← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 87

Sashe 57

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Sadiya tayi bayanin haka ce ta faru dasu, a ranar da suka yi karyar na™udarta ta tashi a ranar suka Wauki mota su biyu kawai ita ke tu™awa suka nufi can wannan ™auyen da a lokacin ake ce masa Yakura, amma a yanzu ya koma Garun Albasu, anan suka sami matar da babu wani bata lokaci suka bata kudinta ita kuma ta basu yaro, inda murnarsu ta ™aru ganin namiji ne.

Daga nan suka kama hanya suka dawo da cewar ta haihu kuma har an sallamo ta daga asibiti, kuma babu wanda ya zarge su aka shiga murna da shagalin suna... Kuma tun daga wannan lokacin suka binne wannan abin a tsakaninsu su biyu kawai ta yadda ko sauran ´anuwansu basu taSa sani ba sai a yanzu da ™waryar da suke ri™e da ita ta faWi har kasa ta tarwatse.

Yana iya jin muryar Hajiya Mardiyyan a cikin kansa har yanzu, yana jin yadda take magiya da kuma kukan gayawa Alhaji Bashir cewa wallahi sauran ™annensa mata da ta haifa shekaru biyar bayan shi ´a´an su ne na cikinta, ita da ´aruwarta sunyi garaje ne kawai na tunanin bata haihuwa na tsawon shekaru bakwai kafin lokacin da ta sami cikinta na gaske.

Ya rufe idanunsa a hankali ya buWe su kafin ya amsawa Aunty Sadiya da abinda take jira.

"Ina hanyar Kaduna..."

"Kaduna?"

Ta tambaya a lokaci guda.

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un.... Haba Jawad me yasa zaka kama hanya da sassafen nan? Tun Wazu muke nemanka, ina zaka tafi? A™alla ka saurare mu mana..."

Ina zai tafi? Ta yaya zai cigaba da zama a gidan nan alhali tun a daren jiya labarin komai ya zagaye gidan daga bakin Hajiya Yagana da bashi da tsntamar cewar ta ji dukkan tattaunawar da akayi.

Ta yaya zai kara zama yana kallon idanun kowa ba tare da wani bayani mai gamsarwa da zai iya kare kansa a wajen su ba? Bai ce ba zai dawo ba don ko Alhaji Bashir da yaje yiwa sallama abinda ya gaya masa shine zai dawo bayan ya sami ´anuwansa, kuma shi bai hana shi ba ko yace masa yayi garaje sai su....?

"Ka yiwa Allah da ma'aikinsa ka dawo Jawad, ka sani a cikinmu babu wanda ta taba cutarka, kuma bamu yi komai don mu cuce ka ba, to me yasa ba zaka saurare mu ba Jawad? Me yasa ko sau Waya ba zaka ji daga bakin mahaifiyarka ba... Tunda komai ya fito fili ka tunanin zamu sake Soye maka wani abu ne?"

Ya girgiza kansa a hankali kamar tana kallonsa.

"Kar ku damu Aunty Sadiya zan dawo...."

Abinda ya faWa kenan kawai sannan yatsun hannunsa suka ni kashe kiran, sai dai muryarta ta sake kwararowa kafin hakan.

"Ina wannan yarinyar Jawad? Ina Zainab?"

"Tana tare dani."

Amsar ta fito cikin tattausan amon muryarsa da tsabar ruWani da kuma tashin hankalin da yake ciki ya haifar dashi.

Kuma daga shi har Zainab Win, suna jin salatin da Aunty Sadiyan ta ruWe dashi kafin ya kashe wayar.

Šib kiran ya katse a kunnen Zainab, yana sake tonawa kanta sautin zuciyarta dake bugawa a ™irjinta, kuma bata juyo ba, bata juyo ta kalle shi ba, kanta na sunkuye tana kallon yatsunta dake girgizawa akan cinyoyinta, nemanta suke yi ita ta sani, shi tasa ko baccinta na jiya ta cika da mafarkai masu nauyi... Watakila gani suke tana da hannu a duk abinda Jawad ke yi.

