← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 87

Sashe 53

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mun same shi Ma'aruf, ga address dinsa nan, ka shirya mu tafi... ko waye wannan Awwalun yau dubunsa ta cika!"

***

_Su wa kuke tunanin sun kama Awwalu?_

_A wane lokaci kuke tunanin su Ma'aruf zasu isa gidansa?_

_Tare da mutanen nan?_

_Ko bayan sun tafi da Awwalun?_

_Ina Kilishi?_

_Kuna tunanin Hajiya Salamatu ta hakura da zancen dan ta?_

_Ta yaya Jawad zai gano mahaifiyarsa?_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
3/15/22, 15:57 - Ummi Tandama=ØÞ: °°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©ýÿAYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*18*

~~~~~~

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka, ina mika ta'aziyyata da kuma jaje ga dimbin al'ummar musulmi da ma jama'ar Kano game da tashin hankalin da muka fuskanta a cikin satin nan na kisan gilar da aka yiwa ´ar ™aramar yarinyar da bata da laifin komai a duniyar nan, ina rokan Allah ya bawa iyayenta ha™urin rashi, Allah ya ™ara kare mu da iyalanmu, Allah kuma ya kawo mana karshen dukkan tashin hankalin da muke ciki lafiya. Ameen.*

***

Motoci guda huWu zaka fara gani a ™ofar gidan kafin idanunka su lura da cewar kofar motar guda Waya a bude take hade da mukullinta a jiki.

Don a lokacin da suka tsaya, tunanin Ma'aruf da kuma duk wata nutsuwarsa tayi kaura daga cikin kansa, fatansa kawai shine su sami mutumin da suka zo nema a cikin gidan nan, Awwalu!

"Nan ma baya nan...!"

³an sanda na ™arshe da suka dawo daga bayan gidan suka fada suna shivowa cikin falon inda dukkaninsu ke tsaye, sun duba koina a gidan sun duba koina, kuma hasashen Ma'aruf na cewar babu mutum a cikin gidan tun sanda ya tako ™afarsa ciki shine ya tabbata.

Babu kowa, babu kowa a cikin gidan banda shatin tayoyin motar da suka tarar a jikin kasar waje ta compound Win gidan, shatin da ´an sandan suka tabbatar da cewar bai daWe ba, babu daWewa da fitar mota a gidan.

Bai san lokacin da yayi baya ya zauna kan wata kujera dake cikin falon ba yayin da hayaniyar ´an sanda da kuma sauran tanen da suka zo dasu ta tafi kan wata jaka da suka tsinta a cikin falon, wata jaka da babu komai sai tarin wadu CD's da kuma computer guda daya.

Yana jin abinda suke fada, yana jin suna fadin cewa kayan ba karamar kadara bace da zata iya kaisu ga abinda suka zo nema, amma shi ba wannan ne a ransa ba, ba hakan yake do ba, ba kuma hakan yayi fata ba. Burinsa yaga ko waye wannan Awwalun, burinsa yaga fuskarsa yaga WAYE SHI, ya ga waye wanda ya daWe yana cutar dasu a duniyar nan ya kuma san dalilinsa.

So yake ya tambaye shi me suka yi masa? Me suka yi masa shi da mahaifinsa da dauki aniyar tarwatsa su? Wane irin laifi duka yi ko kuma ta ta yaya suka cutar da rayuwarsa da yake bata lokacinsa yana kuma sadaukar da dukiyarsa da fasaharsa don ganin karshensu? Abinda yake so a wannan lokacin kenan, so yake ya ri™e wuyansa a cikin hannayensa ya tambaye shi me suka yi masa... So yake ya dake shi, ya mare shi, ya naushe shi har sai yaga ha™oransa suna biyo jini suna fitowa....

"Kusan duka Cd's Win are write-protected, sai mun je office zan iya aiki akansu."

Cewar wani a cikin ´an sandan nan yana ™o™arin danne-danne a cikin computer dake hannunsa bayan ya gwada CD guda Waya a ciki, kuma bayan hakan yana ji mutum biyu da suka buWe computer hannunsu suna faWin itama a ™ulle take da password.

Wayarsa tayi kara a lokacin, hannunsa ya zaro ta a hankali daga aljihunsa, Ishaq ne.

"B kana ina? Tun dazu nake kiran wayarka ta™i shiga, gani har nazo Airpot daukan Abdurrahim, ka manta ko?"

Sai kawai ya cusa hannusa gabaWaya cikin gashin kansa.

"Wallahi na manta Ishaq, ina nan ina wajen aikin nan ne, amma bari mu gani, may be kafin jirgin nasu ya sauka I'll be there."

Ishaq dake zaune a cikin motarsa a harabar filin airpot din ya gyada kansa.

"Kayi kokari Dan Allah Ma'aruf, don kafin in fito Baffa yayi fadan me yasa baka gida bayan ka sani."

Ya sake gyada kansa a lokacin da Faruk dake tsaye tare da wani Wan sanda ya matso daidai inda yake zaune.

"Zan zo yanzu insha Allah, bari mu kammala."

Kuma da haka wayar tasu ta kare, ya sauke ta san da Faruk din ke cewa.

"Kar ka damu Ma'aruf, zamu sami wani abu a cikin waWannan kayan insha Allah, kuma zasu saka security daga yanzu za'a saka ido akan gidan nan 24/7, we are close to finding them Insha Allah."

Abinda dukkaninsu basu sani ba shine, amsar da suke nema a yanzu tare da mabuWin da zai bude komai ya kuma kawo karshen komai Win yana dab da taka kasar Nigeria!

