← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 87

Sashe 18

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kilishi ta gyada kanta tana daukan cake guda a cikin farantin fake gabansu.

"Ni kaina na sani Salamatu ina da laushi fiye da dukkan tunanin mai zato, laushin da zan iya ruWar ko waye a duniyar nan ya dulmiya zuwa cikin tarko na da bashi da ™arshe. Shi yasa tun farko na gaya miki cewa ita kanta yarinyar na shirya mata, kuma gashi tun amba'aje koina bakan ta tabbata r miki da abinda na fada cewar babu wata mace da ta isa tayi tasiri a zuciyar Ma'aruf sama dani, a yanzu na gama yi mata shirin da ba zata taSa iya bari Ma'aruf din yayi tasiri a zuciyarta ba balle har ta iya tsallake umarni na.

Na tsorata ta, kuma ta gama tsoratar akan al'amarinsa, zata ganshi ne kamar yadda na haska mata shi, zata ganshi a matsayin wani abu daban ba mijin aure ba, don ko ciki bata isa Wauka ba."

Salamatu tayi dariya.

"Na san zaki aika ai Kilishi, kawai dai a farko ne nayi tunanin ke kanki baki gana sanin halin yarinyar ba na jiye miki wannan tsoron, amma tunda har kin taka matakin nasara akanta tun ba'a je koina ba, mu cigaba a inda muka tsaya, ki gaya min ta yadda kika sami kudaden nan."

Kilishi ta daga kanta sau daya sannan ta cigaba da magana.

"Kwantar dashi nayi kamar yadda na gaya miki sannan Awwalu ya sanya min yaran sa suka fara binsa tun daga lokacin da ya bar gida, muka sa wani yaje ya daki motarsa sannan kuma ya zage shi don in tabbatar idan har yarinyar nan ta bashi maganin, ilai kuwa nan da nan mood dinsa ya rikice ya kama dukan mutumin, a wannan hayaniyar wasu da muka saka suka samo min wallet dinsa har dama wayoyinsa wanda muka yi amfani dasu."

Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.

"Ban gane ba, kuka yi amfani dasu ta yaya?"

Kilishi ta ajiye cake din da har a lokacin bata kaishi baki ba, ta gyara zamanta sosai tana kallonta sannan tace.

"Ma'aruf yana da wayo da dabara sosai Salamatu, na sha gaya miki tun bai kai haka ba. Don haka bayan sun gama wannan bincijen shi da wannan abokin aikin nasa, sun gano cewar tabbas alert din da suka samu na bogi ne, sai ya canja shawara, yace wannan karon cash zai karbi kuWi ta hannun mutanen da suka yiwa aiki ba ta account ba kuma da kansa yadda zai je ya saka a banki don kar a sami ma wata matsala ba.

Abinda bai sani ba shine, tunanin Kilishi da nasa ba daya bane, a cikin maganganunsa kawai na gane abinda yake shirin aikawmtawa tun kagin ma su gama aikin a saka ranar karbar kudin, shi yasa na tsara komai, na tsara iya kwanakin da zasu ishe ni har in tunkari Amina ta gama shawararta tazo ta amince dani da kuma iya kwanakin da zata sanya masa gubar har ya kwanta kafin ranar.

Kuma na sami komai Salamatu, I.D cards da kuma wayar Ma'aruf Win kaWai muka nunawa mutanen nan da kuma wani dan bayani kaWan suka yarda suka bamu kudin a madadinsa, kuma mun karbo ba tare da wata matsala ba Salamatu, Ma'aruf kuma yana nan a kwance duk da ance min ya fara samun sauki amma wannan ba damuwata bace, ko yanzu idan ina son ya kara komawa, umarni kawai zan bata, muna zaune anan zaki ji komai ya kara rikicewa."

Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.

"Ba kya tunanin idan ya tashi ya tuntubi mutanen zasu iya shaida masa abinda ya faru da kuma yanayinku? A tunanina ba kya Wanyen aiki Kilishi."