Kuma ta sani ko a gaba suka sa ta bata da yadda zata iya yi musu bayanin cewa bata san komai ba, bata san me yake yi ba ko kuma su abinda suke yi, kamar koyaushe a rayuwarta babu wanda ya taba bata zabi a rayuwarta, komai faruwa kawai yake a gaban idanunta yayin da take jin tamkar an rufe bakinta an kuma daure hannayenta, kamar tana tsakiyar wani waje ne da bata da mafita kotawanne Sangare,kamar tana cikin kwale-kwale ne a tsakiyar teku ta yadda ruwa ya zagaye kowanne bangarenta... Don haka bata da wani zaSi illa ta zuba ido taga yadda Allah yayi da ita kawai.

Tana ji sanda ™arar wani kiran ta cika motar, sannan taji sanda muryar wani namiji ta amsa.

"Oga sir.."

Shine abinda ya fara faWa bayan sallama. Ta gefen idonta taga sanda ya dafe kansa yana yin baya dashi kafin ya amsa.

"Sulaiman ina ga a location dina saura bai fi minti biyar ba na kusa isa zuwa garin, ka tabbata mutumin da zaka hada ni dashi Wi yana nan a gari?"

Daga cikin wayar Sulaiman din yace.

"Yana nan Yallabai, bai fi minti biyar ba .a da muka yace min ya riga ya fito bakin titi yana jiranka, sunansa Nura, na gaya masa kalar motarka to da ka iso zai gane ka kawai."

Ya gyaWa kansa sau biyu yana faWin.

"Shikenan, nagode."

Sannan ya kashe wayar. Taji ™arar sanda ya ajiye ta a gefen dake tsakaninsu kafin abinda bata yi zato ba ya biyo baya...

"Zainab zaki ci wani abu?"

Muryarsa a hankali ta fito,cikin amon dake shaida mata cewa nasa ne, ya dawo daidai ba kamar Wazu da ta tabbata baya cikin hayyacinsa ba.

Sai kawai ta rufe idanunta a hankali tana jin Wumin kwalla na kokarin cika su.

"Kina jin yunwa?"

Ya ™ara tambaya a hankali, sai ta girgiza kanta a hankalin itama ba tare da tace komai ba, shiru ya sake ratsa motar na wasu sakanni kafin ya kunna ta su sake hawa kan titin, kuna tafiya yar kadan ta isar dasu cikin wani tsohon gidan mai da ya koma kasuwa kuma maciyar mutanen hanya, wajen da ya hada da tarin kantinan da kusan duk wani abinda matafiyi ke bukata zai samu.

Bai kashe motar ba ya barta a kunne har da mukullin a jiki sannan ya bude ™ofar motar ya fita, Zainab ta bishi da kallo ta cikin mutanen dake wajen, kayan jikinsa wani kalar yadi ne mai ruwan toka, tafiyarsa kadai ta banbanta da tarin mutanen wajen har zuwa sanda ya bacewa ganinta,  Idonta ya shiga yiwa cikin gidan man kallon sani amma nan da nan ta ™aryata kanta, ta dawo da idonta ya dawo kan mukullin motar.

Zuciyarta ta ayyana mata yadda zata koma mazaunin direban ta murda shi, da zarar ta tashi sai tashi sai ta juya kanta ta fita daga wajen, ta komawa dukkan hanyar da suka biyo a baya har zuwa cikin gidansu. Wata™ila idan tayi hakan zata iya wanke kanta a wajen Hajiya Mardiyya da kuma Deluwa, watakila zasu iya yafe laifinta su mayar da ita gida wajen mahaifiyarta komai ya ™are, komai... Har dashi kenan? Wani bari na zuciyarta ya ayyana mata, kuma rashin sanin amsar yasa ta haWiye wani abu a ma™ogwaronta.