***

"Naira miliyan tara!"

Muryar mutumin ta furta a hankali yana kallon wanda ke gabansa, a zaune yake akan doguwar kujera da ta cika kusan rabi na dakin, don bayan ta mi™e ta zagayo ta bari Waya cikin wani shape mai kama da C, kalarta milk ce kamar yadda tattausan carpet Win da aka baje a Wakin yake, akwai labulaye da suke kalar brown, kalar da ta dace da fentin Wakin da kuma sauran kayan furnitures Win da kyawunsu ke ™ara haska haduwar Wakin.

Mutumin na zaune ne daga shi sai gajeren wando da kuma wata yaloluwar T-Shirt yayin da teburin gabansa ke cike da wasu kwalabe da kuma kule-™ullen da ba sai an tona ba kowanne mai hankali zai san cewa abubuwa ne da ya kamata a li™a musu ayar tambaya.

"Naira miliyan tara ba wasa bane..."

Mutumin ya sake faWa yana Wora kafafunsa duka biyu akan teburin dake gaban nasa wanda hakan yasa wasu abubuwa dake kan teburin suka faWi. Awwalu dake zaune daga can ™arshen Wakin hannuwansa da kafafunsa duka a Waure, idanunsa suka bi kayan da suka fadi sannan ya sake dawo dasu kan mutumin.

"Munyi yarjejeniya da kai Awwalu, ka san ni, na sanka kuma ka san ba'a a cin kuWina  a kwana lafiya..."

Ya faWi haka sannan ya Wago daga kishingiWar da yayi, a gefensa katinan bankin Awwalun ne wanda suka samu a cikin wallet Winsa, ya Webo su guda uku sannan ya watso su, suka taho tun daga inda yaken har zuwa kan fuskar Awwalun kafin su tarwatse a jikinsa.

"Babu komai a cikin waWannan accounts Win, mun duba gidanka ma babu ko sisi..."

Mutumin ya hade hannayensa biyu sannan yace.

"Bana so in taba ka Awwalu ka sani, ka san wannan ne dalilin da ya sa na daga maka kafa tsawon watanni, ka san wannan ne dalilin da yasa na dade da yi maka shiru kuma ka san shine dalilin da yasa ni da kai muke kallon juna a yanzu..."

Ya kai idanunsa kan agogon dake manne daga can saman dakin sannan yace.

"... Zuwa nan da ™arfe shida, zaka iya zama tarihi Awwalu, don zan gwammace in kashe ka da ace ni da kai muna cigaba da rayuwa a duniyar nan kuma babu kudina a tsakaninmu."

Ya kai karshe a lokacin da Awwalun ke kokarin gyara zamansa don duk abinda yake fada gaskiya ne ya sani, Šantaro abokin huldarsa ne da suka daWe suna harkar cinikayya tare, a yanzu kudin da yake faWa miliyan tara, kuWin wasu kayayyaki ne da ya karba a wajensa ya aikawa da wani kaninsa dake can garinsu don ya fara kasuwanci, kuma ba wai ya hana shi kudin saboda wani dalili bane ba, bai bayar bane saboda ya manta, a kwanaki biyun nan da al'amarinsa da na Kilishi ke cakudewa, kwakwalarsa ta manta da tarin abubuwan da bai san lissafinsu ba.

Lokacin da mutanen Šantaro suka shigo gidansa, yanayin shigar kayansu da yadda suka rufe fuskarsu, ya bashi tunanin cewa mutanen Kilishi ne don wannan ne kadai tunaninsa a yanzu, abinda yake gujewa kawai kenan, ya gansu ne da tunanin ire-iren mutanen daya taba hada ta dasu ne wanda suka kashe Jamal.

Sai a lokacin da ruwan da aka watsa fuskarsa ya farkar dashi daga suman da yayi, ya bude idanunsa akan Šantaro da kuna yaransa sannan ya fahimci cewa zaren kaddarar tasa da saura, bai kai karshe ba har yanzu, yana da lissafin wasu kwanaki kafin a zo gabar da sa'ar da ya dade yana talawa zata ™are, don ya riga ya sallama a yanzu, tunda har bai samu abinda zai bashi yardar Hajiya Salamatu ba shikenan duk wani shiri da kuma fatansa ya kare, don a tsarinsa yana so yayi amfani da Hajiya Salamatun ne su boye laifinsa wajen tonawa Kilishi asiri.

Amma tunda bashi da wani mataimaki a yanzu, to ya san babu ta yadda za'ayi yaje ya tunkari iyalan Bakori don tonawa Kilishi asiri ba tare da ya bankada nasa ba shima.

Don haka fatansa kawai shine ya bar garin Kano a yanzu, yayi nisa da arewa ma  gabaWaya, ya tafi inda ko yanuwansa baza su sani ba, idan yaso da ya sami lokaci sai ya zauna ya gyara wadannan CD's din da ya dade yana recording muryar Kilishi a ciki, ya cire duk inda ta ambaci sunansa da kuma muryarsa, idan yayi haka, sai ya turawa da Ma'aruf hakan yana daga inda yake, ya tonawa Kilishi asiri ba tare da kowa ya sanshi ba, idan yaso duk binciken da za'ayi idan basu gano shi ba, za'a karyatata ne a dora laifin akanta ita kadai.

Don haka a yanzu da Šantaro ya kama shi zaiyi amfani da wannan danar ne kawai ya kwana biyu a wajensa, zai bari su rike shi ne har zuwa lokacin da hankalin Kilishi zai karkata daga kansa don ya san Šantaro karya yake ba iya kashe shi zai yi ba, shi Wan kasuwa ne kawai mugu, amma muguntarsa ba ta tsallake wani geji.
Chapter 53 · 0% Book details