Itama ta girgiza kanta.

Ba tunanin kike ba Salamatu, tabbas bana danyen aiki, don wannan Win ma gasashshe ne. Wani saurayi muka samo daga Prison, wata na biyu Salamatu ina barar da kudi a prison din nan ina neman kafa, don kawai a ara min shi na rana guda yayi wannan aikin kuma da kyar muka samu.

Awwalu ne yayi masa I.D card din kamfanin sak a matsayin babban ma'aikaci, don haka muka tura shi a matsayin hakan ya karbo mana kudin da bayanin cewa shi maaikacin wajen an aiko shi ya karSi sakon ne bayan ya nuna musu kayan Ma'aruf harma da wayarsa don haka nan da nan suka yarda.

Suka bashi dukkan kudin mu kuma muka bashi rabonsa tare da na iyayen gidansa muka maida shi inda muka dauko shi. Shi yasa nace miki aikin gasashshe ne Salamatu tunda kin san duk naci da binciken Ma'aruf babu ta yadda zai kamo mutumin dake cikin Prison duk kuwa iya bincikensa."

Hajiya Salamatu ta kyalkyale da wata irin dariyar da bata shirya mata ba tana girgiza kai.

"Zama dake alheri ne Kilishi, na sha gaya miki yadda kike bude nin kwakwalwata akan abubuwa, yana bani saukin warware nawa matsalolin gabana na nima."

Kilishi ta gyada kanta.

"Abinda na gayawa Saratu kenan ai, kowacce mace tana da irin tata dabara da kuma mafitar matsalarta a cikin kanta, yanzu da ta saurare ni ba gashi nan daga ita har ´a´an ta mijin ya tafi dasu Egypt din ba, amaryar da ake takama da ita da farko wata daya tayi ya dawo da ita.

Kawai jahilci ne yasa mutanen farko ke bin wasu bokaye da suke maza ma don samun biyan bukatar fa bata dorewa. Kowa ta sani cewa tunda aka halicci duniyar nan har kawo yau, ™arya ne a samu aikin wani bokan da ya zama mai dorewa har abada.

Amma idan mace tayi amfani da dabara da kuma tunaninta wajen kwatarwa kanta ´anci ko a wajen waye, ina tabbatar miki wannan abin ba mai gogewa bane balle har ya lalace, akwai abubuwa da yawa da suke Wamfare da tare da halittar mu, kawai bama barin kanmu mu gansu ne.

Kwakwalwar mace kamar littafi take, dauke da tarin abubuwan da tana bude shafukan gaba tana kara fahimta, wadda bata bude ba kuma zata yi ta jallon bangon ne kawai ba tare da ta taba sanin meye a ciki ba.

Salamtu ta kara gyada kanta tana yarda da dukkan maganganun kamar yadda Kilishin ta dade tana ambata mata.

"Na taya ki murna kwarai na samun wannan burin da kika daWe kina lissafinsa a Wan kankanin lokaci Kilishi, kin tafi zuwa gaba kuma saura kiris ki kai ga cimma msnufarki gabadaya. Sai dai yanzu na san baza'a sake samun irin wannan aikin a kusa ba, za'a dauki tazara koda baza'ayi dadeear da nake tunanin ba. Don haka meye a gabanki yanzu?"

Tambayar ta yiwa Hajiya Kilishi dadi, me yasa ne take buWewa Salamatu cikinta dama? Me yasa take gaya mata dukkan tsarinta duk sanda ta tambaya? Ba saboda tana gaya mata daWaWan maganganunn dake wanke zuciyarta suna bata kwarin gwiwa a kodayaushe bane?

"Hamida ce target dina na gaba Salamatu.."

Ta faWa kai tsaye tana kallonta.

"... wannan yarinyar, wannan ´ar ta mai gaskiya, ina son Ma'aruf amma bana son duk wani abu da zai zana nasa, don hakan ba karamin na™asu zai jawo min a zuciyarsa ba.

