← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 87

Sashe 6

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zaki yi waya a kawo mana wata motar ne?"

Ya tambaya, ta girgiza kanta.

"Baka da zurfin tunani Awwalu, ta yaya hatsarina zai zo rana daya dana Jamal? Tsaftataccen aiki nake yi a kodayaushe ka sani, bana yin sajacin da zan bari ko da Wigon baki da zai kawo zargi a zuciyar wani na."

Awwalu ya gyaWa kansa yana cigaba da wani murmushin kafin yace.

"Na yarda dake wallahi Hajiya."

""Kaje ka siyo wata tayar, a daura sai mu tafi."

Kuma wadannan kalaman nata na lokacin sune tushe, shine sanadin faruwar wasu abubuwan da har a yau ba'a warware su ba, don Awwalu ya dauki tsawon lokaci kafin ya iya samo sabuwar taya da kuma mai daurata kasancewar safiya ce lokacin, don haka kafin su koma gida matafiyan nan sun tafi.

"Mami, Ya Ma'aruf ya shigo yace ya kira wayarki a kashe, yace idan kin dawo in gaya miki ya bi Ya Jamal zuwa Abujan, zaku yi waya idan kin dawo."

Kalaman da Salma ta faWa mata kenan bayan ta koma gida da misalin karfe goma saura na wannan safiyar.

Kuma a tarihin rayuwar Kilishi kaf! Idan zata misalta kalmar tashin hankali, zata kwatanta ta ne da wannan ranar, ranar da zuciyarta ta buga a kirjinta, kafafunta suka zube gar a ™asa yayin da idonta ya shiga hasko mata gawar Ma'aruf din da bata tsara a lissafinta ba tare da ta Jamal!

***

*Present Day.*

"Halima."

Alhaji Sulaiman dake zaune a cikin Wakinsa ya kira sunan matarsa dake shirin sa kai ta fita bayan ta ajiye masa flask din ruwan zafin da ta dafa a dawowarsu yanzu da safen.

Tsintsiya ce a hannunta wadda ta dauka don zuwa  ta kara share falo inda aka kwantar da Aminun, taso ace tun jiya su Maryam sun zo sunyi sharar kafin su dawo, amma haka kurum ta kasa kiran iyalan gidan Kawu Malam inda su Maryam suka tafi da wannan umarnin, tana da kawaici akan ´a´an ta kowa ya sani, abinda mutane basu sani ba shine tana ajiye wannan kawaicin a gefe idan har aka zo gabar da za'a cutar mata dasu.

A kofar dakin ta saki tsintsinyar sannan ta juyo ta dawo ciki, don daga yanayin amon muryar Baban ta san magana ce mai muhimmanci zasu yi.

Ta sami waje gefensa ta zauna yayin da idanunta farare irin na Amina sak ke kallonsa, kallo na saurare da kuma jiran umarni.

"Jiya na hango ki kina waya da ´arki."

Ta gyada kanta sau Waya bayan ta gane cewa Amina yake nufi.

"Akwai wata matsala ne da take fuskanta a gidan?"

Mamakin tambayar tasa ya kamata, sai kawai ta sunkiyar da kanta kasa a hankali, a shekarun zamanta dashi kaf! ya sani ko da sau Waya bata taba zuwa ta bashi labarin wata matsala ba walau ta danginta ko kuma ta wani da ya shafe ta ba kuma shima baya taba tambayar abu makamancin hakan ba sai idan har zancen ne yazo a dole su fade shi, don haka abinda ba'ayi a baya ba, ba za'a fara shi yanzu ba.

Amina yarsa ce, ta san yana da hakki akanta amma a tunaninta ya riga ya gama taka rawarsa akanta, yayi ruwa yayi tsaki wajen kaita rayuwar da babu ta hanyar da bata kalubalance shi ba. Shi da kansa ya fada cewa ba zai iya tuna ranar da tayi masa musu akan wani abu ba, amma bai ko duba wannan kawaicin nata na tsawon shekaru ba, da yake shi namiji ne ya rufe idonsa ya juya mata baya, ya dora yar tasa a wani mizani da dole nasa umarnin zata dauka.

A yanzu anyi hakan, komai ya wuce ba tare dacta nuna fushinta ba, kuma gashi sun fara fuskantar kalubalen da ta guje musu shi, to don me yasa zai tambaye ta kuma?

Ta fahimci har yau Sulaiman bai gama buWe halayenta ba, don da ya san wacece Halima da bai Sata bakinsa ma wajen tambaya ba, bata gori, bata cewa 'dama na fada...' zata yi iya kokarinta ne a farko don ganin ta kawar da matsala daga karasowa gare ta, idan kuma ta kasa, sai ta fara shirin tunkararta ta hanyar da zata iya kawar da ita, wannan shine babban abinda ke ri™e da zaman lafiyar gidanta dama zamanta tare dashi. Shi kansa idan zai tuna yana da zafi da kuma zuciya a lokacin kuruciyarsa har zuwa aurensu, amma da wannan halayen nata ta canja shi a lokacin da bai ma sani ba.

Don haka sai ta gyara zamanta kawai a hankali sannan ta girgiza kai.

"Babu wani abu, wata yar matsala ce kawai tamu ta mata."

Ya kalle ta tsawon wasu mintuna kafin ya sake kiran sunanta.

"Ina fata a yanzu kin daina ganin laifina Halima, don kowa shaida ne daga ganin yarinyar nan an san tana cikin nutsuwa."

Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Amma, mazan kenan! bata jin har abada za'a zo lokacin da kwakwalwar kowanne namiji zata bude game da al'amarin mata, suna ikirarin sun san komai a kullum, amma tarin abubuwan da ake lullube su a ciki suna da yawa, wanda hakan na Waya daga cikin abubuwan dake juya duniya, don da zasu san kowacce kissa da dabara irin ta matan to da zaman auren ma zai gagari kowa ce ™abila a duniyar nan.

Tun a lokacin da aka jawo kayan kefen Aminan kallo Waya tayi wa akwatunan da aka zuba kayan kwalliya zuciyarta ta Warsa mata wani abu da sai a yanzu take ganewa. Kilishi ta narka ma™udan kuWaWe na gaske wajen siyan tsadaddun kayan gyaran jikin da zasu karbi fatar Amina, ta yadda a waje kowa zai sanya ta cikin layin nutsuwa da kwanciyar hankali da kallo daya, yadda komai zurfin da zuciyarta zata yi babu mai iya gano hakan don za'a shagala da kallon canjawar fatarta maimakon damuwarta, gashi kuwa hakan ya fara aiki har akan mahaifinta da ya kawo ta duniyar nan, wai sau nawa ne zata fada? Kilishi mugun ice ce da gaske!

Sai kawai tayi wani murmushi a hankali sannan ta gyada kanta tace.

"Haka ne."

Shima ya gyada nasa kan.

"Sai dai mu bisu da addu'ar dorewar zaman lafiya.

"Tabbas kuwa."

Amman ta sake fada tana jin wani abu kamar raha na ratsa zuciyarta, tana ™ara yarda cewa mata duniya ne, Allah ya basu damar juya namiji duk girma da tsufansa a tafin hannunsu, kawai da yawa ne basa amfanin da danarsu.

"Mun yi waya da Kawu Mallam yanzu, yace za'a rako su Maryam din anjima, tunda kike ta kallo na a hanya na san abinda kike so kice in tambayo miki kenan."

Ta girgiza kanta.

"Ni ban aike ka ba, idan zasu kara kwana ma ba zan damu ba."

Kice zaki iya bacci babu Hafsatu a gidan nan?" Ya tambaya

"Kafin in same ta fa?"

"Kina da Amina."

Sai kawai ta mike tana dariya, ta Wauki tsintsiyarta ta fita. Alhaji Sulaiman ya bita da kallo yana jin zuciyarta wani iri, kamar bai gama yarda da kalamanta ba, amma kuma babu yadda zaiyi, matarsa daban ce a cikin mata ya sani, halayenta wani abu ne da ba zai taba iya kwatanta su ba, juma abinda bai sani ba shi e matarsa iri daya ce da kowacce mace, natan ne kawai basa gane cewar nutsuwar zuciyarsu a kowanne fanni na rayuwarsu taba zaune cikin ™wa™walwar su.

Awanni biyu bayan hakan ya baro cikin gidan, Ya fito ya nufi titi don tafiya ga sana'arsa.

Daidai lokacin da Awwalu dake zaune cikin motarsa a can gefen layin ya tada motar shima yabi bayansa.

****

*A wannan safiyar.*

Ma'aruf ya tako cikin gidan a hankali, hannunsa daya na sanye cikin wandon shaddar dake jikinsa kalar ruwan toka yayin da Wayan ke rike da wayar dake kare a kunnensa, kayan jikinsa kalar ruwan ™asa ne wanda ta haska cikin safiyar, ™afafunsa na tahowa cikin falon a hankali yayin da yake saurarar bayanin da Faruk ke yi masa a cikin wayar.

"Mutumin nan sh*ge ne B, ˜arfe biyun dare ya kira ni wai shi daga sannan yake amsa waya, wallahi har na zata yan fashi ne suka shigo mana."

Yayi murmushi kaWan.

"Baka da hankali Faruk dan fashin ne zai fara kiranka a waya ya gaya maka cewa gashi nan zai shigo tukunna? ka gaya min yaya kuka yi dashi kawai?"

"Yes, ya karba. But sai mun bashi wani abu tukunna, kuma ka san shi cash yake baukata, kuma gayen yana da matsala wallahi don yace dole yau yake bukatar kuWin, shi yasa tun farko ni raina bai kwanta da mu saka shi cikin al'amarin nan ba."

Ma'aruf ya girgiza kansa.

"Kar ka damu, zanje na ciro kuWi anjima sai ya gaya mana inda zamu same shi."

"Shikenan, I will talk to him zuwa yamman, zan gaya maka."

Da haka wayar tasu ta kare, daidai lokacin da Ma'aruf ya shiga hanyar koridon zuwa kitchen, inda ™arar motsin kwanuka ke tabbatar masa da cewar tana ciki.

Da gaske yake abinda ya faWa mata jiya cewa tana ™ara ™awata duniyarsa, don duk da har yanzu bata gama sakin jikinta dashi ba, ya sani cewa shigowarta cikin rayuwarsa ya fara samun wata nutsuwa da shi kansa baya gane mata, abinda kawai ya sani shine abinda yaji tun daga ranar da ya fara ganinta shi yake jan ragamar sa akanta.

Tsakanin jiya da yau kaWai yana jin sunyi sabon dashi da Ru™ayya basu sami hakan a Wan kankanin lokaci ba, ya nuna mata cewar da gaske yake wajen gyara alakarta dashi, kuma hakan bai bashi wuya ba don da gaske ne yarinyar bata da matsala, tana da hankalin da bai san da me zai kwatanta shi ba, tana da hankalin da ya fahimta sosai a cikin dukkan amsoshin da ta bashi don sunyi hira sosai a jiya, yayi mata tarin tambayoyin daya fahimci kusan rayuwarta gabadaya a dun™ule.
Chapter 6 · 0% Book details