Cikin abinda yake ™asa da minti goma Jawad ya dawo har a lokacin tana sake-saken a ranta, bata ko ganshi ba sai ji tayi an buWe ™ofar gefenta, kuma kafin ta dago ya ajiye tarin ledojin hannunsa akan cinyarta sannan ya mayar da kofar ya rufe.

Idonta yabi ledojin da kallo tana jin kanshin kayan abinci kala -kaka da kuma nauyin robobin ruwa dana lemo da suke cikin tasu ledar daban, a cikin wata ´ar karamar leda fara, ta gano magunguna, irin magungunan da ya siyo mata jiya sak wanda suka bari a falon Sangarensa.

Mamaki ya kamata, tsananin mamakin wani irin mutum ne Jawad da kuma halayensa, sai dai wannan mamakin bai kai koi'ina ba sai a lokacin da suka isa kofar shiga garinsu 'Garun Albasu' minti biyar bayan barinsu daga gidan man nan, a lokacin da ta Wago kanta jin ya rage gudu suna kokarin sauka daga titi, lokacin da ta Wago da idanunta suka sauka akan kasuwar ™auyensu ta bakin titi kafin ka dangane da cikin garin, da kuma fuskar Wanuwanta Nura, (Wan mijin mahaifiyarta) yana washe baki yana tunkaro motar tasu da saurinsa.

A wannan lokacin abinda taji yayi kama da fadowar zuciyarta a cikin kirjinta, taji kamar ta faWo ne ta fice ta ™asan motar, tayoyin baya kuma suka bi ta kanta suka tarwatsa ta, jininta ya fallatsa a koina na jikin motar!

***

A cikin harabar tsakar gidan, mata ne kala-kala da kuma yara dake wasan su, matan na ayyukansu na yau da kullum wanda ya haWa da girke da kuma surfen hatsi kala-kala, kusan rabinsu na goye ne da ™ananun yara a bayansu yayin da suturarsu kaWai idan ka kalla, banda gini kasan dake zagaye da tsakar gidan zai shaida maka cewa mutanen karkara ne.

A wannan lokacin ne kuma sallamar wani dattijo ta karaWe koina a tsakar gidan, sau daya ya furta sallamar amma a lokaci guda yanayin wajen ya canja, yara suka mike a guje suka nufi kasan rumfar dake barandar dakuna suka taru waje daya gabadayansu yayin da matan kowacce ta mike tsaye suna amsawa, yan tsofaffin dake zaune suna aikin busa ne jadai basu mike ba.

Mutumin ya shigo sanye da vabbar rogarsa wadda ta banbanta da yar ciki, hular kansa mai kyau ce wadda dattin dake tattare da ita ya boye hakan.

"Ina Talatu? Talatu, Talatu....!"

Kakkaurar muryar tasa ta fada yana karasowar ciki. Matar dake amsa sunan Talatun tayi saurin sakin itace da ta debobdon kara wutar girkinta tayo gaba tana faWin.

"Gani Malam.."

Kuma tsaye ya nuna ta yana fadin.

"Wato Talatu rashin mutincin naki bai kai karshe ba dama? Sakin da na dannewa zuciyata ban yi miki wancan karon ba shi kike nema?"

Ba shiri Talatun ta dafe goyon ´ar dake bayanta sakamakon faWuwar gaban da taji ta ratsa har ta bayanta tana shirin kwance goyon.

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un Malam me kuma ya faru? Wallahi Malam vabu abinda na kara yi."

"Babu abinda kika kara yi? Karya nake yi miki kenan? Ko kuma shi wancan ™aton Gardin  da Nura Wan gidan Malam Sadi ya rako min shi har majalisa suka zo nema ki dake ™aryar suke? Dududu kwana nawa kenan da kika shigar min da mutum har Wakin aurenki? amma ace duk uw*r tarzomar da aka sha baki hankalta ba? Allah wadaran auren jinin Hanne wallahi...!"

Ya fada muryarsa na dagawa, dagawar da tasa sauran matan dake gefe murmusawa suna kallon junansu. Talatu ta sake talkafe goyon bayanta tana girgiza kanta.
Chapter 57 · 0% Book details