacin Amma, na kula kamar kwana biyu hankalinta ya rabu ne kan wani abun, tana yawan fita sannan bata maida hankali kan abubuwan gidan sosai."

Amman ta gyada kanta a lokacin sannan tace.

"Watakila ta fahimci binciken da suke yi ya fara doso ta ne, watakila kuma tana da tsarin wasu abubuwan bayan sha'anin yarinyar shi yasa tayi miki shiru.

Kilishi tana da tsari, ta san me take yi... Wasu abubuwan take saitawa kafin ta waiwaye ki, ba zata baki aikin a lokacin da ta san hankalinta baya kanki sosai ba, watakila kuma tsuntsu biyu take neman jifa da dutse Waya, abu biyu zata haWa a lokaci guda. Ba lallai ki iya sani ba, amma idan kin ga alamar wani abu ki gaya min watakila zamu iya samo wani abun a cikin takunta."

Ta gyada kanta a lokacin sannan ta Wago ta kalle ta sosai kafin tayi tambayar da ta daWe tana ci mata rai a zuciyarta.

"Amma idan har ta kawo maganin ta yaya zanyi amfani dashi? Lokacin da muka yi magana kince komai zai faru amma kuma ba abinda zai faru? Kince a idonta kawai Hamidan zata makance amma ba a gaske ba."

Murmushin da Amman tayi mai fadi ne a lokacin kafin tace.

"Kar ki damu, har na fara wannan shirin Amina, na gaya miki takunta zamu Wauka kamar yadda muka fara yanzu, zamu shammace ta ne ta hanyar da take shammatar mutane, ta hanyar da take ganin tata ce itace mai ikonta, don haka ki bari lokacin yazo zaki san komai, nafi so a yanzu ki tsaida hankalinki akan gidanki tukunna, nan ne Sangare mai girman da yafi kowanne bukatar tallafawarki a yanzu."

"Wani abu kike ciki yanzu a gidan?"

Tambayar Maryam ta dawo da ita duniyar zahiri, sai tayi saurin girgiza kanta.

"Ina nufin tunaninta bai isa yafi na mutanen gidan da yanayin wayewarsu da komai ba, na gaya miki yadda su Samiran nan suke, yanayin rayuwarsu ta banbanta da namu ta hanyoyi da yawa."

Ba tare da ta fahimci komai ba Maryam tace.
Chapter 39 · 0% Book details