← Book details Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 87

Sashe 64

Farar Wuta Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gashi nan ya iso Nasir, yanzu zai shigo."

Ta fada, kuma lokacin da Maigadin ya dauka bayan bugu daya, taji ne kamar tayi ihu wajen saka masa albarka.

"Akwai bako a waje ka shigo dashi yanzun nan."

"To Hajiya."

Ya amsa da sauri shima jin yansyin muryarta, Hajiya Salamatu ta ajiye wayar sannan ta tafi da sauri wajen tagar dakin dake fuskantar saitin bakin gate ta buWe labulen, tana ji Nasir na cewa kar ta fita ta bari ya karaso tukunna.

Akan idonta maigadin ya fito daga dakinsa, ya bude kifar gate din ya fita sannan bayan sajanni uku kofar ta sake budewa suka shigo tare, tana hango su suna tahowa zuwa ciki kuma tun daga can zuciyarta ta shaida mata cewa ba wani babban mutum bane kamar yadda ta zata,matashi ne yaro daga shigar dake jikinsa ta wando da riga mai hula da kuma ™irarsa ma, suna kara matsowa tana kara ganin tsawonsa kamar na daWuwa, tsawon da a lokaci guda tasirinsa a idanunta ya zarce cikin zuciyarta ya sami mazauni.

Nasir ya riga ta tafiya ga kofar falon a lokacin da suka karaso, don bayan ta saki labulen ta juya da sauri ta tadda shi hana kokarin bude kofar tin kafin ma su buga.

"Yallabai barka dai, barka... Dama Hajiya ce tace a shigo dashi, bakonta ne."

Maigadin ya fada a lokacin da kofar ta bude a gabansu, tana tsaye daga bayan Nasir Win sanda Maigadin ke fadar hakan sai dai ta tabbata daga ita har Nadir din bashi suke kallo ba, idonsu na kan matashin ne da ya saka hannu ya ture hular da ya rufe kansa, fuskarsa ta fito tar a cikin hasken fitilar wajen.

Ibrahim.

Shine mutumin da Hajiya Salamatu ta gani tsaye a gabanta.

Ibrahim Shanawa.

Mijinta na farko a duniya, mijin da ta fara zaman aure tare dashi, shine sak a tsaye! Cikin shekaru da kuma ™uruciyar da ta aure shi, wannan lokacin da kyawunsa da kuma dukiyarsa suka rufe mata idanu daga ganin kowa a duniyar saSanin shi... Amma ta yaya zai cigaba da kasancewa a haka bayan ita ta tsufa ta manyanta?

Wannan tunanin shine ya daki tsakiyar kanta a lokaci guda yana son tabbatar mata da cewar abinda take gani ba daidai bane, sai dai muryar Nasir da ta fito a lokaci guda ta katse wannan tunanin daga tabbatuwa, ta gaya mata cewa ba ita kaWai take ganin abinda idanunta ke nuna mata ba...

"Innalilahi wa'inna ilaihir raji'un...!"

***

*Bakori Enterprises*
*Administrative Office.*

_Zan iya fara restarting wani amma still shima ba lallai sautin ya buWe ba sai da Frea-dat Win._

Idon Ma'aruf ya karanta abinda Abdurrahim ya rubuta a fuskar wata Tablet da koyaushe tana hannunsa da ita yake nagana ta hanuyar rubuta dukkan abinda zai ce da dan yatsansa, ya karanta yaje har karshe sannan ya gyada kansa da sauri.

"Kar ka damu, just carry on yanzu zai ™araso insha Allah."

Ya faWi hakan sannan ya juya gefe, daga can barndar katon ofishin da suke ciki inda Faruk ke tsaye yana faman magana a cikin waya, maganar da bata komai bace illa bayani da kuma kwatance wa wani mai online shop guda Waya da suka samu da suke da Fre-dat Win da Abdurrahim yake nema, wani abu da su basu taSa saninsa ba don haka a yanzu Faruk Win na waya dasu ne don su san yadda  za'ayi a kawo.

A safiyar yau ´an sandan da suke aiki tare dasu suka kira Faruq da cewar basa tunanin akwai wani abu a cikin wannan tarin jakar cd's din da suka samu a gidan Awwalu, suka gaya masa cewar sun yi iya bincikensu amma basu iya ganin komai a cikin kowanne CD ba, don haka ba tare da Sata lokaci ba ya aika a aka dauko masa jakar don shi ya riga ya yarda cewa ba zai taSa yiwuwa ace an tara Cd's fal a cikin jaka guda ba tare da wani amfani ba, don haka suka bar wa yan sandan sauran aikin na nemo mai motar da ya Wauki Awwalun kamar yadda mutumin nan da suka samu a unguwar ya shaida musu cewa ya gane lambar motar.

Faruk yasa an dawo da Cd's Win office ne da tunanin idan komai ya natsa zasu nemo wajen da zasu iya kaiwa a buWe musu ko a wacce kasa ne, sai gashi tun ba'a je ko'ina ba, tun ranar da akayi hakan bata kai ga faduwa ba, tun shi kansa bai kai ga zuwa ma yaji me ake ciki ba, Allah ya kawo Abdurrahim cikin wajen, kuma kamar da wasa Faruk yace hannunsa ya kai kan jakar ya buWe ta yana zaro guda Waya a lokacin da suke hira game da kamfanin da kuma dawowarsa.

Yace kallo Waya kawai yayi wa Cdn ya rubuta masa sunansa da kuma abin da ake yi dashi, sannan ya tambaye shi me suke boyewa a cikinsa... Kuma dogon bayanin da yayi masa shi ya kaisu ga  kokarin da Abdurrahim din ya fara yi da Computersa wajen kokarin bude cikinsa.