Rukayya bata taba damunsa ba shi yasa nima bata taSa damuna ba har tayi yayinta ta tafi, amma wanna ´ar tata Salamatu, naga wani abu a cikin idanun Ma'aruf a ranar da yake ri™e da ita a asibiti, na ga wani abu da ban taba ganin irinsa tare da kowa idan ba ni ba Salamatu. Shi yasa tun awanvan ranan na rufe idanuna naso kawo karshenta, amma Allah yayi da sauran ruwanta a gaba shi yasa ban samu nasara ba, amma a yanzu ina jin cewa ko ta halin
™a™a zan iya canja kaddarar yarinyar nan  Salamatu. (Waiyazubillahi!)

Ta rufe bakinta daidai lokacin da kofar dakin ta bude, Samirah ce ta shigo jai tsaye hannunta rike da wata ™atuwar jaka kalar Pink mai kyau, dukkaninsu suka bita da kallon yayin da kafin Hajiya Kilishin tayi magana Surayya kuma ta biyo bayanta, hannunta dauke da ´ar yarinyar da a lokaci guda kamanninta suka doka wata irin fargaba zuciyar Hajiya Kilishi.

Hamida ce, ri™e a hannun Surayyan ta makalkale ta yayin da take zare manyan idanunta irin na maifinta sak! akan kowannensu.

"Mami yanzun nan direban gidansu ya kawo ta, wai cewa akayi akai ta wajen Ya Ma'aruf."

Murmushin da ya sabuce a bakin Hajiya Kilishi wani murmushi ne da ya taSo har acikin zuciyarta... Tana son mutane masu saukaka mata ayyuka, a rayuwa, Allah ma ya sani.

****

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un..."

Sune kalaman da suka fito daga bakin Ma'aruf a lokacin da yake zaune kan kujerar falon yana sauraran bayanin da Faruk ke masa a cikin wayar, kayan jikinsa dogon wando ne ba™i da kuma wata riga kslar ruwan toka mai haske.

"Wallahi sun nuna min evidence da komai cewa kai ka turo mutumin da ya karbi kudin, don har I.D Card dinka da sauran credit cards dinka ya nuna musu a matsayin shaida."

Ma'aruf ya cije lebbensa.

"Na kasa ganewa Faruk, na kasa gane wanda zai sace kayana a wannan lokacin kuma har ya san ina da appointment da mutanen a wannan wajen kuma a wannan time din."

"Saboda already sun san hakan ne, sun san kana da wannan appointment din shi yasa suka tare ka a wannan wajen kuma suka kwashe dukkan wayoyi da wallet dinka."

"Are you thinking this is all planned?" (Kana tunanin duk wannan abin haWawa akayi?)

"Ba tunani nake ba, ina ™o™arin tabbatarwa ne, don tun safe muke waya da Ishaq, ya gaya min mutumin da rigimar ta hada ku har yanzu baiyi filing case Win ba, tunda ka san da sun yi dole za'a neme shi, ka duba al'amarin nan ka gani hankali ba zai dauka ba Ma'aruf ace kayi masa wannan abin amma ko shi ko ´anuwansa basu dauki wani mataki ba."

Yayi shiru kafin yace.

"Amma har da nawa contribution Win Faruq, ta yaya kake tunanin zasu iya ýÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹ŒŽ‘’“”•–—˜™š›œžŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏÐÑÒÓÔÕÖרÙÚÛÜÝÞßàáâãäåæçèéêëìíîïðñòóôõö÷øùúûüýþÿsaka ni nayi abinda ban yi niyya ba, ina shan magani na cikin ™a'ida sannan ina kiyaye dukkan ™a'idojin da aka rubuta a wannan takardar. To ta yaya zasu iya controlling emotion dina?"

Faruk yayi shiru shima kafin ya amsa.

"Da wannan kuma B, amma zamu gano komai a hankali idan muka bincika. But there's no way da zan yarda cewa wannan al'amarin accident ne kawai."
Chapter 18 · 0% Book details