Kuma kafin karasowar Ma'aruf, kafin zuwansa wajen yayi nasarar bude guda daya da ya fara dauka har sun ji muryar dake ciki, sai dai sakanni goma sha biyar ne kawai a cikinsa inda shiru ya cike fiye da sakanni goma sha biyu, sai a cikin sakanni ukun karshe ne kawai suka ji wata murya daga can nesa tana magana da wasu kalmomi da ba wanda ya iya fahimta a cikinsu balle ma su tantance sautin.

A yanzu yana kokarin buWe na biyun ne wanda a cikinsa har ya gano cewar anyi amfani da kusan minti talatin na sauti, don haka a yanzu yana kokarin buWe kowannensu ne yadda da ya samu Free-dat Win da suke nema, za'a karasa bude su nan take.

"A Kaduna suke ashe mutanen nan, flight nake dubawa daga Kadunan zuwa nan, sun ce zasu aiko da wani yaron su ya kawo..."

"Ba lallai ne a samu flight da wuri kafin yamma ba, mu duba wani wajen kawai..."

Ma'aruf ya fara fada amma Abdurrahim yayi saurin katse shi ta hanyar riko hannunsa sannan ya rubuta masa a cikin Tab dinsa cewar.

_"Nasu original ne, ba'a ko'ina ake samun abin nan ba, wasu zasu iya faking Winsa."_

Sai kawai Ma'aruf ya zura hannauensa gabaWaya cikin gashin kansa sannan ya gyada kai kafin yace da Faruq.

"Shikenan kayi musu booking Flight din zamu jira..."

Ya fadi hakan wani abu na wucewa ta makogwaronsa da vai san meye ba,kuma a cikin wannan ofgice din suka shafe awanni suna cigaba da aikin tare da Abdurrahim din dake iya bakin kokarinsa wajen ganin yayi decrypting kowanne CD, har sai da ya zama kusan duka aikin tare suka yi shi su uku, wasu awanni da a cikinsu Ma'aruf ya kara fahimtar tarin abubuwa da yawa game da Abdurrahim din wanda ko a baya idan kowannensu yazo gida hutu bai sani ba kasancewar basu cika zama waje guda ba, a kullum shi yana tare da Hajiya Kilishi ne yayin da shi kuma Abdurrahim din ba zuwa nan yake ba.

Kuma a cikin awannin nan Ma'aruf ya kira wayar Baffa da kuma Ishaq wanda a yanzu su uku ne har da Baba Usman a wajen Hajiya Kilishi fiye da ™irgensa, hatta mutanen gida sunyi waya dasu yana shaida musu halin da ake ciki gane da Mamin kasancewar bayan zuwan wani likita an sake shiga da ita wata tiyatar tunda sunce ta farka amma still bata iya bude idanunta.

Sau Waya suka sake magana da Amina, bayan ta aiko musu da abincin da yaga banda tuwonsa har kuma da karin wasu girke-girken guda biyu duk da yace mata jar tayi, sai dai sunyi amfani mutuka don dasu Faruk da Abdurrahim suka cika cikinsu tunda ba inda suka fita, daga sallar la'asar har ta magriba anan cikin office din suka yi jam'insu, bayan haka bata kara kiransa ba, bata ™ara cewa komai ba tayi masa uzuri kamar yadda ta fahimci yana bu™ata wanda shi kaWai ya san daWin hakan da yaji a zuciyarsa.

Kuma bayan Sallar magaribar ne sa™on ya iso, wani matashi dashi aka aiko da Free-dat ya iso har cikin office din bayan Faruk ya tura anje an dauko shi daga airpot din.

Ya iso yana ta godiya da kuma murna kamar ya san su dama, a cikin drawer office fin Fatuk din Ma'aruf ya ™irgo dubu arba'in yace ya sake booking wani jirgin ya koma suma sun gode. Kuma bayan godiya har sai da yayi abinda yasa dukkaninsu yin murmushi kuwa duk da irin zagayen halin da suke ciki.

Bayan fitarsa ne Abdurrahim ya gama installing Free-dat Win nan a cikin labtop dinsa sannan ya shiga saite-saite da kuma taSe-taSe cikin kokarin bude CD na farko da suka saka a ciki.

Karfe takwas da rabi na dare a sannan, kuma a wannan lokacin tabbas ne da za'a auna jinin kowannensu zai yi sama fiye da zatonsu, idanunsu gabadaya yana kan labtop din yayin da koren layin ke tafiya a hankali zuwa inda zai kai karshe kafin sautin ciki ya buWe.

Idan ka Wauko hoton office din daga sama sai ka kalla sosai sannan zaka iya gane inda suke ma, don a hargitse yake gabadaya da tarin takardu da kuma wayoyin abubuwan da aka jojjona a cikin computer Abdurrahim, sannan ga kwanuka da flask din abincin da suka ci kowanne ya kalli hanyar garinsu.

Wannan koren layin na kan lamba ta 75 lokacin da wayar Ma'aruf tayi kara a aljihunsa, ya zaro ta hannunsa na wani abu kamar rawa ya kalli sunan da ya fito... Ishaq ne.

"Hello... Ya akayi?"

Bai ma san hakan ya faWa ba lokacin da ya kara ta a kunnensa.

Ishaq ya shafo nasa gashin daga can cikin asibitin da yake tsaye, idonsa ya kai kan Baffa da kuma Baba Usman dake kokarin shiga office din wani likita da yasa akayi kiransu kafin yace.

"An fito daga aikin Ma'aruf...."

"Alhmdlilah...."

Muryarsa ta faWa da karfin  da yasa daga Faruq har Abdurrahim din juyowa su kalle shi.

Ishaq ya girgiza kansa daga can kafin yace.

"Mami ta rasa idanunta B, bata gani...."
Chapter 64 · 0% Book details